Showing 93001 words to 96000 words out of 142497 words
Chapter 32 - NI DA YAYA SADAM Complete Document by Binta Umar Abbale.txt
tana kuka aikuwa ta tashi da wani matsanancin ciwon kai wanda ya haddasa mata zazzafi mai zafin gaske. Tun Mammah na sanya ran fitowarta har ta gaji ta le'ka d'akin nata sai ta ganta nad'e cikin bargo ta shiga dakin da sauri tana kiran sunanta.
Sayyada ta amsa a hankali Tace"Tun dazu nake tsammanin fitowarki naji shiru anya lafiya kuwa." Da kyar tace"Kaina ne yake ciwo."
Ta zauna kusa da ita ta cire bargon dake lullube a jikinta hannu ta dora kanta taji zafi rau! tace"Eh gashinan kuwa akwai zazzabi ma bayan ciwon kan tashi maza ki karya ki kintsa da kaina zan kaiki asibiti a dubaki."
Sayyada tace"Mammah ba sai munje asibiti ba ma." Tace"wai me yasa duk sanda zance muje asibiti idan baki da lafiya sai kice a'a ko har yanzu baki daukeni a matsayin uwa bane." ?
Hawaye na zuba ta girgiza kai tace"to ki tashi ki shirya muje asibiti a dubaki." Sayyada ta mike zaune a hankali ta bita da kallo gwanin tausayi yarinyar ta sanya damuwa cikin ranta tana zaune ta shiga toilet ta dauraye jikinta ta fito ta kimtsa tsaf suka fita tare.
suna kokarin futa daga gidan motar Sule ta shigo direban dake jansu ya tsaya suna gaisawa yace."Mamma ina zakuje da sanyi safiya haka."? tace"Sayyada zan kai asibiti ba tajin dadi."
Jiki na rawa ya fito daga motarsa tare da bawa direban key wai ya gyara masa parking shi kuma ya karbi key din hannunsa ya shiga motar yana tambayar abunda ke damunta
Tace"Ciwon kai ke damunta tasha magani har yanzu ya'ki sauka." Yace."Bari muje a dubata sosai."
Yana draving yana kallonta kamar tsohon maye Sayyada kuwa ganin kallon da yake mata yayi yawa ya sanya ta ki dago kanta ballanta ta kalleshi wani irin haushinsa takeji. haka suka isa asibiri likita ya dubata tare da bata magani suka nufo gida Sulaiman ya tsaya yayi musu siye siye kamar hauka wanda mamma ta san ba don ita yayi wannan uban siyayyar ba sai dan Sayyada. Haka suka isa gida Sule sai rawar jiki yake kanta Mahaifiyarsa har ta sauya masa take ganin wacce yake dominta ko kallo bai ishehi ba.....Daki ya bita da ledar maganin "Sayyada tashi kisha magani." Ya fada yayin da yake tsaye a kanta.
Ta d'ago kanta tana kallonsa hannusa rike da gorar ruwa da cup wanda ya tsiyaya ruwan a ciki.
mikewa tayi zaune ta kar'bi ruwan da maganin kafin ya ankara ta watsa masa ruwan a jikinsa ya dago a firgice yana kallonsa shaddar dake jikinsa ta jike tabi fatar jikinsa ta kwanta.
Kallonta yake cike da dumbin mamaki! Tace."kana mamaki ko? to baka fara mamaki ba tukkuna wannan abun da nayi maka somin ta'bi ne tunda kai ka zama babban kwabo mutum mai son kansa da shegen nacin tsiya wannan maganin da kayi wahalar siyowa ka siyo a banxa domin gwara in mutu akan inyi amfani da abinda ya fito daga hannunka."
Sulaiman yayi mutuwar tsaye yana mamakin kalaman yarinyar zuciya sai cinsa take kan ya hukuntata wata zuciyar na fadin "ka bari tazo hannunka sai ka hora ta karyar rashin kunya take."
Tace"Ka fice min daga d'aki bana son ganinka idan ina kallon wannan mummunar fuskar taka to zuciyata zata iya tarwatsewa."
Sulaiman ya kama hanyar fita daga d'akin jikinsa duk a sabule tace"Tunda kace dole sai ka auri Sayyada to nemi maganin hawan jini domin sai na kunsa maka bakin ciki da takaici kamar yanda ka kunsa min."
