Showing 108001 words to 111000 words out of 142497 words
Chapter 37 - NI DA YAYA SADAM Complete Document by Binta Umar Abbale.txt
gashi dare yayi sosai dan sha daya ta wuce sukansu ababen hawan jefe jefi ne ke wucewa ranta ya 'baci! ganim suna ta tafiyar 'kafa babu wani babur da yazo wucewa ballanta su tsayar dashi.....Sai ta nemi guri ta tsugana bakin titi tana kallonsa yana ta tafiya ba tace masa komai ba haushinsa takeji sosai tsananinsa ke bata haushi.
Jin ya daina jin sahun tafiyarta a bayansa ya sanya ya juyo aikuwa can nesa ya hangota a tsugune! ransa ya 'baci ya koma da baya yana mata masifa.
Sai ta fashe da kuka tana fad'in"Wannan ai shiga hakkine kasan baka da abun hawa menene zaka ce dole sai na biyo ka kawai ka sanya tafiya mai tsayi irin wannan kai idan ka saba ni ban saba ba."
Yace."Ni kike d'agawa murya ko."? Shiru tayi tana goge hawaye ya 'bata rai! tare da fad'in"Wuce muje babban titi ba zamu rasa abun hawa ba."
"Ni dai ka kyaleni na koma inda na fito wai dole ne sai na kwana a gidan wasu mutane."
"Gidana ne ba na wasu ba." Yafad'a yana jin saukar 'bacin rai a ransa al'amarin yarinyar na sake dugunzuma shi kwana biyu ya huta da wannan matsalar tata."
Sai da ta gama nu'ku-nu'kunta sannan ta wuce shi tana 'kun'kuni! tafiya take kamar ba taso ya fuzgi hannunta yana janta da sauri da sauri tanayi tana hard'ewa da hijab dinta haka suka fita babban titi.......Nan ma sai da suka shafe rabin awa a tsaye Sayyada tayi ta kuka saboda takaici sannan wani mai babur ya tsaya a gabansu Sadam yace.'' Gaba kad'an zaka aje mu wajejen Samegu." Mutumin yace."To nawa zaka biya."? Yace."Muje malam ko nawa za'a biya ka."
"Tashi malama." Yafada yana kallonta da tayi zaman durshan bakin titi.
Tashi tayi tana buge zaninta ta shiga babur din sai dauke kai take....Kusa da ita ya zauna har kafad'arsu na gogar juna gabanta ya fad'i! Da sauri ta matsa gefe tana takur jikinta cikin hijab.
Yana kallonta baice mata komai ba...........Haka suka isa Har 'kofar gidan ya ajesu suka fito tsakanin Titin ja'in wajen masallaci da Unguwar samegu babu wata tazara mai tsayi haka Sadam ya ciro gudan dubu ya bawa direban ya kar'ba yana kokarin dauko sanji. Yace."Ka rike ka siyawa yara alawa." Mutumin yabi Sadam da kallo yana mamaki yace."Nagode to Allah ya biya bukatu." Hannu kawai ya daga masa suka wuce........Key yasa ya bude gidan ya kunna wayarsa yana haskawa Sayyada kamar kar ta shiga sai dai ta daure tabi bayansa.........Dakinsa ya bude yace"Shigo mana." Ta shiga dakin tana kalle kalle ya kunna fitilarsa ta solar gidan yayi haske ko ina Sayyada ta dinga bin dakin da kallo.....katuwar katifa ce da karamar sif mai murfi biyu sai lokoki guda biyu redionsa akai da tarkacen kudad'ensa da sauransu kasan dakin kafet ne ja da jan labule shi kansa zanin gadon Ja ne mai gashi gashi.....Yace."Zauna ina zuwa." Kafin tace komai ya fita daga dakin......Shiru tayi tana nazarin dakin wai Yayanta mijinta masoyinta shine yari rayuwar aure tare da wata matar a cikin gida d'aya wasu zafafan hawayene suka shiga zubowa a idonta ta shiga girgiza kanta tana cizan lips dinta wata ta rigata sanin waye shi ta rigata! ta rigata! tarigata!!!!! Kuka tasa cikin tashin hankali ta matse kanta tsakanin cinyoyinta......Jin motsin shigowa gidan yasa tayi saurin goge hawayenta......Ta sunkuyar da kanta ya shigo hannunsa rike da leda indomee ce da kwai ya sanya aka soya mata yace."Ga abinci nan in za kici." Sharesa tayi ba tace komai ba,
Shima baice komai ba ya shiga cire kayan jikinsa wanka zaiyi ya kwanta saboda ya gaji sosai yayi zurga zurga jikinsa duk yayi tsami! tana kallonsa ya fita daga dakin ta waiwaya tana karewa katifar kallo wai a wannan shimfidar da take kai ya turmushe 'yar mutane idanunta ne ya hango mata wani abu da sauri ta sanya hannu ta janyo.......Vest din Harira ce wacce ta barta a dakin tun ranar da zata bar gidan.......Sayyada tayi saurin jefar da ita ta mi'ke tsaye da azama ta bar gurin bakin kofa taje ta tsaya aikuwa kome zai faru sai dai ya faru ba zata kwanta a shimfidar nan ba.
