Showing 60001 words to 63000 words out of 142497 words
Chapter 21 - NI DA YAYA SADAM Complete Document by Binta Umar Abbale.txt
haihu baku fini so zanyi abinda kuke so shikkenan ko."!?
Baba Ladi tace"Shikkenan magana ta wuce kuma ka fita daga fushin ubangiji domin ita Sayyadar ai kana shiga hakkinta fisabilillhi ai rai dangin goro ne." Jin abinda Baba Ladidi ke fad'a ya sanya Sayyada ta fito daga d'akin tana cunkusa fuska tace"Wai ni Baba don Allah me yasa kike min haka nice nace miki ina bukatar wani abu ni dai don Allah ku daina yi min irin wannan."!!! Baba Marka ta bud'e baki cike da mamaki! tace"Kaji ni da ja'ira ko? ana nema a 'kwato miki martabarki kina nema kiyi shashanci to mu meye laifinmu anan."?
Murya na rawa tace"Idan ta wannan hanyar zaku kwato min martaba to bana so haka kawai sai ku dinga cewa ina bukata to ni me nake bukata nifa bana son irin haka kawai ku kyaleshi wai dole ne ma sai anyi abun." Baba Marka ta dauki maficin dake kusa da ita ta jefa mata tace"Kaji ja'ira ko wuce ki bawa mutane guri shashasha kawai." Sayyada ta zumbura baki daki ta shiga tana surutai tayi bala'in jin haushin abunda suke mata sai wani cusa masa ita yake yana basarwa alhalin basu san iskancin da yayi mata jiya ba.
Sadam dariya yake kyakyatawa yana kallon Baba Ladidi sai sababi takeyi da fad'in"Ai dama nasan duk laifin daga gurinki ne kece bakya bashi had'in kai shiyasa yace sai kinyi kwari ni na ta'ba ganin sokuwar mace irinki humm! Sayyada anyi mahaukaciyar yariya." Sayyada ta fashe da kukan takaici me yayi zafi har da ce mata mahaukaciya gaskiya lamarin su Baba Ladidi a kwai ban mamaki. Yace."Baba kice mata ta shirya mu tafi da wuri bana so sha biyu tayi mana a garin nan." Tace."au! yau d'in zaku tafi."!? Yace."Abbah ne fa ya aiko ni biko kinga yana da kyau na koma akan kari." Tace."Hakane don Allah ka janye wannan kudirin naka ka taki matarka zuwan farko idan munyi mu ganta da ciki." Yace."Karki damu baba za'ayi insha Allahu." Tace."Yauwa kokai fa ."Mikewa tayi ta shige daki tana sake maganar Sayyada na kuka tace"Wallahi Baba sam! baki da aji kin cuce ni kawai kina zubar min da mutumci sai wani cusa masa ni kikeyi dole sai ya kwanta dani ni wallahi karki sakeyi min haka." Baba Ladidi tace''Ashe bakinki bai mutu ba Sayyada ni kike fad'awa wannan maganar."Mikewa tayi tana buga kafafu tace"Ni wallahi sai nace ma ba zan bishi ba ai wallahi kun bani haushi." Baba Ladi ta rike 'kugu tana kallonta tace"To ko dukana zakiyi ne."!? Ni ba dukanki zanyi ba ni dai nace kawai ki daina min haka." Tace"Auwo! ai na dauka zaki gaura min mari ne saboda nace mijinki ya neme ki dama ai nasan duk laifin daga gurinki ne." Sayyada tace"Eh naji laifina ne ni dai ki daina yi min haka." Baba Ladi tace"Ai na daina uwata ki harhad'a kayanki ki fito ko tafi." Sayyada ta zumbura baki tana 'kunkuni Baba Ladi tace"Kyaji dashi kina so kina kaiwa kasuwa humm."!
Baba Ladi na fita Sayyada ta nemi guri ta kwanta tana tunanin abinda ya faru tsakaninta dashi jiya da daddare lumshe ido tayi ta takure jikinta guri guda ajiyar zuciya take saukewa jin wani irin shau'ki na fizgarta.
A hankali ya shigo dakin hannunsa duk a cikin aljuhu kallonta yake tana ta mutsu mutsu ga idonta a lumshe!! gyaran murya yayi tayi saurin bude idonta suka kalli juna lokaci guda ya fahimci halin da take ciki yarinyar fitinanniya ce kamarshi, Had'e fuska yayi kamar bashi ne mutumin da yake mata sambatu jiya ba yace."Ke! kina kwance baki shirya ba ko Baba bata fad'a miki bane."?