Ya juyo da ido jawur yace."Sayyada kuka da kanki idan kika shigo hannuna sai kin raina kanki." Yana gama maganarsa ya kama hanya ya fita taja tsaki tare da kwanciya tana tunanin mafita
Komai yayi tsanani maganinsa Allah a hankali a hankali al'amura suka cigaba da gudana gidan Jatau hankalinsu ya kwanta domin Allah ya sanya albarka cikin sana'oin da sukeyi yau da gobe kasuwanci sai bunkasa yake maganar kuma auran Sadam! da Harira tayi nisa domin a tsakaninsu sun dai-dai ta kansu iyayen kuma sun shirya tsaf! tare da tsayar da ranar daurin aure sati hudu masu zuwa.......Akwai wani fili piloti guda dake jikin gidan nasu Sadam da Munkaila suka hada kudi suka siya suka fara gini dake akwai kudin akasa cikin sati biyu kacal gini yayi nisa abunda yayi sauran rufi da siminitin kasa dan har fulasta anyi a gidan ciki da rumfa rumfa ne guda biyu sai katon tsakar gida da bandaki da kicin ko wanne yana da guda daya Sadam ya shiga kasuwar kwari da kansa ya had'owa Harira lefe akwati biyu dai-dai gwargwado ya sanya dukanin abun bukata a cikin lefensa.
****
Ranar da aka daura auran Sulaiman da Sayyada a ranar sai da ta kusa mutuwa saboda tsabar kuka Baba Ladidi tun suna fad'an sukaga ba sara ba sai suka dawo rarrashi da bada baki Sayyada kawai jinsu takeyi tana daukarsu a matsayin manya manyan makiyanta wa'yanda basa kaunarta da kaunar farin cikinta.
Zumudi gurun Sule ba'a magana sai shige da fice yake yana so ya 'kebe da Sayyadar babu fuska ni kaina sai da nace banta'ba ganin mutum mara zuciya ba kamar Sulaiman duk wulakancin da Sayyada take masa baya gani kullum sake nani'ke mata yake tana shareshi.
Kwanta uku a gida bayan daurin auran su Baba Ladidi sai baki suke bata Baba Ladidi dai har dasu kuka duk akan al'amarin ganin haka ta sanya ta sassauta tace"Su kwantar da hankalinsu komai ya wuce zasu zauna lafiya.
Da kansu suka kaita dakinta dake gidan Sulaiman din Aunty Luba ta tar'besu hannu biyu suka zaunar dasu duka sukayi musu fada da nasiha kan cewar su zauna lafiya da junansu.
Aunt Luba tace"Insha Allahu zata rike Sayyada da amana kuma ba zata dauketa a matsayin kishiya ba zata dauketa a matsayin yar uwarta ta jini."
Aikuwa suka dinga shi mata albarka da sanyawa iyayenta albarka sallama sukayi musu suka kama hanya suka tafi.
Sayyada ta shige dakin da yake a matsayin nata ta kulle da key ta sannan tasa sakata tayi kwanciyarta rungume da hoton Sadam data 'boyoshi cikin kayanta.
Misalin karfe goma sha daya da rabi na dare Aunty Luba ta dinga jin bugun kofa da karfi firgigt ta mike zaune ta sake jin wani bugu me mugun karfi a guje ta diro daga bed dinta tayi waje da sauri.
Sulaiman ta gani tsaye bakin kofar dakin Sayyada daga shi sai gajeran wando yana ta aikin bugu kofar dakin tare da fad'in"Sayyada ba zaki bude min kofa ba ko ki bude nace wato ashe ba kiji nasihar dasu baba sukayi miki ko." Sayyada na jinsa tayi masa banza.
Ya dinga bugun kofar kamar wani zautacce wani irin maganin karfin maza yaje yasha duk dan kawai yayi maganin yarinyar sai ya dawo ya tarar ta rufe kofar dakinta ya dauka da key ta rufe sai ya samo spire yasa jikin kofar domin ya bude koda ya bude sai yaji ashe sakata ta zura ka kofar irin me kauri ce da karko babu hakin ya jijjigeta shine fa yake ta wannan haukan bugun.
Lubabatu tace"Haba ango yana da kyau ka saurara haka ba don komai ba saboda dare yayi bugun kofar da kake bashi da amfani ka bari da safe sai ku hadu."
Kamar wani wawa ya juyo yana kallonta da idanunsa wanda suka kankance da sha'awa yace."Lubabatu ashe yarinyar nan bata da mutunci ni zata rufewa kofa ki duba kiga yanayin da nake ciki lubabatu.''
