Showing 72001 words to 75000 words out of 142497 words

Chapter 25 - NI DA YAYA SADAM Complete Document by Binta Umar Abbale.txt

09 Dec 2024

50467

ala'ka dake a tsakaninku.''? Girgiza kai tayi yace." Na soma zarginki Sayyada kamar yanda nake zargin Sule kema naso zarginki dashi saboda haka zan daukeki daga gidanan gwara zamanki a bracck ya fi mun kwanciyar hankali." Ya karashe maganar cikin 'kunar zuciya da d'acin rai! tare da yun'kurowar kishi mai tsanani daga cikin ranshi.


Tana kuka take cewa"Kana zargina ne da d'an uwanka uwa d'aya uba d'aya kome? Ni ba 'yar iska bace kuma ko zanyi zina ba zanyi da d'an uwanka d'an uw....... kafin ta karasa Ya gwa'be mata baki da bayan hannunsa.


Yana huci! yace."Idan zarginki nake dan ubanki! ba kece kika janyo ba? tun yaushe na rabaki da Sule? amma saboda ke baki da mutunci kin'ki ji kina abinda kike so kuna fakaicewa da cewar 'yan uwane kuna cutata to zanyi maganinku daga ke harshi sai na dauki mataki mai tsauri a kanku.


Kuka take sosai hannunta damke da bakinta da daka! Yace."Don ubanki idan na daukeki daga gidan sai inga ta kafar da zaki samu damar ganin Sulaiman din har ya baki wata wayar."


Hannunsa yasa ya murd'e hannunta ya kwace wayar ya cire kafafunsa daga tsakaninta ya fita ya barta a dakin.......Sayyada tayi kwance a dakin tana wani irin kuka mai tsuma zuciya shin wai ya zatayi ne da wannan mutumin mai bakar zuciyar tsiya ya zatayi ne! wane mataki zata dauka a kansa ? kuka take taba burgima a tsakar dakin tare da kiran sunayen su Baba Ladi da Marka domin a ganinta sune suka cuceta suka hada ta aure da mugu Sadam!
[6/23, 1:22 PM] Bintu Zama yayi kan kujera yana dudduba wayar numbar uku kacal ya gani a ciki daga tashi sai ta Lubabatu data kanwarta Asiya ganin bai ga numbar Sulaiman din a cikin wayar ba ya sanya hankalinsa ya kwanta amma dai duk da haka dole ne ya tauna aya don tsakuwa taji tsoro.


Mi'kewa yayi da wayar a hannunsa ya fita harabar gidan cikin sa'a yana fita motar Sulaiman din ta shigo gidan sai yaja tunda ya tsaya hade da harde hannunsa a kirji har Sulaiman din ya karaso inda yake.......hannu ya mika masa su gaisa Sulaiman ya kama hanya zai wuce ciki Sadam ya dakatar dashi ta hanyar fad'in" Jima na."


Sulaiman yaja ya tsaya yana masa wani irun duba.


Hannu ya sanya a aljuhun wandonshi ya ciro wayar ya mika masa .


Sulaiman ya sanya ido yana kallon wayar nan ya gane wayar da ya siyawa Sayyada ce.


Sadam yace."Kar'bi wayarka mungode bana bukatar Sayyada ta rike waya yanzu kuma ko ina bukata ba kaine kake da hurumin siya mata ba nine."


Sulaiman yace."Haba Sadam! laifi ne ashe don na siyawa Sayyada waya gani nayi zata d'ebe mata kewa kuma tare na siya musu da Lubabatu."


Sadam! yace."Ta fad'a min tare ka siya musu da Luba kawai ni bana son ta rike waya yanzu sai nan da wani lokaci lokacin da tayi hankali sosai tasan abunda takeyi tukkuna."


Sulaiman yayi murmushi cikin nuna komai ba komai ba yace."Naji bani da hurumin siya mata waya amma kar ka manta da cewar Sayyada kanwata ce ta jini bayan haka kuma gata matarka ni a ganina ba komai bane don na siyawa Lubabatu waya itama na siya mata kuma kafin in bata wayar nan sai da na gargade kan ban yarda da shige shige ba ku daukar numbobin mutane barkatai na siya mata ne kawai domin ta d'ebe mata kewa idan zargi kake to ka duba wayar da kyau na tabbata da cewar ba zaka samu numbar ta ba."