Mikewa tayi zaune tana daura dankwalinta tace"Ni bata fada min komai ba yace."Okey ni na fada miki ki shirya zamu wuce Kaduna yanzu."
Shiru tayi yace."Ko bakya ji ne?"!? "Ina ji." okey shine kikayi min shiru ni ne mahaukaci kenan."!? tayi kasa da kanta yace."Minti goma na baki ki fito ki same ni." Fita yayi bai saurari amsar da zata bashi ba.....Ta jima kafin ta mike ta dauko jakar data zo da ita ta gyara kayanta hijab ta zura ta fito tana zum'bure-zum'bure! Baba marka tace"Ai tuni ya fita yana can kofar su Amina kije ki same shi." Cikin zuciyarta tace'cm''Ni ba zanje kofar su Amina ba idan ya gama ya fito ya same ni." Hanyar fita ta nufa Baba Ladidi tace"To Allah ya jishshemu alkairi.'' Allah ya kiyaye hanya." Ciki-ciki ta amsa tana fita ta ganshi tsaye da Amina suna magana kici-kici tayi da fuskarta ta wuce su.... Amina tace"Sayyada a sauka lafiya a gaishe min da aunty Luba da mutan gida." Ko kallonta ba tayi ba ta fita ranta in yayi dubu ya 'baci tilas ta nuna masa 'bacin ranta dangane da tsayuwarsa da Amina.
NI DA YAYA SADAM
NA
BINTA UMAR ABBALE
27
Can inda yayi parking din motarshi ta nufa ta tsaya jikin motar tana jiran fitowarsa, ranta na masifar 'baci a duk lokacin da taga ya tsaya da Amina suna magana ta 'bangaranshi tasan babu wata matsala ta 'bangaran Aminar ne take zargin wani abu babu shakka har yanzu Amina bata daina son Yaya Sadam ba."
Cikin sassarfa ya 'karaso gurin ta dauke kanta tana kumburi yace."Ke! a maimakon ki bude motar ki shiga sai kiyi tsaye anan gurin saboda tallata kai."!
Ba tace masa komai ba ta bude motar ta shiga ta zauna...Ya bude boot ya saka akwatin kayanta kana ya zagayo ya bude motar ya shiga.....Bisilimillahi yayi ya kunna motar suka gangara kan hanya........Sai da suka hau kwalta sannan ta juyo ta kalleshi tayi bala'in had'e rai tace"Wai don Allah Yaya Sadam! meye had'inka da Amina ne."?
Ya san za'a rina dama wannan kumburin da take yi ya gane kona menene kishi ne da yarinyar ba na wasa ba 'bata fuska yayi yace."Ke! wannan wace iriyar magana ce kikeyi."?
Jikinta a d'an sanyaye tace"Naga kamar akwai wata ala'ka a tsakaninku shine nake son sani."
Yace."Wato ke kina kokwanto ne ko."!? Ta daga kai tana kallonsa.....Murmushi yayi yace."Kin manta da cewar Amina 'yar uwata ce kamar yanda kike 'yar uwata." Shiru tayi shaf ta manta da hakan tace"Ni fa ba wannan ala'kar nake nufi ba." Yace." Wace ala'ka kike nufi bayan wannan." Cikin rashin dubara tace"Sai naga kamar kuna soyayya ne." Dariya ta bashi yace."To idan ma soyayya muke akwai aibu a ciki ne ai ba laifi ba ne."
Gabanta ya fad'i tace"Yanzu kai zaka iya auran Amina." Yace."Me zai hana idan Allah ya kaddara hakan." Shiru tayi ranta yayi 'bakikirin.....Shi kuwa tukinsa yake hankali kwamce in banda abun Sayyada ina shi ina wani aure yanzu ita d'in ma bai samu nutsuwa da ita ba.
Tunda ya fad'i haka sai ta ci kunu ta dauke kanta tana kallon hanya shi kuma yana dan satar kallonta ta gefan ido mamakin yarinyar yake wai kishi takeyi ko da yake dole tayi kishinsa tunda tana sonsa.....cikin zuciyarsa yace"Idan miskilanci kike ji dashi na fiki yarinya....Bai kara tanka mata ba har suka isa kaduna Sayyada na nukufurci shi kuwa idan ba kiranshi akayi a wayarshi ba kajin muryarshi ya daina kallon inda take kwata kwata.
