Showing 111001 words to 114000 words out of 142497 words

Chapter 38 - NI DA YAYA SADAM Complete Document by Binta Umar Abbale.txt

09 Dec 2024

50499

sai yau da safe amma dai yanzu komai ya dai-daita insa Allah."


Yace."Dr meye ya jawo mata shiga wannan yanayin jiya har dare muna tare da ita mun jima muna hira naga babu wani alamun ciwo a tare da ita.


Dr yace."Hakane kasan al'amarin Ubangiji babu yanda ba yayi amma mu kanmu munyi mamakin abunda ya jawo hakan muna tunanin jinin da aka 'kara mata ne bai gama ratsa jikinta ba amma dai yanzu mun shawo kan matsalar insha Allahu zata warware."


Yace."Allah ya yarda yanzu ina da damar shiga gurinta." Dr yace."Ka bari sai anjima tukkuna lokacin ta farko." Yace."Okey shikkenan."


Yana fitowa ya tarar da Sayyada tsaye da baby a hannunta tana jijjigata yaji wani irin tausayinsu ya ratsa shi Allah ya hukunta ba Sayyada ce zata haifeta ba.


Kuka babyn take tana tsotsar ya tsanta da alama yunwa takeji ganin suna ta kokarin kan yarinyar ta'kiyin shiru yasa ta kar'be ta daga hannun Abu aikuwa sai tayi shiru Sayyada ta sa'ba ta akafad'a tana jijjigata tausayi yarinyar take bata.


Nan ya shaida musu cewar su kwantar da hankalinsu insha Allahu sun shawo kan matsalar zata samu lafiya da yardar Allah.


Da jin wannan bayanin sai suka dan samu nutsuwa amma da sunyi masifar tsorata da yanda su kaga Harira ta shiga wani irin hanayi mara dad'i.


Kallonta yake tana Jijjiga yarinyar tana d'an sumbatar goshinta hakan sai ya burgeshi Sayyada na kaunar babynsa sai ta sake samun matsayi a cikin zuciyarsa........"Ina fidar ta take." ? Ta fad'a tana kallon Hansatu.


Da sauri tace"Kinganta nan gwada sanya mata a baki ko zata kar'ba da d'uminta."


Sayyada ta d'an tsugana a gefe ta 'kar'bi bulunbotin wanda yake dame da mara ta jirajirai ta sanya mata a baki cikin ikon Allah ta kar'ba kad'an kad'an tana tsotsa Abu tace"Wannan yarinya da wayo take duba ki gani ta kar'ba tana sha saboda tasan hannun uwarta take ai dazu babu yanda ba'ayi da ita ba kan ta'karba tasha ta'kiya sai kuka." Hansatu tace"Ai 'yayan yanzu da wayonsu ake haifarsu.


Sayyada na jinsu ba tace komai ba amma dai jikinta na bata idon Sadam a kanta yake shiyasa ta kasa d'ago kanta ta kallesu......Ringing din da wayarta keyi ne ya sanya ta gyara a hankali ta ciro wayar......Sai da gabanta ya fad'i ganin wanda ya kira "Yaya Sule tabd'ijam! A hankali ta daga wayar da sallama a bakinta.


Ya amsa mata kafin yace." Baby ban isa ki kirani a waya ba ko? ina a matsayin mijinki baki damu dani ba gashi ni da na damu dake na kasa jurewa na kiraki."


Tace"Ya Sule kayi hakuri." Jin ta ambaci sunan Sule sai ya tsura mata ido yana kallonta, ta d'an kalli gefan da yake tsaye ta cigaba da wayarta.


Daga d'aya 'bangaran Sule ya sassauta murya cikin sigar rarrashi yace."Baby ina nan ina kewarki ni kadai ne na damu dake zuciyata na nema ta tarwatse saboda kaunarki baby ki tausayawa dan uwanki ki sassauta mun nayi nadamar abubuwan da nayi miki insha Allahu zan gyara ki dawo mu gina rayuwa cikin aminci wallahi nayi nadama sai yanzu da bana ganinki na gane ba karamin sonki nake ba kuma na sake tabbatarwa da kaina kece mahad'in rayuwata."


Ji tayi ba zata iya bashi amsa ba a cikin jama'a sai ta mike da babyn a hannunta ta makale wayar da kafadarta Hansatu ta mikawa babyn ta bar gurun.......Wani irin kallo ya bita dashi me yarinyar nan take nufi ne? ba zatayi waya a gabansu kome."? Ko dai da mijin nata take waya.? Zuciyarsa ce ke ayyana masa hakan sai kawai ya bi bayanta.


