Showing 27001 words to 30000 words out of 142497 words

Chapter 10 - NI DA YAYA SADAM Complete Document by Binta Umar Abbale.txt

09 Dec 2024

50474

duk a firgice gashin kanta duk ya tuje tace"Ki fad'a min gaskiya ko wani abu yayi miki domin ban yarda dashi ba." Tace"Babu abinda yayi min kawai ya shigo duba fulas din shayi ne wai zai sha sai nace masa ai baki dafa ba shine yake ta masifa." Baba Ladidi ta sauke ajiyar zuciya tana d'an 'kara naxarin d'akin da ita kanta Sayyadar tace"To ki kwanta sai da safe amma don Allah ki daina biye masa kuna fad'a ko kin manta aure za'ayi muku kiyi masa biyayya." Tace"To insha Allahu baba." Tare suka fito Baba Ladi ta koma shimfidarta ta kwanta ita kuma ta dauki buta ta nufi bandaki. Ko da wasa ba taji motsin mutum a ciki ba sai da ta tura sannan ta ganshi tik yana wanka Allah yasa babu haske sosai amma duk da haka taga abinda ta gani....Cikin razana ta saki 'kofar ta koma da baya tana zare ido....Kaciyarsa da ta gani a mi'ke shine abinda yayi masifar razana ta to me hakan yake nufi? ita dai tasan ba haka kaciyar maxa take ba to shi tashi ya akai take a tsaye!? babu me bata wannan amsar sai gabanta ya dinga fad'uwa cikin ranta tace"Kila bashi da lafiya ne sai kawai taji tausayinsa addua take masa Allah ya bashi lfy.
Tana nan tsaye ya fito daga shi sai dogon wando da singlet fuska a daure yazo ya gifta ta ya wuce ko da wasa taki dago kanta su had'a ido..... tana ganin shigewarsa ta afka bandakin ko addua ba tayi ba....Wandonta ta cire tayi fitsari tasa hannu tana tsarki kawai sai taji tana wanko wani abu mai yau'ki ta dinga wankewa sai da ta daina jin yau'kin abun a hannunta sannan ta hakura ta fito jikinta duk a sanyaye daki ta nufa ta cire wandon ta sauya wani kana ta nemi guri ta kwanta ta rungume pillow tsananin sha'awa na damunta wanda ita takasa tantance menene da kyar bacci ya dauketa .......To shima nasa 'bangaran hakane yayi ta fama da joystick dinshi dan ta mi'ke masa sosai kawai yana tunano yanayin da ya shiga lokacin da ya had'a jiki da yarinyar taushin fatarta da yanayin yanda ta dinga narke wa a jikinsa tana mutsika shi shine abinda yake daga masa hankali dalilin kenan da ya sanya joystick din taki kwanciya haka ya dinga mirgin mirgin kan katifa yana lumshe ido gagarimar sha'awa ce ta taso masa sha'awa ta shakara da shekaru Sadam ya sha wahala a cikin daran nan kafin ya samu ya dawo norml bacci me nauyi ya dauke shi......Sai kusan shida na safe ya tashi don ba yanda Habu baiyi dashi ya tashi suje masallaci ba ya kasa tashi saboda baccin dake kansa Yana idan da sallahar ya fita suka gaisa da kawu Tanko kana ya shiga sauran 'kofofin suka gaisa da jama'a tare da yi musu sallama.....Koda ya dawo kofar su Baba ladidi sai ya tarar ta dora tukunyar kunu kan kurfoti baiyi magana ba ya dauko bokiti ya juye ruwan sai wani shan kunu yake yaje ya sanar da Habu ya fito yayi wanka a cewarsa baya so ko minti ashirin su kara a garin.....Captain Habu ya fito da shirin wanka Shi kuma ya kuma ciko tukunyar da ruwa ya dora kan wuta yaja ya tsaya had'e da rungume hannu a kirjinsa kafatanin hankalinsa na kan ruwan da ya dora kan wuta yaji motsi a bayansa....Sayyada ce ta fito da kai buyaya! da riga iya gwiwa yaji wani bala'in takaici ya kamashi dauke kai yayi daga kanta, Tana magagin bacci ta dauki buta cike da ruwa zata afka bandaki......Razananniyar tsawa! ta buga mata! sai butar ta fad'i! da sauri taja ta watsatsake! ta tsaya tana kallonsa....Ya dinga maka mata harara kafin ya ya mutsa fuska yace."Mahaukaciya me bankad'a band'aki babu tambaya to da akwai mutum a ciki." Sai tayi saurin kallon kofar 'bandakin taji motsin ruwa.....Jiki a sanyaye ta aje butar zata koma daki domin tayi bala'in jin haushin sunan da ya kirata dashi wai mahaukaciya!!! Ya dinga watsa mata wani irin kallo yana ya mutsa fuska haka ta shiga dakin Baba ladidi ita kuma ta fito da karamin bokiti cike da gasarar kunu sai ta ganshi a tsaye tace"A'a gadi aka bakane na ganka a tsaye ko da yake na manta kai yanzu ko shekara zakayi a tsaye ba damuwa zakayi ba." Shiru yayi mata tazo ta bude tukunya tana fad'in"Nasab ruwan har ya gaji da tafasa ma." Tana budewa taga kurmemen ruwa a tunkuya kuma baiyi zafin kirki ba....."Da alama dai kaine ka juye ruwan zafin nan ko."!? tafada bayan ta aje abun dake hannunta.....a dakile yace."Captain Habu na juyewa yana wanka wannan ma da kika dora ni zanyi dashi. da wuri zamu dauki hanya." Tace"To to! ko dana naji! amma dai ai ka bari ku karya tukkuna sai ku tafi daka bari an fara dama kunun." Shiru yayi mata sai ta wuce ta dauko daya kurfotin ta zuba gwayi ta hada wuta tana fad'in"Miskili kafi mahaukaci ban haushi ta inda Sulaiman yafi ka kenan." Sadam! na jinta ya share Baba marka ta fito da carbi a hannunta da alama lazimi take suka gaisa ta nemi guri ta zauna Baba Ladidi tace"Kina jina da wannan bahagon mutumin ko? Baba marka tace"Ina jinku ai naji yana yau zasu koma." Baba ladi tace"Tabbas gashinan ai a tsaye da bamu tashi da wuri ba da sai dai muga gidan wayam! sun tafi sai kace wanda ake kora." Shi dai Sadam baice komai ba Captain Habu na fitowa ya juye ruwa ya shiga wanka Captain Habu ya shirya tsaf ya fito suka gaisa dasu Baba ta zuba masa kunu mai zafi cikin jug da kosai mai zafi cikin wata samira tace "Ka karya a nutse kafin ya fito abokin naka."