Lokacin da suka isa gidan aunty Luba na asibiti zata haihu babu kowa a gidan Sadam ya kira Mammah a waya ya sanar mata gasu sun sauka tace"Suma gasu nan zuwa yanzu aunty Luba ta haihu amma d'an babu rai! Sadam yaji wani iri a jikinsa sosai ya kwallafa rai kan dan da aunty Luba zata haifa yana da bala'in son yara Sayyada kuwa har kuka sai da tayi suka zauna jiki a sanyaye suna jiran dawowarsu.
Alhamdullahi Aunty Luba jikinta da sauki suka shigo gidan Mammah na taimaka mata Sulaiman na bayansu hannunsa rike da manyan ledoji fuskarsa babu wani alamun alhini da damuwa ya karaso palon kicin ya nufa ya aje ledojin hannunsa ya fito.
Sayyada ta rungume auny Luba tana mata ya jiki tausayinta takeji sosai tace"Wallahi aunty na tausaya miki Allah ya kawo mai albarka ke kuma Allah ya baki lafiya."
Aunty Luba ta share hawayen dake zubowa a fuskarta tace"Ameen sayyada nagode da addua....Shiru palon yayi kowa ranshi babu dad'i in ka cire Sulaiman da ya harde kafafunshi yana latsa waya tamkar bashi abun ya shafa ba.
Sadam! yasha jinin jikinsa ya dago kai yana kallon Mammah yace."Wai haihuwa tayi babu rai ko kuma bayan ta haihu d'an ya koma."!?
Mammah tace"A'a ai bata haifeshi da rai ba likitocin sunce ta dad'e tana nakud'a ne har d'an ya galabaita basu tafi asibiti ba shine yasha ruwan haihuwa ya mutu." Yanda take fadin maganar zaka tabbatar da cewar ranta babu dad'i!
Sadam! ya girgiza kai yana kallon Aunty Luba yace."Aunty Luba ya akayi kika bari haka ta faru haba tamkar ba wayayyiya ba kina ciwo ki kasa tafiya asibiti har sai da kika galabaita sannan gaskiya banji dadin wannan abu ba."
Aunty Luba tayi shiru kanta a 'kasa sai zubar da hawaye take....Tabbas Sulaiman ya cuce ta ta rasa d'anta dama tunda taga yana nuna halin ko in kula akan cikin tasan baya so itace take kid'anta tayi rawarta kan cikin banda shi.....Tun farkon dare take nakuda tayi tayi dashi ya tashi ya kaita asibiti yace shi bacci zaiyi haka tayi ta fama da ciwo har garin Allah ya waye koda gari ya waye Sulaiman baiyi yunkurin kaita asibiti ba sai da ya gama komai na rayuwarsa sannan ya dauketa ya kaita asibiti lokacin tayi masifar galabaita haka likitoci suka dinga fad'a.....Kuma saboda tsabar mugunta irin nashi Yace."Ba zata fad'awa kowa ba har sai da tashi wannan mugun yanayin da yasa ta rasa dan da tasha mutukar wahala a kansa Tabbas inda tasan Sulaiman bashi da kyawun hali babu abunda zai sanya ta aureshi.
Sadam! ma ya dan fuskanci wani a dangane da al'amarin tun farko Dan uwanshi ba mutum ne me son yara ba duka d'abi'unshi na nasara ne yanzu ya fahimci da saka hannunsa komai ya faru.....Ganin Aunty Luba na kuka ya sanya ya dinga rarrashinta shi kuwa Sulaiman din hankalinsa na kan waya charting yake da 'yan matansa....Sai da ya gama sannan yasa baki kamar gaske yake fad'in"Kiyi hakuri mana wanda ya baki ya amshi abinsa idan kin kwantar da hankalinki sai kiga kin samu wani."
Aunty Luba ta kalleshi da mamaki! wai shine yake wannan maganar shida farkon samun cikinta yace a zubar da ta'ki yarda shine ya sakar mata wahala wulakacin yau daban na gobe dabam gashinan sai da yayi sanadiyar da yasa d'an yazo babu rai amma saboda tsabar munafurci yake wannan maganar.........Sallamar 'yan uwanta ne ya katse musu hirar Sadam! ya nufi sashensa Sulaiman kuwa zama yayi suka gaggaisa da yan uwan aunty luba kamar gaske sai wasa da dariya ake dashi.
Daki guda Mammah! tasa aka gyarawa aunty luba tace ta zauna a gabanta tayi jego zata kula da ita yanda ya kamata Yan uwan aunty Luba sunji dadi sosai suka dinga fad'in"Lubabatu kinyi sa'ar Uwar miji.