Tana zaune bayan wani d'aki tana magana 'kasa-'kasa tun kafin ya 'karasa yaji tana fad'in"Haba Ya Sule duk me ya kawo wannan maganar? kawai ka nemi za'bin Allah amma ni ba wai ina 'kin'ka bane akwai dal.......! Ganinsa a tsaye a kanta yasa ta kasa 'karasa maganar ta bishi da kallo bakinta na motsi ga Sule sai magana yake mata ta kasa cewa komai.


Hannu ya mi'ka zai kar'bi wayar tayi saurin gocewa gabanta na fad'uwa.....'Karfi yasa ya murd'e hannu babu walwala ya kara wayar a kunnansa yana sauraran muryar Sule inda yake cewa "Baby shikkenan sai kin dawo Allah ya tsare ki yasa ki samu nasara kan abunda kike nema." Ko daga bacci ya farka murya Sule ba ba'kuwa bace a gurinsa bai fahimci kan abunda suke magana ba tunda karshen maganar kawai ya riska ya mi'ka mata wayar da fad'in"Na dauka ai da mijin naki kike waya ." Shiru tayi masa tana binsa da ido ta gode Allah da bai fahimci maganar da suke ba......Yace."Na daina fad'a miki ko da wasa karkikuskura ki sanar dasu cewa ina raye na fiso su ganni a bazata."


Ba tace masa komai ba sai dai ido da take binsa dashi kamar ya san abunda take ayyanawa a ranta yace."Ke ban yarda dake fa bani wayar nan in rike miki."


'Kin bashi tayi tayi gaba ya bi bayanta yana murmushi wani irin so yake mata mara misali mussaman da ya lura tana kaunar babynsa.


Sunanan zaune cikin katuwar rumfar da 'yan jinya ke zama suna jiran tsammani Sayyada dai duk ta 'kosa sai satar kallonsa yake suna zaune dasu Jatau kan wani bainci mamaki take sosai 'kiri-'kiri dai ya watsar da iyayensa ya sake sababbi taga sai wani girmama mutumin yake ta dinga jin wani irin haushinsa na kamata dama can shi bai wani da damu da iyayensa ba a ganinta sune suka damu dashi ta lura sunyi tarayya hali guda da Sulaiman sun fiye son kansu da yawa ko mey dalilin da zai hanata sanarwa da iyayensa bayyanuwarsa oho shi dai ya sani.


Sai misalin karfe uku na rana sannan aka basu izinin shiga duba majinyatar su kowa gadon dan uwansa yake nufa......Suka kewaye bakin gadon da Harira ke kwance tana bude idonta a hankali a hankali ta dinga binsu da kallo.....Sayyada ta dinga jin wani irin tausayin yarinyar na ratsa ta ashe ma 'karama ce wannan ai ta girmeta ma dole tasha wahalar haihuwa addua tayi mata ta fito daga dakin ta barsu.
Da sauri ta kama hanya ta fuce daga asibitin.....Sai da ta shiga babur kana ta saki jikinta ta kira wayar Saliha tace"Yanzu kuna ina ne."?


Saliha tace"Muna gida yau bamu fita ba." Tace."Okey ni zan wuce Freedom redio sai fa anyi shirin nan dani." Saliha tace"Lallai Sayyada shikkenan to bari mu kunna redio mu saurara." Sayyada tace"Okey sai nazo kenan." Kashe wayarta tayi gabakid'aya.


Tana shiga tashar uku da rabi ta cika dama uku da rabi suke fara shirin su gama hud'u saura minti biyar........Cikin sauri ta isa dakin da ake gabatar da shirin ta nemi guri ta zauna babu magana saboda an riga an jona na'urori dama a shirye take tsaf! mai gabatarwa ya fara kana suka tsunduma cikin shirin tare da 'bakinsu..........Bakin asibiti yake tsaye hankalinsa nakan ababen hawa dake wucewa ga wayarsa a hannunsa sai dubawa yake kana ganin fuskarsa za gane yana cikin bacin rai yabi ya tattare girar sama da 'kasa sai shan toka yake.......Wani mai siyar da kyan koli na cikin willbarow yazo wucewa ta gefansa yana sauran redio karaf! kunnansa suka jiye masa muryarta inda take fad'in.


