Showing 48001 words to 51000 words out of 142497 words
Chapter 17 - NI DA YAYA SADAM Complete Document by Binta Umar Abbale.txt
yana kwance bashi da lafiya amma ya'ki barin hankalin kowa ya kwanta kullum tashin hankali babu zaman lafiya." Tana hawaye take maganar.
Baba Marka tace"Ikon Allah me ya samu Sadam! din naji kince yana kwance babu lafiya.....Sulaimai yayi saurin cewa"'Yan boko haram! suka harbeshi a kafada kin san shi da shegen rawar kan tsiya wai dole ya isa haka zai je ya cuci kansa a banza a wofi."
Jin abunda ya samu Sadam! din yasa baba ladidi fashewa da kuka tana fad'in"Yanzu abunda ya samu Sadam! kenan amma a rasa wanda zai fad'a mana a cikinku wato idan ma mutuwa yayi shikkenan sai dai ku aiko mana ya mutu! ke Sayyada ban san baki da hankali ba sai yau! ace mijinki alburushi ya huda masa kirji ki iya tsallake shi ki tawo nan uwar me zakiyi mana a gida yarinya mara hakuri malam."!
Sulaiman yace."A'a Baba abi komai a sannu a hankali Sayyada ma tana da 'korafi ai gashi ta kawo muku 'korafinta kun juyawa magana ai idan daddawa da wari to 'bera dole yayi sata ya kamata ku duba maganar nan fa.
Baba Ladi na kuka tace"Habawa Sulaiman ai lalura ta wuce komai wallahi ban san da cewar kaima baka da hankali ba sai yau kai da ya dace ka dinga tausarta kaine zaka daukota ka dawo da ita gida yanzu meye amfanin abunda kayi."
Yace."A'a baba kar kiga laifina ni mutum ne me baiwa mutum 'yan cinsa bana so in ga ana muzgunawa mace ko wace irice ballanata sayyada da take jinina hakika Sadam! na zalintarta dan dai kawai kun ce dole sai kun aura masa ita ne ni dai ina me baku shawarar tun wuri ku warware auran nan don Wallahi Sadam! ba son Sayyada yake ba yana da budurwarsa Halima sunyi alkawarin auran juna."
Baba Ladidi tace"Wallahi mutukar ina raye a duniyar nan babu mahalukin da ya isa ya warware auran nan sai dai idan Sadam din ne yace ya saketa to wannan dole in hakura amma auran Sayyada da Sadam! mutuwa ce zata raba insha Allah." Sulaiman yaji d'acin maganarta sai kawai ya girgiza kai yace."Ai shikkenan baba wanda baiji bari ba....! Tace"Haba Sule ai dole Sadam! ya hana Sayyada shiga sabgar ka saboda da alama kaine kake zugata har yaushe akayi auran ma da za a fara yaji ba zai yiwu ba." Baba Ladidi fad'a take tamkar ta ari baki "Yau yau d'in nan zaki koma d'akinki kije ki cigaba da jinyar mijinki to kaji."""! Da jin abinda Baba ladi tace sai Sayyada ta fashe da kuka tana fad'i " Allah kuwa baba ba zan koma sai yazo da kansa sai ya gane ina da matsayi a gurinsa sannan sai ya tabbatar muku da cewa *Dabi* nan ne tushensa."
Baba Marka ta ri'ke baki tana fad'in" Oh! kiji wata magana a gurin Sayyada shi Sadam! din ne da bakinsa yace miki *Dabi* ba nan ne asalinsa ba ko 'ka'ka."!?
"Eh mana yana nunawa budurwarsa haka sannan suna kirana da 'yar 'kauye to shima dai 'kauyen ne asalinsa."
Baba Ladi tace"Babu shakka kema kinyi magana Sayyada ni na tsani mutumin da zai dinga kushe asalinsa Sadam! zai zo ya same ni har gida ku rabu dashi tabbas ba zaki koma ba sai yazo da 'kafafunsa."
Ajiyar zuciya ta sauke taji dad'in yanda Baba Ladidi ta fahimce ta.....Shi kuwa Sulaiman haushi da takaici ne suka cika masa zuciyarsa yayi musu banza yana ji suna hira da maida magana ya sharesu tunanin yanda zata 'bulle masa kawai yake da yaga babu haza sai ya mi'ke......Baba Marka tace"Ina zakaje kuma yanzu nake shirin dora abinci." Yace."Idan kun girka kuci abinku ni na tafi." Duk suka bude baki suna kallonsa cike da mamaki!