Sadam yayi shiru yana nazarin maganar Sulaiman din jikinsa yayi sanyi sai Sulen ya bashi tausayi Yace."Kasan wani abu ne."? Sulaiman yace."Sai ka fad'a.'' Yace."Wallahi ina tsoron sharrin waya domin duk wani abu na lalacewa yanzu ya koma kanta shiyasa bana so Sayyada ta rike waya yanzu kasanta da shegan rawar kan tsiya."


Sule ya shafa sajensa as'usel yace."Kana da gaskiya anan to ai zaka iya rike wayar idan an kwana biyu ka lura da nutsuwar yarinyar sai ka bata."


Yace."Ina tunanin haka zanyi." Sule yace."Yawwa ka kawo maslaha yanzu mu shiga ci ko." Tare suka nufi sashen iyayen nasu kamar basu ta'ba samun sa'bani ba.....Hajiya Fatsima taji dad'in wannan kusancin nasu ta saki jiki sosai tana musu addua Allah yasa zumuncinsu ya d'ore.......Tare suka ci abinci suka 'koshi Sadam! hankalinsa na can kan Sayyada yana tunanin ya barta tana kuka ko wane hali take ciki oho ga lokacin cin abinci ya wuce bata shigo ba.....Mikewa yayi ya nufi sashen nasa.


Inda ya barta nan take kwance taci kuka ta koshi bacci ya dauketa....Ya jima a tsaye a kanta yana kallonta kafin ya dauketa cak! ya kaita bed ya kwantar


Yana ajiyeta ta bude ido mikewa tayi zumbur tana kallonsa sai shsheka takeyi tana sauke ajiyar zuciya alamu sun nuna taci kuka ta koshi


Ya kalleta hade da had'e fuskarsa yace."Ke! tashi malama ki cire min riga kinbi kin jika min da majina da hawaye har da yawun bacci."!


Ko kallonsa ba tayi ba ta tashi a zuciye! ta cire jallabiyar zir!! ta dawo babu ko pant ballanta briziyya ko a jikinta ta jefa masa rigarsa a jiki tana zumbura baki ta wuce wardrobe ta soma burkito kayanta.


Sai da ya kusa hauka ganinta a haka ya dinga wata iriyar makyarkyatar jiki yana tsuma!! wai shin me yake jira da yarinyar nan ne? tana masa iskanci yanda take so wato shi ta jefowa riga a fuska lallai xai ci ubanta yanxu.


Ta sunkuya tana duba kaya ya dauketa cak! cilla kafafu ta shiga yi tana buge buge ya jefa ta kan bed din yana kokarin kwabe rigar jikinsa ta mike a guje ta dirgo daga gado hanyar fita ta kama jikinta na makyarkyata ya bita dauri ya cafko ta sake makata yayi da gadon ya karasa cire rigarsa yana kokarin ya afka kanta ta mike tsaye ya afka kan katifar a sukwane ya mike zaune ya ganta lokon gado tana tsalle nonowanta na buga tsalle wannan idan ya daki wannan sai ya daki wannan gasu a tsaye car car dasu.....Sai ya kara gigicewa yayi kanta a gigice ta kwallara 'kara ta tureshi a ya fad'i kan katifar rigarsa da ya cire ita ta dauka a hannunta a guje tayi waje tana tafiya tana zura rigar dake jallabiya ce ba tada wahalar sakawa idanunta ya sauka kan hijab dinta dake kan kujera ta dauka ta zurma a guje ta bude kofa ta fita wanda yayi dai-dai da fitowarsa daga dakin yaga fitarta window ya nufa da saurin ya dage labule.


Yana kallonta ta tsaya ta goge fuskarta kana ta wuce sashen Mammah tana waiwayen bayanta.


'Kwafa yayi ya koma ya zauna yana fad'in"Zaki dawo ne yarinya sai kin raina kanki.


Koda ta isa sashen babu kowa a palon don Suleiman ma bayan fitar Sadam din fita yayi bayan ya duba matarshi ita kuma Mammah na kicin suna aikin abincin dare da Mai aikinta.....Sai ta shige gurin aunty Luba nan ma ta tarar da ita tana wanka ta zauna kasan kafet tare da janyo kayan abincin dake gefe ta hada tana ci tana tunanin abinda tayi wa Sadam! ta dauki alkawarin haka zata dinga yi masa shima yaji d'aci a ranshi kamar yanda yake 'kunsa mata bacin rai.


Aunty Luba ta fito daga wanka taga Sayyada na cin abinci tace"Sayyada yau har mun gaji da cigiyarki tun safe baki shigo ba."


