Showing 117001 words to 120000 words out of 142497 words
Chapter 40 - NI DA YAYA SADAM Complete Document by Binta Umar Abbale.txt
wa'ina ilaihi raji'un!.
*****
Kwanansu Uku a *Dabi* kulawa da kauna da so babu irin wanda su Baba basa bawa Harira da 'yarta Sadam! kam kullum yana d'aki abun duniya ya dameshi adduarsa a kullum shine Allah ya cire masa son Sayyada dake nema ya kaishi barzahu Hakika tunda Sayyada ta zama matar dan uwansa to ta haramta a gareshi...
Yau Asabar yau ne suka shirya zuwa garin Kaduna domin su san abunda ke faruwa tunda Sadam din ya'ki amincewa ko da a waya ne a shaidawa iyayensa cewar yana raye bai mutu ba.......Dukaninsu suka d'unguma Garin kaduna garin gwamna..............
NI DA YAYA SADAM
*BINTA UMAR ABBALE*
49
Al'amarin yayi mutukar girgixa Abbah da Mammah ganin d'an nasu cikin koshin lafiya harda albarkar haihuwa ashe gaskiyar Sayyada ta fito
inda take fadin"Sadam na raye bai mutu ba Mammah sai da ta zubar da hawaye ganin Asalamiya baby Sadam kenan yarinya kamarsu daya da ita ta rungume 'yar tana share hawaye ashe kaddarar haihuwar wannan 'yar shine ya ritsa da yaronta.
Alhaji Auwal kuwa sai ya dinga jin kunyar hada ido da d'an nasa yasan samu labarin abunda yake da akwai to hakikanin gaskiya shi ba laifinsa bane a wancan lokacin tursasawar su Baba Ladi ce amma shi da don tashi ne ba zai had'a auran Sule da Sayyada ba.
Sun jima suna jajanta al'amarin kafin Alhaji Auwal din ya shiga sanar dashi dauki ba dad'in da suka dingayi gurun nemansa nan ya shaida masa irin tsautsayin da ya ritsa da abokinsa Habu wanda a halin da ake ciki yanzu ma baya ji sosai sai anyi magana da kyau duk ta dalilin dukan Captain Saleh yayi masa ya sanar masa da rashin lafiyar General AbdulSalam bayan abunda ya sameshi ya fada masa cewar yanzu haka yana can kwance a wani asibiti dake india.
Sadam! ya tausaya mutanan nan biyu wato General AbduSalam da babban abokinsa Habu tabbas dole su shiga rudani ta dalilin rashinsa tunda dukaninsu zaman Allah da annabi suke kuma suna kaunar junansu abunda Captain Saleh sukayi kuwa zasuyi abunda yafi haka tunda dama basa tsoron Allah.
Tunda suka shigo gidab gabanta ke wata irin faduwa Sulaiman yayi parking din motar da sauri ya fito ya bude mata murfin motar ta fito itafa wannan abunda Sule ke mata sam bata so kawai dai don babu yanda zatayi ne ta riga ra iya motar amma kullum ya dorawa kansa nauyin kaita makaranta ya dawo da ita.
Jakarta ma na hannunsa sai wani rawar jiki yake mata ita dai kallonsa kawai takeyi haka suka shiga cikin gidan........Kusan faduwa tayi ganinsa zaune kan kujera suna magana da Abbah.
Shi kuwa Sule hankalinsa baya cikin palon yana kanta sai magana yake mata.
Ganin sauyarwa fuskarta tana kallon guri guda sai ya mayar da hankalinsa gurin da take kallo.....Ji yayi kamar ya ruga da gudu saboda tsorata wanda duk wanda ke cikin palon sai da ya fuskancin rud'ewarsa....Kafin kice kwabo gumi! ya ji'ke masa jiki shaddar jikinsa ta jike jagab! Hannu ya mika yana nuna Sadam! bakinsa na rawa ya kasacewa komai saboda tsabar rudewa
Baba Ladi tace"Ku 'karaso mana kun tsaya bakin kofa ku karaso ciki yau dai Allah ya bayyana mana Sadam gashi nan a gabanmu shi da iyalinsa.
A sanyaye Sayyada taje ta zauna kan kujera sam! ta kasa d'aga ido ta kalleshi saboda nadama da tausayin kanta.