Sai bayan fitarsa sannan suka dauke kansu daga hanyar da yabi suka cigaba da hira suna mamakin yanda ya sauya lokaci guda Sulaimn bai ta'ba zuwa *Dabi* ya tafi a ranar ba sai ya kwana biyu yake tafiya amma yau ko awa guda baiyi ba ya juya lallai akwai wata 'akasa.
****
Hankalinsa kaf na kan kofar shigowa daga yaji motsi sai ya dauka itace Hjy Fatsima tace"Anya Sayyada ta samu abun hawa kuwa? bari muje kawai yanzu Baban gida zai kawo ta." Kai kurrum ya iya d'agawa Har mahaifiyar tasa ta fita ya kasa cewa komai jikinsa ke bashi babu lafiya.....Koda Hajiya Fatsima ta koma gida duk ta duba ko ina bata ga Sayyada ba sai ta fito farfajiyar gidan tana tambayar mai gadi yace."Hajiya naga Alhaji Sulaiman ya dauketa a mota. sai ta sauke ajiyar zuciya ta koma ciki gidan tayi tunanin Sulaiman din yaje mai da ita gurin Sadam din ne shiyasa hankalinta ya kwanta.
Kusan awan Mammah biyu da tafiya ya rasa abinda ke damunsa shiru har yanzu bata dawo ba ya mike tsaye yana zagaye dakin hankalinsa duk ya tashi......wayarsa ya dauka ya kira numbar Mammah ta dauka kafin yace."Komai tace"Sulaiman ya kawo ta ko."!? Yace."Ban gane ba Mammah."! tace."Ina nufin Suleiman ya kawo Sayyada domin da na dawo mai gadi yake shaida min da cewar Sulaiman din ya dauketa a mota." Gabansa ya fad'i le'bansa na rawa yace."Bai kawo ta ba."! Tace"A'a bai kawo ta kamar yaya? ina ya kaita to? shiru yayi mata sai ta kashe wayar hankali a tashe ta fara kiran wayar Sulaiman d'in.....Lokacin yana kan hanyar dawowa gida tace"Sulaiman ina Sayyada."? kai tsaye yace."Tana *Dabi."* Hajiya Fatsima ta sanya salati tace"Me yake faruwa ne? me taje yi a *Dabi."?* yace."Mammah ki bari idan na dawo mayi maganar yanzu ina kan hanya. " Tace."To Allah ya saukeka lafiya."
Yana kashe wayar kiran Sadam! ya shigo sai da ta kusa katsewa ya dauka......."Ina Sayyada."!? yafad'a murya a sama! Kai tsaye yace."Tana can *Dabi."*
"What!." Yaf'ada jikinsa na kyarma! Sulaiman yace."abunda kunnanka ya jiye maka! Sayyada ba zata zauna a cikin irin wannan halin ba kana fifita yarinyarka kanta wannan cin zalina ne da shiga hakki duk sanda ka san muhimancinta kaje ka dawo da ita."
Wani irin jiri ne yake nema ya kayar dashi a gurin yace."Yanzu kana so ka sanar min da cewa kaina ka jagoranci tafiyar ta ko 'ka'ka."!? "Kwarai kuwa yanzu na kaita har na juyo ina kan hanya zuwa gida."
Murmushi yayi mai ciwo yace."Kasan wani abu Sulaiman."? Yace."Sai ka fad'a." Wani murmushin ya sakeyi kana yace."Komai nacin ka! komai binbininka! komai mayatarka! ko mai sharrinka! Sayyada tayi maka nisa! Wutsiyar ra'kumi! tayi nesa da 'kasa! duk abunda kake ciki na sani tuntuni kana son Sayyada kana min zagon 'kasa a matsayinka na d'an uwana da ya sha nono ya bani Duk maganganun da kazo ka shirya mata jiya a kunne na wanda kai duk a tunaninka ko bacci nake hummm! kayo shuka a idon makwarwa! Sule! Sayyada tafi 'karfinka mutukar ina raye a duniya duk inda za'aje za a dawo da gida ni Sadam! sai na nuna maka kai 'karamin d'an akuya ne."!!!! 'Kit! ya kashe wayar......Sulaiman ya gangara bakin titi yana sakin wani irin nuffashi kan motar ya buga da karfi yana fad'in"Wannan yaron matsiyaci ne! ni yake fad'awa wannan maganganun babu shakka zai gane cewar tsalle d'aya mutum yake ya fad'a rijiya amma sai yayi dubu bai fito ba zasu zuba dashi dashi sai ya kassara masa rayuwa.