Tace."Wallahi aunty Luba yau yinin bacci nayi kinga ma na tashi da yunwa shiyasa ina zuwa ban saurari komai ba sai abinci."


Aunty Luba ta hau dariya tace"Ai dole mybe tun jiya rabonki da abinci." Tace"Kamar kin sani aunty da safe ba wani abincin kirki naci ba bacci na fizgata."


Aunty Luba ta shirya jikinta ta zauna suna hira haka 'yan uwanta suka dinga sallama suna shigowa Sayyada ta mi'ke ta basu guri domun su samu sakewa.


Kicin tabi Mammah aka cigaba da aikin abincin da ita.


Sai bayan sun kammala komai sannan Mammah tace Sayyada ta d'ibi nasu ta kai musu sashensu.


Anan idanun Sayyada suka raina fata bata son ta koma ta tarar dashi domin tasan karonsu ba zaiyi kyau ba, babu yanda ta iya hakanan ta dauki kwamdon abincin ta wuce sashen dashi.


Shiru da ta shiga ta dinga komai salau salau! domin batasan ta inda zai fito ba har ta ajiye a bincin ta fito bata ji motsinsa hakan ya nuna mata cewar baya d'akin, ajiyar zuciya ta dinga saukewa tana godewa Allah.


Sadam kam bayan fitar Sayyada da minti ashirin ya shirya ya nufi barkin nasu....Part dinshi wanda aka mallaka masa ya sanya aka gyara masa babu abunda babu na jin dadin rayuwa kayan abinci kawai ya sanya aka kawo masa.....Sai da ya tabbatar da komai ya dai-dai ta sannan ya nufo gida domin daukar Sayyada yau yayi alkawarin dauketa daga gidan gabakidaya gwara da ita dashi su koma barkin da zama hakan shine kwanciyar hankalinaa.
*NI DA YAYA SADAM


BINTA UMAR ABBALE*


31


Duk suna zaune a palo ya shigo da sallama a bakinsa....Kai tsaye ya karasa kujerar da mahaifinsa ke zaune hannu ya mika masa sukayi musabah da juna ya mikawa sulaiman hannu shima suka gaisa kana ya nemi guri ya zauna yana gaishe da Mahaifiyar tasu.....Tace"Duka yau ina ka shiga ne tun dazu Sayyada ta kai maka abinci gurunku bakanan." Yace."Can bracck dinmu naje yau d'in nan nake so mu koma can da zama."


Sayyada dake zaune kasan kafet ta dago kanta da sauri tana kallonsa dama tun sanda ya shigo ta sunkuyar da kanta gabanta na faduwa.


Alhaji Auwal yace."Amma dai kai kad'ai zaka koma banda Sayyada ko."? Yace."Abbah har da ita mana meye amfanin komawa ta bracck ita na nan."


Alhaji Auwal yayi shiru yana jimanta abun.....Mammah tace"Ni kuwa da zakaji shawara kayi zamanka cikin gidanku meye amfanin zuwa bariki da zama idan kuma dole ne to kai sai kaje ka zauna ka bar Sayyadar anan."


Yace."Mammah ba zai yiwu ba akwai dalili shiyasa kikaji na yanke wannan shawarar." Sayyada ta fashe da kuka tana fad'in"Abbah ka sa baki mana ni wallahi bana son zama barikin sojojin nan duk arna ne kafurai basu san komai ba sai iskanci."


Sadam! ya buga mata tsawa tare da fadin"Ashe nima arne ne kuma d'an iska tunda kin jam'u waye ya fad'a miki babu musulmai a gurun."


Tana kuka take cewa"Ni dai ba zan bika ba kawai ka barni gaban iyaye na yafi min kwanciyar hankali."


Sadam! ya tsura mata idonsa da suka rine da 'bacin rai mugun haushi yarinyar take bashi taurin kanta yayi yawa.


Alhaji Auwal yayi gyaran murya a nutse ya kalli Sadam! din yace."Soja ban ban katse hanzarinka ba duk dai ban san dalilinka na dauke Sayyada da gabanmu ba amma ni ina neman alfarma ka bar Sayyada a gabanmu zuwa nan da wani lokaci idan ta kara wayo da iya mu'amula da jama'a sai ka dauketa ka kaita wannan guri a yanzu to zata wahala tunda babu wanda ta sani guri ne da ya tara jinsin mutane daban daban! zata shiga kadaici da damuwa abunda bama fata kenan ya faru tunda kai kasan da cewar amana ce a hannunmu saboda haka nake neman wannan alfarma a gurunka ka bari ko zaka dauketa ka kaita bariki ba yanzu ba tukkuna."


