Showing 39001 words to 42000 words out of 142497 words

Chapter 14 - NI DA YAYA SADAM Complete Document by Binta Umar Abbale.txt

09 Dec 2024

50464

mifici ta dauka tana masa firfita duk kuwa da cewar akwai fanka a dakin idanunta kurrr gurin ciwon tana mamakin jinin da ya dinga tsiyaya d'azu.


Idanunta taji suna lumshewa alamun bacci na soma ya dauketa dama tasan za'a rina mutukar ta ci bashin bacci to duk inda ya kamata sai tayi take jin dadi.....A hankali ta ra'ba gefansa ta kwanta tana kallon fuskarsa, 'Kare masa kallo take sosai tana gazgata maganar mutane inda suke cewa duk family nasu ya fisu kyau sai dai su nuna masa hasken fata, ita yanzu kalar fatarshi ma burgeta take, ta tsurawa karamin bakinsa ido wanda wani bakin gashi me gazarzar! ya kewaye lebunansa lumshe ido tayi gabanta yana faduwa....Ta sanya hannu a hankali ta shafo kirjinsa! tare dashi suka sauke ajiyar zuciya, cike da tsoro ta zare hannunta gabanta na dukan uku uku!!! Sadam! bai san wainar da take toyawa ba kawai ajiyar zuciyar ce tazo a lokacin......minti biyu ta sake d'ora hannunta kan kirjinsa, Ta lumshe idonta tsigar jikinta sai tashi takeyi......Haka bacci mai nauyi ya dauketa.


Idonsa ya bude a hankali sai ya ganta kwance a gefansa hannunta a kirjinsa ya jima yana kallon hannunta ya kasa daukewa....Gyaran murya yayi tayi saurin bude idonta a firgice ta mike zaune! kauda kansa yayi ya mi'ke zaune itama mikewa tayi ta nufi toilet ta wanke baki ta fito....Tana kallonsa yana kokarin sakkowa daga bed din tana jin tsoron tunkararsa bata son hayaniya da hargagi ta lura shi kuma komai lalura baya fasa halinsa.


Yazo ya wuce ta ya shiga bandakin alwala ya daura bayan ya wanke bakinsa ya fito fuska a daure Sallah ya tayar yana idarwa akayi knocking din kofar...kallonsa tayi ya watsa mata harara! tayi kasa da kanta.....Mikewa yayi yaje ya bude kofar....Baban gida ne da kwandon abinci anan ya dakatar dashi ya karbi kwandon abincin Baban gida ya dubashi yana masa sannu da jiki ya amsa babu wata cikakkiyar walwala kisin Sayyada ne kawai ke sasakar ransa ta riga ta gama nuna masa matsayinsa ta nuna masa tafi kaunar Sulaiman a kansa ba tun yau ba dama ya fahimci akwai wata a 'kasa a tsakaninsu."


Ajiye kwandon abincin yayi bai ce mata komai ba ya haye gadon wayarsa ya dauka yana dubawa.....Ganin lokacin shan maganinsa na nema ya wuce tace"Ko na had'a maka abincin kaci kasha magani." Idab dotse na magana to shima zaiyi ya shareta yana duba waya......Ta'be baki tayi duk yana kallonta ta 'kasan idonsa ya girgiza kai fuskarsa a daure Yace."Ke!!! ba cewa nayi idan Mammah tazo ki bita ba ke wace irin mara zuciya ce ne."!? taji wani sagewar jiki!! da jin abinda ya fad'a ido ta zuba masa tana kallo Cikin shan mur! yace."Da daddare ba sai na sake yi miki magana tana zuwa sahunki a likkafa ki bi bayanta."! Shiru tayi masa bakin ciki na sasakar zuciyarta......Sunanan zaune akayi Nocking din kofar a karo na biyu." Tashi kije ki bud'e."Ya fad'a hankalinsa kan waya, kamar kar ta tashi sai ta mike taje ta bud'e kofar suka had'a ido da ita tana sanye da ingilish wear riga da seket tayi rolling da karamin mayafi fuskar nan taci mai tayi make up kamar hauka ido ta sanya masa gashi sai kace aljannu hannu rike da key na mota da karamar pose Halima 'Yar gidan General AbdulSalam Shugaban sojojin Najera kenan....Wani matsiyacin kallo ta watsa Sayyada ta tsartar mata da yawu" Bani hanya na wuce."!! tafad'i cikin izgili da d'agawa! Sayyada bata san sanda ta kauce daga hanya ba tana kallo ta shige ta barta a tsaye a gurin.


