Showing 123001 words to 126000 words out of 142497 words

Chapter 42 - NI DA YAYA SADAM Complete Document by Binta Umar Abbale.txt

09 Dec 2024

50483

dauko su Jatau domin a gudanar da komai a gabansu dama suna waya da Munkaila ya shaida masa abunda ke faruwa dan haka a shirye ya tarar dasu abinci kawai sukaci suka dauko hanya gabadayansu.
NI DA YAYA SADAM


*BINTA UMAR ABBALE*


51
Tar'ba mai kyau da muhimanci su Abbah sukayi wa su Jatau, aka kewayesu da abubuwan ci da sha Harira ta dinga murnar ganin iyayenta suma sukayi murnar ganinta ta murmure tayi kyau sosai tamkar ba d'iyarsu Harira ba hakika sun yaba da dattijan taka tasu Abbah suma su Abbah din sun Yaba da karamcinsu.......Sosai Sadam yayi musu hidima ya basu kulawa mutuka ya jima tare dasu kafin ya kira Habu yazo ya daukeshi suka nufi brcak din nasu wanda anan zadu gudanar da walimar da suka shirya masa.


Captain Saleh da ire-irensa sun ke'be kansu guri guda suna 'kananun surutai dan babu wanda ya tunkari inda su Sadam din suke kowa yaja zugarsa shi kuwa Sadam sam basa gabansa dasu da mai daure musu gindi wato General Abbah Jaddah kenan wanda shima a zahiri ya nuna bakin cikinsa a fili dangane da bayyanuwar Sadam din dan ko da Sadam din ya shiga ofis dinsa su gaisa da kyar ya amsa gaisuwarsa Sadam ya 'ka kansa ya fito ba tare da wata damuwa ba.


Tsaf! suka shirya komai yanda ya kamata anata sanarwa a kafafen yad'a labarai rundunar sojojin najeria ta shirya gangami na murnar bayyanuwar dan uwansu abokin aikinsu da a da ake zargi 'yan bunduga dad'i sun kashe ashe yana nan raye bayan tsayin shakara da wanni abun Allah ya bayyanashi saboda haka suka shirya masa walima domin taya shi murna dawowa cikin danginsa.


Ranar da zasu gudanar da Walimar sosai guri ya soma cika da manya mutane dan su Abbah da abokanansa ma duk suna can Jatau da iyalansa ma suna can sai shi uban gayyar da bai tafi ba yana shiryawa.


Captain Habu ya kirashi a waya da fadin''Gashinan cikin mota zai zo daukarshi yace."Babu matsala yana kintsawa ne.


Bayan gama wayarsu da Habu Sai ya kira Sayyada ya shaida mata cewar ta shirya zasu tafi walima tare kamar tace masa ba za taje ba sai wata zuciyar tace kije kawai amma karki bashi fuska ki nuna masa ajinki.....Ta shirya tsaf cikin duguwar rigar ta shadda wanda taji uban stone work a jiki ba tayi wani make up amma ta zuba wani bala'in kyau hallintun girmanta sun bayyana sosai mussaman kirjinta da yayi masifar cika kwankwansonta ya sake budewa sosai kai duk inda cikakkiyar mace ta kai Sayyada ta kai.....Turare ta fesa mara kamshi sosai kana ta yafa mayafi ta nemi guri ta zauna tana jiran kiranshi.


To can 'bangaran ma Sadam da kanshi ya shirya harira saboda yasan cikin manyan mutane zasu shiga maza da mata sam baya so a raina masa mata ya shiryata tsaf cikin wani material mai uban kyau da tsada ya kuma tayata shirya baby Asalamiyya sosai sukayi masa kyau ya kasa hakura ya rungumesu gabadaya ya fiddo da wayarshi ya dinga daukarsu a hoto yana sanye da kayansa na soja ya kafa fecing cap mai dauke da sunansa a sama da kuma matsayinsa sosai Sukayi kyau mutuka Sadam har ya dinga mamakin kyawun yarinyar ashe dan bata samu kulawa bane.


Wayarsa ya kira Sayyada cike da shan toka yace"Idan kin shirya ki fito muna jiranki." Ba tace masa komai ba ta kashe wayar ranta a 'bace wannan shan kunun da yake in zaiyi mata magana yana 'bata mata rai amma babu komai zata bishi in taga wani abu da baiyi mata sai ta dawo gida abunta.


A kan idonsa Captain Habu ya shigo da mota cikin gidan.


