Showing 96001 words to 99000 words out of 142497 words

Chapter 33 - NI DA YAYA SADAM Complete Document by Binta Umar Abbale.txt

09 Dec 2024

50497

alkairi." Aunty Luba ta amsa da ameen y rabbi kanwata.


Suna zaune suna hira sukaji shigowar motarsa gidan har ya dawo daga kai su Baba ladi gida Sayyada ta mike zumbur tayi hanyar dakinta aunty Luba tace"Kar ki bude komai bugun da zaiyi." Tace"To aunty ai ba sai kin fada ba."


Ya shigo cikin nishadi yana karkada key ganin Lubabatu a zaune a palo sai ya watsa mata banza kallo wai shi me amarya ya nufi dakin Sayyada yana jan kofar ya jita gam gam! buga kofar yayi a hankali yace."Baby bude na dawo daga kai su Baba." Shiru tayi masa ya dauka abun wasa ne ya dinga bugun kofar yana fadin"Baby ko kina toilet ne? ki bude min kofa mana." Sayyada na jinsa tayi shiru Ita kuwa aunty Luba tv ta kurawa ido tana kallo abunta.


Yafi minti ashirin a tsaye a gurin yana aikin buga kofa Sayyada bata bude masa ba a fusace! ya juyo yana yiwa aunty Luba mugun kallo kamar zaice wani abu sai ya kuma ya fasa ya buge rigarsa ya kama hanyar futa ransa a mugun bace.


Lubabatu na jin futarsa da mota tace"Sayyada ki bude ya fita." Babu kunya Sayyada ta bude kofar dakin ta fito aunty Luba tace"Baby kina wahalar min da miji fa."! Sayyada tasa dariya tace"Aunty wannan mijin naki ai shine ya jawowa kansa."


Dariya sukayi tare kafin su shiga kicin su soma hada sanwar dare.


Duk wani abu da zata bukata naci da sha Lubabatu ta kai mata dakinta saboda haka ganin tara na dare tayi sai sukayi Sallama da juna Sayyada ta shige dakinta ta kulle Aunty lubabatu ma ta shige nata dakin ta kulle da mukkuli ko wacce tayi bacci cikin kwanciyar hankali.


Gogan ya dawo ya dinga bugu tsakanin kofofi guda biyu babu wacce tayi gangancin bude masa haka ya hakura ya kwanta a palo yana murkususu Sulaiman mugun hariji ne da baya gajiya da sex ko yanzu ya sauka daga kan mace daga zarar yaga wata to sha'awarsa zata tashi yau ma yaci burin hawa kan Sayyada ganin yanda ta saki jiki dashi harda zama kusa dashi tana masa hira shine ya dau rai ya saka akanta ashe munafurci ne.


Da safe da ya tashi sai yayi zaune a palo yana muzurai koda aunty luba ta fito ta tarar dashi zaune a palo sai ta gaisheshi ba tare da ya amsa ba ya rufe ta da fada har da cewa yaga alamar kamar itace take shiga tsakaninsa da Sayyada to mutukar yayi bunkice yaga hakane to sai ya saketa.


Murmushi kawai tayi ta wuce jahilci ne yake damun Sulaiman in banda haka abu kadan sai kalmar saki ta biyo baya Allah ya kyauta


Tana kicin tana aiki zuciyarta na tafasa da bacin rai wai shin meye riba a auranta da Sulaiman da har yake mata barazana da saki da kyar ta kammala break fast ta fito nan ta tarar dashi yana ta bugun kofa kamar wani mahaukaci fadi yake"Gwara ma ki bude kofa don wallahi komai abunki sai na karbi sadaki na ni ba Shashan namiji bane irin Sadam da zan tsaya ina kallonki ni cikakken namiji ne mai iko a gidansa."


Sayyada na jin haukan da yake tace"Mahaukaci kawai so take kawai yayi ya gama ta fito lokacin makaranta yayi har yana nema ya kure Saliha sai kiranta take a waya.


Sule ya bar kofar dakin a fusace dakinsa ya nufa yayi wanka ya shirya ya fito Luba tace"Zaka fita baka karya ba kuma." Wata tsawa da ya buga mata sai da ta tsorata ta tabe baki tare da fadin ",A sauka lafiya ni bani na kar zomo ba rataya aka bani." Baice komai ba kada kai ya fice daga gidan


Bayan futarsa da minti biyar Sayyada ta fito cikin hijab kafadarta rataye da jakarta suka gaisa da aunty Luba a gurguje ta karya ta wuce makaranta abunta.