Tsaf! ya fito cikin milk din yadi kashmir wanda akayi masa d'in *Kufta* yadin yayi masa kyau sosai ya gyara sumar kanshi dama shi ba ma'abocin sanya hula bane yana fitowa tsakar gidan ya d'umame da kamshin turare Sadam! ma'abocin turare ne kasancewar sa mutum mara son wari ko wane iri yana da tsafta ta ban mamaki farcensa ma abin kallo farare tas tas dasu, A nutse duk ya gaishesu yanzu fuskarsa ta d'an sassauta ba kamar d'azu ba Baba Marka ta had'a masa abun kari sannan ta zubo musu farfesun su na jiya katon plate sai turiri yake tamkar yanzu akayi ta kawo masu manya manyan gurasa masu kyau da taushi.....Kunun yasha sosai bai kalli inda kosai yake ba sai ya hau yagar gurasar yana dangwala da miyar yana ci sosai girkin tsofaffin yake masa dad'i shiyasa komai zasu dafa su bashi yake ci ba tare da wani 'kyan'kya mi ba........Ta fito daga d'aki tana cika tana batsewa tayi wanka tsaf da shirin zuwa isilamiyya suka gaisa da Captain Habu a mutunce Sadam! yayi tsammanin yarinyar zata gaishe shi sai yaji shiru ransa ya 'baci ya lura Sayyada ta gama raina shi da yawa har ta gaisa da abokinsa shi ta kasa gaisawa dashi ya cika ya batse ko da wasa bai kalli inda take zaune ba tana karyawa suna hira da Habu ta saki jiki sai 'babbaka dariya takeyi...........Yana kammalawa ya mike ya shiga masaukinsu minti biyar ya fito da jakar kayansu ya kulle dakin key din ya mikawa Baba ladidi Ya kalli Captain Habu a tur'bune yace."Idan ka gama zubda girman sai ka taso mu tafi ko." ! Captain Habu ya mike yana murmushi yayiwa su Baba sallama addua suke Allah ya tsare hanya.....Sadam! ne a gaba yana tafiya sahunsa na dukan 'kasa kamar wanda zai rusa gini saboda zafin nama. shi kuwa Captain Habu sai da ya tsaya sukayi sallama tsaf da su Baba sannan ya bi bayansa.