Sai da ya tabbatar da ya shige sashen Sadam din sannan ya fito daga ma'boyarsa.


Hannusa rike da wani abu kamar almakashi ya nufi inda motar take ya kwanta karkashinta kome yake oho! sauri sauri yayi abunda zaiyi 'karkashin motar ya fito hannunsa duk ba'kin mai da datti! da sauri ya bar gurin.


Suka fito cikin walwala da farin ciki Captain Saleh sai daukarsa a hoto yake cikin iyalinsa shi kuma sai murmushi yake mai yafi wannan dad'i lokaci guda Allah yayi masa tagomashi matansa biyu gashi duk 'yan kananun yara Allah kenan babu yanda baya tsara lamarinsa.


Captain Habu ya bude masa motar yana fad'in"Ka fara shiga kafin su shigo." Ya sunkuya da niyyar shiga motar sai kuma ya fasa ya tsaya yana nazari kafin yace."Habu nayi mantuwa ina zuwa dan Allah.


Kafin Habu yace.Wani abu tuni ya juya da sauri ya nufi sashensa.....Suka bishi da kallo har ya 'kurema ganinsu.


'Karamar bundigarsa ya dauko ya gyarata sosai ya tabbatar da lafiyar ta kana ya zuba mata bullet ya zura a aljihu ya fito a gaggauce ya shiga motar Captain Habu ya zauna gurin tuki yaja motar suka fita mai gadi na d'aga masu hannu.


Sai da suka hau titi sosai Habu yace."Jama'a fa sun cika gurin nan har da wanda bakayi tsammani ba ga 'yan jarida kamar me." Sadam! Yace."Kasan wasu mutanan fa ba wai Walimar ce ts kawo su ba wasu munafurci ne amma dai kun sanya matakan tsaro sosai a gurin ko."!?


Captain Habu yace."Kwarai kam su Captin Salim da Nura suna bakin kofar shiga insha Allah babu matsala."


Motar tayi shiru babu wanda ya sake magana Sadam daurewa kawai kusancinsa da Sayyada ya haifar masa da matsananciyar kasala daurewa yake shiyasa ma bai kalli inda take ba itama tun gaisuwar data ratsa a tsakaninsu babu wani abu da ya sake ratsawa.Ballanta Harira kuma da ta zama 'yar kallo duk da dare ne hakan bai hanata kallon gari ba.


"Ya Salam!!! suka fad'a a tare lokacin da motar ta cije tsakiyar titi ta'kiyin gaba ballanta baya.....Sadam yace." Ya akayi ka dauko motar da kan bata da cikkakiyar lafiya."


Habu yace."Haba dai motar nan 'kalau take wallahi kamar baka san sharrin karfe ba, bari na gani." Sai ya bude motar ya fito Sadam ya dan ja tsaki hade da duba agogon hannunsa tara da wani abu na dare abunda akace takwas da rabi za'a gudanar da komai amma har tara ta wuce yasan jama'a nacan na jiranshi.....A hankali ya kai idonsa kan baby Asalamiyya dake kusur-kusur hannun mamanta Ya shafa fuskarta hade da manna mata kiss a goshi ya kalli Harira da fad'in"Ki bata nono kar ta fara wannan kukan nata." Tace"To." Ta fara kokarin ciro nonon shi kuma ya dauke kansa yaki kallon Sayyada ballanta ya kula ta.......Captain Habu ya shigo motar yana fadin wata 'kusa ce ta kwance amma na murd'eta."!


Ya kunna motar yana mirza sitiyarin a guje! ta fafara!!!!! Sai suka gigice dukanunsu suna Salati! Sadam! ya dinga fad'in"Habu kashe motar nan bata da lafiya innalilihi wa'ina ilaihi raji'un!!


