Showing 90001 words to 93000 words out of 142497 words

Chapter 31 - NI DA YAYA SADAM Complete Document by Binta Umar Abbale.txt

09 Dec 2024

50489

ni na shiga gari ko Allah zai sanya na had'u da wani nawa."


Jatau! yace."Soja ba zan iya rabuwa da kai ba saboda ban san hannun da zaka fad'a ba idan na sallameka wa ka sani a garin jos gurin wa zaka fake gari da babu lafiya ni na yanke shawarar siyar da komai nawa dake cikin garin nan na tarkataku gabakidaya mu bar garin."


Sadam! yaji wani irin tausayin mutumin a cikin ransa a kansa an koreshi daga gari kuma ya yarda zai bar garin saboda shi tabbas mutumin ba karamin kaunarsa yake ba.


Jatau! Yace."Yanzu kaje gona ka kira Munkaila ni kuma zanje can gidan Alhaju Tanko mai siyan gidaje nasan ina zuwar masa da wannan maganar zai amince mun tunda dama a kwanakin baya yazo min da bukatar yana so in siyar masa da gidana zaiyi gidan gona nace masa gidana bana siyarwa bane to wannan karon kuwa dole ne na siyar dashi."


Sadam! Yace."Baba idan ka siyar da wannan gidan to wane gari kuma zamu koma da zama."?


Jatau! yace."Kasan garin kano."? Sadam! ya gyada kai alamun bai sani ba Jatau! yace."A wannan tunanin naka dama bai zama lallai kasan garin ba nasan da a cikin hayyacinka kake zaka san garin gari ne dake da karrama bako kowa yaje garin ya zama dan gida to can zamu nufa sai mu siyi gida ginanne mu zauna kafin mu san abunyi."


Sadam! Yace."Baba da ka kyaleni na tafi." Jatau! ya 'bata fuskarsa yace."Soja ka daina wannan maganar kaji ko muna tare har abadah dani da kai mutukar kaga na rabu da kai to kace min naga danginka."


Sadam! ya goge kwallar dake idonsa ya mike tare da fad'in"Bari na kira Munkaila a gona." Jatau yace."Yawwa maza maza."


Koda Jatau! ya shaidawa Munkaila halin da ake ciki baiyi gaddama ba ya nuna amincewarsa saboda sam baya son wulakanci da tozarci a gari ya san halin maigari Falalu zai iya tozartasu a garin.


Jatau na samu Alhaji Tanko mai 'kasa da maganar yayi Ala ragaf da maganar a take suka nufo gidan tare Alhaji Tanko ya shiga dudduba gidan lungu da sa'ko ya fito yana murmushi yace."Jatau! gidanan naka duk ya ru'be kai kanka kasan jar 'kasar da akayi ginin gidan da ita ba mai kwari bace ko na siya to sai na rushe ginin gidan gabadaya sabida haka siyan fili za muyi wa wannan gidan naka."


Jatau! babu yanda ya isa ya amince da cinikin Alhaji Tanko yayiwa gidansa siyan fili naira dubu dari uku da ashirin......Jatau! ya amince kai tsaye suka nufi fadar maigari domin su shaida su kuma zama shaida kan cinikin.....Maigari najin yanda akayi cinikin gidan Jatau yace."Ai yayi tsada saboda haka wannan dubu ashirin din ta kai to za'a kawo ta fada ne kowa dake gurin yace"Kwarai wannan magana haka take....To hakane ya kasance dubu dari uku Alhaji Tanko ya kawowa Jatau dubu ashirin kuwa ya kai fadar maigari kamar yanda maigarin ya umarta.


*****


Cike da farin ciki ya shiga gidan nasa Aunty Luba na zaune a palo tana kallo ya shigo ta amsa masa sallamarsa tana masa sannu da zuwa.


Ya zauna kan kujera hade da cire hular dake kansa aunty Hauwa ta dauko masa ruwa mai sanyi da lemo ta ajiye kan tebur din dake gabansa zama tayi tana fuskantarsa tace"Yau dai kana cikin farin ciki alamun sun nuna a fuskarka."


Dariya yayi yace."Lubabatu kenan kwarai kuwa ba kiyi karya ba ina cikin farin ciki kema kuma ina fatan xaki tayani farin ciki in kinji alherin da ya same ni."


Tace."Dole in taya ka murna mana karfa ka manta duk lalacewarka mijina ne kai."