Sayyada kam a gurinsu ta tare ta saki jikinta sosai da 'kannan aunty Luba suna ta hira kanwar aunty Luba mai suna Asiya jininsu ya had'u da Sayyada sai da ta girmi Sayyada da kusan shekaru biyar amma sai ka lura zaka fahinta saboda ita Asiya tana da karamin jiki......Suna kicin suna aikin abinci Asiya tace"Sayyada na lura fa tun dazu baki le'ka mijinki ba alhalin kin san yana gida bai fita gaskiya yana da kyau kije ki duba shi koda akwai abunda yake bukata."!
Sayyada tace"Asiya kenan baki san halin wannan ba mybe ma ina zuwa zai koro ni shi ba ayi masa gwaninta."
Asiya tace"Duk da haka dai kije ki gani sai ki dawo mu karasa aikin abincin." Sayyada tace"To ban'ki taki ba bari na 'karasa murza fulawar nan sai naje." Asiya tace."Yawwa ko kefa su maza ba'a sanya a kansu ballanta irin naki da mata suke rubibi yanzu sai kiga wata ta kwace miki shi wallahi."
Sayyada tasa dariya tana fad'in"Kai Asiya nifa wallahi ina ganin beken matan dake rubibin namiji ni duk kyau da haduwarka baka isa nayi rububi a kanka ba." Asiya tace"Humm Sayyada kenan baki san abinda ke faruwa bane a wannan duniyar ni dai shawarar da zan baki tunda kin samu to ki rike hannushi bibbiyu."
Sayyada Dariya kawai tayi ta wanke hannunta tace"Bari naje na dawo." Asiya tace"To shikkenan."
Waya sukeyi da Captain Habu Yace."Habu bana jin zan iya fita aikin dare wallahi jikina duk a mace yake ni kaina na rasa abinda ke damuna kwana biyu wata iriyar kasala da mutuwar jiki ke damuna."
Captain Habu yace."Hakanan zaka daure ka fito domin tun safe su Saleh ke bunkice a gurin kuma dazu munyi waya dashi yace akwai tabbacin mutanan nan a gurin saboda haka kaga zuwanka nada amfani domin kafi mu dabaru masu kyau."
Yace."Allah ya nufe da zuwa yanzu na idar da Sallah isha'i zan shigo bracck din." Captain Habu yace."To shikenan a huta gajiya da kyau komai xakayi kayi kafin ka fito domin kar kasala ta sanya ka kasa aiki."Cikin sha'kiyanci yake masa magana Sadam! yace."Okey wato ka fassara magana ta da wata manufa ko."? Habu yace."No kawai dai na fadi hakane." Dariya sukayi dukaninsu kafin su kashe wayar a tare.
A hankali ta turo kofar ta shigo dakin bakinta dauke da sallama.
Ya d'aga kai a nutse yana kallonta zum'bura baki tayi ta wuce zukud'um!zukud'um! zata shige masa d'aki.
Yace."Ke! meye haka zaki wuce mutane ki shiga d'aki wani abu kika ajiye a ciki kome."?
Ja tayi ta tsaya tayi kici kici da fuska har yanzu haushinsa takeji kan maganar da yayi zai auri Amina.
Ya 'bata rai sosai yace."Wai shin wannan fizge fizgen da kikeyi na meye? na lura dake tun muna hanya kike wani cin kunu wa zaki nunawa miskilanci."
Shiru tayi kanta a 'kasa Tsaki! yaja ya dauke kansa.....Dakin ta shiga ta zauna gefan gado kwallah ta cika mata ido.....Haka kawai da ta kalleshi sai taji haushinsa idan ta tuno da maganarsa.
Ya shigo dakin yana tattare hannun riga toilet ya nufa domin daura alwala ya fito a nutse ya wuce ta masjid ya nufa domin yin sallah......Sayyada da kyar ta mike taje ta daura alwala ta fito sallah ta tayar ta zauna kan daddumar tana lazimi tana jin kiran sallah isha'i sai ta mike ta gabatar da tata zama tayi kan daddumar bayan ta idar da sallahr tana jiran shigowarshi.
Koda ya shigo ya ganta a zaune bai ce komai ba ya nufi wardrobe dinshi kayanshi ya soma cirowa yana kimtsa jikinsa.....Sayyada ganin yana sanya kayan aiki sai gabanta ya fad'i! da alama aiki zai fita kallon bayansa takeyi babu kiftawa jikinsa ya bashi ana kallonsa yana juyowa suka hada ido tayo saurin sunkuyar da kanta kasa.