****
Yau juma'a yaune aka daura auran Harira da Sadam kan sadaki dubu goma wanda jama'a suka shaida Sadam ya bayar da hannunsa limami na unguwar ya zama waliyinsa an daura aure cikin aminci da yardar Allah aka gudanar da sabgar buki a gidan Jatau dake cikin ungywar Samegu karfe takwas kuma aka wanke amarya tsaf 'yar unguwa abokanan arziki suka rakata dakinta na aure.


Munkaila da ya zama yayan amarya shine ya zama kuma abokin ango wannan dalilin ya sanya Sadam! din ya shiga gidansa shi kadai saboda yana kunyar yace Munkaila yazo ya rakashi siyan baki.


Hannunsa rike da 'kunshi leda biyu sai maiko take yayi sallama dakin amaryar tasa.....Harira na lullu'be cikin mayafi ta amsa masa sallamarsa tana shashshekar kuka.....A hankali ya karaso inda take ya zauna yana kallonta......Hannu yasa ys dauke gyalan da ta lullube jikinta dashi lokaci guda gabansa ya fad'i! ganin tana masa yanayi da wata hallita da ya sani ya tsurawa fuskarsa ido sosai yana kallonta.......Harira ta dinga sunkuyar da kanta tana jin kunya yayi murmushi a hankali yace."Kiyi hakuri amaryata.'' Daga kai tayi yace."Tashi muyi sallah nu godewa Allah." A hankali ta tashi ya bita da ido yana kallo da san tuno wani abu da ya shud'e a rayuwarsa girgigza kai yayi ya kama hannunta suka fita tsakar gida dama da ruwa a buta sai suka daura alwala suka dawo ciki.


Sallah sukayi raka'a biyu suka godewa Allah Sadam ya bude ledar da ya shigo da ita suka zauna suna ci a hankali a hankali yake jin wani abu na d'arsuwa a cikin zuciyarsa a game da Hariran sai yake ganin kamar ya ta'ba wata mu'amula da mace a wani lokaci a take ya dinga jin sha'awa na yun'kuro masa ya kalli tudun kirjin Harira suka bashi sha'awa baiyi tunanin komai ba ya dora hannunsa akai Harira ta takure jikinta tana masa kuka......Lokacin hankalinsa baya tare dashi bai saurari kukan da take ba ya dauketa cak! ya dure kan gado ya kwanta a kanta yana sassanata tare da wasa da sassan jikinta.........To daga haka kuma sai al'amura sukayi ta faruwa Sadam ya raba dare kan yarinyar mutane sai da duk ya zubar da wani abu dake damunsa tsayin shekarun da suka wuce ya mayar da Harira cikakkiyar mace ya amshi budurcinta yaji dadin sosai da ita kuma yana mutukar alfahari da kasancewarta a matsayin matarsa.


****


To tsayin sati biyu gidan Sulaiam zaman dai da kuka sani irinsa ake sai abunda ya sake 'karuwa domin kusfa kusfa na iskanci Sayyada babu wanda ba tayi wa Sule shi kuma kamar maye baya gajiya da sambatu da rarrashi hade da bugun kofa duk daran duniya watarana kuma idan jarabar ta ciyoshi sai ya nemi Lubabatu ita kuma tace''Bai isa ba nan zaiyi ta zaginta yana fadin dama ai bata da amfani a gurinsa kuma lokaci kadan yake jira zai saketa.......Taikaci yasa aunty luba tayi ta kuka don akwai ranar da ta hada kayanta tace tafiya za tayi ta gaji da wulakanci Sayyada ta dinga kuka tana bata hakuri da kyar ta yarda ta hakura.