Hararata yayi yace."Lubabatu ni kike kira da lalatacce."? Tace"Humm! Sulaiman kenan kaida ai sha'ani kawai."


A fusace! Yace."Luba ashe baki da mutunci ni mijikinki kike kira da wannan kalmar."?


Tace"Kaga Sulaiman Allah ya baka hakuri don Allah ni ba tashin hankali na nema da kai ba."


Yace."Okey za kiga lalacewa ta ganin idanunki sannan ina so in sanar miki da cewar ki shirya nan da makwanni biyu zakiyi ba'kuwa a cikin gidanan ko da yake wannan ba bakuwa bace matar gida ce ina mai tabbatar miki da cewar iyayenmu sun tsayar da maganar daurin aure tsakanina da Sayyada."


Lubabatu taji wani irin fargaba da tashin hankali lokaci guda sun duro mata ta kalleshi bakinta na rawa yace."Ki kalleni da kyau aure zanyi zan auri Sayyada na kara jaddada miki."


A sha'ke! tace"Yanzu Sulaiman da gaske kake auran Sayyada zakayi matar d'an uwanka Sadam."!


Yace."Ke! gyara bakinki malama Sayyada dama dan ni kadai akayi ta Sadam shishshigi ne ya sanya ya shiga gonar da ba tashi ba gashinan ya tafi ya bar min matata saboda haka kar ki sake kiran Sayyada da matar Sadam Sayyada matar Sulaiman ce."


Aunty Luba ta mike tsaye da sauri tace"Na kira ka da lalattace kace akan me!!! Yo ai wannan sunan ne ya dace da kai in banda tsinancewa da lalacewa ka rasa wacce zaka aura sai matar dan uwanka wanda ko wata biyar baiy........ Kafin ta 'karasa ya wanke mata fuska da lafiyayyan mari! yana huci! yace"Karki kuskura kice zaki kawo min wata maganar banxa a nan gurin idan ba hakaba zan dauki tsatstsauran mataki akanki Wallahi zan iya sakinki kan wannan maganar."


Aunty Luba ta dafe kuncinta tana kallonsa cikin tsantsar bacin rai da bakin ciki gami da dana sani......."Wannan shine last warning d'in da zanyi miki kan ki iya bakinki kan wannan a'lamarin babu ruwanki idan ba haka ba to zan auna ki gidan ubanki." Yana gama maganarsa ya buge rigarsa ya shige daki.


Aunty Luba ta zauna kan kujera jikinta a sanyaye shiru tayi tana naxarin al'amarin......."Idan kika sake sanya bakinki cikin wannan maganar zan iya aunaki gidan ubanki." Wannan maganar itace ke amsa kuwwa! a kunnanta.


****


A gajiye ta dawo daga makaranta tayi zaune a palo tare da dafe kanta kwana biyu haka take fama da ciwon kai! da yawan fad'uwar gaba sai da duk sanda gabanta ya fadi tayi addua amma kwata kwata rayuwar ba dad'inta takeji ba hakuri kawai takeyi..........Mammah ta fito daga kicin ta ganta a zaune tace"Sayyada ashe kin shigo wato dai ba zaki daina wannan tunanin ba ko."?


Ya'ke tayi tace"Mammah kwana biyu bana jin dadi wallahi kaina ke ciwo ga faduwar gaba."


Mammah tace"Ayya amma kikayi shiru Sayyada baki fada ba sai ki zauns da ciwo shikkenan ki bari idan Sulaiman ya shigo anjima sai kuje chamis ko kuma ya kai ki clinic."


Jin ta ambaci sunan Sulaiman yasa Sayyada had'e fuska har sai da Mammah din ta fahinta Sayyada idan akwai wanda ta tsana a yanzu bai wuce Sulaiman din ba kwata kwata bata kaunar ta ganshi ballanta wata magana ta shiga tsakaninsu tuntuni ta daina yarda ya kaita makaranta itake tafiyarta ta dawo da kanta ko haduwa sukayi da kyar take gaisheshi mara zuciya yayi ta shishshige mata ta rasa wace zuciya ce dashi......Tace"Mammah ba sai munje chamis ba ina ganin idan nasha panadol ma ya isa kawai gajiya ce da zurga zurga."


