Showing 114001 words to 117000 words out of 142497 words
Chapter 39 - NI DA YAYA SADAM Complete Document by Binta Umar Abbale.txt
suna murnar yaushe gamo Sayyada tace"Aunty bari nayi wanka na fito akwai labarai."
Aunty tace"Shikkenan Sai kin fito."
Sayyada ta dauka Sulaiman xai biyo ta daki ganin yanda yake zumudi a kansa har ta gama abunda take ta fito bai biyo ta ba.
Yana zaune suna hira da Luba ta fito daga dakinta cikin doguwar riga yau bata sanya hijab dalili kenan da ya sanya Sule ya kura mata ido yana kallo....Yace."Baby idan anjima zamuje can gida ku gaisa ko."?
Tace"To shikkenan Ya Sule." mikewa yayi jikinsa a sanyaye yace."Ni zab futa." Sukayi masa fatan dawowa lafiya ya kama hanya ya futa.
Sayyada ta kalli Luba tace"Aunty wai ya akayi Ya Sule ya gyaru ne naga al'amura duk sun sauya a gidan ba kamar da ba."
Aunty Luba tace"Ai bayan tafiyarki abubuwa sun faru marasa dadi amma kuma ta bangaranmu sai suka zama masu dadi in fada miki dai Sule garin yawonsa na bariki yaje ya nemi matar wani babban d'an sanda Allah ya toni asirinsu wai matar ashe har gidanta take jansa tana ce masa ita bazawara ce ashe karya take ranannan kawai tace masa yaje da daddare ni dai naga ya ci uwar kwalliya ya futa ashe tsautsayi ne ya futa dashi matar nan ashe mijinta ne yayi tafiya ta kira Sule Allah yasa basu fara komai ba mijin ya dawo saboda yayi mantuwa kawai yaga Sule rashe rashe a gado ai sai ya zaro bunduga Sule ya tsure ya dinga bashi hakuri matar ta fito daga bandaki ta dinga bawa mijin nata hakuri da fadin"Sule dan uwanta ne can bangaran babanta dake Minna da kyar dai mutumin ya yarda ya sallami Sule yanda ya dawo gida a gigice sai na tsorata a gidan duk ya sanar dani abunda ya faru yana zufa! yake fadin da sai dai akawo miki gawata kinji abunda ya faru.......Yayi ta neman gafarata yana hawaye shine fa yanzu muke zaman mutunci dashi a cewarsa yanda yaga police din nan ya fito da bunduga ya tsorata dan bai shirya mutawa yanzu ba."
Sayyaa dariya harda hawaye tace"Lallai Ya sule matsoraci ne wai!!! ai dole yaji tsoro yaga bunduga 'karara! tandijam Wallahi nayi farin ciki da faruwar hakan kinga sai ya zama izina a gareshi nasan tunda yana tsoron mutuwa koda wasa ba zai kara tunkarar matar wani ba. Ke kuma aunty Luba ki cigaba da hakuri dashi da halinsa kin san ko wane bawa yana tare da kaddarasa ki dauka zamanki da Ya Sule kaddarace kuma kiyi ta yi masa addua insha Allahu Allah zai shiryeshi."
Aunty Luba tace"Addua kam kullum cikin yi masa nake Sayyada kema ki tayani da addua." Tace"Insha Allah aunt." Danning suka nufa domin cin abinci.
****
Yau kwanan Harira biyar a asibiti ta samu lafiya sosai sai dai har yanzu kumburin bai sa'be ba tana kuma haki sama sama Dr ya dora ta kan magani tare da kafa mata sharadai. kana ya basu sallama suka nufo gida.
Duk wani abu da yake yanayinsa ne cikin dauriya da jajurcewa ko da wasa bai sake kiran wayar Sayyada ba ballatana ta fada masa magana mara dadi sai dai duk kwanan duniya da ita yake kwana da ita yake tashi a cikin zuciyarsa kullum kuma kara kaunarta yake a ranshi.
Ranar suna yarinya taci sunan Baba Ladi Suwaiba sai suke kiranta da Asalamiyya yarinya tayi 'kiba kwarai ta murmure duk abunda Uba kewa 'danshi na al'ada Sadam yayiwa 'yarshi da yake jin tamkar bashi da kowa sai ita a duniya kullum kara masa kaunarta ake a zuciyarsa.
Sayyada tayi ta tsammanin kiran wayarsa taji shiru gashi yau kwananta biyar da dawowa babu labari sai ta dinga tunanin ko ta kirashi ne wata zuciyar tace kamar kin damu shi kenan ki bari zai kira ki da kansa.