_To masha Allah 'bakinmu mungode kwarai da kuka bamu lokacinku muka tattauna daku dangane da abunda ke addabar al'umma wanda shine taken shirin namu mai suna *Matasan mu a ina matsalar take* tashar freedom redio na muku fatan sauka lafiya kana kuma ni da abokin aikina Wato Jibirin Musa muna muku fatan sauka lafiya sannan muna fatan duk sanda muka sake bukatar ku kasance damu cikin wannan shirin namu mai albarka zaku amsa gayyatarmu"_


Suka amsa da "Insha Allahu."


Tace"


_To masu sauraramu nan zamu 'kar'kare wannan shirin namu saboda gabatowar lokaci Ni Sayyada Lawali Dabi da abokin aikina.......Jibirin Musa ya fadi sunansa kana tace muna muku sallama irin ta addinin musulunci sai Allah ya sake had'amu daku a mako na gaba bisalam."_


Miyau! ya nema ya rasa a bakinsa wato yarinyar nan wucewa tayi ta fati gabatar da shiri ta barshi yana bilayin nemanta wai shin me Sayyada take so ta zama ne? ya ma akayi ta rainashi irin haka? bashi me bashi wannan amsa dole tasa ya bar inda yake ransa idan yayi dubu ya 'baci ya koma cikin asibitib yana sake traying din numberta wayar akashe take tun bayan da suka gama waya da Saliha ta kashe abarta kuma tana sane ta kashe saboda tasan zai dameta.


Alhamdullahi Harira ta dan samu dan har abinci taci kuma tayi magana da iyayenta da mijinta sannnan an kara mata babyn a kirjinta ta shayar da ita......Wannan ya sanya hankalisu ya kwanta sosai sauki dai na Allah ne amma da dama dama ba kamar dazu ba...........Kiran duniya wayar is swich Up dole tasa ya dauki hanya Ja'in masaukinsu.


Isa da Harun na can gidansu wani abokinsu a can zasu kwana shiyasa suka kulle 'kofar gidan da wuri saboda unguwar irin shiru shiru ce babu hayaniya daga zarar dare yayi shikkenan kowa zai kulle gidansa dalili kenan da ya sanya Suna idar da sallahar isha'i suka gar'kama sakata.......Ya shigo unguwar karnuka nayi masa haushi sai kace wani 'barawo haka ya ratso layin nasu yana haska hanya da fitilar wayarsa.....Kofar gidan ya tsaya yana kokwanto nan ne ko ba nan ba gudun kar ya bugawa mutane gida ya sanya ya sake trying din wayarta still Swich Up Sai kawai yayi shahada ya fara buga gidan.....Sayyada gabanta ya fad'i! tasha jinin jikinta shine tunda yanzu su gama waya dasu Harun suka sake tabbatar musu da cewar sai gobe zasu shigo.....Lamfo tayi tana jin bugun 'kasa-'kasa! Saliha tayi firgigit ta mike zaune a hankali tace"Sayyada bugun kofa duba time ki gani." Sayyada tace"Waya ta babu charge tun dazu kunna wayarki ki duba."


Aunty Rabi tace"Kar wanda ya bude kowaye ya gaji ya tafi." Sai kuma tace"Af Sayyada anya ba Yalla'bai Sadam! bane."?


Sayyada tace"Ayya aunty bashi bane ai munyi waya dashi d'azu yace ba zai shigo ba yau sai gobe sai yazo muyi sallama kafin mu wuce."


Tace"To ku koma ku kwanta ko waye ya gaji ya tafi."Ba tare da wata damuwa ba ta koma tayi kwanciyarta babu abunda zai sanya ta bude masa kofa ya tirsasata binsa gidansa.


Sadam! bugun 'kofar yake yana jan tsaki! ga karnuka har sun kewaye shi sun fara haushi dole tasa ya kama hanya ya bar gurin cikin 'kunar zuciya da masifar damuwa gami da azazzala bai ta'ba tsammanin zai shiga 'kunci da damuwa ba kan yarinyar ha'kika Sayyada na nema ta sanya masa mugun ciwo wanda zaiyi sanadiyarsa.


