Showing 81001 words to 84000 words out of 142497 words
Chapter 28 - NI DA YAYA SADAM Complete Document by Binta Umar Abbale.txt
shi da yaga gawar Sadam din to da hankalinsa zaifi kwanciya yasan da cewar dan nasa yayi shahada ne tunda gurin Yaki aka kashe shi kuma dama mutuwa dole ce tana wuyan ko wane musilmi. Bangaran Sule kuwa babu yabo babu fallasa ya d'an jimanta al'amarin amma ba sosai ba dama ai tuntuni yasha fada masa cewar aikin soja aikin wahala ne da wasa da rai! gashinan yayi mutuwar wulakanci mutuwar da ba'a son irinta. daya sashen na zuciyarsa kuma yana ayyana masa cewar bukatarsa ta kusa ta biya dama ta samu da zai mallaki Sayyada hankali kwance.
****
Wasu 'yan mata ne da basu wuce shekaru goma sha uku ba suke tsugune gaban wani katon ruwa dake gudana gare gare dashi ko wacce ta sanya kwarya tana d'ebowa tana zubawa cikin fantekar ta sunayi suna raye raye irin na 'kauye....Can suka dinga hango abu na biyo ruwa yana zuwa inda suke.........."Harira ke! Harira kalli can gurin kamar mutum ne." Wacce aka kira da Harira tayi saurin dagowa tana kallon gurin aikuwa lokacin fuskar Sadam! ta bayyana sosai ruwa yayo sama dashi
A guje! suka mike suka ranta ana kare suna salati da ihu!
Daf da zasu fita daga gurin ne Jatau mai jakai ya dawo daga gona ya hangosu suna gudu karce! ta daka musu tsawa tare da fad'in"Harira baku da hankali kuke guda ina fantekun naku suke."?
Suka tsaya suna haki da waiwayen bayansu Jatau! yace."Menene a cikin rafin kuke gudu ko maciji ne."?
Harira tace"Baba ba maciji bane mutum muka gani ruwa ya koroshi."
Jatau! yace."Harira yi min da hausar da zan gane." Tace."Baba muna tsaka da zuba ruwa muka ga mutum a cikin ruwan."
Jatau! yace." Ku muje na gani." makalewa sukayi suna jin tsoro....Sai da suka ga ya shige gaba sannan suka rufa masa baya gabansu na faduwa.
Suna isa Jatau ya hango Sadam! ruwa ya kawo shi bakin ga'ba.
Jatau ya dinga salati yana kiran sunan Allah! Ya juya da sauri yana kallon su Harira yace."Kuyi maza kuje ku kira min Munkaila a gona yanzu yanzu."
Da sauri suka tafi suna mamakin wannan abu.
Jatau! ya 'karasa inda Sadam ke kwace yayi bisimillah kana ya sanya hannu yana Janyo shi daga ruwan......Gabansa ya fad'i ganin kaki! na soja a jikinsa sai jikinsa ya dinga kyarma yana ji kamar ya gudu ya barshi mutumin kauye akwai tsoron soja da d'an sanda.
Daurewa kawai yayi ya janyo Sadam! din ya kurawa fuskarsa ido sai salati yake tabbas mutum ne kuma daga ni musulmi ne hannu ya sanya ya dinga danna masa cikinsa wanda ruwa ya cika yayi tatsir! dashi.
Ruwa ya dinga 'bul'bulawa ta baki ta hanci da kunnensa Jatau! ya dinga matsa masa ciki har sai da yaga ruwa ya daina fita sannan ya kyaleshi ya sanya hannu a kirjinsa domin yaji shin yana da rai ko babu.
'Das!'das yaji bugun numfashinsa in banda wannan babu abunda ke motsi a jikinsa....Hamdala yayi a cikin ransa da akwai sauran rai a tare dashi....Ya mike tsaye yana waiwayen bayansa ya hango Munkaila rataye da fatanya a kafadarsa.......Su Harira na bayansa.
Jatau! Yace."Maza ka 'karaso da sauri." Munkaila ya 'karaso da sauri yana fad'in"Baba lafiya dai wannan mutumin fa?"
Yace."Cikin ruwa muka tsince shi da alama kuma Soja ne duba kayan jikinsa da kyau." Munkaila yace."Babu tamtama soja ne Baba ga kayan jikinsa nan." Jatau! yace."Maxa ka daukeshi muje gida yanzu na duba naga akwai sauran rai a tare dashi bai mutu ba." Munkaila ya jefar da fatanyar hannunsa ya ciccibi Sadam! ya sa'ba a kafad'a suka kamo hanya suka fito daga rafin.