To Har ta cika sati biyu da dawowa bai kirata ba sai ta soma rama a tsaitsaye tana shawarar ko kawai ta fadawa iyayensa abunda yake da akwai in yaso sai su suje su daukoshi ta lura dai kamar su Jatau! din sun asirce sun gama dashi haba mutune sai kace mayu.
Sulaiman kuwa sai kokarin kafa gwamnatinsa yake a gurin Sayyada hidima yake mata da jikinsa da aljihunsa Kullum sai ya fita da ita ya koya mata mota kuma duk wannan kusancin nasu bai sanya ko d'an yatsanta ya rike ba shidai yanzu burunsa ta kula dashi ta kaunaceshi.....
Wani abun idan yanayi mata har tausayi yake bata ta tabbata kauna da son da Sule ke mata Sadam bayayi mata kwatankwacinsa itace kawai take haukanta a kansa.
Sadam! tsakaninsa da Harira babu yabo babu fallasa yana sakin jikinsa da ita amma ba sosai ba kuma ko da wasa baya gigin ra'bar jikinta da sunan wani abu tausayi take bashi ba sha'awa ba shiyasa duk wani nauyi dake kansa yake kokarin saukewa.
Yau kwanansu Arbain da shida a yau din ne kuma Sadam ya shirya musu tafiya zuwa *Dabi* ya sanar da Jatau! yace"Ai babu komai ya kawo tsaraba mai yawa ya bashi shima Sadam din ya hada da tashi tsarabar kana suka dauki hanyar shida Iyalinsa.
*LNI DA YAYA SADAM
BINTA UMAR ABBALE*
48
Sadam da Harira sai suka zama kamar wasu surukai gwara itama tana sakewa dashi shi kam ko magana zaiyi da ita baya iya kallon fuskarsa haka kawai yake jin kunyar hada ido da yarinyar yana ganin kamar bai kyauta mata ba.....Ko a cikin mota ma hakance ta kasance zaman kurame sukeyi sai dai jefe jefi ya 'karbi babyn daga hannunta yana taya ta raino haka suka isa *Dabi* kamar wasu surukan juna.
Baba Ladi da Marka suna zaune a tsakar gida kamar yanda suka saba hira sukeyi sukaji Sallama dukaninsu sai da gabansu ya fadi jin muryar Sadam! suka kurawa kofa ido aikuwa shine ya shigo kafadarsa sa'be da yarinyarsa sai Harira dake bayansa.
Da sauri Baba Ladi tace"Innalillahi wa ina ilaihi raji'un! jama'a wa nake gani kamar Soja"! Baba Marka ta saki kad'in Lagwanin da takeyi tana neman mikewa ta shige dakin don tayi masifar tsorata da ganinsa.
Baba Ladi ce mai dan dauriya amma itama in zaka tona zuciyarta zaka ga tashin hankali daurewa kawai tayi ba arce ba.
Ya 'Karaso gefan tabarmar da take zaune tayi saurin dauke kafafunta tana binsa da kallo."Wai da gaske ne Sadam Soja nake gani a gabana ko kuma dai aljani ne ya siffantu da siffarsa." A rude take maganar
Miskilin murnushinsa yayi ya kalleta sosai kana yace."Ni ne ba wani ba wato ku da kun dauka na mutu ko to inanan a raye kuma ina rayuwa cikin hukuncin Ubangiji."
Da jin muryarsa ta sake fitowa tar! sai suka dauki kabbara da fadin "Allahu akubar! ashe d'an nan yana raye a duniya bai mutu ba.''! Sai suka fashe da kuka mara masali......
Ya dinga kallonsu ya kasa ce musu komai Harira tace" Baba ku daina kuka Allah zaku godewa daya bayyana muku shi cikin aminci da yardarsa."
Baba Ladi tace"Bari 'yar nan ai dole ne muyi kuka kai jama'a!!! Ashe yaron nan na raye muka dinga kasafi da kayansa muka tsawwalawa matarsa sai tayi aure ashe dai Sayyada tafi mu gaskiya da take fadin baka mutu ba kana raye alhamdullahi tunda Allah ya bayyana mana kai Allah mungode maka."