Habu nata kokarin ganin ya tsayar da motar abun ya gagara kamar ma sake kwanceta yake sai tafiya take da 'karfin gaske........! "Innalihi wa'ina ilahi raji'un!!! Abunda suka iya fad'a kenan lokacin da motar tayi 'yar hantsile ta hantsila can 'karkashin wani rami! motar ta jirkice kasanta ya fara ci da wuta......! Cike da jarumta ya doke!! murfin motar dake kusa dashi ta bude a gigice ya jawo Sayyada dake sume ya sanya hannu ya jawo Harira da rabin jikinta ke ci da wuta itama ba tasan halin da take ciki ba baby Asalamiyya babu abunda ya sameta cikin hukuncin Ubangiji sai tsanyara uban kuka take....Ya dauketa had'e da rungumeta kam ya zagaye mazaunin Captain Habu kanshi a kife kan sitiyarin motar ya sanya hannu a d'imauce ya dago shi kansa ya fashe sai zubar jini yake..... Jiki na kyarma ya zaro shi daga motar ya aje gefe guda....." Innalilhi wa'ina ilaihi raji'un!!! kalmar da yake ambata kenan wacce take amsa kuwwa! hakan ya janyo Hankalinsu Captain Saleh suka durfafo gurun dama suna la'be duk abunda ya faru a idonsu......Suna isowa gurin sai suka soma harbi! a guje! ya samu mafaka ya boye tare da 'yarshi bundugarsa ya fito da ita ya gyara yayi lamfo yana jin sawun tafiyarsu kusa dashi ya saita bundugarsa ya sakar masa harshashi a gwiwa a take Saleh ya fad'i a gurun yana kururuwa bundugar dake hannunsa tayi nata gurin Sadam ya sake sakar masa harsashi a daya gwiwar tashi kafin kice kwabo Saleh ya fice daga hayyacinsa jini sai tsartuwa yake a gurin sai da yaga ya daina motsi sannan ya fito.


Sukuwa sauran abokan Saleh na jin ihunsa suka durfafo gurin ganinshi kwance magashin yan jini na tsartuwa a kafafunsa sai al'amarin ya basu tsoro! sai kawai suka yanke shawarar guduwa take suka juya da gudu zasu bar gurin Sadam ya fito ya saita bundugarsa ya sakar musu bullet a kafafunsu a take suka fad'i a gurin dama su uku ne......Ya karasa inda suke Asalamiyya na kafadarshi sai faman ihu takeyi yana zuwa ya fara haskasu da wayarshi suna kwance sai ihu! suke da rike kafa........Lokacin da idanunsa sukayi masa tozali! da d'an uwansa Sule a cikin mutanan da ya harba sai da ya kusa fad'uwa saboda furgici! yace."Sulaiman me ya had'aka da aikin soja? meye ala'karka dasu Captain Saleh."? Wasu shaharrun hawaye suka shiga gudana a kumatun Sule bakin na rawa yace."Karshen tika tiki tik!!! tabbas 'karya fure take bata 'yaya." Da fad'in wannan magana tashi sai ya zube a gurin alamun babu rai a tattare dashi,


Sadam ya gigice mutuka ya dinga salati yana kiran sunan Allah wai shin meke faruwa ne! Wayarshi ya ciro ya kira Abbah da sauran wadanda zasu bashi taimako ya fada musu halin da ake ciki kana ya koma gurin iyalinsa yana duddubasu lokacin Sayyada ta dawo hayyacinta sosai take kuka ganin yanda wuta ta cinye rabin tufafin dake jikin Harira abunka da material cinyoyinta duk sun kone!! kuka take tana kiran sunan Allah hade da kiran sunan Harira.!


😟
Allah ka rabamu da aikata aikin dana sani Allah ka rabamu da sharrin zuciya amin.


Kuyi manage sai a hankali zamu hadu daku anjima insha Allah.


*Littafin na
NI DA YAYA SADAM


*BINTA UMAR ABBALE*


52
Cikin tsananin tashin hankali su Abbah suka iso gurin shi da jama'ar sa da sauran sojojin dake gurin.........Ganin Harira kwance cikin wani irin hali ya sanya hawaye ya wanke fuskokin d'an uwanta Munkaila, Jatau kuwa sai salati yake yana nanata kalamar innalilihi wa'ina ilaihi raji'un ba tare da bata lokaci ba motocin daukar marasa lafiya suka iso gurun duk aka kwashe su Captain Saleh da Sulaiman dake a sume bai san wanda yake kansa ba.


Mota guda aka dauki Harira da Captain Habu duka aka nufi asibiti dasu wannan al'amarin da ya faru yayi masifar tashin hankan kalin duk wani mai imani.


A daran Allah yayiwa Harira rasuwa Shi kuma Captain Habu yana can sai abunda hali yayi Saleh da Sule sun farfad'o sai zare ido suke yi ga tsananin azabah da ta damezu kafafunsu a sama an nade da bandaji sai ihu suke.


Mutuwar Harira tayi masifar girgixa Sadam! zubewa yayi a gurin ya sanya kuka hawaye wani na bin wani bakinsa sai kyarma yake ya tunkari dakin da take.