***
Sai bayan motarsu ta hau kan kwalta ne sannan ya sauke ajiyar zuciya Captain Habu ya kalleshi a nutse yace."Don Allah ka dinga sassautawa zuciyarka wani abun mana Abokina nasan akan abunda kake wannan hucin! kar ka manta da cewar yarinyar nan fa bata da waye ba irin ta mutananmu sannan akwai kuruciya a tare da ita zafin zuciya ba shine zai sanya ta dawo yanda kake so ba kai da kanka zaka dinga nusasheta ga yanda zatayi karka ina biye mata ina koya mata mu'amula ne Amma yanzu kishi ba naka bane."


Wata ajiyar zuciyar ya sauke yace."Habu ina kishin yarinyar mutuka bansan meye dalili ba ko da kai naga tana magana sai raina ya 'baci! yau da ban san waye kai ba da sai na d'ora allon zargina akanka to nasan kai ba irinsu bane ba zaka tsare min mutuncina da kyau.....Aboki ina jin tsoron aje Sayyada cikin breeck dinmu yarinyar nada rawar kai sosai kuma kasan akwai ma'kiyana a gurin sannan akwai 'yan iska irinsu Shu'aibu, duk sanda na tuno hankalina na tashi mutuka."!


Captain Habu yace."Kome xakayi kayi da kyakkyawar niyya insha Allahu babu abinda zai faru ai akwai masu gadi kuma nima kar ka manta nawa iyalin na ciki insha Allahu babu abinda zai faru zaka sanya ido sosai nima zan sanya ido. Allah zai tsare mana iyalinmu."


Sadam! yace."Insha Allah amma kasanni kasan bani da sauki kan komai Allah duk wanda yayi gangancin shiga hurumi ranar sai dai uwarsa ta haifi wani."!!!! Captain Habu yace."Insha Allahu hakan ma ba zata faru ba." To da wannan magana ta Sadam suka rufe maganar suka shiga wata.


****


Sulaiman ya dawo daga kasar hindu cike da nasarori na rayuwa, tsaraba yanda yayiwa matarsa haka yayiwa Sayyada akwati biyu cike da kananun kaya Pakistan irin na indiya da irin kayansu na kwalliya Mahaifiyarsa ya bawa akwatinan yace."Gashinan a had'a a lefen Sayyada Hajiya Fatsima taji dad'i sosai tana fatan zumuncin yaranta ya d'ore har 'yayansu da jikoki.


****


Yau sauran kwana uku daurin aure.....Ya dawo gida misalin karfe shida da kwata na yamma yayi parking harabar gidan suka gaisa da mai gadi yana kallon motar Sulaiman yasan ya dawo gari, kai tsaye cikin gidan ya nufa


Yana hakimce kan kujer hannunsa da katuwar waya yana latsawa fuskarsa dauke da murmushi me kyatarwa sulaiman kenan matashin da 'yan mata keso ga kudi ka kyau!!!! Sadam! yayi sallama a nutse ya tsaya daga bakin kofar ya kwance takalminsa, Sulaiman ya dago kansa yana kallonsa bai amsa sallamar ba, ya karasa babu yabo babu fallasa ya mi'ka masa hannu"Barka da yamma."! yafad'a cikin wata baud'ad'ddiyar murya wacce kana jin sautinta zaka san babu wasa a cikinta.


Cikin izzah da hakimcewa ta alhazawan birni ya mi'ka masa nasa hannun "Da fatan na same ku lafiya? Ya aiki ina fatan komai lafiya."!?


Hannunsa ya zare yana d'an ya mutsa fuska yace."Aiki alhamdullahi." Sai ya nemi guri ya zauna had'e da d'aure fuska tamau!! Wannan d'agawar! da girman kan! da izzar! da Sulaiman keyi na masifar bashi haushi wai shi nan me kudi ya dinga wani abu wanda shi a ganinsa wannan abun da yakeyi ba karamin hauka bane. Shiyasa duk sanda yaga yana wannan iskancin yake mugun shan kunu ya hade fuska tamau ya nuna masa shi din banza shi din wofi!!!!