Sadam! yace''Kwarai duk naji labarin abunda ya faru daga bakin ita Sayyadar wacce ta zama silar dawo dani cikin tunani na ......Tiryan tiryan ya zayyana musu abubuwan da suka faru tun bayan da 'Yan fashin nan suka buga masa bunduga ya fada musu irin hallacin da su Jatau sukayi masa da yanda akayi ya auri Harira har ya haihu da ita.
Tun kafin ya karasa suke kuka suna fadin"Kai Jama'a! Ubangiji dai babu yanda baya iya tsara lamarinsa ashe yaro nan rabo ne ya kaishi can wani gari rabon haihuwa 'ya mace me albarka kai Allah mungode maka daka bamu ikon daukar wannan kaddara." Cikin damuwa da alhini suke maganar.....Yace."Hakane nima na shiga rudu da naji labarin abunda ya faru bayan na dawo nutsuwa ta kuma alhamdullihi na dauki kaddararta hannu bibbiyu wannan itace matata Harira wannan kuma itace yarinyata SuwaibatulAsalamiya."
Baba ta fashe da kuka tana katse hawaye take fad'in"Sannu 'yar nan sannu mungode da karamci gaskiya iyayenki mutanan kwarai ne hakika ke da iyayenki kun cancanci a yaba muku saboda kunyi sadaukarwa."
Harira tace"Babu komai baba muma Allah ne ya bamu ikon mu taimakeshi.".
Baba Marka ta kar'bi yarinyar tana fadin"Babu shakka Ladi kin samu takwara kai masha Allahu gatanan kamarsu daya da ubanta."
Ladi ta sanya hannu ta karbi yarinyar tana washe baki da fadin''Kai amma soja baka ta'ba burgeni irin haka ba ashe takwara akayi mun nagode kwarai Allah kuma ya rayata."
Suka amsa da ''ameen." Baba Marka ta mike da fadin"Bari inje in samu Talle ya yanko kaji sai ayi musu miya kai alhamdullahi Allah ne abun godiya........Tana daf da futa Amina ta shigo ciki Baba marka tace"Amina yau muna cikin farin ciki yanzu nake shirin zuwa Kofar ku in sanar muku da cewar Sadam ya dawo gida da iyalinshi ashe yana raye bai mutu ba."
Amina gabanta ya fadi tace"Baba wace iriyar magana ce wannan."?
Tace"Ke! yar nan shiga ciki idonki ya gane miki Sadam na raye bai mutu ba."
Jiki a sanyaye ta wuce ciki da sauri itafa bata so hakaba gaskiya don lokacin da suka tabbatar da ya mutu a lokacin taji hankalinta ya kwanta dama fatanta ita da Sayyadar kowa ya rasa kullum burinta taji labarin ya saki Sayyada sai kuma labarin mutuwarsa ya riskesu taji babu dadi sosai saboda tana sonsa amma data tuna da cewar Sayyada zata shiga damuwa sai taji dadi ta kwantar da hankalinta ta tsayar da miji cikin samarinta yanzu haka saura wata uku daurin auranta.......Da ta san Sadam din bai mutu ba da babu abunda zai sanya ta amince da wani.
Tana shiga idonta suka hade da nasa gabanta ya fadi ashe dai da gaske baba take.
Kuka ta fashe dashi taje ta gurfana gabansa "Ya Sadam! ashe baka mutu ba kana raye."?
Yace." Gashi kuwa kin ganni da raina da lafiya ta."
Tace"Wallahi dukannimu munyi tsammanin ka mutu mun shiga tashin hankali da damuwa daga karshe muka barwa Allah."
Yace"Dama shine ya tsara komai shi yafi kamata a barwa lamarin gashi da yayi nufin dawowa ta na dawo gareku."
Ta kalli Harira tana fadin"Ya Sadam wannan wacece.'? Yace"Matata ce Harira wannan babyn kuma 'yata ce da muka haifa tare."
Amina taji wani irin rashin dadi a ranta sunkuyar da kanta tayi 'kasa gurun yayi tsit baba Ladidi na can tana hura wuta.
Amina ta dago kanta tana kallon Sadam dake magana da Harira tana shayar da Asalamiya nono
Tace"Ya Sadam! gwara da kayi auranka wallahi domin nan ma Sayyada ba'aja wani dogon zango ba da mutuwarka tayi aure abunta."
Yace."Duk na sani Amina." Tace"Kasan wanda ta aura.'? Yace"A'a! Tace"Yaya Sulaiman fa ta aura."!
Gabansa ya dinga wani irin bugu! ya 'kurawa Amina ido yana kallonta le'bansa sai rawa yake.