Jingina jikinta tayi a bango tana kallon ikon Allah.....Halima ce ta isa inda yake ta d'ora kanta a gefan kirjinsa tana shashshekar kuka!" Sweetheart abinda ya same ka kenan! wayyo na shiga uku ina can Gombe gurun bikin kawata Captain Saleh ya sanar dani halin da ake ciki me yasa kai baka fad'a min ba." A marairace take maganar." Har yanzu kanta na damtsen hannunsa na hagu......Motsi yayi yana so ya tashi fuskarsa da akwai alamun sassauci yace."Halima abun alkairi shi ake shela ba irin wannan ba dama kin tsaya a inda kike kin gama shagalin bukinki."


"A gaskiya Sweetheart baka sona ta yaya zan iya xama a wani gurin kana cikin wannan hali karfa ka manta da cewar kaine za'bin raina farin cikin zuciyata."


Sayyada taji wani irin gumi mai d'umi!! na tsiyaya a jikinta....Ido jawur take kallonsu shi kuma sai murmushi yake kamar bashi ne masifaffan nan ba.....Inda suke ta nufa ta tsaya kansa"Baiwar Allah daga ina? kin shigowa mutane daki babu sallama babu neman iso sai kace wata kafura ai kafuran ma suna sallama da Hi ko makamancin hak"


Wani wawan kallo Halima kewa Sayyada cikin nuna ke wacece tace"Ke! ni kike fad'awa wannan maganar."? Sayyada tace"Baiwar Allah ba magana bace gyara ne nayi miki domin naga alamar kina yin abu irin na marasa hankali."


"Kutttt!!!! Sweetheart wannan wace jahilar yarinya ce take min maganar banza yanzu zan sanya a daureta wallahi."


Ya kalli Sayyada yana wani cin mur!!! "Ke bar gurun nan kinzo kin tsaya kan mutane saboda rashin tarbiya."


"Wallahi ba zan bar gurin nan ba.." Tafad'a cikin fad'awar gaba ga dukanin alamu matar nan nada matsayi mai karfi a gurinsa......"Wai Sweetheart wannan yarinyar a ina ka samo ta dagani 'yar kauye ce duba da yanda take maganar *He da He* ." Dariya ce ta kusa kufce masa yanda Halima ta fad'i maganar sharri ne kawai amma Sayyada bata irin wannan maganar ta *He da he* "Zaki bar gurin nan ko sai na sanya yanzu anzo anyi waje dake." Halima ce tayi wannan magana cikin hayaniya....Sayyada ta gyara tsayuwarta har da rike karfen gado tace"Sai dai in kece zaki fita daga dakin nan wallahi baki isa ki tambaye shi matsayina a gurinsa."!


Halima ta kalleshi wanda ya zuba musu ido kawai yana kallo Tace"Sweetheart bana son munafurci shin kai ma ka soma tara mata irin nasu Saleh." Yace."Ke bana son hauka malama wannan kanwata ce ita." Sayyada tace"Meye zaka 'boye mata kace mata ni matarka ce in yaso kome zatayi sai tayi."


Halima ta mike tsaye a zabure! tana fad'in"Da gaske take wannan maganar data fad'a."!!!!
'Karamin tsaki yaja "Ke! kinga nayi kama da wanda zai auri wannan 'yar 'kauyen Halima."! Tace." Nima dai haka na gani Sweetheart. " Sai ta koma ta zauna tana yiwa Sayyada kallon banza....Sayyada takaici ya turnuketa lallai Yaya Sadam! ita yake dizgawa gaban mutane......A zuciye tace"Ke Karuwa tashi ki fita daga d'akin nan ko kuma in tara miki jama'a."!! Halima tace"Ke!!! ni kike kira da karuwa don kutumar ubanki kin san waye ubana kuwa."!?? Sayyada tace"Oho! miki ko waye ubanki bai dame ni ba." A zafafe! Halima ta tsinka mata mari! ta sha'ke mata wuya ga hijab a jikinta......."Ke!!! Halima saketa."! yafada cikin karfin murya."Sweetheart kana jin abinda take cewa ko."!? "Eh naji saketa." Halima ta saketa tana huci!! Sayyada ta karkad'e hijab dinta ko a jikinta itama sai huci take....."Sayyada fita daga d'akin nan."!! cikin tsawa! yayi maganar da nufin tozarta mutum. gwiwowinta duk sukayi sanyi ta kalleshi ya ware mata manya manya idonsa wanda sai zaiyi rashin mutunci yake bud'esu."Ko bakiji abinda nace ba Fita a d'akin nan."!!! Wani 'karfin zuciya yazo mata tace"Ko baka fad'a zan fita yanzu." 'Kofar fita ta nufa zuciyarta na wata iriyar tafarfarsa..........!