Ya fito ya tarar da ita tsaye bakin kofa yace."Meye haka kin tsaya bakin kofa ki baki san dare yayi bane."? Shuru tayi masa ya shige ciki yana jan tsaki Jallabiya da gajeran wando ya zura a jikinsa ya zauna gefan katifar yana kallonta.
"Sayyada wai meye hakane? me yasa ne kullum kinfi so ina magana akanki kizo kiyi kwanciyarki ni babu wani abunda zanyi miki."! Yafad'a babu wasa a tare dashi.
Shiru tayi masa tana ta shirya maganar da zata fad'a masa wacce zata sanya shi cikin damuwa kamar yanda ya sanyata damuwa.
" Wallahi kika sake nazo nan sai na 'bata miki rai! Ya ina miki magana kin mayar dani wawa ni sa'anki ne."? a kufule yake maganar..........."Tarayyamu da kai a d'aki d'aya ta haramta domin a halin yanzu ni ba halalinka bace halilin wani ce."!! Tafad'a tana kallonsa sosai take so ta tabbatar masa da gaskiya ne."
Yace."Ke! wace iriyar maganar banza ce wannan wato hurd'a da mutane da kuma had'uwa da 'yan iskan abokai ta sanya kin soma hauka ko wace banzar magana kike mun."
"Wannan magana da nake maka babu 'karya a cikinta domin itace gaskiya ni matar wani ce a yanzu kaga kwanciyarmu a d'aki! d'aya haramun ne tunda kaid'in ba muharramina bane."!!!!!!
Wani irin juyi yayi ya dirgo daka bed din jikinsa na kyarma! ya durfafo inda take...................!
NI DA YAYA SADAM
BINTA UMAR ABBALE*
45
Inda take tsaye yazo yayi mata rumfa 'kwayar idonsa ta riked'e daga fari zuwa jaaa! Murya a sha'ke! yace."Ke! ki san irin maganar ta zaki dinga amfani da ita gurin magana wannan maganar da kika fada min a yanzu ta sanya ni jin wani iri a jikina bana son irin wannan wasan daga yau." a sanyaye karashe maganar yana me riko hannunta.
Tayi saurin cire hannunta daga nasa murya na rawa tace"Wallahi Ya Sadam maganar nan babu wasa a cikinta bayan mun tabbatar da mutuwarka da wata shida su Abbah suka daura min aur........."Innalilhi wa'ina ilahi raji'un!!! Ya katseta da fad'ar wannan kalma.
Tsorata tayi da sauri ta matsa gefe guda tana kallonsa.
Ya d'ago yana kallonta da nunata da hannu le'bansa sai rawa yake yana so yayi magana amma ya kasa.......Zubewa tayi 'kasan gurin tana shashsheka babu shakka Ya Sule ya cutar da ita a rayuwa da yasa aka 'ka'kaba mata wannan 'kaddararan auran nasa.
"Waye shi? waye wanda yayi wannan ganganci! ki fad'a min wanda ya shiga gonata alhalin ina raye a duniya."
Gwiwarsa a 'kasa yake wannan maganar yana kamo kanta dake dukufe tana gocewa.
"Sayyada ki fad'a mun waye wannan me 'karar kwana da har ya amince ya aureki bayan yasan ban mutu ba."
Ta dago kanta idonta jage jage da hawaye abun mamaki sai taga kwarmin idonsa ya cika da kwallah le'bansa sai rawa yake duk ya hada gumi.
Tayi saurin mayar da kanta 'kasa tana goge fuskarta.