Shi kuwa Sule tsaye yayi bakin kofa sai magana ake masa ya kasa motsi shawarwari yake da zuciyarsa ko kawai ya gudu ne! Babi Ladi tace"Sule meye abun razana da shiga furgici! ka 'karaso ciki nasan abunda kakewa Insha Allahu babu matsala Sadam! ya amince maka."
Jiki babu laka ya karaso palon ya zauna sam yaki yarda su hada ido da Sadam din kamar wani munafiki sai sunkuyar da kai kasa yake kuma har yanzu gumi bai daina yanko masa ba.
Harira kallo Sule take tana so ta tuna inda ta san fuskar tabbas kamar ta ta'ba ganinsa tayi ta nazari da tunani amma ta kasa tunowa dole ta hakura da takuwa zuciyarta.
Sosai suka fuskanci furgici gami da tashin hankali a tare da Sule sai suka shiga mamaki mutuka har shi Sadam din rud'un da Sulaiman din ya shiga ya bashi mamaki mutuka......A nutse yace."Ya Sulaiman ka kwantar da hankalinka na fahimci ka shiga damuwa da gani na kar ka damu da komai Sayyada matarka ce har abadah ni na bar maka na tabbar maka da cewa dama can ban d'ora mata iddah ba nasan zaka fi kowa sannin haka saboda haka ka daina damuwa dan Allah kai dan uwana ne na jini wata mace bata isa ta shiga tsakanina da kai ba."
Sayyada da kanta ke sunkuye ta dago da sauri tana kallonsa sai hawaye shaaaaa! ya wanke mata fuska cikin wata irin tsana gami da nuna ke baki isa ki shiga tsakanina da d'an uwana ba ya kalleta ya watsar ya cigaba da magana da Sule wanda yayi zukud'um a zaune sai fifita yake da hularsa.
Wannan hukuncin da Sadam ya yanke yayi yawa iyayensa dadi mutuka sai suka shiga shi masa albarka da fatan gamawa da duniya lafiya.....A wannan lokacin Alhaji Auwal ya kira line General AbduSallam ya sanar masa bayyanuwar Sadam din cikin koshin lafiya yayi masa takaitaccen bayanin yanda al'amarin ya faru ya sanar masa da cewa Sadam gashi harda albarkar haihuwa......General Ya dinga godewa Allah yana ji tamkar yayi tsintsuwa ya ganshi a nejeria Sadam ya kar'bi wayar daga hannun Mahaifin nasa suka shiga gaisawa dashi Yana 'kara tisa masa abubuwan da suka gabata General yace."Ka kwantar da hankali insha Allahu idan na dawo komai zai normal domin ina da labarin abunda ke faruwa a bracck din tare da goyon bayan General Abbah Jaddah wanda ke daure musu gindi to insha Allahu daga zarar na dawo shima zai kwashi kashinsa a hannu sannan ina neman alfarma ka shirya ranar monday ka koma bakin aiki nasan ka da kokari ka fara aikinka kafin Allah yayi min dawowa."
Sadam! Yace."Yallabai bana jin zan cigaba da aikin soja gaskiyar magana kenan ada nayi alkawarin nida aikin soja sai mutuwa amma saboda wani dalili ya sanya na janye kudirina.
General Yace."Ashe ba da namiji nake magana ba Haba Sadam kar ka bani kunya mana duk ina jarumtarka take!!! ashe kana so su Saleh suyi maka dariya kenan ai kaje ka nuna musu kanan a raye kuma ka dawo a cigaba da fafatawa da kai shine magana ba kace ka janye kudirinka ka sake daura d'amara da zage damtse kan aikinka."
Sadam! yaji wata 'karfin gwiwa gami da jarumta sun kamashi a lokaci guda ya 'kame!! tamkar yana gaban general din yace."Yes sir yanda kace hakan za'ayi na dawo fagen daga bakin rai bakin fama insha Allahu."
Daga can 'bangaran general din shima ya 'kamewa Sadam! din yana fad'in"Yes sir Allah ya shige mana gaba." Sadam ya kashe wayar ya mikawa mahaifin nasa wayar yana sake jin wata karfin gwiwa na kamashi.
To su Baba Ladi dai basu hukuncin da Sadam din ya yanke ba sunso kawai ya ajiye aikin ya samu wata sana'ar ta fi masa to da yake dai rarrashinsa suke babu wanda yace masa komai kan hukuncin da ya yanke sai ma fatan alkairi da suke masa yana amsawa da "Ameen" Mikewa yayi yace zai shiga sashensa ya huta sai anjima zai fito.