Da 'kyar ya kai kansa gida ya sanya sakata kai tsaye dakinsa ya bude ya shiga ko solar din bai kunna ba yayi kwanciyarsa cikin duhu kamar wani maraya haka yayi lamo kan gado abun duniya ya dameshi kukan zucci yake wanda yafi na sarari zuciyarsa sai tafarfasa take....Ya mike zaune tare da dafe kansa da dukanin hannuwansa wai shin me yake damunsa ne? Me yasa ya tsallawa ransa ne kan yarinyar? me yasa zai dami kansa akanta me yasa yake jin masifar kishinta? me yasa baya so mutane ke sauraran muryarta? iya adadin mutane nawa ne suka saurari shirinta na *Matasanmu a yau?* dukanin wad'annan amsoshin bashi da mai bashi amsa sai 'kwa'kwalwarsa haka yayi ta zancan zucci zuciyarsa na sa'ka masa abu mai kyau da mara kyau.....Da 'kyar yayi ya'ki da shaid'an yaje ya dauro alwala ya dawo dakin.


Dadduma ya shimfida ya tada sallah raka biyu yayi ya sallame ya jima yana addua kafin ya shafa a fuskarsa yaje ya kwanta duk cikin duhu yake al'amarinsa sai kace wanda aka hanashi kunna fita......Cikin hukuncin Allah ya samu sassauci cikin ranshi bacci mara dad'i ya d'aukeshi.


Sayyada kuwa bacci tayi sosai domin dama jiya ba wani baccin arziki tayi ba sun kwana suna dambarwa dashi dan haka sai ta saki jiki ta kwashi baccinta babu wata damuwa a tare da ita.


Ya tashi cikin kasala da mutuwar jiki don da kyar ma yayi wanka ya shirya jikinsa ko tunanin karyawa baiyi ba ya bar gidan.....Yana cikin babur ya dinga trying din numbar tata da ta fara ringing sai ta katse daga karshe masa yaga busy line abun ya bashi mamaki mutuka da asibiti yayi niyyar zuwa amma sai ya sanja shawara ya cewa direban ya kaishi Ja'in wajan gidan man *'Dan marna* aikuwa mai a dai-daita ya dauki hanya kamar yanda aka umarceshi.
NI DA YAYA SADAM


BINTA UMAR ABBALE*


47


Dake yau dama basu shirya zuwa ko ina ba zasu d'anyi kintse kintse ne su shirya kayansu tunda tafiyarsu ta gabato shine dalilin da yasa basu bude kofa da wuri na Sayyada da Saliha wankin kayansu suke hadawa suna hira aunty rabi kuma na hada musu abunda zasu karya dashi sai suka soma jin bugun kofa.


Cike da mamaki aunty Rabi tace"Wai jama'a waye yake mana bugu ne sai kace wad'anda suka ci bashi tun jiya da daddare ake bugun kofa Sayyada jeki tsaya daga soro ki tambayi waye karki bude kofar." Sayyada jikinta ya bata shine dan har hazar yau bata kunna wayarta ba.


Ta tsaya bakin kofar tana le'kensa ta kafar mukkuli yana tsaye sanye da farin yadi fuskarsa ta nuna alamun damuwa matsananciya......Sauya murya tayi tayi kamar ba tata ba tace"Waye."? Sadam ya saki ajiyar zuciya a hankali yace."Nine Sadam mijin Sayyada."! Ta sake ma'ke murya da fad'in"Ayya ba gidan bane......Jim yayi yana naxari da sake bin gidan da kallo duk da cikin dare yazo gidan ai ba zai kasa ganewa ba ya tsaya yana mamaki.


Tana kallonsa ya fito da wayarsa yana latsawa jikinta ya bata ita yake nema a waya.....Minti kusan biyar yana faman abu daya dan tana jiyo sautin tsakinsa a kunnenta, tana kallo ya mayar da wayarsa aljihu ya bar gurin.


Ajiyar zuciya ta sauke sai taji jikinta yayi sanyi ta dan tausaya masa amma ba sosai ba cikin gidan ta koma cike da tausayinsa da tausayin kanta.


Yau ma haka ya yini cikin damuwa matsananciya kiran wayar Sayyada kuwa har ya zame masa jiki in ya gaji da kira sai ya hakura ta 'bangaran Harira kuwa sai godiya don jikinta na kara kyau masa Allah babynshi na kara kuzari da lafiya.


****
Yau kwanakinsu suka kare dan haka dama duk Sunyi sallama da abokanan arzikinsu suka dauki hanyar Kaduna cike da nasarori.......Sai da sukayi nisa sosai ta kunna wayarta aikuwa test messages ne ya shigo guda shida duk daga Sadam! Dubawa take wani ya sata dariya wani kuma ya bata haushi.........Zata karshen wannan iko da gadarar nan shi sam bai iya rarrashi ba komai sai ayi ta fada anta'ba soyayya ma da masifa.