Ganin ta'ki masa magana sai ya fusata da fad'in"Ashe dama ke mayaudariya ce Sayyada ashe dama duk ikirarin kina sona karya kikeyi? meyesa zaki yaudareni ki auri wani namijin bayan da aurena akanki shin waye ya fada muku na mutu da har zaku yanke wannan hukuncin akaina wallahi ban yarda ba ko waye shi dole ya sake ki ki dawo hannuna ai ba haka musulunci yace ba."
A d'an dake! tace"To Ya Sadam nima ba laifina bane su Abbah ne suka yanke wannan shawarar ka daina kirana mayaudariya saboda ba ita bace kaima ka duba cin amanar da kayi mun kayi aure ka haihu duk ka manta dani da irin son da nake maka ai bani kad'aice naci amana ba."
Ya mi'ke tsaye yana goge gumin goshinsa yace."Wallahi ba'a cikin hayyacina na aikata wannan aikin ba Sayyada ki fahimce ni bana da ra'ayin auran mace sama da d'aya a rayuwata ke kad'ai kin isheni wannan al'amari da ya faru tsakanina da harira 'kaddarace wacce ta riga fata kuma kin san dai wad'annan mutane sunyi mun hallacin da har na mutu ban manta dashi ba sosai ya cancanta na rikesu a matsayin iyaye kana kuma na kula da 'yarsu."
"To ai bance wani abuba nima nasan 'kaddara saboda haka nima sai ka 'dora al'amarina a matsayin 'kaddara shikkenan ka zauna da matarka ni kuma sai na zauna da mijina dama haka Allah ya 'kaddara mana."
"Baku isa ba."! Yafada kamar wani mahaukaci jikinsa na kyarma! ya mike tsaye yana safa da marwa a dakin ya juyo yana fuskantar da fad'in''Ki sake yi mun maganar ke matar wani ce wallahi sai na gurje miki baki yanzu ni zaku mayar mahaukaci ko okey dukaninku zan maka ku kuto in yaso al'kali sai yayi mana shari'a."
"Yanzu Yaya Sadam! zaka iya maka iyayanka da kakaninka a kuto."? Cikin mamaki ta fad'i maganar.
Kamar baya cikin hayyacinsa yace." Me zai hana tunda dai sun kauce hanya a'ina aka ta'ba haka? 'kai'ida shekara uku ne idan sun neme ni sun nemeni basu ganni ba to sai su yanke wannan hukunci amma wata shida kacal kawai su kama su daura miki aure da wani bayan kuma ina raye a duniya kema ai babbar mai laifi ce da kika zauna har haka ta faru."
"Ya Sadam ka daina kirana da mai laifi kaima fa mai laifi ne kuma a'lamarin nan ka jingina shi a matsayin 'kaddara to ba shikkenan ba meye na d'aga hankalinka dama fa ba sona kake ba sau nawa kake ikirarin cewar zaka sakeni to ka gani Allah ya huttasheka......Nifa ban damu da auranka ba wallahi na dauka haka Allah ya kaddara zakayi aure a wani gari har ka haihu dole idan rabo ya rantse a ko'ina ne sai an sameshi saboda haka don Allah ka daina wata maganar kuto domun kanka zaka tonawa asiri."
Ya dinga girgiza kai yana sauraran kalamanta da suke kokarin mayar dashi kurman karfi da yaji! Wai mafarki yake ko kuma gaskiya ne al'amarin........Hannu ya kai ya d'ora a jikinta ta zubura da sauri ta matsa gefe.
Nan ya gazgata gaskiya ne ba mafarki yake ba Sayyada ce a gabansa take kuma shaida masa ita d'in ba matarsa bace matar wani ce....."Innalilihi wa'ina ilahi raji'un! wannan wace iriyar 'kaddara ce Allah ya d'ora masa!! Ya jima zaune a kusa da ita kansa a 'kasa sai d'igar da gumi yake idan ba idanunta ne ke mata gizo ba sai taga kamar harda hawaye bayan gumin! jikinta yayi sanyi yau jarumi wanda yake da juriya da jajurcewa kan komai shine ke kuka lallai abun babbane tausayi ya bata amma bata nuna ba sai ma sanja gurin zama da ita.........Ya mi'ke ya fita daga dakin tana jin sanda ya zare sakatar gidan ya futa gabanta ya hau dukan uku uku karfe kusan daya da rabi na dare ina zashi.
Mintina goma yayi ya dawo jarabar san haya'ki ce ta ciyoshi wanda ya manta da wata sigari sai yau ita kawai yake bukata ya zuka ko ya samu sassauci wai futa yayi ko zai samu masu siyarwa gari yayi tsit ya jima a tsaye yana dube dube da ya gaji ya dawo gidan yana wani irin layi kamar wanda yasha giya.