Mammah tace"To idan an gama abincin matarka zata kawo maka ya amsa ya sa kai ya fice daga palon ko sake bi takan Sule da Sayyada baiyi ba.
Sayyada kamar kasa zama tayi a palon cikin sanyin jiki ta mike dakin Mammah ta nufa ta zube kan bed dinta hawaye sai ambaliya yake a kumatunta ashe da gaske Sadam zai iya hakura da ita innalilhi wa'ina ilahi raji'un! Ita me zatayi da wani Sule bashi take so ba Sadam take so me yasa zai mata haka ashe dama karya yake da yake fadin idan yazo sai yayi sharia da iyayensa da wanda ya aureta ashe dama ba gaskiya bace yaudara ce.....Kuka take sosai da sosai duk ta rasa wani mataki zata dauka.
Wayarta ta dauka ta yanke shawarar fada masa cewa har yanzu a matsayin matarsa take tunda zargin da yake bai tabbata ba kamar yanda ya tafi ya barta da budurcinta haka ya dawo ya tarar dashi domin Sule bai santa a matsayin mace ba kamar yanda yake zargi.
Har ta fara ringing sai kuma ta sanja shawara tayi saurin kashe wayar ta kwanta lamo tana tunane tunane.
Sadam na fitowa daga wanka yaga misscal kuma daga Sayyada yayi mamaki sai ya basar kawai ya lalubi kayansa dake cikin dakin komai a kintse kamar yana rayuwa a ciki ya sami jallabiya ya sanya ya kwanta kan bed hade da kurawa cilling ido yana nazari.
Akwai alamu rashin gaskiya a tare da Sulaiman tun lokacin da ya shigo ya fuskanci haka daga gareshi tsabar kwarewa kan aikinsa ya sanya tafarar daya yake gane mutum mara gaskiya amma babu komai koma meye Allah zai bayyana shi.
Su Baba Ladi sun lalace gurin wasa da Asalamiya Sule ya sulale ya fice daga gidan ba tare da ya sanarwa da kowa ba.
Kai tsaye bracck din su Sadam ya nufa yana isa yace yana son yayi magana da Captain Saleh aikuwa duk suna ciki suna iskanci ga aiki sunki futa sai shirme suke da shaye shaye aka sanar dashi yana da bako.
Captain Saleh na ganin Sule ya shaida shi suka gaisa Sule yace magana ce nake tafe da ita kuma maganar sirri ce a tsakanina da kai.
Captain Saleh yace"Aiki ya tashi kenan."? Sule yace"Kwarai kuwa....Kasan da cewar abokin aikinka Sadam Auwalu ya dawo gida ko."
Captain Saleh ya firgita yana kallon Sule din yace"Kai wace irin magana ce wannan kake ka ta'ba ganin wanda ya mutu ya dawo."
Sulaiman yayi wani murmushi mai ciwo yace"Wallahi tallahi Sadam ya dawo gida harda iyali tabbata inda yayi rayuwa cikin kwanciyar hankali yake wato kunanan kuna ganin kun kashe maciji ashe baku datse masa kai ba to ka shirya mutuwa a kurkusa domin dai Sadam! yayi rantsuwar dukaninku sai ya ragargazaku."
Saleh yaji wata iriyar gudawa na neman zubo masa babu shakka Sadam jarumi ne Allah ne ya bashi nasara akansa a wancan lokacin.....Tabbas mutukar ya sake Sadam ya shigo bracck din nan to babu shakka kashinsu ya bushe mussaman shi dole ne ya dauki matakin kare kansa tun kafin dare yayi masa.
Yace"Gaskiya nagode kwarai da gaske zan dauki mataki kafin yazo ya cimmani anan gurun."
Sallama sukayi kana Sule ya bar barikin Shi kuma Saleh ya koma cikin 'yan uwansa yana isa ya tarar dasu suna ihu!!! Captain Habu na shaida musu labarin bayyanuwar Sadam din sai murna suke da sowa 'yan adawa kuwa sai bakin cikin suke Mussaman Captain Saleh.
Nan suka mike kusan su ashirin da wani abu suka shisshiga mota da niyyar zuwa famiy house dinsu Sadam din domin yin tozali dashi.....Captain Saleh da abokanansa su uku aka bari a gurin suna shirya mana'kisar da zasu shiryawa Sadam din.