Sulaiman ya aje wayarsa ya kalli Sadam! da murmushi a fuskarsa yace."Lokaci nata matsowa ko? idan nayi lissafi dai-dai yau saura kwana uku daurin aure hakane ko."!?


Ba tare da ya kalleshi ba yace."Tabbas! bakayi makuwa ba hakane ranar juma'a daurin aure insha Allah."


Murmushi yayi ya shafa sajansa wannan sararsa ce shafa saje a kai-kai! minti biyar goma kana magana dashi sai ya shafa sajansa wannan d'abiar ma na masifar bawa Sadam! haushi sai ya dinga wani abu tamkar wani boss!!! mtsssw!!!!


Yace."Wai ke don Allah me yasa bakajin shawara ne yanzu da wannan aikin naka zaka iya rike iyali? tuntuni nace kazo muyi kasuwanci ka'ki wai kai dole sai kayi aikin soja! wanda babu komai a cikinsa sai had'ari da tashin hankali kawai kaje a kasheka a banza a wof..........."Ya isa."!!!!!!! kafin ya 'karasa maganar ya katse shi a mugun fusace! ya mi'ke tsaye....Sautin muryarsa da yanda yayi maganar a zafafe shine ya fito da Hjy Fatsima daga kicin jikinta na 'bari! tace"Meke faruwa ne."!?


"Wai Mama wannan guy ina ruwana dashi ne? me ya dameshi da rayuwata da abinda na za'bawa kaina ina ruwansa da iyalina ina ruwansa da aikina aikin soja na za'bawa kaina ba dan kudi ko daukaka ba ba don nayi suna ko a sanni ba na za'bi aikin soja ne domin na taimaki 'kasata ! Najeria wani gardi! 'katon banxa bai isa ya sauya min ra'ayi ba don haka Mamah tun muna shaida juna ni dashi kija masa kunne babu ruwansa dani ya ri'ke girmanshi idan ya sake ya fad'i a gurina to zan bi takai in tattaka in wuce!!!! maganar Iyalina babu ruwanka da ita meye dameka tunda banzo nace ka taimake ni ba bana fatan zuwan wannan ranar albashina ya isheni na rike matata da 'yayana Kai! kake son duniya da har kake shirya zama a cikinta kana kawatata ni duniyar ma ba a gabana take ba mtwwwws."!!!!! Yana gama maganarsa ya buga hannun kujera fuuuuuuu! ya fita dafa palon.


Hajiya Fatima ta zaune kan kujera jikinta duk a sanyaye ta kalli Sulaiman da ya wani marairaice fuska tace" Meye ya had'aka da d"an uwanka shin ka manta zafin zuciyarsa ne."!? Yace."Wallahi Mama ba wani abun bane me zafi ya hasala kawai ina bashi shawara ne kin san dai saurin daukar zafi irin nashi."
.Tace"Ni narasa me yasa bakwa jituwa da juna kaine babba don Allah ka cigaba da hakuri da halinsa ko bayan raina kuyi zumunci insha Allahu shima ya fara ajiye iyali zuciyarsa zata sassauta."
Yace."Karki damu Mamah! insha Allahu zan cigaba da tausar zuciyata a kansa." Hjy Fatsima ta mike ta koma kicin.
Suleiman shiru yayi yana tunanin abinda ya faru tsakaninsa da Sadam! girgiza kai kurrum yakeyi ransa a masifar 'bace! Ana kallo Sadam! nayi masa abinda yake so savoda tsabar kin gaskiya ace yayi hakuri shine babba to babu shakka hakurinsa ya 'kare zai dauki tsatstauran ma taki a kansa.