Yana kashe wayar yayi jifa da ita gefe guda zama yayi gefan gadon ya rufe fuskarsa da tafukan hannunsa wai Sulaiman ne ke son matarsa shin wannan wace iriyar rayuwa ce ? uwa daya uba daya yana cin dunduniyarsa! Innalilahi wa'ina ilahi raji'un!
***
Hajiya Fatsima na zaune zaman jira shigowar Sulaiman ya shigo da sauri ta mike tsaye yace."Mammah ki zauna naga duk kin tashi hankalinki." Tace"Ya zanyi iya zama na kwantar da hankalina sulaiman ina yarinyar mutane."? Yace."Sayyada fa tana *Dabi* tace"Kan wane dalili ka kaita *Dabi* me akayi mata? Yace."Zauna nayi miki bayani." Zama tayi tana kallonsa yace."Mammah na shigo gidan nan ba tarar da Sayyada zata fita da jakar kayanta tana kuka da kyar na rarrasheta ta shiga mota na tambayeta abunda ke faruwa tace ba zata fada min ba sai na kaita *Dabi* nace ni kuma ba zan kaita ba sai ta sanar min da komai tace to idan ban kaita ba wallahi zamu nemeta mu rasa wannan magana data fada sai ta bani tsoro kawai sai na yanke shawarar kaita in yaso idan munje ta fad'i dalilinta sai mu dawo saboda nasan babu yanda za'ayi Baba Ladidi ta barta ta zauna......Sai da muka isa take shaida mana cewar Sadam! ke nunawa karuwansa ita bata da mahimanci a gurinsa ya sanya daya daga cikin karuwansa ta doketa har ta fitar mata da jini babban abunda ya tayar min da hankali shine wai ya hanata kulani ko gaisheni bai yarda tayi ba saboda yana zargin wai ina sonta Mammah raina ya 'baci! mutuka me zanyi da matar d'an uwana? da jin wannan maganar sai Baba Ladidi tace"Sayyada ba zata dawo ba sai yazo da kansa ya nuna musu mahimancita a gurinsa....Yanzu kafin shigowata Sadam ya kirani a waya ya 'kare min zagi Mammah na rasa abunda ke damun Sadam a rayuwa."
Hajiya Fatsima ranta yayi masifar 'baci! da jin abunda ya faru wai me yasa ko wace iriyar matsala ake samunta ta 'bangaran Sadam! ne? Wannan karon dole ne ta nuna masa kuransa babu shakka itama tana goyon bayan Sayyada ta zauna har sai Sadam din ya gane tana da mahimanci a gurinsa kuma dole ne ta nuna masa kuskuransa kan abinda yayi.
*****
Sayyada da 'kyar taci abinci ta kwanta kan gadon Baba ladi tana share hawaye a yanda take son Sadam! bata ta'ba tsammanin zai fifita budurwarsa a kanta ba ai babu komai duk da tana bala'in sonsa dole sai ta nuna masa kuransa sai ta nuna masa bambamci d'an kyauye da d'an birni zata nuna masa shima d'an kyauye yasan muhimancin kansa.
Sai kusa karfe uku na rana ta tashi daga bacci tayi wanka ta shirya ta fito baba Marka ta dauko mata dambun masara wanda yaji zogale da albasa da gyada gai man gyada zuryan sai kamshi yakeyi ta d'ebo mata ruwa randa mai sanyi sai lalla'bata sukeyi taci dambu sosai kana ta zauna suna hira daga zarar ta tuno dashi sai gabanta ya yanke ya fad'i!!! Yanzu ko wane irin hali yake ciki oho Allah dai ya dinga kula da kansa yana shan magani kan lokaci tasan halinsa sam bai damu da lafiyarsa ba, kaf tunaninsa ya dame ta sai ta mike salau!salau! taje ta kwanta had'e da rungume pillow tana kuka "Ya Sadam! ban so na barka ba ina sonka kai kuma kana nuna min tsana me nayi maka na damu da lafiyarka kai baka damu dani ba." Zancen zucci takeyi har ya fito fili baba ladi tana jinta sa'ilin da ta shigo dakin bata ce mata komai ba ta dauki abunda zata dauka ta fita daga dakin.