Innalillahi wa'ina ilahi raji'un. Wuta tayiwa Harira Illah dan bayan kafafunta data ci har fuskarta sai da ta 'kone gefan kanta duk ya kwaye sam ba zaka taba cewa ita bace duk kamaninta sun sauya.....amma duk da hakan Sadam rungume gawar yayi yana wani irin kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro. Har su Jatau ma suka fishi tawakkali ya zamana ma sune suke bashi hakuri suma dai kukan zucci kawai sukeyi....."Allah ya jikanki matata Allah yasa aljanna makomarki Harira ni mijinki na yafe miki insha Allahu kece uwar gidana cikin aljannar firdausi na yafe miki babu abunda kikayi min na yafe miki." Abunda yake ta fada kenan, duk wanda yake gurin sai da ya zubar da hawaye tsabar tausayi......Da kyar likitoci suka fito dashi daga dakin aka rirrikeshi mahaifinsa ya zaunar dashi yana rarrashinsa da kalamai masu sanyi da kyar dai ya daina zubar da hawayen ya dinga bin mutane da kallo.


Sayyada kam kamar zautacciya haka ta zama sai bawa su Mamma labari take yanda al'amarin ya faru tana kuka wiwi! su kuma suna tausarta tace"Mammah ashe dai dan adam ba a bakin komai yake ba duba ki gani muna tare da juna ashe kwananta ya kare bamu sani ba kai Innalilhi wa'ina ilaihi raji'u!sai ta fashe da kuka tana fadin"Harira Allah ya jikanki da gafara ya raya abunda kika bari."


Haka suka kwana cikin asibitin rayukansu duk babu dad'i da asubah Suka dauki gawar Harira aka nufi gidan abba da ita ko takan Sule basu bi ba domin kowa yayi mamakin abunda ya aikata wai har a hada baki da kai a cuci dan uwanka Allah ya rufa asiri.


Bayan an kai Harira ne gidan yayi shiru kowa na kukan zucci dukaninsu carbi ne a hannunsu suna ja mai gadi ya shigo yayi musu gaisuwa kana yace"Alhaji da ba don kar ace nayi gulma ba da sai na fadi wata magana.


Alhaji Auwal yace ka fadi maganar ka babu komai


Yace."A gaskiya Alhaji Sulaiman shine silar faruwar wannan al'amarin dan da idona na ganshi karkashin motar Sadam din ya kwanto wani abu cikin sauri sauri ya fita daga gidan jikinsa duk ya 'baci!


Alhaji Auwal yace."Sam banyi mamaki ba da jin maganarka saboda tun sanda na nunawa Sulaiman cewar dole sai ya hakura da Sayyada naga ya 'kwafe wani abu a ranshi nasan zai kulla wani abun da bai dace ba, gashi yayi hankalinsa ya kwanta anyi asarar rai! ko wannan hakkin ma ba zai barshi ba sannan abun shima ya shafe shi tunda dai gashi can a kwance rai a hannun Allah idan ya mutu cikin wannan halin me zai fadawa Allah, rayuwace ai."


Aunty Luba dai na gefe guda da carbi a hannunta sai share hawaye take ita kuwa Mammah har ta gaji da kukan ta hakura carbi take ja tana nadamar haihuwar Sulaiman a rayuwarta wai shine ya aikatawa Sadam haka duk dan mace! Allah ya wadaran Sule abunda yayi kuma zai gani insha Allahu."


Baba Ladi da Marka sun sha kuka da jin mutuwar Harira baba Ladi fadi take''Yarinyar arziki ta mutu kai Ubangiji Allah ya gafartawa 'yar nan.....Hankalinsu bai kara tashi ba sai da suka sauka a gidan Mammah ta tabbatar musu da cewar Sulaiman ne silar faruwar komai......Baba Ladi kuka wiwi tana tsinewa Sule da fad'in zuciyarsa irin ta fir'auna ce har su gama zamansu ba zasuje inda yake ba shima gwara ya mutu rayuwarsa sam bata da amfani.


Sadam! yana waje tare da abokanshi suna jajanta masa da yi masa ta'aziyya dan har manema labarai sai da suka zo gurin makokin duk dan suji karin bayani daga bakinsu ko kallonsu baiyi ba ballanta ya tsaya ya sauraresu.