Tsakar gida ya sameta a tsaye ta ganshi yana wata tafiya kamar zai kifa tayi saurin matsawa ta bashi guri yana isowa ya ingizata cikin dakin......Ta fad'i kasan kafet tayi saurin mikewa tana ja da baya.....Hannu ya nunata da fad'in"Kin'ki ki fad'a mun waye mijin naki ko."? Sayyada tayi shiru tana kallonsa........Ya shiga girgiza kansa yana kokarin cire riga da fad'in"Laifin duk ba na kowa bane nawa ne da har na tafi ban 'kar'bi hakkina ba yanzu zan 'karba kuma ba zamu koma kaduna ba nan zamuyi ta zama har 'karshen rayuwarmu yanzu na gano babu wanda yake sona daga su Abbahn harsu Baba Ladidi duk 'karyan banza suke.
Kanta yayo tayi saurin kaucewa ya rungume bango (garu) Hanyar fita ta nufa jikinta na 'bari!!!
Ya biyota a sukwane! ya cimmata a sora daukarta yayi cak! ya nufi dakin da ita.
Ta dunga dukansa tana kuka da kiran "Karkayi mun haka Ya Sadam! ba haka mukayi da kai ba karkaketa mun haddi."!!!
Wannan magana da tayi ta dugunzuma shi sosai ransa ya 'baci matuka shida halalinsa amma ake masa kafurar magana.
Danneta yayi yana lalubarta yaji Brest dinta sun cika masa hannu har sunyi rara ga wani uban taushi da fatar jikinta ke dashi.....Yayi bala'in gigicewa ya dinga ya mutsata yana kokarin cire mata hijab. Ta kudundune jikinta tamau ta dinga ture hannunsa daga jikinta shi kuma duk ya gigice da fad'in"Yau sai nayi miki cikin 'yan biyu in yaso inga wane shegene zaice ke d'in ba matata bace."
Da jin wannnan maganar tasa sai ta hau wata iriyar fuffuka tana turje turje da taune harse kamar wata mai iskoki ta dinga buge buge tana ture shi.........Kuma a lokacin wani irin karfi ne yazo mata domin ko da wasa ba zata bari ya samu wani abu daga gareta ba alhalin bata san matsayinta ba ko zata bashi kanta to ba yanzu ba.
'Dagata yayi yana kallonta tana buge buge ya rike hannunta ta fuzge karfi ya sanya ya danneta yana tofa mata adduao'i sun jima cikin wannan halin kafin ta daina tayi lamo gumi na tsatstsafo mata.
Sakinta yayi ya fita daga dakin.
Mikewa tayi da sauri ta sauko daga gadon babu abunda zai sanyata ta kwanta kan gadon da yayi mu'amular aure da wata.
Shiru taji bai dawo dakin ba ta kudundune jikinta cikin hijabi ta kwanta kasan kafet tana wani irin kuka mai tsuma zuciya.
Sadam kuwa da ya fita kai tsaye dakin Harira ya bude ya shiga ya kwanta kan doguwar kujera ya rasa wane irin tunani ma zaiyi wannan wace iriyar kaddarace ta same shi gaskiya iyayensa ba suyi masa adalci ba sun nunawa duniya basu damu dashi ba yama za'ayi ace daga 'batansa ko shekara bai cika ba sun aurar da matarsa ga wani wannnan shine babban kuskuran da suka tabka dole kuma suyi sharia dasu da wanda ya aure masa mata.
Akan kunnenta aka kirayi sallahar asubahi tana jin motsin fitowarsa tayi lamo tana sauraran motsinsa yana daura alwala tana jin sanda ya zare sakata ya fita daga gidan
Ta mike jikinta duk babu kuzari ta fito a hankali ta daura alwala ta koma dakin........Sai da gari ya soma haske sannan taji motsin shigowarsa gidan.
Rufe idonta tayi cikin hijab ya shigo dakin ya jima tsaye a kanta kafin ya tsuguna yana kokarin janye hijab din ta bude ido suka kalli Juna.....Mikewa tayi zaune tana kauda kai sam bata so su hada ido dashi.
"Tashi Zamuje asibiti." Yafada da alamun alhini a tare dashi..........Kallonsa tayi yace."Eh bayan fitowata Sallahr asubahi Baba ke fad'a mun Harira babu lafiya kuma jiya 'kalau na baro ta."