13/6/202
NI DA YAYA SADAM


NA
BINTA UMAR ABBALE


20*
Da sauri ta bude kofa ta fice daga dakin zuciyarta na wata irinyar tafarfasa rarraba ido take a harabar gurin....Kai tsaye kawai sai ta nufi 'katon gate d'in da yake cike da sojoji ko tsoro ba taji burinta kawai ta fice daga bracck d'in bata ta'ba tsammanin Sadam! zaiyi mata irin wannan wulakancin ba, tana tafiya tana share hawayen bakin ciki tayi tayi ta tsayar da hawayen abun ya fassakara dole ta kyalesu suna zuba


Bayan fitar ta daga d'akin saboda ya san wautarta sai ya dauki wayarsa ya kira d'aya daga cikin sojojin dake bakin gate din yace."Za suga wata yarinya ta fito 'yar kimanin shekaru 15 ko kasa da haka tana sanye da atamfa blue kar su barta ta fita......Aikuwa hakane ya faru Sayyada na isa suka tare mata hanya tayi tayi su bude mata suka 'ki kawai sai ta nemi gurin bakin gate din ta sanya kukan bakin ciki.


Lokacin da yake wayar Halima ta sha'ka da yawa bayan ya gama wayar tace"Wai menene idan ta fita da zaka damu nifa jikina ya soma bani akwai wani abu a tsakanika da yarinyar nan wallahi." Yace."Babu wani abu a tsakaninmu na fad'a miki kanwata ce karki damu." Dake ta saba da wannan dad'in bakin nasa sai ta warware tace"Ya maganar auranmu to." ? kallon shashasha! yayi mata yace."Ashe baki aje wannan maganar a gefe ba kenanan."! Halima ta tunzura tana huci! tace"Wallahi ba zan ajiye maganar nan ba har sai na cimma burina akanka kome zakayi min zan jure.''Shiru yayi mata kawai.....Ta cigaba da cewa"Yanzu ka bakaji kunyar fada min wannan maganar ba? wane irin sone ban nuna maka ba zakace na ajiye maganar aura a tsakanina da kai insha Allahu kamar anyi an gama."


Kallon mahaukaciya kawai yake mata yo shi wannan ko da matan duniya zasu kare baya ta'ba jin xai iya auranta......Wayarshi ce tayi kara yana dubawa yaga Mu'azu daya daga cikin sojojin bakin gate yace."Yallabai yarinyar nan fa gata ta zauna tana turjiya kan hanya kuka kawai takeyi."


Yaji wani iri a jikinsa jin abinda Mu'azu yace."Please Mu'azu kayi kokarin kawo min ita dakin dana ke kwance." Mu'azu yace."Okey insha Allah."


Babu irin rarrashin da Mu'azu baiyi mata ba amma fafur ta'ki binsa ita dole sai sun bude mata kofa ta fita.....Mu'azu ya kara kiran numbarsa a karo na biyu Yace."Kayi kokari ka bata wayar kace zamuyi magana." Nan ma Sayyada ta'ki kar'bar wayar zuwa yanzu ta daina kukan sai dai bakin ciki dake cin zuciyarta.....Koda Mu'azu ya sanar dashi cewar ta'ki kar'bar wayar sai hankalinsa ya tashi har ya yunkura zai tashi da nufi yaje ya dawo da ita sai zuciyarsa ta raya masa cewar kar yaje ya rarrasheta mutuncinsa zai zube a gurinta....Ya koma ya kwanta fuska a cud'e!......Halima kam tana ganin hankalinsa ya tashi kan yarinyar sai ta fashe da kuka ta mike a zafafe take farfad'a masa ba'kaken maganganu....Wanda suka sanya ya buga mata muguwar tsawar da ta sanya ta d'ibi takalmanta a hannu ta fice daga dakin......Hankali a tashe ta nufi bakin gate d'in ganin Sayyada a tsugune ya sanya ta isa inda take ba tare da tace mata komai ba ta mikar da ita tana girgiza kafadarta ''Ki fad'a min gaskiya meye alakarki da Sadam! Dazu kinyi wata magana wacce ta sanya jikina yayi sanyi don girman Allah karkiji tsorona." Sayyada tace"A kan me zanji tsoronki Ci kike bani ko sha ko kuma aljanna kike rabawa da zanji tsoranki gaskiyar magana shine Ni Sayyada matar Sadam! ce yau kwananmu shida da daurin aure."