Koda aka kira General AbdulSalam aka sanar masa da abunda su Saleh sukayi ya shiga rudu da tashin hankali ya kuma tausayawa Sadam! sosai.....Ya kira General Abbah Jadda a waya suka dinga muyasar yawo dashi General AbdulSalam na nunawa Abbah Jaddah da sanya hannunsa komai ya faru shi kuma sai kare kansa yake, kaca! kaca! suka rabu dan sosai General AbdulSalam ya bude masa wuta kuma ya dauki alwashin daga ya dawo to shima ya kiyayi kansa dan sai ya sanar da gwamnati da sanya hannunsa a cikin 'barnar da take afkuwa a brckk din.


Sosai yayiwa Sadam ta'aziyya kana ya sake tausarsa da fad'in''Kada faruwan hakan ta sanya yace ya janye kudirinsa kan aikinsa yayi hakuri ya dauki kaddara ya koma bakin aiki." Bai san Sadam din faruwar wannan al'amarin sai yaji tamkar an sake 'kara masa son aikin a cikin ranshi nan ya tabbatar masa da cewar har yanzu yanan kan aikinshi bakin rai bakin fama!


Sai bayan Sadakar bakwai ne su Jatau suka shirya tafiya Abbah ya nuna musu cewar suyi hakuri mana su bari ayi sadakar ar'bain Jatau! yace."Gwara dai su koma saboda sun baro harkokinsu kuma dai zamansu ba zai sanya yarinya ta dawo ba zasu cigaba dayi mata addua kafin su riski inda take.


Abbah yaji 'kudirinsu sai ya kyalesu ya had'a musu shatara ta arziki haka Mammah turamen atampopi ta basu masu kyau da tsada, Sadam yace"Duk wani abu da ya kasance mallakinsa ya bar musu yace da Munkaila wannan gidan da suka gina tare ya bar masa nasa bangaran halak malam kuma insha Allahu zumuncin yanzu suka fara da juna.....Jatau yace."Anya Sadam abun baiyi yawa ba kuwa? akwai abubuwanka da yawa da kudi duk kace bar mana gaskiya yayi yawa yace."Baba komai da kasani indai nawa ne to wallahi na baku shi halak malak aini kun gama yi mun komai a duniya bani da abunda zan iya biyanku dashi.......Baba Ladi tace'"Babu shakka maganarka gaskiya ce Sadam! wad'annan mutanan 'yan halak ne da kai damu bamu da abunda zamu iya biyansu dashi sai dai addua kuma ba za mu taba mancewa dasu ba har abadah.


Kafin su Jatau su tafi sai da suka ruwa rana dasu Abbah sunce dole sai sunje asibiti sun duba Sulaiman Abbah yace bai yarda wani nashi yaje asibiti duba Sule ba Jatau ya dinga rarrashinsa da kalamai masu sanyi har dai zuciyar Abbah tayi sanyi yace su shirya suje gabadayansu.


Halin da suka ga Sule a ciki yayi masifar basu tsoro kwana goma kacal da faruwar al'amarin ya lalace yayi wata shegiyar rama ga kafarshi guda sai da aka cire aka bar masa daya domin dai wacce aka cire din harsashi ya ragargata cireta shine yafi alkairi


Ganinsu ya sanya shi fashewa da kuka kukan nadama ya dinga rokon Sadam ya gafarta masa Sadam kam kallonsa kawai yake yana mamakin halin adam.....Jatau da Munkaila sukayi tsam! suna sake nazarta fuskar Sulaiman din suna so su tuno inda suka santa....Shima Sulaiman din ganin suna kallonsa sai yasha jinin jikinsa Cikin kunya da nadama yace."Ni ne wallahi ku daina tamtama nine wannan ba'kon da yaje garinku ku daina tunani.......Ni dan uwana Sadam ne uwa daya uba daya nayi nadamar abunda na aikata a gareshi.


Jatau da Munkaila suka shiga mamaki ashe dama dan uwansa ne a lokacin ya nuna bai sanshi ba.....Abbah ya nemi sanin abunda ya faru nan Jatau ya fad'a masa abunda ya wuce da zuwan Sulaiman din gurinsu.


Alhaji Auwal ya sake jin tsanar Sule cikin ranshi shima yanzu nadamar haihuwarsa yake dan kaf rayuwarsa bai ta'ba ganin mai bakar zuciya irin ta Sule ba.


Haka kowa ya dinga mamakin lamarin Lallai ashe dama Sule tuntuni yasan Sadam

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login