Mammah dai ba yarinya bace ballanta a kife ta itama ta lura da Sayyada sam bata kaunar abunda zai sanya dan nata ya ra'beta shiyasa ma bata takura mata yanzu fargabarta d'aya shine idan Sayyadar taji abunda iyayensu ke kullawa dangane da auranta da Sulaiman din ya zatayi tabbas tasan akwai drama a gidan sai dai kawai Allah ya sassautawa zuciyarta ta amince ba tare da ankai ruwa rana ba.


Sayyada mikewa tayi ta nufi dakinta tana shiga tayi arba da hoton Sadam kan bed dinta jikinta a sanyaye ta isa bakin bed din ta ajiye jakarta ta zauna a salu'be ta dauki hoton ta rungume a kirjinta tana lumshe idonta lips dinta ta sanya a bakinta ta dan ciza wasu zafafan hawaye suka shiga gudana a fuskarta soyayyarsa mai zafi take tunowa a gareta kwanciya tayi rigingine tana shashshaka "Ya Sadam! rayuwata na cikin wani hali babu kai a cikinta na rasa farin ciki na rasa jin dadi komai na duniya yayi min zafi ka dawo gareni ina bukatarka masoyinaaaaa."!! kuka ne yaci karfinta ta d'amke hoton a kirjinta tana shashsheka!!!!!


A hankali ya iso inda take kwanta hannunsa ya zuba a aljihunsa yana mata wani malalacin kallo wani mugun kishi na cin zuciyarsa ganin hoton Sadam a manne a kirjinta.....Gyaran murya yayi ta dago a furgice suka hada ido dashi yana tsaye ya wani sha kunu.


Itama ta bata fuska sosai ta mike zaune tana masa wani irin kallo na tsana! Yace." Babu gaisuwa Sayyada."? banza tayi masa ya girgiza kansa yana had'iye wani abu mai mugun d'aci a bakinsa yace."Wato dai har yanzu baki saurarawa kanki da wannan koke koken ba ko."? Ta maka masa harara tana ta'be bakinta.


Yace."Komai zakiyi min sai dai kiyi dole ne na fada miki gaskiya kanki zaki cuta kina ta faman wahalar da kanki kan wanda bai san kinayi ba sadam ya mutu yayi tafiyar da ba zai ta'ba dawowa ba saboda haka idan ma zaki daina rungume hotonsa kina kuka ki daina domin shi tuntuni ya riga ya manta dake kece kike wahalar da kanki a banza."


"Yaya Sule dakata mun."! Ta fada tana wani 'kankance ido za tayi rashin kunya kenan Sulaiman ya tsaya yana kallonta cike da mamaki.


" Bana son irin wannan shishshigin da kake min shin wai ina ruwanka da rayuwata ne? ko gani kayi ina hawayen jini babu abunda ya shafeka dani saboda haka na roke ka ka daina shiga sabgata kuma ka daina shigo min Daki ba tare da izinana domin ni nan da ka ganni nasan darajar aurena har yanzu da auran Sadam! a kaina ni ban yarda ya mutu ba kamar yanda kuke ta fada mutukar ba gawarsa na gani ido da ido ba to ba zan yarda ba."


Sulaiman ya dinga share zufa! yana kallonta da bacin rai yace."To kece kike haukanki a banza kuma sabgarki da kike magana kar na sake shiga kamar na shiga na gama tunda nan da dan lokaci 'kankani kin zama mallakina saboda haka kinga kuwa dole ne in sanya ido akan lamuranki."


"Wallahi baka isa ba.'!!!! Ta fad'a a fusace! ta cigaba da cewa" Sai naga ta inda ake aure kan aure na rantse da Allah ka tsanantawa kanka aurena to sai na zama ajalinka macuci mayaudari kawai aini ban san haka kake ba ashe dama so kake Sadam din ya matsa ta baka guri ka aureni to baka isa ba kayi kad'an! Sayyada Sai Sadam!!!! Sadam! sai Sayyada forever."!! tana wata girgiza take maganar.


Sulaiman ya dinga goge gumi yana kallonta tana zabga masa harara ya rasa ma abunda zaice yace."Shikkenan idan na aureki to sai ki kashe kanki ki bi Sadam din tanan zan gane cewa ku masoya ne na ha'kika." Fuuuuu! ya kada kai ya fita daga d'akin.