*****
To kamar yanda take ciki cikin damuwa shima haka yake cikin damuwa domin ko da Captain Habu ya shigo sai da ya fada masa halin da ake ciki Captain Habu ya nuna masa kuskuransa kan abinda yayi kana yace shi bai ga laifin Sayyada don ta tafi ba sai ya samu me jinyarsa.....Kaca!kaca sukayi dashi kan yace Sayyada bata da laifi shine yaji haushinsa.....Halima ma kasa gane kansa tayi ko tazo gurinsa korarta yakeyi ya gwammace ya zauna shi kadai a dakin yana tunanin mafita.......Sulaiman kam ko da wasa bai sake zuwa dubashi ba saboda yasan baxa su kwashe da dadi ba dalili duk laifi an taru an dorawa Sadam! din a maimakon ya kashe wutar a'a kullum 'kara ingiza iyayen nasa yake suna ganin laifin Sadam din abin duniya yayi masa yawa dan ma jarumin namiji ne baya sa damuwa a ransa......Mammah ta daina zuwa duba shi sau biya a rana yanzu sau daya take zuwa da safe shikkenan sai wata goben kuma hakan bai dameshi ba burinsa kawai yaji sauki ya koma bakin akinsa Sayyada kuma da suka kama suka rike suje su jikata su sha yayi rantsuwar sai dai su gaji su dawo da ita kuma har abada ba zai saketa ba kuma idan ya samu wacce hankalinsa ya kwanta da ita ya aura sai me.!?
****
Sayyada yau kwanata biyar da zuwa *Dabi* ta soma raina kanta domin har 'yar rama tayi sabida ta kwallafa ranta kan Sadam! kullum dashi take kwana a ranta duk ta rasa ya zatayi sai ta 'buya a daki taci kukanta ta koshi Baba ladidi ta gane duk halin da take ciki bata ta'ba tanka mata ba idone nata gaba idan ance ta sake yin yaji tayi tunda gashi tun ba'aje ko ina ba ta raina kanta shi kuma Sadam! din zai zo ya same ta ne."!
Cikin hijab ta fito Baba Marka na kad'in lagwani tace"Ina zaki je kuma."!? tace"Gidansu Ummi." Baba Ladidi na kicin tana kad'a miya tace"A'a Sayyada kin san dai kina da aure yanzu ko bana son shashanci kuma ni bana son ki fita saboda gudun surutun mutane ki koma ban yarda ki fita ba."
Tace."Bafa dad'ewa zanyi ba yanzu zan dawo." "Eh duk da haka dai ki koma kar ki fita idan kuma ban isa ba to shikkenan." Tace."To baba bari na shiga 'kofar su Amina na sami yaro sai ana aikashi gidansu Ummi din." Baba Marka tace"Haba Sayyada wa zaki fadawa halinki koma dai ki zauna ni bari na samo miki yaron." Baba marka ta mike ta dauki hijab ta zura Ta fita Sayyada ta koma ta zauna sai kumburi take.
Baba Marka suka shigo da 'kanin Amina baballe tace to ga yaro na samo miki ki aike shi.....'Daki ta shige ta 'kwalawa yaron kira ya daga labule ya shiga tace"Kai Baballe kayi maza kaje gidansu Ummi kace tazo yanzu nazo garin."
Baballe yace."To." ya fita kwanciya tayi tana tunanin shawarar data yanke.........Minti goma Ummi ta shigo suka gaisa dasu Baba tace"Ina Sayyada ko dai karyar Baballe ce." Baba marka tace"Tana cikin daki ki shiga." Ummi ta bankada labule ta shiga tana Sayyada kina ina."? Sayyada ta rungumeta suna dariya Ummi ta cikata tana kallonta Sayyada kinyi kyau sosai." Dariya Sayyada tayi tace"Ummi zauna muyi magana dake." Ummi ta zauna tana kallon Sayyada abun sha'awa.
Sayyada tace"Dallah wai kallon me kike min ne." ? Ummi tace"Gani nayi kinyi 'kiba Yau kwanaki goma sha biyar ko."? Sayyada tace"Eh Sayyada ta zayyane wa Ummi abinda Sadam! ke yi mata Ummi tace"Lallai ma Yaya Sadam! din nan dan wulakanci ne wallahi gwara da kika gudo gida idan ya damu dake sai yazo ya baki hakuri." Sayyada tace"Lallai Ummi baki san waye Ya sadam! ba miskiline wallahi ba zai bani hakuri ba ke nifa yanzu tunaninsa ne yayi min yawa na rasa yanda zanyi kullum da kyar nake bacci." Ummi tace"To me kike so ayi yanzu."