Ta d'anji wani iri cikinta a hankali tace"Allah ya bata lafiya." Ya mike yana fadin"Ki shirya yanzu kafin in shigo.'' Ta bishi da kallo har ya futa daga dakin.
Mikewa tayi ta fito da brush da markilin daga cikin jakarta ta fita daga dakin.
Ba dauki soso da sabulunsu ba da ruwa tayi wankan ta wanke bakinta a gurguje ta fito ta sauya kaya da hijabi ta zauna tana shafa basilin.......Ya shigo gidan da ledoji a hannunta abun kari ne ya siyo mata tea da bread da wainar kwai kadan tasha saboda babu nutsuwa a tare da ita.........Ya shigo dakin bayan futowarsa daga wanka jikinsa da karamin wando Sayyada ta dauke kanta daga kansa......Ya dauki kayansa ya futa daga dakin.....Gani tayi tsakanin jiya da yau sai wani abu yake na marasa kuzari.
Ya fito daga dakin Harira yana fad'in"Fito mu tafi." Ta mike had'e da dauko ledar kayanta.
Hannunta yabi da kallo yace."Ina zakije da wannan ledar."?
Kai tsaye tace"Kayana ne a ciki ai." mayar dasu ya fad'a had'e da daure fuska tamau!
"Kaga Yaya Sadam! bafa zan 'kara kwana cikin gidanan ba gaskiya bai dace ba gashi na fad'a maka abunda yake da akwai kuma kace wani abu komai fa ya faru kaddarace kaje ka ruke 'kaddararka nima na rike 'kaddarata shikkenan."
Harara ya watsa mata yace."Baki da hankali ko? jiya bance miki karki sake mun maganar nan ba? Ok kece kika iya d'aukar 'kaddara ni ba zan dauki wannan shashashar 'kaddarar ta son zuciya ba na fad'a miki keda komawa kaduna sai a lahira in yaso in suka nemeki suka rasa sai su daurawa mijin naki aure da wata."
Ta dinga kallonsa da mamaki a tare da ita.....Yace."Ki shige muje malama." Zumbura baki tayi ta wuceshi ranta a 'bace aikuwa tayi al'kawari sai ta gudu ko ta halin 'kakane yanzu dai zata bishi masa suje asibitin amma sai ta gudu dan ba zata zauna irin wannan zaman dashi ba
*Littafin
NI DA YAYA SADAM
*BINTA UMAR ABBALE*
46
Likitoci sun kai biyar tsaye a gadon da Harira ke kwanta tana wani irin nishi kirjinata na kaiwa yana kawowa, idanunta a rufe ruf ga wani uban kumburi da tayi a lokaci guda duk jikinta ya suntume wanda jiya ko alamu bai nuna ba sai tashi sukayi da kumburin......Kokarin makala mata oxcgyen abun zu'ku nufashin ake abun yaci tura dan wata iriyar jijjiga take gadon da take kwance yana wata iriyar 'kara.....Hankali a tashe likitocin suka rufu a kanta domin ceto ranta lokaci guda jininta ya hau irin wanda ba'a so gashi har ya janyo mata jijjiga mai mugun hatsarin gaske.
Da kyar suka sanya mata Uxcgyn din kana suka bata taimakon gaggawa ta dawo dai-dai sai dai har yanzu jawo numfashin take da 'kyar da kyar.....Sai wani irin hawaye dake biyo gefan idonta lokaci guda tayi wata masifar rama mai tsanani.
Hankalinsu Jatau! ya tashi matuka domin akan idanunsu 'Yar tasu ta fara ciwon kuka kawai Hansatu take itafa tuntuni ta cire rai da 'yar tata.
Cikin wannan halin suka samesu Sadam! ganin fuskokinsu babu walwala sai ya sha jinin jikinsa suka gaisa dasu Hansatu kana ya tambayi jikin Hariran to kafin suyi masa bayani Dr dake kula da Hariran ya fito ya nemi san yayi magana dashi.
Ofis dinsa ya bishi Dr yace "Sadam! matarka na cikin tsananin tension mu kanmu mun rasa ko nameye jininta ya hau sosai tsakanin jiya da yau al'amarin ya bamu mamaki tunda lafiya kalau ta haihu sai dai tace kanta yana ciwo a jiya ashe al'amarin yayi tsanani jiya da daddare ta dinga jijjiga to ba tayi karfi ba