Kan jakin Jatau! ya kwantar dashi ya dafe bayansa Jatau yaja akalar jakin suka nufi gida.....Cikin alhini da mamakin al'amarin
'Katon Gidane ginin jar'kasa mai gajeriyar katanga da rufin azara Gidan nada girman sosai da yalwar bishiyo na dirimi da giginya da darbejiya....Dakuna biyu ne kacal a uban gidan sai bukkoki sun kai biyar tsali tsali zaka gansu a katon tsakar gidan garken dabbobi daban yake a kewaye da dangar kara....Mata biyu ne a gidan wanda suka kasance matan Jatau mai jaki! kenan.......Hansatu na share tsakar gida Abu kuma na surfen dawa a katon turmi hira sukeyi cikin fahintar juna, Su Jatau! sukayi sallama cikin gidan.
Amsawa sukayi suna masa sannu da zuwa Ya amsa a gurguje Yace."Abu maza ayi shimfid'a a waccar bukkar dake gyare nazo da 'bako.''
Abu ta aje abinda takeyi da sauri ta shiga dakinta ta dauko tabarmar kaurani ta nufi bukkar da aka umarce ta shimfida tabarmar tayi ta kawo wani zani ta shimfida ta kai ta fito da sauri ta dauko kofin silvar daga dakinta ta bude randa ta ciko ruwa a kofin ta kai ta ajiye.
Tana fitowa Munkaila ya shigo gidan da Jaki wanda Sadam! ke kwance akai......Hansatu na gaban murhu tayi saurin mikewa tana dage kirji "Malam me zan gani Soja a cikin gida." Yace."Hansatu ku kwantar da hankalinku kunji ko wannan bawan Allah a cikin ruwa muka tsinceshi yana bukatar taimakomu."
Jikinsu yayi sanyi da jin abunda mijinsu ya fad'a.....Jatau ya taimakawa Munkaila suka shigar da Sadam! cikin bukkar yace."Munkaila yi kokari ka cire masa ji'kakkun kayan nan ni kuma bari na shigo da wuta dakin ya samu dumi."'
Munkaila yace."To Mikewa yayi ya nufi dakinsa ya dauko wani kod'addan yadi daga cikin kayansa ya koma bukkar.....Sadam! na kwance kamar matacce Munkaila ya cire masa kayan sojojinsa ya sanya masa wannan yadi kana ya gyara masa matashi ya kwantar dashi.....Jatau! ya shigo da wuta cikin kaskon 'kasa ya aje gefe ya zauna gefan Sadam! din ya sanya hannu yana me dafa kirjinsa har yanzu yana kirjin na harbawa.....Hannu ya kai saitin hancinsa wai ko zaiji hucin numfashinsa yaji shiru.....Munkaila yace."Baba mu bari zuwa dare idan numfashin nasa bai dawo ba sai mu kira Mai magani ya duba shi.
Jatau yace."Insha Allah kafin dare numfashinsa zai dawo dai-dai! Saboda ya sha'ki ruwa da yawa ne ya sanya amma kaga yanzu babu wani sauran ruwa a cikinsa duk na matse shi." Shiru sukayi tare da zubawa fuskar Sadam din ido suna mamaki gaskiya duk inda akayi a gurin ya'ki ya samu wannan hadarin shiyasa suke so ya dawo hankalinsa ya fada musu a wane gari yake su sada shi da danginsa.
_Yau bani da charge sosai kuyi manège nagode_
NI DA YAYA SADAM
*BINTA UMAR ABBALE*
35
Sunfi rabin awa zaune gabansa suna kallonsa Jatau! ya dage sai tofa masa addua yake da iyakacin abinda Allah yasa ya sani Sadam! ko gezau yana nan inda yake baya motsa koda d'an yatsansa.
Munkaila da ya gaji da zaman jugum! sai yayiwa mahaifin nasa sallama ya koma gona.
Sai da lokacin cin abincin rana yayi sannan Jatau ya gusa daga inda Sadam! yake shima a gurguje yaci abincin ya koma dakin.
Hansatu ta 'leko dakin tana fad'in"Malam yau ba zakaje ciyawa ba kenan."?
Yace."Hansatu ina naga ta ciyawa wannan yaro na cikin wannan hali wallahi tausayinsa nakeji nasan duk inda ya fito to suna can hankalinsu a tashe."
Tace"Gaskiya kam Malam al'amarin akwai abun mamaki a ciki adduarmu itace Allah ya sanya ya farfad'o lafiya sai ya shaida mana daga inda yake." Abu ta le'ko dakin itama ta tsaya ana maganar da ita dukaninsu kallon Sadam din suke suna tausayawa rayuwarsa.