Tace"Kayi hakuri idan na 'bata maka rai Amma maganata gaskiya ce Sayyada Ya Sule ta aura Dan uwanka."
"Amina me kike fad'a haka? kina nufin kice mun Sayyada d'an uwana na jini take aure a halin yanzu."?
" Wallahi kuwa Ya Sadam! babu yanda ba'ayi da ita ba kan ta hakura dashi ta'ki amincewa a cewarta ai shine yafi cancanta data aura tunda shine dan uwanka kuma idan ba mantawa kayi ba kasan dama can kamar akwai soyayya da shakuwa a tsakaninsu shiyasa shima baiyi wani jayayya ba ya amince da bukatarta.
Ido jawur! yace"Kina nufin kice mun itace ta tilasta dole sai anyi aure tsakaninta da Sule."?
Tace"Kwarai kuwa Ya Sadam!
Sunkuyar da kanshi kasa yayi gumi na tsatstsafo masa saman goshinsa......Babu shakka biri yayi kama da mutum ashe Sayyada dama Sule take aure? Sule dan uwansa Uwa daya uba daya!! Mamaki yake mutuka dama ashe Sule zai iya auran matarshi? koda yake ai dama akwai soyayya a tsakaninsu zuciyarsa ke fada masa haka, karkayi mamaki dama can Sayyada tafi son Sule a kanka ko ka manta irin yanda take fifita shi da jin maganarsa sau nawa kana gargadinta akansa tana bujirewa hakan ba abun mamaki bane dan sun auri juna wanda dama tuntuni suna son junansu...........Baba Ladi ta karaso gurin tana dariya da fad'in"Yau dai na rasa wane irin farin ciki xanyi wallahi kai alhamdullahi Allah nagode maka daka bayyana mun jikana cikin kwanciyar hankali."
Ganin sai surutu take babu wanda ya amsa sai ta kalli fuskokinsu taga kowa na tare da alhini mussaman Sadam da idanunsa sukayi wani irin ja.!
A sanyaye tace"Lafiya Soja."? Ya dago manya manyan idanunsa da suka jirkice da tashin hankali da 'bacin rai yace."Baba ban ta'ba tsammanin bakwa sona ba sai yau na gazgata saboda haka zan koma inda na fito.
Sai ta fashe da kuka tana fyace majina da gefan zaninta "Nasan wannan ja'irar ta fada maka abunda ke da akwai to kayi hakuri ba laifinmu bane kaddarace yanzu ba gashi kai kayi aure ka haihu ba to ita tanan har yanzu bata haihuwa ba sai sanya ido muke kuma da yaya ma muka shawo kanta har ta hakura ta zauna a dakinta......Kar kaga laifin Sayyada da 'dan uwanka Sulaiman mune muka matsa da lallai sai anyi auransu.
Hannu ya d'aga mata rai a'bace yace." Kuka matsa kodai suka matsa da lallai sai kun daura musu aure nasan fa komai na kuma san duk abunda yake faruwa in banda al'kawarin Baba Shatu dake kaina da babu abunda zai hanaku aurawa Sule Sayyada kafin ni saboda dama can kunfi sonsa dani wane irin bambamci ne bakwa nuna min akansa."
Baba ta dinga kuka tana fad'in"Tsaya ka saurareni soja duk abun ba na tashin hankali bane kayiwa al'amarin kyakykyawar fahinta kaddarace wacce ta riga fata mun san dai kana raye a duniya babu abunda zai sanya mu mu yanke wannan hukuncin."
"Kinga Baba babu abunda zan tsaya na saurara da maganarki." Ya kalli Harira dake share hawaye yace."Maza goya min 'yata ki tashi mu tafi."' Harira takiyin abunda ya sanyata kuka take tana tausayin 'yar tsohuwar........Wata iriyar tsawa ya buga mata......Ta mike a gigice har 'yar na shirin faduwa Yace"Idan kika yar min da yarinya sai ranki ya 'baci goya ta mu 'kara gaba." Harira ta hau goya Asalamiyya tana kuka......Baba Ladi ta mike tsaye tana gyara daurin zaninta take fad'in"Haba d'an nan komai fa a sannu ake yinsa ka daina razana musu yarinya wai shin kai mai yasa baka da fahimta ne? ba kaga irin sakamakon da Allah yayi maka ba a lokaci guda ya baka mace mai ladabi kyakkyawa wacce tafi Sayyadar ma sannan kuma ga kyauta ya baka wacce ba kowa yake bawa ba shine kuma kake 'kokarin butulce masa.