****
Sadam amarci yake sha sosai da matarshi yayi 'kiba sosai yana kuma neman kudinsa yanda ya kamata ba irin kauyen da baya zuwa saro kayan abincin danginsu shinkafa masara dawa wake gero da sauransu yanzu haka shagunansu biyar duk na siyar da kayan hatsine alhamdullahi gidan Jatau sai godiyar Allah


***


Kimanin wattani biyar kenan da faruwar al'amarin ta 'bangaran Sadam an samu cigaba matuka domin dai yanzu Harira ciki ne da ita dan wata biyar dan ana tsammanin ma haduwarsu ta farko ta sameshi.....'Bangaran Sulaiman kuwa al'amura duk san jagube domin ta kai ta kawo Sule ya gane da sanya hannun Lubabatu kan abunda Sayyada take masa ba tare da bata lokaci ba ya dankara mata saki biyu lokaci guda ya koreta.......Sayyada na kuka ta nufi family house dinsu ta fada musu abunda ke faruwa aikuwa Sulaiman ya raina kansa domin kowa shi ya bawa rashin gaskiya Mammah tace yayi maza yaje ya dawo da matarsa idan ba haka ba to babu ita babu shi.


Haka yaje bikon Lubabatu dake dama iyayenta dattawan arzikine ba tare da doguwar magana ba suka maido ta dakin mijinta.....Sai kuma ya sauya wata muguntar ya daina shigo musu da kayan abinci sai da ya basu dubu daya itace safe da rana da daddare su biyu a take suka shiga cikin yanayi na wahala da takura sunfi wata uku cikin wannan yanayi aunty Luba taga suna cutuwa sai ta sameshi tana masa magana yace!"Ita ta dinga amfani da kudin ba sai ta ciyar da Sayyada ba dama ai da ita kadai yake hutawa idan bukatarsa ta tashi ita kuma Sayyada taje ta ciyar da kanta.


Aunty Luba ta zauna tana so ta fahintar dashi ya buge rigarsa ya kara gaba kwana biyu wata asharariyar bazawara ce ta dauke masa hankali sosai yake jin dadi da ita kudi kuwa ta ko'ina sakar mata yake tayi bushasharta.


****
Alhamdullahi Captain Habu ya samu sauki bayan doguwar jinyar da yasha wanda mutane da yawa suka cire rai dashi to dama hakane cuta ba mutuwa bace in mutum ya mutu to tabbas kwanansa ne ya kare babu wanda baije dubashi ba lokacin da yake kwance yana jinya banda Captain Saleh wanda ya dinga shirya plan iri iri kan ya cimma burinsa a kansa domin ganin ya rabashi da duniyar Allah bai bashi nasara ba Captain Habu ya fito daga asibiti da kudirin tonawa Saleh da mukarrabansa Asiri sai dai kash! wanda zasuji maganar dashi wato general Abdulsalam babu lafiya tun bayan mutuwar Sadam jikinsa ya kasa dad'i yanzu haka yana can kasar hindiya domin duba lafiyarsa ka'idar asibitocin hindu basa sallamar mara lafiya sai sun kwantar dashi ya karbi magani tsawon shakara ko kuma rabin shekara wata shida kenan to sun rike General din sai ya dauki tsawon shekara guda tukkuna zasu sallameshi a lokacin suke tunanin ya dawo normal dangane da lalurar dake damunsa.


Bracck din ta 'baci sosai domin mutumin da maye gurbin general halinu daya dasu Saleh ya sake dorasu a turba mara kyau cin hanci da rashawa dannewa me hakki hakkinsa da dai sauransu duk wannan abun ba wani abu bane a gurinsu yanzu kowa abunda yake so shi yake aiki kuwa sai wanda yasa kansa yake.......... General Abba Jaddah ya bawa ko wane soja 'yancin yin abunda ya ga dama koda Captain Habu yaga abunda ke gudana a bracck din duk sai yaji aikin soja ya fita da ransa dama wasu ke 'bata wasu babu abunda su Saleh suke sai mugunta da kar'be kud'ad'en mutane kuma ga aiki 'kiri-'kiri suna gani su'ki futa ko sun fita basa komai sai sunga zasu samu sannan suke mi'kewa daga inda suke. Haka dai ya hakura ya shiga cikinsu yana kara nazarinsu gabadaya da kuma daukar muryoyinsu a lokacin da suke kan aki yana so komai zaiyi to yayi shi da hujja.


Alhamdullahi karatun Sayyada ya mika sosai domin har sun soma shirye shiryn zuwa trining jahar kano tashar Freedom redio..........Sun shirya tsaf sun tsayar da ranar tafiya tare da wakiliyarsu malama Rabi'atu. wacce zata jagoranci tafiyar tasu.