***
Cikin rashin 'karfin gwiwa suka shigo gidan....Abbah ya zube kan kujera yana goge gumin goshinsa
Shi kuwa Sulaiman firji ya bude ya dauko gorar ruwa mai sanyi a maimakon ya mikawa mahafin nasa sai kawai ya zauna kan kujera yana shan abunsa.
Hajiya Fatsima ta fito daga dakin ta gansu zaune Abbah ya rufe fuskarshi da hularshi shi kuma Sulaiman da robar ruwa a hannunsa, ganin yanayinsu ya sanyayar mata da jiki ta 'karaso a hankali ta zauna Abbah ya cire hular fuskarshi yana kallonta.....Mammah tunda taga yanayin mijin nata sai ta soma hawaye baki na rawa tace."Shikkenan mafarkin Sayyada ya tabbata ko Abbah."!?
Yayi shiru yana kallonta yama kasa cewa komai sai kukan zucci da yake.
Kuka tasa tana tana fad'in"Innalillahi wa'inah ilaihi raji'una."!!! Wannan yaro ashe dama wannan aiki ne ajalinka ashe dama bani da rabon sake ganawa da kai ashe babu rabon inga 'Yayanka! na yafe maka Sadam! na yafe maka Ubangiji Allah ya jikanka da gafara."
'Karar da Sayyada ta 'kwallara itace ta sanya duk suka waiwayo kanta Ai tuni ta zube a gurin......Sulaiman ya karaso da robar ruwan hannunsa ya kwara mata a fuska.
Ajiyar zuciya ta sauke ta mike zaune a razane! ta sake 'kwallara wata karar tana zabure-zabure!! Alhaji Auwal da kansa yazo ya rirrike hannunta yana tofa mata adduo'i, ta dinga binsu da kallo wani iri "Mammah da gaske kike abunda naji kina fad'a? dama wai! da gaske ne Mammah kece fa kikace min mafarki baya zama gaskiya yanzu da gaske ne sun kashe min mijina masoyina farin cikina rabin rayuwata!!!!! Na shiga uku Allah ka kasheni na huta! bani da sauran amfani a wannan duniyar tunda babu rabin raina a cikinta."
Sayyada sambatu take tana kuka kamar wata zautacciya Mammah da taga tana kokarin kauce hanya sai tayi saurin rufe mata baki da hannunta tana girgiza mata kai da fadin salati zakiyi ba ihu! ba Sayyada a yanzu Sadam! babu abunda yake bukata a gurunmu sai addua itace kaunar da zamu nuna masa."
Da Sauri ta soma fad'in"La'ilahailllahu Muhammad rasulilihi sallalahu alaihi wasalam! Ta dinga nanatawa tana rarraba ido gumi sai tsatstsafo mata yake a jikinta.....Cikin ikon Allah sai ta soma samun nutsuwa ta kalli Abbah a nutse tace"Abbah ina gawar mijina take."!?
Sai a lokacin zuciyarsa ta karye wani zazzafan hawaye ya shiga sintiri a fuskarsa.
Tace."Abbah ka daina masa kuka kana so ya samu rahamar Ubangiji ko."? Ya daga mata kai tace"To kadaina kuka Abbah.'' Yace."Na daina Sayyada, Kiyi hakuri da abunda zan fada miki yanzu." Tayi shiru tana kallonsa Yace."Sun kashe Sadam sun 'batar da gawarshi Sayyada neman duniya munyi a wannan guri bamu ganshi ba sai gajiya mukayi muka dawo gida kiyi hakuri kiyiwa mijinki addua nasan duk inda yake yana cikin rahamar Ubangiji."
Wasu zafafan hawaye masu radadi suka shiga gudana a fuskarta bakinta ya dinga rawa tana so ta cigaba da fadin kalmar La'ila ha'illahu amma harshen ya hard'e sai tayi shiru kawai tana fad'a a zucci sunkuyar da kanta tayi 'kasa ta kurawa guri guda ido tana kallo.......Sulaiman da ya sanya mata ido yaji wani kafirin kishi na kama shi Gaskiya Sayyada na son Sadam mutuka yanzu idan ya aureta ya za'ayi ya sanya ta cire son Sadam din daga zuciyarsa.....Wani sashe na zuciyarsa yace."Kayi addua ma Allah yasa ta yarda ka aureta, Ji yayi gabansa ya fad'i! ya kalleta kanta a kasa....Sai ya shiga zance da zuciyarsa tana fad'a masa ai dole ma ta aureka ko kuma ka 'bullo mata ta bayan gida.