Sadam! Ranshi ya 'baci sosai yaci buri yau din nan zai kawar da kwadayinsa kan yarinyar a inda yake ganin babu me takura masa ya shirya tsaf ya zai zubar da abunda yake damunsa shekara da shekaru amma shine zasuyi masa haka saboda rashin adalci amma babu komai zai amince da bukatarsu zuwa kuwa to sai randa ya ga dama zai zo musu......Sulaiman ya kalla yana girgixa kai shi kansa yana daya daga cikin dalilan da ya sanya shi tunanin dauke Sayyada daga gidan....Wannan magana da mahaifinsa yayi itace ta ruguza komai dole tilas idan ya cika shi dan halak ne ya hi umarninsu.


Yace."Shikkenan Abbah yanda kace haka za'ayi ni zan tattara komai nawa zan koma can da zama na dinga zuwa duk week end."


Alhji Auwal yace."Naji dadi da amincewarka Soja Allah ya dafa maka ya shige maka gaba dukanin al'amuranka." Ya amsa da "Ameen." Yana kokarin mikewa Sayyada tace"Abbah ina da magana."


Alhaji Auwal yace."To ki fad'a mana gaki ga mijinki kan ya tafi." Tace"Abbah kace ya barni na cigaba da makaranta kaji."


Alhaji Auwal yace."Alhamdullahi wallahi na jima ina wannan shawarar cikin raina Abubuwa suke sanya na manta da ita Sadam! zauna muyi magana da kai mai muhimanci."


Kamar yace." Babu lokaci sai kawai ya zauna ransa a dagule Sayyada ta gama dashi tunda ta sanya ana turke shi kan abunda baiyi niyya ba ita sai ya ba'kanta mata rai.


Alhaji Auwal yace."Sanin kanka yanzu ilimi shine ginshi'kin komai shine kuma cika maki na jin dad'in rayuwa mussaman ilimin d'iya mace yakan taimaka mata ta hanyoyi da dama yau ko iyalinta ta ilimantar ta wadatu kai ma ka wadatu kuma zata iya shiga ko ina tayi mu'amula da mutane albarkacin wannan ilimi da take dashi walau na boko ko na muhammadiya kasan duka suna tafiya dai-dai ne saboda haka nake so ka janye wannan kudiri naka kan Sayyada ka amince ta cigaba da karatu domin ta inganta rayuwarta."


Sadam! yace."Abbah ba ra'ayina bane iyalina zirga zirga tare da cud'anya da maxa da sunan karatu shiyasa tun farko nace ku bari tayi karatun kafin ku daura aure kuka ki amincewa ni ina da kishin kaina shine dalilin da ya sanya ma bana da ra'ayin matata tace makaranta alhalin da aurena akanta to amma tunda duk kun rinjayeni da maganar karatu na janye Allah ya bata me amfani."


Yanda ya fad'i maganar zaka tabbatar da cewar ba a san ransa ya amince ba dan dai an fi karfinsa ne kawai ya amince......Alhaji Auwal yace."To alhamdullahi naji dadi daka fahimce ni Kuma insha Allahu ilimin sayyada zai amfani al'umma da yawa kaida ka kwantar da hankalinka akan lamarin ka bamu goyon baya dari bisa dari in Allah ya yarda zakayi alfahari da ilimin data samu."


Yace."Shikkenan Abbah ai magana ta wuce kuma Allah ya shige mana gaba." Duk suka amsa da "ameen." Har Sule dake zaune a gefe wanda tunda aka soma maganar baice komai ba saboda tsananin iya taku irin nasa.


Sadam! na fita Mammah tace"Ki tashi kije kuyi sallama mana nasan yanzu dai bai isa ya bar gidan ba."


Sayyada najin abinda mammah tace jikinta yayi sanyi ita ba abin tayi mata musu ba......Simi-simi! ta mi'ke ta nufi sashen nasa.


Ya shirya kayansa tsaf! a cikin jaka yana shirin fitowa ta shigo kanta ta sunkuyar 'kasa tana wasa da hannunta.


Yace."Me kika shigo yi kuma."!? A sanyaye tace."Mammah tace nazo muyi sallama."


Yace."Bana bukatar yin sallama dake malama yi waje ki bawa mutane guri 'yar kauye kawai."!!