A gajiye ta isa gidan ta d'ebo rana da yunwa ta zube kan kujera tana firfita da gefan mayafinta Aunty Luba tace"Sayyada sannu da hanya kinsha rana da gani." Tace"Wallahi kuwa aunty al'amura sun dauki zafi ashe haka abun yake aunty ina ganin kamar karatun nan da nake bashi da wani wahala kan sauran sai da aski yazo gaban goshi sannan na gane bani da wayo aunty duk kokarin da nake a gida wallahi sai anci gyarana yanzu dai mun tsayar da rana zamu tafi training kano insha Allah."


Aunty Luba tace"Waye ya fad'a miki karatun jarida bashi da wahala a hakane kike ganin bai da wuya amma aiki ne mai wahala da kuma wasa da rai don idan aikin had'ari ya taso ko ina ne sai kinje kin dauko rahoto tunda kinji kin gani kin amince kinga kuwa shi da aikin soja suna tafiya dai-dai ne sai dai na soja yafi da wasu abubuwan."


Tace"Aikuwa na gani aunty in ba dan na mai da hankalina ba a kwanakin baya da sai dai inga anayi wallahi amma dai yanzu komai ya dai-dai ta."


Aunty Luba tace"To alhmadullahi yanzu yaushe kuka tsayar da ranar tafiyar."? Tace"Ranar litinan me kamawa saura kwana hudu kenan.'' Tace"Sai ki fadawa Sulaiman ko." Sayyada tayi shuru tana nazarin maganarta itafa tunda ta samu ya daina takura mata sam bata son abunda zai sake hadasu yanzu sun kai sati hudu basa magana watarana gata gashi zai wuce ko kuma tana tsaye a kan titi zaizo ya wuceta a mota fuuuuu! baya ta'ba rage mata hanya to itama tafi son haka domin tana da kudin abun hawa wanda Abbah ke bata duk sati.....Tace",Yanzu dai abinci zanci sai na wuce can gida na sanar musu in yaso idan ya dawo da wuri banyi bacci ba sai na fada masa."


Luba tayi shiru cikin damuwa tace"Sayyada babu abinci a gidanan wallahi domin yau ma 'yar dubu din da yake bayarwa bai bayar ba yayi ficewarsa tun safe haka nake zaune in banda ruwan tea din da na dafa mana muka kur'ba."
NI DA YAYA SADAM


*BINTA UMAR ABBALE*


41
Sayyada ta shiru tana mamakin ba'kar mugunta irin ta Sulaiman yanzu ace kamarsa yana da uban kudin da bai san iya adadinsu ba amma yake wannan rayuwar a gidansa, tasan saboda ita ya tsiri hanasu abinci tunda ai da can ba haka yake ba gaskiya idan hakane to an shiga hakkin Lubabatu tunda laifin wani ai baya shafar wani azabar da Sule yake gana musu tayi yawa.


"Aunty ni dai na yanke shawarar i dan naje gida yanzu zan sanar da iyayensa halin da ake ciki gaskiya abun yayi yawa aunty Luba Ya Sulaiman bashi da imani wallahi."


Tace"Sayyada kar ki fad'awa kowa domin idan kin fad'i wannan maganar to za'ayi tone tone domin zasu zaunar dashi su tuhume shi a kan me yake hanamu abinci shi kuma zaice ga dalili kinga daga karshe duk laifin zai dawo kanki gwara kawai kiyi shiru da bakinki tunda Allah yasa kwana biyu hankalinsa ya dauke daga kanki shikkenan amma daga zarar kinyi wannan maganar a gida to labari zai sha bambam."


Sayyada tace"Gaskiya hakane aunty Luba domin dama tuntuni na fahimci Ya Sulaiman hanya kawai yake nema da zai had'ani dasu Abbah ba zanyi maganar ba amma nasan yanda zanyi kar ki damu aunty Luba."


Tace"Yanzu kafin shigowarki mukayi waya da Asiya tace tana kan hanyar zuwa na sanya ta ta 'karbo min kud'i gurin babban wanmu da bai dad'e daga dawowa daga tafiya nasan dai 'yar dubu ashirin zan samu daga gurinsa sai mu siyi kayan abinci muga abunda Allah zaiyi."