Kafin kice kwabo labarin mutuwar Sadam! ya baza garin kaduna da kewayenta Labarin mutuwar Sadam da rashin ganin gawarsa ya isa *Dabi* Baba Ladidi sai da ta suma saboda tsananin firgice da tashin hankali suka dinga kuka tare da yi masa addua duka dangi suka tarkato garin kaduna domin yin zaman makoki.
Koda General Ya samu labarin cewar Alhaji Auwal ya kafa rumfuna na zaman makokin Sadam! yaje ya same shi tare da fad'in"Ya sallami jama'a domin shifa yana tantama kan mutuwar Sadam din jikinsa na bashi yana raye don haka ma ya 'kara tura jami'an tsaro suka sake bunkice a gurun da kewayen 'kauyen da al'amarin ya faru.
Da jin wannan magana da general yazo da ita sai Sulaiman ya tayar da hankalinsa takaici duk ya isheshi ya za'ayi ma ace Sadam din bai mutu ba shi da yana da yanda zaiyi to dashi kanshi general din bai kai labari ba da har zaizo ya dawo masa da hannun agogo baya.
******
Fitilar a ci bal-bal ce ke haska dakin!! shiru bakajin komai sai kukan gyare dake tashi a gidan da alama duk mutanan gidan sunyi bacci abunsu.........Harira ta fito daga dakinsu ta dauki buta a bakin 'kofa ta nufi bandaki....Minti biyu ta fito da butar a hannu sai ta soma jin wani irin ihu!! na tashi daga d'akin da 'bakon gidansu ke ciki a guje! ta jefar da butar tayi dakin babansu tana kwala masa kiraaa Kafin ma Jatau ya fito tuni Munkaila ya isa d'akin a guje!
Sadam! ne zaune ya rirri'ke! kanshi da hannunsa duka biyun yana wani irin ihu! mai firgitarwa! Abunka da dare tuni ko ina ya dinga amsawa.
Jama'ar gidan duk suka rud'e suna salati Jatau! da Munkaila suka rirrikeshi suna tofa masa adduar duk da tazo bakinsu.....Saboda tsabar yanda yake ji da 'karfi duk ya watsar dasu ya zabura! a guje! zai futa.....Munkaila dake shima ingarma ne kuma kakkarfa sai ya tare kofar fita ya tura Sadam! din ciki da karfi Jatau! ya jashi ya zaunar dashi hannunsa ya rike tam tam! Munkaila ya koma bayansa ya dafe kafadunsa....Sadam! ya dinga binsu da kallo yana masu maganar kurame!!! da hannu yake magana yana so yace wani abu amma bai san me zaice ba.
Albarkacin adduar da suke masa ta sanya ya samu 'yar nutsuwa dakin yayi shiru sai saukar nuffashinsu da sautin tofin da Jatau kewa Sadam din.
A hankali Munkaila yace."Bawan Allah meye sunanka."?
"Bawan Allah meye sunanka."? Shima ya fad'i maganar da Munkaila ya fad'a.
Duka suka kalli junansu cikin d'umbin mamaki!
Jatau! Ya dafa kad'arsa Sadam ya juya yana kallonshi.....A hankali Jatau yace." Bawan Allah daga wane gari ka fito."?
"Bawan Allah daga wane gari ka fito."? ya sake maimaita maganar Jatau!
Hansatu tace" Anya kuwa wannan mutumin nada hankali."? A take ya sake maimaita maganar Hansatu! Duk sai cikinsu ya d'uri ruwa dan har Abu ta gudu d'akinta cikinta sai kartawa takeyi dama ita matsoraciya ce sosai dan tun sanda Sadam din ya fara kurma wannan ihun take makyarkyata.
Munkaila yace.''Anya Baba zamu zauna da wannan mutumin cikin wannan halin kuwa inga gwara kawai mu kaishi cikin gari a kaishi asibiti irin nasu." To da yake wannan magana da Munkaila yayi tayi tsayi sosai yasa Sadam! din bai iya maimaitawa ba sai dai fa idanunsa kan bakunansu suna magana in sunyi maganar da bata da tsayi sai ya amshe idan kuma tayi masa tsayi sai dai ya bisu da kallo. Haka suka dinga yi har lokacin sallah asubahi yayi Munkaila ya riko hannunsa suka fito tsugunawa yayi yana alwala shima sai ya zuba ruwa a buta ya dinga kwatanta yanda Munkaila ke alwala..... Munkaila ya rike hannunsa suka nufi massalaci.