****
"Haba Sayyada wannan kukan da kikeyi sam! bashi da amfani don Allah kiyi hakuri ki fawalawa Allah lamarinki komai kikaga ya samu bawa to da sanin Allah....Dama can Allah baiyi nufin zakuyi wani dogon zama da Sadam ba saboda haka sai kiyi hakuri ki cigaba da zama tare da mijinki farin ciki Sule na sonki to kema kiyi hakuri ki zauna dashi tunda shi Sadam din yace ya hakura ya bar masa."
"Haba Baba wannan wace irin magana kike min? kullum idan nace kuncuceni sai kuce ba hakaba wallahi har na mutu ba zan ta'ba mantawa da abunda kukayi min ba ni me zanci da Sule sanin kanku ne biyayya ce ta sanya na amince da bukatarku amma ni kwata kwata bana son Ya Sule Ya Sadam nake so shine farin ciki idan kun amince in cigaba da zama da Ya Sule to na tabbatar muku da cewar rayuwata tazo 'karshe dan zan kashe kaina ne na huta."
Baba Ladi ta tsorata da furucin Sayyada jikinta a sanyaye tace"To yanzu ya kike so ayi Sayyada kin san dai har abadah kin haramta a gurin Sadam a halin yanzu kuma ya shaida mana cewar kafin rabuwarku bai d'ora miki iddah ba to kin gani yanzu shekara daya da rabi da auranki da Sule na tabbata ya sanki a Matsayin mace ta aure dan haka kin riga kin haramta a gurin Sadam."!
''Baba idan zanyi miki rantsuwa ki yarda dani to na rantse miki da wanda raina yake a hannunsa babu wata mu'amular aure da ta ta'ba shiga tsakanina da Ya Sule asali ma ko hannuna bai ta'ba rikewa ba har hazar yau."
Baba Ladi ta shiga cikin mamaki da al'ajabi tace"Kikace Sule bai kusance ki ba."? Sayyada tace"Wallahi tallahi bai kusance ni ba Baba."
Baba Ladi tace"To ai wannan auran naku haramtacce ne a musulunce ya haramta shekara daya da watanni babu wata mu'amular aure kina kallonsa yana kallonki babu shakka aure ya lalace duk da dai ni ba malama bace amma dai nasan i jima'in wasu malaman zasu tabbatar da magana."
Sayyada tace"To sai ku warware aurenku da kuka daura dan wallahi ba zan koma gidan Ya Sule ba na dawo gida mijina kuma shine Sadam wanda kaddara ta ritsa dashi."
Baba Ladi tace"Haba 'yar nan aiko baki fada ba babu inda zaki koma yanzu zan sanar da iyayenku abunda ke faruwa ni kam ban ta'ba ganin solo'biyon namiji ba kamar Sule ka zauna da mace babu wata mu'amula Allah ya sawake masa."
Baba Ladi ta futa daga dakin tana mita da kananun magana sosai al'amarin ke bata mamaki tabbas yanzu take kara nadamar abunda suka aikata aure kan aure shin wai wane za'a dauka a ciki dole sai malamai sun zauna sunyi bayani kan al'amarin.
Sosai yaji dadin zuwan abokanan aikinsa ya sanya aka kawo masa Asalamiya suka dinga mamakin kudurar ubangiji addua suka shiga yiwa yarinyar wasu daga ciki sai daukarta a hoto suke a wayoyinsu da dama wasu naso suga matarshi ya hana duk da baya jin yarinyar cikin ranshi amma yana kishin kansa ya riga ya haihu da ita dole yaji kishinta a ransa.
Sule kam da ya fita sai ya wuce majalisarsu daga zarar ya tuno da Sadam sai gabansa ya fad'i shawarwari yake da zuciyarsa yaya za'ayi ya kassara masa rayuwa shifa kwata kwata baya so yaga yana wani motsi a duniyar nan.
Kusan karfe takwas da rabi ya shigo palon yana sanye da t_shart mai karamin hannu fara tas da ita sai wando wanda ya zarta gwiwa da kad'an 3qutar kamshin turaransa yake as'usel yazo zauna kusa da Baba Ladi tace"Dama yanzu nake so in aika matarka ta kira ka to dama so nake kowa ya hallara a palon Sule kawai muke jira ya shigo."
Yace"Wani abu ne kuma."? Baba Ladi tace"Babban al'amari kuwa bari dai Sulen yazo sai duk kuji komai." Palon yayi shiru kowa ya 'kagara Sule ya shigo....