Halima ta silale a gurin ta fad'i ji take kamar ta d'ora hannu aka tayi ta kurma ihu!!! gumi duk ya jikata....."Ni Sadam! zai yaudara jama'a!?? Hawaye ne suka soma kwarya a fuskarta


Sayyada ta saki baki tana kallonta wai kuka take kan d'a namiji lallai bata da hankali....To ganin Halima na hawaye sai hankalin sojojin nan ya tashi sanin wacece halima yasa suka fara gutsi tsoma a tsakaninsu suma sai yanzu suka fahimci cewar ashe Sayyada itace amaryar Sadam! da yaje can kauye aka aura masa lallai Sadam bai kyauta ba kuma a zahirin gaskiya ya yaudari Halima domin ta sakankance da cewar zai aureta amma ya yaudareta.


Mikewa tayi a jigace ta gyara yafan mayafinta ta dauko pose dinta ta koma dakin da Sadam din yake......Ya mike tsaye idanunsa a kan kofa yana so yaga shigowar yarinyar halima ta fado dakin yanda ya ganta a Jigace sai da gabansa ya fad'i yasan hali bata da hankali yanzu zatayi masa hauka sai ya daure fuska tamau! yana kallonta yace."Ba cewa nayi ki fice ki bar min daki ba tunda kema b......Bai karasa ba ta daga masa hannu "Rufe min baki bakin algungumi azzalimi! Sai ya saki baki yana kallonta tace" Nan ka fada min cewar yarinyar kanwarka har da rantsewa yanzu kuma ina fita ita ta tabbatar min da cewar matarka ce yau kwana shida da daura muku aure Sadam! ni zaka yaudara? ashe dama xaka iya yi min haka a irin kauna da son da nakeyi maka."? tana hawaye take maganar....Tausayi ta bashi yace."Kinga Karki dauka wannan auran zaiyi tasiri sam! bana son yarinyar kawai umarnin iyaye na nabi amma ke kanki kin san yarinyar ba sa'ar aurena bace idan kin kwantar da hankali ki nan gaba kadan zata zama 'yar aikin gidanki."


"Ai na daina yarda da wad'anannan kalaman naka na yaudara wallahi ka bani mamaki Sadam! ashe kai mayaudari ne ban sani ba."


Shan kunu yayi yace."Idan kin san ba'kaken maganganu zaki fad'a min to sawunki a likkafa ki kama hanya ki fice idan raina ya 'baci ba zakiji dad'i ba."


Kallonsa tayi taga yaci kunu tasan halin rashin mutumcinsa idan abun ya motsa masa duk da bashi da lafiya zai iya dukanta.....Tace"Idan ni 'yar halak ce daga yau na rabu da kai." tasa kai ta fice daga d'akin....Kafad'a ya d'aga alamun abun bai dameshi ba ya isa bakin kofar ya tsaya yana kallon dambarwar dake faruwa tsakanin Sayyada dasu Mu'azu.......Ana budewa Halima gate Sayyada tayi waje da gudu Halima ta fice da motarta. Yaga lokacin da ta fita daga bracck din sai ya koma dakin a gaggauce ya kira lamar Habu. Yana dagawa yace."Habu duk abinda kake ka aje yanzu yanzu yarinyar nan ta fita ban san ina ta nufa ba." Captain Habu yace."Wace yarinyar wai."! Cikin kufula yace."Sayyada fa nake nufi."!! Habu ya kashe waya hankali tashi ya fito daga ofis gate aka bude masa ya fita can ya hangota tana tafiya gefab titi ya bi bayanta da sauri Sayyada najin sahun mutum a bayanta ta waiwaya sai taga Habu ne ranta ya 'baci itafa ba xata koma ba ta riga tayi alkawari....To da yake tafiyar ba daya bace Captain Habu ya iske gabanta ya tare yace"Sayyada ina zakije yanzu wa kika sani ? kika fito kan titi kina tafiya."! Ta share hawayen dake zubo mata tace"Zan koma *Dabi* ne." Akan wane dalili Sayyada me yayi xafi."!? Sai ta fashe da kuka ta tsuguna a gurin.....Tausayi ta bashi ya dinga rarrashinta sai da yaga tayi shiru sannan yace."Sadam! ne yayi miki laifi ko."? Daga kai tayi yace."Kiyi hakuri da abokina yana da zafi ne amma kuma mutum ya iya zama dashi mutum ne mai saukin hali ki taso mu koma yanzu haka shine ya turo in daukeki."