Tayi saurin dago kanta tana kallonsa.....Ta tsani ya kirata da 'yar kauye.....Manya manyan idanunsa ya zare mata duka yace."Ko bakiji abinda nace ba ne."? Cikin zafin rai! Ta juya zata fita Yace."Jimana."! Jiyowa tayi tana kallonsa idanunta duk sun cika da ruwan hawaye.


Yace."Bukatarki ta biya ko."? Shiru tayi tana so ta fahimci inda maganarsa tasa ta dosa....Yace."Burunki ya cika kin sanya Abbah ya tursasani amincewa da abinda banyi niyya ba....Zaki cigaba da karatu amma ki sani ba a son raina ba tursasani akayi saboda ba ra'ayina bane hakan....Ki kiyaye da kyau! ke matar aurece idan kin watsar da martabarki kanki kika cuta bani ba kuma duk namijin da kikayi abota dashi Allah ya isa ban yafe ba."


Sayyada ta kalleshi da sauri yace."Ki kalleni da kyau! kina so kiyi ilimi domin a daina kiranki da 'yar kauye ko? kina so ki zama wayayyiya domin ki kamo wayewar 'yan matana to komai abunki ba zaki kama 'kafar budurwata Halima ba yarinyar da nake shirin aura kenan.......Kina tunanin dan kin'ki bina bracck dinmu damuwa zanyi? kece a cikin matsala ko yanzu naje zan tarar da Halima na jirana saboda haka ni naji dad'i ma da Abbah yace kiyi zamanki gida.......Sannan magana ta takarshe dake shine kizo ki kwashe tsummokaranki daga nan zan rufe dakina."


Dama tun kafin ya karasa take share hawaye wanda tayi tayi ta hansu zubowa abun ya fassakara dole ta barsu suna zuba tana gogewa ta rasa ma abunda zata ce masa sai ta kama hanya zata fita ya buga mata razananniyar tsawar da ta sanya ta juyo da sauri tana kallonasa.


Jajayen idonsa ne a kanta yace."Bakiji abinda nace bane kizo ki washe tsumokaranki bana bukatar komai naki a dakina."


Jikinta a sanyaye tazo ta wuce ta gabanshi ta shiga uwar dakin nashi kai tsaye wardrobe dinsa ta nufa ta bude gefan da kayanta suke ta fara tattarowa tana zubasu cikin jaka tanayi tana kuka da sha'kar hanci takaicin duniya duk ya isheta ji take kamar tace masa ta hakura da karatun zata bishi sai wata zuciyar tace kawai ki kyaleshi idan ya gama fushin zai hakura ke dai kawai ki mai da hankalinki kan karatunki ya daina kiranki da 'yar kauye.


Sai da ta kwashe kayanta kaf sannan ta zuge zuf din jakar ta dauka da kyar tazo ta wuce shi ya bita da harara yana ya mutsa fuskarsa bayanta yabi da tashi jakar kayan ya kulle dakin.....Yana kallonta tana ta kici-kici da jakar kayanta yayi mata banza.....Kai tsaye motarsa ya nufa ita kuma ta nufi cikin gidan da jakar kayanta jikinta duk yayi sanyi kwata-kwata bata kaunar 'bacin ransa duk sanda yayi mata irin wannan fushin takan shiga halin damuwa da dana sani.


*******


Yau kwana uku kenan da tafiyar Sadam! kullum zai kira wayar Mammah su gaisa amma baya ta'ba cewa ta bashi Sayyada fushi yake da ita sosai.....Wanda ko muryarta ma baya kaunar yaji.....Yau ma misalin goma da rabi na safe ya kira wayar a lokacin Mammah na bedroom dinta tana wanka Sayyada da Aunty Luba na zaune a palo suna hira wayar Mammah na kan kujera a ajiye kiran nasa ya shiga....Sayyada itace ke kusa da wayar tana dubawa taga numbarshi domin ta gane da sunan da Mammah tayi serving *Soja* sai ta'ki d'aukar wayar saboda tana gudun ya dauki wayar ya zageta ko ya hantare ta.....Wayar har ta katse wani kiran ya kara shigowa.


Aunty Luba tace"Sayyada kece kike kusa da wayar ki dauka mana."


Sayyada ta girkgiza kai tana ta'be bakinta.


Aunty Luba tace."Kin duba kinga wanene."? Sayyada ta kalli fuskar wayar ta dauka tana nuna mata.


Cike da mamaki aunty Luba take kallonta tace"Mijinki ne fa." Sayyada tace"Ai shiyasa na'ki dauka.


Aunty Luba tace"Sayyada kwana biyu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login