Tsawon kwanaki uku ana bunkice ko Allah zai sanya a samu labarin wani abu da ya danganci Sadam din duk babu wani labari an saka cigiya gidajan tv da redio babu wani labari.....Dole tasa General ya hakura akayiwa Sadam! zaman makoki kamar yanda al'ada ta gadar........Captain Saleh Sulaiman bukatarsu ta biya al'amarunsu suke hankali a kwance, duk wannan abun dake faruwa Habu na kwance gadon asibiti bai san ina kansa yake ba domin ba karamin illah Saleh yayi masa ba, kuma cikin sojojin da suka san da yanda al'amarin ya faru babu wanda yayi kuskuran fad'awa general yanda al'amarin yake......Shi kuma Captain Saleh kullum cikin shiri ya zaiyi ya 'karasa Habu dan yasan daga zarar ya dawo hayyacinsa to zai tona masa asiri ne.
****
Sayyada ta rame ta fyad'e! kullum tana nad'e jikin Baba Ladidi tana hawaye itafa cikin wannan halin duk wanda zaice mata kar tayi kuka to gani take ma'kiyinta ne ya za'ayi ta rasa masoyinta ace ba zatayi kuka ba....An kashe mata miji an jefar da gawarsa kuma ace ta kwantar da hankalinta taci abinci tayi walwala ai ba zaiyu ba......Wani lokacin har mamakin mutan gidan take Mammah da Abbah kamar basu suka haifi Sadam din ba kwana uku kacal har sun sake suna hira da cin abinci kai har dariya ma in ta kama yi suke ba kamar Sulaiman da kwata kwata yake nuna abun bai dame shi ba kullum idan zaka ganshi cikin walwala da sakewa kuma ya sheka kwalliyarsa babu abunda ya dameshi shiyasa takejin wani irin haushinsa cin ranta duk wannan mutuncin nasa da take gani ta daina ganinsa kuma tana nan ta rike a ranta don har yanzu bai mata gaisuwar Sadam din ba shiyasa ta kullaceshi a cikin ranta.......Mariya da Ummi sunzo sun taya ta jimami Ummi har dasu kuka tana tausayawa kawarta mutuwar miji ba karamin tashin hankali bane.......Amina ma tayi kuka amma ba kamar Sayyadar ba domin itama kwana uku har ta manta tana hirarrakinta shiyasa Sayyada ko kula ta ba tayi ashe dama duk son da take ikirarin tanayi wa Sadam din duk na 'karya ne tunda gashi har ta manta tana sha'anin gabanta.
*****
Babban asibitin dake cikin garin jos plateau shi suka yanke sha'awar kai Sadam! domin a duba lafiyarsa su suna ganin kamar abunda yake yi irin na masu ta'bin hankali ne shiyasa suka yanke wannan shawarar a tsakaninsu.
Al'amarin Sadam! akwai tausayi da tashin hankali da rana zai yini kalau kalau amma anacewa dare yayi ya hau buge-buge da iface!iface! yana rirri'ke kansa duka gidan hankalinsu sai ya tashi Sadam yakan dauki awa daya ko sama da haka cikin wannan hali duk sai ya jigata kansa! ya jigata masu rirrikeshi.......Labari ya soma watsu wa a cikin 'kauyen kunsan al'amarin kauye abu kadan sai su hau zuzuta shi! labari ya iske Mai gari har fadarsa cewa Jatau mai jakai ya tsinto mahaukaci a ruwa ya kawo shi cikin gidansa yana hana mutane bacci da daddare.
Mai gari ya sanya aka kira masa Jatau! Yace."Naji labari daga gurun mutanan gari cewar ka tsinto mahaukaci cikin ruwa yau tsawon kwana biyar kana tare dashi a cikin gidanka kuma a cikin garina ban sani ba shin meye manufarka ta aikata wannan aiki."
Jatau! yace."Ranka shi dad'e wannan bawan Allah na tsince shi ne a cikin rafi baya cin hayyacinsa na daukoshi na kaishi gidana tsawon kwana uku ina masa taimako irin namu har Allah ya sanya ya farfado sai dai kash a maimakon ya farfado da nitsuwarsa sai ya farko cikin rashin hayyaci ranka shi dade al'amarin wannan yaro akwai tausayi a cikin duk mutum mai imani ya gani sai ya tausaya masa, bai iya komai ba sai an koya masa tamkar yaron da aka haifa yau haka yake kuma idan akace maka dare yayi to ya dinga ihu! kenan yana rirrike kai wannan shine dalilin da ya sanya muka yanke shawarar kaishi babban asibitin dake cikin gari."
Mai gari yace."Wannan al'amari kai ta shafa Jatau! sanin kanka ne ni bana son wani ba'ko ya shigo min gari