*Tofa! Yanzu aka fara labari*


9/6/2020
NI DA YAYA SADAM


NA
BINTA UMAR ABBALE


Pege16*
*_Na kue ga duk me sha'awar cigaba da karanta book d'in to sai y
*Yana* fita ya nufi sashensa watsa ruwa yayi ya fito 'kungunsa d'aure da towel kwanciya yayi kan bed dinsa tare da rintse ido yana tunanin maganganun da Sulaiman d'in yayi masa shi a ganinsa wannan ai ranin hankali ne, kan me zai sanya masa ido kan harkokinsa akan me zai dinga kushe masa aikinsa Sojoji nawa ne suka rike iyalinsu da aikin da har yake cewa ya aje aiki ya dawo kasuwanci wato yana so ya zauna a 'karkashinsa kenan! to idan ba haka ba har yaushe zai ce ya ajiye aikinsa ya dawo ya kasuwanci, aikin soja ra'ayinsa ne kamar yanda ya fad'a kuma babu wanda ya isa ya tursashi ya aje aikinsa sai dai idan mutuwa yayi, Haka yayi ta faman Juyi a kwance sai da yaji kiran sallah magariba sannan ya mike ya zura jallabiya mai karamin hannu ya sanya gajeran wando a ciki kana ya fesa turare mai kamshi ya nufu masjid.
Sai bayan sallahr isha'i ya shigo gidan yana cin magani lokacin Alhaji Auwal ya dawo daga kasuwa ya bishi har inda yake suka gaisa da juna Alhaji Auwal yace "Tunda nagan ka anan nasan akwai abinda ke faruwa a brecck din naku." Yace."Kwarai kuwa Abbah aiki ake min a bangarena sunji labarin zanyi aure shine suke min gyare gyare." Alhaji auwal yace."To masha Allah ni kuwa ga shawara ." Yace."Ina jinka Abbah."Alhaji Auwal yace."Me zai hana idan an d'auro auran mun dawo Sayyada ta zauna tare damu sam! bana son zamanta a brecck din nan wallahi." Ajiyar zuciya ya sauke a hankali yace."Nagode Abbah nima na dad'e ina wannan tunanin to kawai bana son in takura muku ne yasa na amince da zamanta a brecck din." Alhji Auwal yace."Kana bani mamaki! Sadam! shin wai su waye iyayenka."!? Yace."Kune Abbah." "To meyasa kake janye jikinka damu ? yanzu dan kazo kace Sayyada ta zauna tare damu sai mu hana kar ka manta fa da cewar dani da mahaifiyar yariyar uwa daya uba daya muke ko babu aure a tsakaninku ni me riketa ne." Yace."Kwarai kuwa Abbah." Alhaji Auwal yace."To don Allah ka daina wannan d'abi'ar taka." Yace."Ayi hakuri Abbah insha Allah." Hajiya Fatsima ce ta fito daga d'aki tana jan akwati ta aje ta dauko dayar tace"Sadam! wannan akwatin d'an uwanka ne ya kawo maka da duk kayan dake ciki yace a had'a a lefe."


Kici-kici yayi da fuska yayi shiru! tace"Naga ka 'bata rai kai bakace komai ba sai hidima ake maka kana kwance."! Yace."To Mamah me zance." Tace"kace ka gode sannan don Allah ka rage zafin rai ka zauna da kowa lafiya d'an uwanka na son ku zauna lafiya amma kai kullum cikin fushi da d'acin rai wannan ba sara bace." Yace."To Mamah! na daina isha Allah." Yasan in ba haka yayi ba to zata dinga nanata maganar ne. Tace"To ka bude kayan ka kalla yace."to duk dan ya faranta mata rai ya bude akwatinan yana dubawa kayane na gani na fada masu masifar tsada sarkoki abubuwan hannu dogwayen riguna dasu pakistan turarrika masu kamshi da tsada.....Sai Uban 'kananun kayan bacci masu kyau.....Sam hankalinsa bai kwanta da kayan ba don ba yarda zaiyi ne ya rufe akwatinan yace."Kaya sunyi Mamah." Tace"To ko kaifa gobe zamu tafi can *Dabin* zamu tafi da akwatinan lefan su gani in yaso sai a dawo dasu. yace."Hakan yayi kyau." To hira ce ta 'barke a tsakaninsu, Sadam! na fad'a musu banan babu wata uku zasuyi tafiya zuwa wani 'kauyen 'kayau dake can cikin Maiduguri domin kwantar da tarzomar da take tashi a yanki wanda masana bunkice sukayi itifakin cewa 'yan boko haram din da suke cikin wannan yanki suna da yawa kuma mafiya akasari sune suke sajewa da mutane su fito cikin gari da cikin kasuwanci suyi aika-aika su gudu kuma neman duniya ba'a ganinsu duk kuwa sojan da yayi gangancin shiga wannan kyauye to sunansa matacce, sai mai tsananin rabo ne yake dawowa da ransa amma fa sai yayi jinya me tsayi domin sai sun rautana shi.
Daga jin yanda yake basu labarin had'arin dake cikin 'kauyan sai duk jikinsu yayi sanyi Hajiya Fatsima tace"Sadam! daka hakura da zuwa wannan gari

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login