Sayyada ta zube kan bed ta dauki hoton Sadam tana kallo tana wani irin kuka take fad'in"Kana ji ko! Ya Sadam! kana jin ta inda suka 'bullo ko!? Zasu kasheka bayan kana raye! wai zasu aura min Sulaiman bayan da auranka a kaina!!! Ya sadam kana ina ne? kayi maza ka dawo gareni kar su kassara min rayuwataaaa."!!! Sai kuka yaci 'karfinta ta dinga tana rirrike kirjina babu shakka suka aura mata Sule sai ta kasheshi ko ta kashe kanta ba zata iya rayuwa da kowa ba sai Sadam dinta shine za'binta shine ruhinta gabad'aya.


*****


Da asubah Jatau da iyalinsa sukayi sallama da garin dan marke koma nasu sun siyar dashi sun hada kudin guri guda daga su sai jakkunan kayanzu suka nufi tasha kai tsaye suka shiga motar da zata sa dasu da garin kano ta dabo dake suna da yawa mutum biyu kacal diraban motar ya 'kara suka dauki hanya ko wanne bakinsa dauke da adduar sauka lafiya.....


Karfe goma sha biyu da rabi suka sauka a unguwar samegu dake jahar kano kai tsaye gidan mai unguwa suka yada zango Jatau! duk ya sanar da mai unguwa abunda ke da akwai to da yake unguwar samegu unguwace sabuwa akwai gidaje na siyarwa na bulu da bulu masu yalwar tsakar gida da shaguna a wajen gidan a take Mai unguwa ya sanya dilallai suka shiga suka fita suka samo gida mai kyau mai dakuna hudu da katon tsakar gida da bandaki sannan da shago manya manya biyu a waje sai dai gidan rufin kwano kawai babu sili ballanta simintin 'kasa babu fulasta da sauran gyare gyare sosai a gidan haka aka zauna akayi cinikin gidanan dubu dari shida da saba'in dake ba kudin gida kadai ke gurin Jatau ba harda kudin katuwar gonarsa da kudin dabbobinsa da siyar sai ya hada kudi kimanin dubu dari takawas da wani abun......A take ya biya kudin gida shaidu suka shaida kwanansu biyu a gidan mai unguwa suka tare a sabon gidansu.........Alhamdullahi komai a hankali a hankali sun sanya a gidan don kasuwar kurmi Sadam da Munkaila suka shiga suka siyo abubuwan bukata na yau da kullum.


Shagunan dake jikin gidan Daya Sadam na awo daya kuma Munkaila na siyar da manja da man kulli a ciki Jatau bayayin komai sai da ya shimfida dadduma a dakalin gidan yayi zamansa yana jan carbi.........Alhamudullahi Al'amura na tafiya dai-dai Sadam nada nasibi kan komai domin gurin awonsa cika yake da jama'a a rana sai ya siyar da buhun shinkafa biyu ko uku garin masara da dawa fulawa da wake da barkona da dai sauransu komai yana siyarwa Shima Munkaila na ciniki sosai sai dai ba kamar Sadam din ba.


****
Saura Sati daya daurin auran Sulaiman da Sayyada mutumin ya jibgo kayan lefe kamar mahaukaci akwati goma sha biyu ko wacce da kyar take rufuwa kaya harda na hauka.......haka yazo ya jibgesu a palo Mammah ta dinga mamaki amma ba tace masa komai ba akai sai dai ta tambaye shi ina na Lubabatu sai ya hau inda inda tace"To itama yaje ya hado mata nata dai-dai gwargwado ai ba haka ake ba.......Sai sannan yaje ya hado mata akwati uku ya zuba mata kaya masu saukin kudi a ciki a cewarsa ai itama a lokacinta anyi mata nata........Sayyada na dawowa daga makaranta taga akwatinan ranta idan yayi dubu ya 'baci tsaki taja ta shige daki fuuuuu! Mammah ta bita da kallo ita kam ta rasa yanda zata bullowa al'amarin nan.


Abbah na dawowa ta tareshi da maganar kan ko za'a janye maganar auran nan saboda gudun shiga hakkin mutum Alhaji Auwal yace."Fatsima idan ba so kike auranki ya mutu ba to kija bakinki kiyi shiru da wannan magana don mutukar kika sake kika fadeta gabansu baba to babu shakka sai rayukanmu sun 'baci ni dake saboda haka addua ce kawai taki Allah yasa hakan shine yafi alkairi."