Tace"YaYa Habu ni bazan koma ba tun jiya yake min masifa motsi kadan fad'a da kyara da hantara me nayi masa kawai don yaga ina sonsa shine fa ya koroni daga dakin saboda budurwarsa.


Cike da mamaki! yace.''Budurwarsa kamar yaya." ? tace"Wata Halima ce tazo shine ta zageni shima yace na fita." Captain Habu ya girgiza kai yasan za'a rina wai an saci zanin mahaukaciya Halima tazo kenan to Allah ya rufa asiri....."Kiyi hakuri Sayyada zan nuna masa kuskuransa har yaushe ne xaka fifita budurwa kan matarka ta sinna kiyi hakuri kinji ko ki zama jarumar mace mai juriya kan komai."


Captain Habu yana da mutuncinta a idonta shine dalilin da yasa kawai ta hakura ta bishi suka koma cikin barikin sojojin.


Yana hango zuwansu ya koma cikin dakin hankalinsa ya kwanta shi kanshi ya rasa gane meke damunsa kan yarinyar yana kishinta mutuka haushin abinda tayi masa kan Sulaiman ne yasa ya koreta......Sai da suka hau sama suka fad'o da Habu sannan suka rabu Captain Habu ya nuna masa abinda yake bai dace ba ko babu aure a tsakaninsa da Sayyada kanwarsa ce bai kamata ya fifita wata akan ta ba, da yaga Habun ya dauki zafi sai ya shareshi ya nemi guri ya kwanta har da lumshe ido....Captain Habu ya kalli Sayyada yace"Idan yayi miki wani abu da bai gamsheki ba to ki sanar dani ai shima yana da na gaba dashi kuma a dokar aikinmu bamu yarda da cuzgunawa matanmu ba." Jin abinda Habu din yake fada mata yasa ya bude ido yana harararsa yace."Zaka zugata ne tayi min rashin kunya dama ba ganin mutuncina takeyi ba."! Habu yace."Ni ba zugata nake ba ina koya mata daburu ne da yanda zata kwaci kanta a hannunka saboda na lura kai din ka fiye son kanka da yawa." Miskilin murmushi yayi ya mayar da ido ya rufe....Captain Habu yace."Me kike so na siyo miki in anjima." Tace."Babu komai."! yace."ki bari zan siyo miki shawarma! kici abinki karki bashi." murmushi tayi tana mamakin karamci da kyautayi irin na Habu.


Bayan Captain Habu ya fita sai dakin yayi shuru Sayyada tayi kici kici da fuska taki kallon inda yake kwance tayi alkawarin ai ta daina rawar jiki a kansa ballanta har ya samu damar wulakantata.


Bude munafukan idanunsa yayi yana kallonta amma sai ka rantse da Allah cewar ba ita yake kallo ba......Yanzu tausayi take bashi sosai gyaran murya yayi wai ko zata juyo ta kalleshi yaga ko da wasa bata juyo ba ya cika da mamaki kwarai! sai ya fara d'an tari! a hankali a hankali to wannan karon ta d'an juyo amma babu walwala a fuskarta da dane da tuni taje inda yake tana rawar jiki sai yaga motsi ba tayi ba a inda take........dauke ma kanta tayi ta dora kafafunta duka kan kujera ta juya masa baya.


"Ke!!!." Ya ambata tasan da ita yake sai ta shareshi "Ko bakya ji ne."!? Sayyada ta ci kunu ta'ki amsawa ballanta ta kalleshi idan ya gaji ya kira sunanta.


" Sayyada." Ya ambaci sunanta cikin kasalalliyar murya...Kallonsa tayi tana zum'bura baki! "Kina ji ina magana kinyi banza ko."? " To ai ba sunana "Ke! ba." "Okey naji ina maganina."? " Nima ban san inda yake ba." Tafada tare da dauke kanta........! shiru yayi mata ya koma ya kwanta dama dan dai yayi mata magana ne yasan ba lokacin shan magani bane.


Dake dakin da tv sai ta kuna kallo ta rage vollom Wani indian film take kallo hankalinta ya dauke kan film din ana soyayya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login