Girgiza kai yayi ya cigaba da shirinsa Ta mike jikinta a sanyaye zata fita yace."Ke! ina zakije da daddaran nan."!? A hankali tace"Zan koma sashen Mammah ne." Yace."A'a kiyi zamanki a naki gurin ni zan fita idan ma nine bakya son gani."
Tace."A'a ni dai gwara ka barni naje can na zauna abunda ma aiki zaka tafi."
Yace."Eh aiki zan tafi yanzu idan ban dawo ba kar ki damu da safe ma had'u."
Tace"Shine kuma kake cewa na zauna ni kad'ai."
Yace."Ina da dalili ai yanzu kika tafi sashen Mammah kika zauna shikkenan Sulaiman zai zo ya saki a gaba kuyi ta shirme."!
Da mamaki! take kallonsa sam! bata ji dadin wannan maganar tasa ba duk da take yarinya mai karanci shekaru ta fahimci tamkar Sadam din na zarginsu ne sai ranta ya baci tace"Wai Ya Sadam! me kake nufi ne."? kar fa ka manta Sulaiman dai d'an uwana ne kusancin dake tsakaninka dashi yafi wanda muke dashi me zai sanya ka dinga zargin wani abu zai shiga tsakanina dashi gaskiya ni na gaji."!!
Yace."Ke! ni zaki kawowa maganar banza da wofi! ni zaki nunawa cewar Sulaiman dan uwana ne? Nace ba zaki koma sashen ba sai me ? idan Sule ke auranki sai ki koma nagani 'Yar kauye kawai wacce bata da wayo.''
Sayyada ta fashe da kuka ta tsani ya kirata da 'yar kauye shin wai me takeyi ne na 'kauyanci da kullum yake kiranta da wannan sunan......Cikin kuka tace"Wallahi ba zan zauna a daki ni d'aya ba sai kace mayya idan ka fita sai na fita kuma maganar 'yar kauye da kake kirana dashi ai duk tushen mu d'aya da ka.........Mari! ya kai mata a fusace!!! Ta matsa gefe tana muzurai! hannunta akan kumatunta kallonsa takeyi cike da tsoro da mamaki!
Yana huci! yace."Ba'a nuna ni da ya tsa Sayyada duk rashin kunyar da kike min kawai ina saurara miki ne! yanzu ma kina so ki zageni a kan Sulaiman ko."? Girgiza kai tayi tana zubar da hawaye. Yace."To in kuma cewa ga yanda za'ayi ki nuna ba haka ba ranki zai "baci! da banyi niyyar rufe ki ba amma yanzu furucin da kikayi ya sanya naji gwara kawai na rufe ki na huta a yanda kike kidahuma! zaki iya janyo min Sulaiman din nan ki cuci mutane."!!! Kuka takeyi tana bashi hakuri yayi mata banza ya cigaba da shirinsa.
Ransa duk ya 'baci da halin Sayyada kullum yana so ya nuna mata cewar ta kiyaye da Sulaiman ba sa'anta bane yana so ya nuna mata illolin Sule a tare da ita tana kaucewa shi ba zai fito fili ya fad'a mata waye Sulaiman ba saboda dan uwansa ne tilas ya rufa asirinsa amma ita saboda tsabar ta raina shi taki daukar maganarshi sai ya fara hukuntata sannan zata kiyaye.
'Kafafunsa ta rike tana kuka " Don girman Allah Ya Sadam! kar ka rufe ni a d'aki don Allah kayi hakuri kaji ko."!?
Yace."Sayyada taurin kanki yayi wa ban isa in fad'a miki magana d'aya ki dauka ba komai nayi miki kece kika jawo kina nuna min da cewar ni ban isa in fadi magana ki dauka ba sai ta sule shin wai Sulaiman ke auranki ko Sadam."!?? Cikin tsawa ya fad'i maganar! Tana kuka tace"Kaine ke aure na ba Sulaiman ba." Yace."Amma shine kike fifitashi a kaina."! " Bana fifita Yaya Sulaiman a kanka Ya Sadam ina yi maka kara ne kasancewarsa a matsayin dan uwanka na jini ni ma d'an uwana." Yace."To bana son wannan karar daga yau na soke ta babu ruwanki da Sulaiman." Tace"To insha Allahu." Ajiyar zuciya ya sauke yace."Cika min kafafu Malama." Da sauri ta cikashi ta mike tsaye tana goge hawayenta a