Tace."Alhaji yarinyar ce naga bata son abun kwana biyu ni kaina wani irin kallo naga tana yi min ta daina sakewa dani sosai shiyasa wallahi sam bana son abunda zai sanya a takura mutum.'' Yace."Kije ki kira min ita yanzu."


Ta mike ta nufi dakin Sayyada tana kwance ta 'kurawa sili ido ta mike zaune jin sallamar Mammah, tana kallonta ta share hawaye a fakaice tace"Sayyada kizo inji Abbanku." Tace"To Mammah." Hajiya Fatsima ta juya ta fita jikinta duk a sanyaye.


A hankali ta mike tasan dai ta tsuniyar gizo to ba ta wuce ta 'koki zancan dai guda d'aya ne.....Ta iske Abbah zaune kan kujera sai ta zauna kasa kusa da kafafunsa kanta a kasa tace."Abbah gani."


Alhaji Auwal yayi gyaran murya a nutse yace."Sayyada sannu kinji sannu da kokari ya karatu?" Tace."Alhamdullahi Abbah." Yace."To Allah ya taimaka." "Ameeen." Abbah ta fada tana mai kara yin kasa da kanta.


Gyaran murya yayi a karo na biyu yace."Sayyada kin san dalilin da ya sanya na aika a kira min ke."? Ta girgixa kai a hankali tace"Ban sani ba Abbah."


Yace."Na aika a kira min ke saboda maganar dai da kika santa nake so in kara tusa miki ita." Tace"To Abbah." Alhaji Auwal yace."Sayyada mu muka haifi Sadam! ni a ganina mune zamu fi kowa jin ciwon rabuwa dashi tunda mune muka zama 'kashin bayar samar dashi a wannan duniyar to Amma saboda muma mun san iko ake damu mun hakura mun barwa wanda ya bamu a lokacin da bamu sani ba ya kuma dauke abunsa alokacin da bamu ankara ba......Ke matarsa ce tilas kiji ciwon rashinsa saboda akwai soyayya mai karfi a tsakaninku bayan haka kuma akwai kauna ta jini irin ta 'yan uwantaka a tsakaninki dashi tabbas zaki shiga damuwa da alhini na rashinsa to amma duka idan kika fawwalawa Allah sai kiga komai ba komai bane tinda dama duniyar da kikazo ai ba'ace zaki dawwama ba a cikinta kowa da kika gani zai tafi inda Sadam ya tafi ko mu dad'e ko mu jima sai ka bar wannan duniyar komai jin dadinta da kakeyi kuwa.....Sayyada ina kara tunasar dake cewar wanda akayi duniyar dominsa ma sai da ya tafi ya barta ballanta mu da muka rakoshi saboda haka nake so nayi magana dake ta karshe kan Auraki da Sulaiman domin naga kin tayar da hankalinki kina koke-koke wanda ba shine mafita a gareki ba......Shi kansa Sadam din da kike kuka a kansa ba zai so wani bare ya aureki ba bayan ga dan uwansa babban abunda zakiyi ki faranta mana ki kuma farantawa marigayi shine ki auri Sulaiman dan uwanki idan kinyi mana haka mu kin gama faranta mana rai kuma zamu dawwama cikin yi miki addua da fatan samun nasara a rayuwa shi kuma Sadam da ya rigamu gidan gaskiya Allah ya jikansa da gafara shine karshen magana ta Sayyada."


Tun kafin ya karasa maganar tasa ta tsinke da kuka yi takeyi mara sauti sai dai uban hawaye dake ambaliya a fuskarta murya na rawa tace"Abbah! idan aurena da Yaya Sulaiman akwai alkairi Allah ya tabbatar dashi kuma insha Allahu zaku sameni me biyayya da abunda kuke so zan auri Yaya Sulaiman Abbah."


Alhaji Auwal yace."To alhamdullahi Sayyada Ubangiji Allah yayi miki albarka keda zuruarki insha Allahu yanda kikayi mana biyayya kema za'ayi miki ki tashi kije wannan ne dama dalilin kiran da nayi miki."


Sayyada ta mike a salu'be ta nufi dakinta tana harhad'a hanya tana shiga ta zube bakin 'kofar dakin ta cusa kanta tsakanin 'kafafunta ta dinga rizgar kuka ji take tamkar zuciyarta zata tsage ta fito waje sabida tsanani tashin hankali da damuwar da take ciki.
NI DA YAYA SADAM


BINTA UMAR ABBALE*


39
Sayyada kwana tayi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login