Tace."Shikkenan aunty nima zanyi kokarin 'karbar kud'ade gurin Abbah kafin tafiyarmu insha Allahu babu abunda zai gagara." Mikewa tayi ta nufi dakinta jiri sai dibarta yake tsabar yunwa da tunani Sunyi mata yawa tayi wanka ta fito ta shirya cikin atampa sauya hijab har kasa ta fito da shirin zuwa gida.....Aunty Luba tace"Ki gaishe mun da Mammah da kyau! Sayyada tace"Zataji insha Allahu. Ta kama hanya ta fita daga gidan hankalinta a kwance tunda ta samu d'an anace ya rabu da ita.


Mammah taji dadin ganin Sayyada sai dai ba taji dadin yanda ta ganta tayi zuru zuru ba tace"Sayyada wai wannan ramar da kike ta mecece ne bana son ganinki a haka wallahi."


Cikin 'Kokarin kauda danuwar dake damunta tace"Babu abunda ke damuna Mammah sha'anin karatu ne kawai wallahi yanzu ma zuwa nayi in fada muku cewar an tura mu kano domin sanin makamar aiki a wani gidan redio dake jahar tafiyar zata daukemu tsawon makwanni biyu insha Allah."


Mammah tace"To a babu damuwa ina fatan kin sanar da mijikin ki ko." ? "A'a bai sani ba so nake ya dawo sai in fada masa na dai fara zuwa na sanar muku ne." Tace"To Allah ya bada sa'a Sayyada." ta amsa da ameen."


Sayyada ta taimakawa Mammah suka shirya daining kana sukeje sukayi sallahar magariba a lokacin ne kuma Alhaji Auwal ya shigo gidan Sayyada tayi masa barka da zuwa da kar'bar abunda ke hannunsa yace."Sayyada karatu ya 'boyeki ba'a ganinki ko." Tace"Wallahi kuwa Abbah.'' Yace."Allah yayi jagora."


Sai bayan da ya nutsu ne ta fada masa abunda yake tafe da ita shima budar bakinsa sai yace."Ina fatan kin sanarwa da mijinki ko." Tafada masa abunda tacewa Mammah yace."To babu laifi wannan tafiyar taki tana bukatar tallafi zan tura miki kudi ta account dinki sai kiyi amfani dashi Allah ya bada nasara." Godiya tayi sosai tayi musu sallama Mammah ta ciko fulas da abinci ta mikawa Sayyadar tare da fadin"Tunda kin'ki ki zauna kici to ki tafi dashi kwaci da 'yar uwarki."


Sayyada taji dad'in hakan sai ta 'karba tana godiya sosai take kaunar mutanan domin karamcinsu.....Tun a cikin a dai-dai tasu taji shigowar alert wayarta koda ta duba sai taga sa'kon Abbah 50k ya tura mata duba hamsin sosai tayi murna kwarai da gaske ta sanya mai a dai-dai ta din ya ajeta dai-dai P.O.S ta cire dubu ar'bain ta bar goman a cikin accont din ta nufi gida da kudin.


Tana shiga gate din gidan taga motar Sulaiman yau ya shigo gida da wuri kenan? bata ta'ba jin fad'uwar gaba a kansa ba sai yau ta hau addaur rinjaye domin yanzu wani irin tsoransa takeji.


Kafin ta shiga palon ta soma jiyo hargaginsa yana zagin Lubabatu " Wallahi ki kiyayeni Lubabatu kamar ni zaki kalla ki nuna da yatsa har guda nawa kike? kar fa ki manta iyayanki basu da komai sai da na zama cinsu na zama shansu kafin na aureki saboda ke butulu ce zakice min bani da hallaci wani irin hallaci kike so nayi miki? Wallahi duk sanda kika sake yi min wata magana a gidanan to a ranar zan datse ragowar igiyar da tayi saura a tsakaninmu shikkenan yar da kwallon mangwaro na huta da 'kuda."


Tace"Ai yanzu ma bata 'baci ba ko ka dauka idan ka sakeni zanji ciwo wallahi ko yanzu ka sakeni bani da asara ko banza nasan na rabu da bakin mugu azzalimi nasan kuma sai ubangiji ya mu sanya min da wanda ya fika sannan kana magana kan cewa ka ciyar da iyayena da kudinka a lokacin babu wanda ya sanya ka siyan abinci ka kai gidanmu kaine ka sanya kanka tunda dai ba a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login