Sayyada tace"Gurin Malam Bashir zaki je ki kar'bo min numbar wayarshi sai muje inda ake kiran waya na kirashi Allah Ummi muryarsa kawai nake so naji gashi bashi da lafiya kin san 'yan boko haram! sun harbeshi a kafad'a."! Ummi ta dafe kirji tace"Da gaske kike Sayyada."!? Tace"Wallahi da gaske nake yana kwance a asibiti fa." Ummi tace"Amma shine kika tawo kika barshi kai Sayyada."
Sayyada tayi rau! rau! da idonta tace."Nima yanzu nake nadama tausayinsa nakeji kuma ina tausayin kaina ni nafi so ya gane mahimancina."
Ummi tace"To yanzu idan kin kirashi a waya kice masa me."?
Sayyada tayi shiru tana tunani tabbs bata da abunda zata ce masa....Tace."Ummi ke dai kiyi kokarin kar'bo min numbar ni nasan abunda zance masa."Ummi tace"To bari naje gidansu Malam Bashir din Allah yasa yana nan."
Ummi ta mike ta fita, Sayyada ta koma ta kwanta tana addaur Allah yasa a sami number a gurin Malam Bashir d'in.
18/6/2
NI DA YAYA SADAM
*BINTA UMAR ABBALE*
23
Tana cika da batsewa ta fito tsakar gidan ta samu gefe guda ta zauna tana gaishesu duk suka amsa suna me kallonta cike da mamaki!
Baba Marka tace"Jikina na bani wannan zuwan naku babu alkairi a cikinsa me yake faruwa."?
Sayyada ta fashe da kuka da shashsheka! Baba Ladidi itama sai ta fashe da kuka tana fad'in "Allah yasa dai wannan yaro ba sakin yarinyar nan yayi ba domin dama ni tuntuni jikina yake bani akwai matsala dangane da al'amarin." Sulaiman yace."Haba Baba ki daina kuka don Allah abun duk bai kai haka ba Sadam bai saki Sayyada ba har yanzu tana a matsayin matarsa."
Baba Marka tace"To alhamdullahi ku fad'a mana abunda ke faruwa." Ya kalli sayyada a nutse yace."To ke kina ji sai ki sanar musu dalilin ki na gudowa gida."
Hawayen fuskarta share tace"Baba na hakura da auran Yaya Sadam! baba marka tace"Kan wane dalili Sayyada ashe kina so ma'kiya suyi mana dariya ko."? idanunta yayi rau! rau! tace"Baba Ya Sadam! baya sona kullum sai ya zageni ya kyareni karuwarsa ma ta fini daraja a gurinsa kuma wai dole sai na daina kula Yaya Sulaiman! Baba Ladidi ba zan iya da halin Ya Sadam ba yana kwance bashi da lafiya amma ya'ki barin hankalin kowa ya kwanta kullum tashin hankali babu zaman lafiya." Tana hawaye take maganar.
Baba Marka tace"Ikon Allah me ya samu Sadam! din naji kince yana kwance babu lafiya.....Sulaimai yayi saurin cewa"'Yan boko haram! suka harbeshi a kafada kin san shi da shegen rawar kan tsiya wai dole ya isa haka zai je ya cuci kansa a banza a wofi."
Jin abunda ya samu Sadam! din yasa baba ladidi fashewa da kuka tana fad'in"Yanzu abunda ya samu Sadam! kenan amma a rasa wanda zai fad'a mana a cikinku wato idan ma mutuwa yayi shikkenan sai dai ku aiko mana ya mutu! ke Sayyada ban san baki da hankali ba sai yau! ace mijinki alburushi ya huda masa kirji ki iya tsallake shi ki tawo nan uwar me zakiyi mana a gida yarinya mara hakuri malam."!
Sulaiman yace."A'a Baba abi komai a sannu a hankali Sayyada ma tana da 'korafi ai gashi ta kawo muku 'korafinta kun juyawa magana ai idan daddawa da wari to 'bera dole yayi sata ya kamata ku duba maganar nan fa.
Baba Ladi na kuka tace"Habawa Sulaiman ai lalura ta wuce komai wallahi ban san da cewar kaima baka da hankali ba sai yau kai da ya dace ka dinga tausarta kaine zaka daukota ka dawo da ita gida yanzu meye amfanin abunda kayi."
Yace."A'a baba kar kiga laifina ni