Ta kalli 'kasansa taga yanda ta cika wando tabbas a bukace yake sosai tace"To ai dama kowa ya sayi rariya yasan zata zubda ruwa ni meye nawa a ciki." Tana gama maganarta ta shige dakinta itama ta zura sakata tayi kwanciyarta
Sule ya koma kofar dakin Sayyada ya dinga bugawa yana kiran sunanta tanaji tayi masa shiru ganin zai mutu ya sanya a kid'ime! ya nufi dakin Lubabatu ya dinga bugawa yana kiran sunanta tace"Lallai wananan mutumin ma bashi da hankali." juyawa tayi ta gyara kwanciyarta tana fad'in"Idan ka kaji ka hakura.
Sulaiman ya dinga aikin buga kofar Sayyada da Aunty Lubabatu kamar zazzare ya dinga sambatu yana zagaye dakin da ya gaji sai yaje ya takure kan kujera ya zura hannunsa cikin wandonshi yana wasa da jijiyar tashi dake masa wani irin hankoro mararasa na wani irin daurewa magani yasha na baturi ovar dose wai don ya nunawa Sayyada bata da wayo sai kuma sharrinsa ya koma kansa haka ya kwana a jigaje da asubah Luba ta fito ta ganshi kasan teyal yayi bacci a takure hannunsa a cikin wando dariya tayi ta tsallakeshi hijab dinta ta dauka ta koma dakinta ta tada sallah.
Sanyi safiya ne ya tashe shi ya mike zaune yana zazzare ido wai mutum da gidansa da matansa har guda biyu amma ya kwana a palo a palon ma kasan tayel lallai Lubabatu da Sayyada basu da mutunci......A dudduke ya mike ya isa dakinsa ya sake zubewa kan gado yana rintse ido mararasa sai suka take masa wai ya zaiyi ne?
Sayyada tayi wanka ta shirya tsaf tsaf dama tana da snacks a firjinta da lemo da kyan tea sai ta kunna hita ta ta tasa tea ta hada abunta tasha ta kwanta tare da daukar hoton Sadam tana kallonsa tana murmushi da safa siririn sajensa da tausasan le'bunansa tace"Insha Allahu wannan budurcin nawa naka ne nayi maka al'kawari komai rintsi ba zan bawa kowa ba idan ma da gaske ne ka mutu to ina fatan na kasance cikin matayenka cikin aljannar furdausi.......Tana cikin wannan sambatun ne ta jiyo tashin motar Sulaiman da sauri taje ta daga labule sai taga maigadi na bude masa gate zai fita tsaki taja ta koma ta zauna tana fad'in"Girma ya fadi Yaya Sule jikina kuma ya haramta a gurin nayi alkawarin d'an yatsana baxan barka ka ta'ba tunda na gane dama can sha'awata kake shiyasa ka hanani zaman lafiya da mijina.
Sulaiman na futa da minti biyar aunty Luba ta buga mata kofa ta bude suka gaisa Sayyada sai sunkuyar da kanta take kasa tana jin kunyarta aunty Luba tace"Sayyada sai kuma ki rufewa angon naki kofa baki kyauta ba."
Tace"Aunty Luba ni ba angona bane Yayana ne Sulaiman angonki ne ke kadai aunty Luba."
Lubabatu tace"Gaskiya kar ki 'kara Sayyada babu kyau ki bashi hakkinsa kamar yanda Allah yace.".
"Aunty Luba mu bar wannan magana don Allah har abada ba zan ta'ba cin amanarki ba Ya Sulaiman ba mijiba bane mijiki ne ni Ya Sadam shine mijina kuma insha Allahu zai dawo mu cigaba da rayuwa wannan aure da suka daura tsakanina da Ya Sulaiman insha Allahu babu inda zaije kuma ba zan ta'ba bari wani abu ya shiga tsakanina dashi ba na dauki wannan alkwarin."
Aunty Luba tace"Sayyada ki dai bi komai a hankali ni wallahi na rasa ma yanda zan fasalta al'amarin Allah dai ya gaggauta bayyana Sadam idan yana raye idan kuma baya raye to Ubangiji Allah ya za'ba miki abunda yafi alkairi."
Sayyada ta rungumeta tana fad'in"Nagode aunty Lubabatu wallahi shiyasa nake kaunarki saboda kiba da saurin fahinta kuma kina aiki da iliminki auntyna ina fatan zaki bani goyon baya a bisa kudurina."