Jin abunda baba ke fad'a kan Harira ya sanya ransa ya sake dugunzuma! wai Mace wacce tafi Sayyada komai da komai dan dai kawai basu san irin yanda yake son Sayyada bane a cikin ranshi yana ma tunanin idan babu ita rayuwarsa ta tashi daga aiki shiyasa ma ya yanke hukuncin komawa inda ya fito gwara yaje ya cigaba da rayuwa dasu Jatau! yafi masa alkairi.
Hanya suka kama zasu futa Baba da Amina suka biyo bayansu suna basu hakuri Baba Ladi dai sai kuka take yau sun ga samu da rashi yanzu take da ta sanin hukuncin da suka yanke kan auran Sule da Sayyada da sun san Sadam din na raye da babu abunda zai sanya su yanke wannan d'anyan hukuncin.
Kawu Tanko da Baba Marka sukayi turus ganin Sadam! na jan kwatinsu ga kuma Baba Ladi da Amina na biye dasu a baya suna rokonsu da suyi hakuri.
Kawu Tanko yace"Me nake gani hakane na tawo da farin cikina kuma nazo na riski wani ba'kon lamari kai Sadam ina zakaje da jakar kaya kuma."?
Yace"Kawu Tanko zan koma inda na fito kawai saboda yanda nake jin zuciyata na zafi a halin yanzu ba zan iya zama cikin wannan gari ba."
Kawu Tanko ya rike akwatin yana rarrashinsa hade da fada masa kalamai masu sanyi gami da nuna masa misalai, Jikinsa yayi sanyi amma fa duk da haka bayajin zai iya cigaba da zama cikin garin gwara kawai ya kara gaba.
Baba Ladi tace"Ga ja'iranan munafukar da ta fesa masa abunda ke faruwa ni naso ya huta tukkuna sai a sanar masa da komai cikin nutsuwa amma Amina ta fada masa ina can ina iza wuta."
Tanko ya kai hannu ya rankwashi Amina tayi saurin kaucewa Simi simi ta shige kofarsu.....Yace."Munafukar yarinyar kawai.
Sadam yace"Kawu ku daina ganin laifin Amina gaskiya ce wato da ba don Amina ta fad'a mun ga wanda Sayyada ta aura da sai dai ku cigaba da 'boye mun maganar auran Sayyada na sani tuntuni ita da kanta ta shaida mun amma saboda tsabar munafurci nata ai bata fada mun waye mijin nata ba."
Kawu Tanko yace."Ka daiyi hakuri Sadam ansan anshiga huruminka dukaninmu mun aikata kuskure kuma kasan d'an adam ajizi ne kayi hakuri ka koma ciki in dai ka daukeni a matsayin uba."
Sadam! yayi jim! yana nazari daga bisani ya juya da nufin komawa gidan duk suka rufa masa baya.
Kawu Tanko Baba Ladi Baba Marka kai harda Hariran haka suka dinga bawa Sadam baki sai hakuri suke bashi da kawo musu misalai wanda shi kawai jinsu yakeyi babu abunda zai sanya shi ya dauki wannan 'kauli da ba'adin nasu.........Yace."Kawu magana ta wuce fa a gurina kamar yanda kuke cewa inyi hakuri in dauki kaddara to nayi na dauki kaddara na barwa Sule Sayyada har abadah ta haramta a gareni tunda ta zama matar dan uwana, a da dai nayi alkawarin kan zanyi shari'a daku dashi wanda ya aure ta saboda an shiga hakkina to yanzu kuma na janye magana ta Sule dan uwana ne na jini ba zan iya sharia dashi ba sannan ina so in shaida muku cewar kun daura auran Sule da Sayyada kan tsari tunda dama can bata da iddah a kaina har muka rabu ban santa a matsayin 'ya mace ba, saboda haka magana ta wuce a gurina ni zan cigaba da zama da iyalina Sule ya cigaba da rike Sayyada a matsayin matarshi."
Jikinsu yayi sanyi da jin irin hukumcin da Sadam din ya yanke.....Baba Ladi ta share hawaye da fadin"Allah Sarki Sadam! kayi hakuri kaji ko Allah baiyi zakayi dogon zama da Sayyada ba sai dai ni naji dadi da farin ciki da Allah ya musanya maka da mace tagari irin wannan yarinya Allah ya baku zaman lafiya."
Suka amsa da ameen harshi Sadam din wanda yake ta faman nanata kalmar innalilihi