Tana tsaka da sake duba message din kira ya shigo wayar gabanta ya fad'i kamar kar ta dauka zuciyarta tace"Dauki kawai kome zaiyi sai dai yayi tunda dai kin riga kinyi masa nisa."


Ta d'aga wayar a dake! tayi sallama." Ajiyar zuciyarsa ta soma ji kana taji sanyayyar muryarsa na fad'in"Saboda Allah abunda kikayi shine dai-dai.''?


Tayi mamakin wannan maganar tashi sam bata tsammaci haka ba ta dauka zai rufe ta da jaraba ne.


Tace"Me nayi maka.''?


"Kin gudu daga asibiti babu kowa nawa a gurin ina kallonki ina jin dad'i kina yi mun kara da d'ebe mun kewa sannan kin kashe wayarki kwana biyu ina nemanki har gidanku nace baku bude min 'kofa hakan ya dace kenan."?


A nutse tace" Wayata ce ta samu matsala lokacin da kayi ta kira na kaita a duba mun shine dalili."


"Okey to me yasa da naje gidan kuka 'ki bude mun kofa."? Yafada da yanayi na rashin jin dadi......" To gaskiya sai dai idan matsala aka samu ba gidan kaje ba amma babu yanda za'ayi kaje gidan kace kaine mu kasa bude maka kofa.


Yayi jim! yana nazarin maganarta hakane sai ta iya yuwa." Yafad'a murya kasan ma'koshi.....Shiru ne ya biyo baya kafin yace."Zan shigo yanzu ina fatan zaki bar wayarki a kunne domin kar a samu matsala.''


"Ayya Ya Sadam! ai tuntuni mun dauki hanya dan saura kadan mu sauka a gida." Yaji wani irin shocking a jikinsa yace."Kamar yaya kun dauki hanya bakiji abunda nace dake ba.


"Eh lokacin da muka d'iba ya cika bayan haka kuma mijina ya matsa mun in dawo gida ya gaji da zama shi d'aya a gida shine dalilin da yasa mukayi tafiyar a gaggauce babu shiri."


Yace."Ni kike fad'awa mijinki ko? Tace"Eh to menene kai ma kana da mata kuma kana da wasu iyayen sai kayi zamanka tare dasu ni na tafi cikin dangina saboda ina bukatar mijina a kusa dani."


Rasa bakin magana yayi yayi shiru yana sauraranta da taji baice komai ba sai ta kashe wayar ta mayar cikin jaka.......Suka cigaba da hirarsu da Saliha yanzu ta dan samu sassaucin abunda ke damunta a zuciyarta.


Guri ya nema ya zauna yana so tunaninsa ya dawo dai-dai! yayi nadamar dawowar tunaninsa sam! yanzu baya jin dadin rayuwar so yake ya cire yarinyar daga ransa abun ya gagara a yanzu ne yake kara jin wani irin sonta na karuwa a cikin zuciyarsa.....Ya jima zaune gurin da yake kafin ya mike ya bar gurin cikin damuwa matsananciya wai anwayi gari Sayyada na furta masa da bakinta cewa ita din matar wani anwayi gari shine yake bin Sayyada yana kokarin shawo kanta tana bujirewa lallai duniya ya rasa wace masifar ce ta sanya ya kasa cireta
daga cikin ranshi.


*****


Sulaiman duk ya wani susuce sai faman zumudi yake da murnar dawowar Sayyada da kansa yaje tasha ya dauketa cikin wata sabuwar mota sai sambatun surutu yake mata a motar ita dai jinsa kawai takeyi duk maganar da yake in ta ga dama ta bashi amsa idan ba taga dama ba tayi masa shiru amma sabida tsabar rashin zuciya ya 'kiyin shuru.....Suna dauka a motar ya mi'ka mata key din.


Ta kar'ba tana dan mamaki yana sakin mayaudarin murmushi yace."Motarki ce na siya miki albarkacin kokarinki ta fanni karatu."


Mirmushi tayi tana duba motar sosai tayi kayau yar yayi sabuwa dal da ita tace"Ya Sule nagode kwarai amma ba zan fara hawa mota ba yanzu sai an kwana biyu."


Yace."Babu damuwa ni da kaina zan koya miki motar." Tace"Shikkenan to."


Cikin gidan suka shiga aunty luba ta gyara daining cike da abinci kala kala Sayyada taga sauyi mutuka daga bangaran Sule yana kula da aunty Luba yanzu yana bata abinci da kulawa sai taga kamar ta kara 'kiba ma.


Suka rungume juna

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login