Aunt Luba tace"Sayyada nayi miki alkawarin zan taimakeki iya iyawata insha Allahu." Tare sukayi brak fast Sayyada ta d'ebo musu cincin da kek suka zauna suna ci suna hira nan aunty Luba ke tambayarta yaushe zata koma makaranta tace"Gobe zan je insha Allahu yau ma don bamu da lectures ne shiyasa."
Sule fitar da yayi bata lafiya bace can mahad'arsu ta yan burni ya nufa ya samu gogaggiya ta fanni iya sex ya barje guminsa akanta yini sukayi suna abu daya sai wajejen shida na yamma ya nufu family house dinsu ......Lokacin su Baba nan basu tafi ba dama sun bari sai gobe tukkuna salau-salau yaje ya zauna kusa da baba ladidi suka gaisa suna tambayarsa mutanan gudan mussaman Sayyada Nan ya samu damar shirya musu karya da karairayi kan cewar Sayyada ta rufe masa kofa yayi ta bude masa taki da safe kuma da ta fito yayi mata magana ta zageshi tas tas! wai sai ta zama ajalinsa......Baba Ladidi ta fusata sosai ta zari mayafi tana fad'in "Tashi maza maza muje gidan shegiyar yarinya me zuciyarka kafurai wallahi yau sai ranta ya 'baci shashashar yarinya wacce bata sannan annabi ya faku ba."! Sulaiman ya dauki Baba Ladi da Baba Marka a mota suka nufi gidansa....suna zaune a palo sukaji tsayuwar motarsa Sayyada tayi maza ta daga labulen taga sai ta hangosu baba sun fito daga mota suna sababin fada. ta saki labulen da sauri ta koma ta zauna tana shirya shawarar abinyi....." Kina ina munafukar yarinya mai 'bakin hali Sayyada dake nake dan ubanki."!!! murya Baba ladidi ke tashi a cikin palon ta mike da sauri tare da sakin fuska sosai tace"Baba Sannunku da zuwa sannu." Baba Ladidi tace"Dallah matsa ki bawa mutane guri munafuka me alkawarin banza."
A marairace tace"Baba me nayi kuma? ku zauna don Allah sai ayi maganar." Duk suka nemi kujera suka zauna aunty Luba ta fito daga daki tana musu sannu da zuwa.......Sayyada ta kalli Sulaiman dake tsaye a bakin kofa ya kura mata ido kamar maye fuska ta saki sosai tace"Yaya Suleiman ka shigo mana ka tsaya anan ka futa bamu gaisa ba aunty Luba abincinsa na kicin ko."? Aunty Luba tace"Eh yana kicin tace"Ya Sule ka shigo ka zauna kaci abinci kaji ko." Ta fad'a a shagwa'be! Da gashi har su Baba sai suka tsaya suna mamaki! Anya kuwa Sulaiman ba sharri yake wa yarinyar ba irin wannan tarairaya da take masa da rarrashi ai sai wanda ake so sai duk jikinsu yayi sanyi suka bi Sulaiman din da kallo wanda ya zauna cikin kujera jikinsa duk babu laka
Sayyada ta kawo abinci ta hada masa komai ta zauna hannun kujerar da yake zaune tana masa firfita." Su Baba dai 'yan kallo suka zama shi kuwa Sulaiman wawa sai ya sake sosai ya fara d'ibar girki yana tunanin ko Sayyadar ta hakura ne zata zauna dashi tunda gashi tana tarairayarsa.
_Kika fit
NI DA YAYA SADAM
*BINTA UMAR ABBALE*
40
Ganin yanda Sulaiman ya shagala da kallon Sayyada ya manta dasu Baba dake zaune a gurin sai hakan ya basu mamaki mutumin da ya kawo 'karane ya shagala gurin mai laifi ya manta da abunda ke gabansa duku loma idan zai kai bakinsa sai ya kalli Sayyada yana washe baki kamar wani sakarai! duk sai suka 'karyata maganarsa da cewar kawai sharri yayiwa Sayyada tunda gashin nan ma tana kula dashi yanda ya kamata kamar ba itace me koke-koken nan ba.
Baba Ladi ta mike tana gyara lillu'binta tace"Marka ai sai mu kama hanya mu tafi domin naga alamun mun zama hoto a gurun" Baba Marka tace"aikuwa dai duba ki gani don Allah sakarai kawai yaje ya dauko muku kafa da kafa ya yasar damu a guri yana ta matarsa."