Sayyada sai satar kallonsa takeyi wani irin sonsa na kara karuwa a cikin ranta wai shin yaya za tayi ne in ta rasa Sadam rayuwarta ta lalace!
A hankali ya d'ago kansa suka had'a ido ya dauke kansa tare da ta'be baki Matarshi ya kalla a nutse yace."Kije gurina ki kwanta mana ke daga kinga duhu ya kawo kai sai bacci sai kace 'karamar yarinya." Harira ta mutsika idonta tana kokarin mikewa Baba tace"A'a kyaleta mana ana hira ka tashe ta idan ka tashi sai kuje tare."
Shiru yayi kansa na kasa yana duba waya Sayyada kuwa hankalinta ne ya tashi da jin maganar da yake da matarsa sai kwalla ta ciko mata ido ita kam ta shiga damuwa da tashin hankali.
Sai kusan tara da kwata Sule ya shigo ganinsu sunyi duru duru a palo sai yasha jinin jikinsa saboda tsabar rashin yarda da kansa ko zama baiyi ba ya kalli Sayyada da fad'in"Baby tashi mu tafi goma ta kusa."
Baba Ladi tace"Haba kai kuwa ai ka zauna sai kace wanda zai tashi sama wannan zaman da mukayi duk saboda kai mukayi shi."
Gabansa ya yanke ya fad'i! yace"menene.'? Baba Ladi tace"Zauna ai maganar ba ta zama bace." Sai ya nemi guri ya zauna yana satar kallon Sadam dake danna wayarsa.
Alhaji Auwal ya gyara zamansa sam! babu wasa a fuskarsa yace"Sulaiman wata magana naji mara dad'i wacce ta fito tsakaninka da Sayyada ashe dama zamanka da matarka Sayyada baka ta'ba had'a shimfida da ita ba."!?
Sai yaji wani sanyi ya ziyarce shi da jin maganar da mahaifinsa keyi sam baiyi tunanin Sayyadar ce zata fad'i maganar ba Yace"Hakane Abbah babu wata mu'amular aure da shiga tsakanina da ita asali ma ko hannunta ban ta'ba rikewa ba amma hakan da ya faru wallahi wallahi ba laifina bane laifinta ne tunda babu irin yanda banyi da ita ba ta'ki amincewa dani shiyasa na hakura na kyaleta sai ranar da ta bukata da kanta."
"Kayi ganganci Sulaiman kayi ganganci ka lalata auranka a musulunce babu aure tsakaninka da Sayyada a 'ka'ida wata shida musulunci ya d'iba mutukar ka kauracewa matarka sama da wad'annan wattanin da musulunci ya d'iba to babu shakka aure ya haramta a tsakaniku saboda haka Sayyada ba matarka bace yanzu."
Sulaiman yaji wani irin gumi ya karyo masa baki na rawa yake fad'in"Abbah ban gane wannan 'kaulin ba nace muku ba laifina bane laifinta ne ta ina kuma auranmu ya haramta na dauka ai fad'a zukuyi mata ta gyara kuma sai ku 'bullo da wannan maganar."
Alhaji Auwal yace"Babu inda mace take fin 'karfin d'a namiji ta 'bangaran komai namiji shine a gaba Sulaiman kayi kuskure mutuka da har ka dauki tsayin wannan wattanin ba ka sauke nauyin da Allah ya rataya shi a wuyanka ba don haka dole ka dauki gammo ka nad'a ka dauki hakuri kan Sayyada idan kuma kana da ja to kaje ka tambayi malamai masana zasuyi maka cikakken bayani."
Palo yayi tsit! kowa na sa'ke-sa'ke ta 'bangaran Sadam! jikinsa na bashi 'karya ne tuni Sule ya riga ya gama da Sayyada duk 'karyar banze ce suke........Sule ya shiga halin rud'u da tashin hankali ya hakane 'kiri 'kire ana nema a haramta masa auransa.
Sadam mikewa yayi da niyar tafi gurinsa Ya kalli Harira tare da bata umarnin ta biyo bayanshi
Sallama yayi da iyayen nashi ya fice daga palon Harira ta sa'ba 'yarta a kafada tabi bayansa.....A guje! Sayyada ta afka d'aki ta zube kan bed tana kukan bakin ciki da takaici.
Babu wata mu'amular arziki tsakaninsa da Harira don ku