Sayyada ta 'kyalkyale da dariya tace"To Baba dama waye yace kozo mana gida haka kawai gwara ma ku koma *Dabi* ku kyalemu mu huta."
Baba Ladi tace"Ai gashinan sai ki tambayeshi dalilin da ya sanya ya dauko mu daga inda muke."
Sayyada ta kalli Sule tana makale murya tace"Ya Sule baba tace wai na tambayeka Allah yasa dai ba wani laifin kaje kace nayi maka ba."Tafad'i maganar a marairaice!
Wata iriyar dariya yake yana kallonta da fad'in"Sayyada wane laifi za kiyi min wanda zai sanya na dauko su Baba ko jiya ma da kika rufe kofa nasan bacci ne ya daukeki saboda gajiyar buki."
A marairace tace"Wallahi kuwa Ya Sule jiya nan na gaji sosai shiyasa banji sanda kake bugu ba."
Sai ya dago kansa yana kallonsu Baba ladidi yana washe baki yace."Kunji ko Baba aini nasan Sayyada ba zata rufe min kofa da gangan ba."
Baba Ladi ta saki baki tana kallonsa cike da tsabar bakin ciki da takaici, gaba tayi ba tare da tace komai Baba Marka ta bi bayanta tana surutan abunda Sulaiman din yayi musu.
Bayan fitar su Ya kalleta yana wani rawar jiki yace."baby bari naje na kaisu gida na dawo me kike so na siyo miki." Babu fara'a sosai a fuskarta tace"komai ka siyo ina so." Saboda tsananin farin cikin da yake ciki na sauyawar Sayyadar ya sanya bai fahimci yanayin da take ciki ba.
Ya zari hularsa da key ya kama hanyar futa har yana tuntube saboda sauri fad'i yake "Sai na dawo baby karkiyi bacci akwai labari me dadi da zanyi miki."
Tace."Okey tom sai ka dawo." Yana fita taja tsaki tare da girgixa kanta sosai halinsa ke bata mamaki.!
Aunty Luba na jin tafiyarsu ta fito daga dakinta Sayyada tace"Auntyna mijinki fa 'karata ya kai gurinsu Baba shine fa suka zo su kare min tanadi ni kuma dana fisu sai na shirya plan dina akan Ya Sulaiman din."
.Aunty Luba tayi dariya tare da fad'in"Baki da dama Sayyada."Tace"ai aunty dole sai da dubara domin wallahi na lura Ya sulaiman yayi nisa baya jin kira."
Luba tace"Sayyada Sulaiman na sonki sosai shiyasa idanunsa ke rufewa mai zai hana ki hakura ki aje komai ki zauna dashi a matsayin miji.'.
"Aunty pls ki daina min wannan magana dan Allah! ni wallahi koda ace Ya Sadam da gaske baya raye a duniya akace na auri Ya Sulaiman wannan bazan ci amanarki ba aunty Luba karkiji haushina kin san dai anayin aure domin so da yardar juna to ni wallahi dai-dai da 'kwayar zarrah bana jin kaunar Ya Sulaiman a cikin raina....Ya Sadam! kadai zuciyata ke kauna dashi ta amince dashi ne kuma ta yarda tayi rayuwar aure aunty Luba bazan iya fad'a miki iya adadin kauna da son da nake wa Ya Sadam! Ubangijin da ya hallice ni shine kadai yasan abunda ke zuciyata." Ta karashe maganar muryarta na wani irin rawa.
Aunty Lubabatu tace"Karkiyi kuka Sayyada insha Allahu zan taya ki adduar kan Sadam in yana raye Ubangiji Allah ya bayyana shi idan kuma Allah ya amshi abunsa to zan tayaki adduar samun miji nagari domin ni kaina bana so ki zauna da Sulaiman saboda mugwayen halayensa Sayyada ke 'yar uwarsa ce amma ki gafarce ni Sulaiman mugu ne domin ni ya gwada a kanki kaina na gani shiyasa bana so ki fada komarsa saboda nasan ba son gaskiya yake muki ba kawai sha'awa ce daga zarar ya samu abunda yake bukata shikkenan idanunsa zasu koma kan 'yan matansa na waje."
Sayyada ta sauke ajiyar zuciya a hankali tace"Nagode aunty Luba nagode da gudumawar da kike bani Allah ya biya miki bukatunki na