Showing 126001 words to 129000 words out of 142497 words

Chapter 43 - NI DA YAYA SADAM Complete Document by Binta Umar Abbale.txt

09 Dec 2024

50461

na raye amma bai fada ba.


Yana ji yana gani suka fita daga dakin babu damar ya bisu sai kawai ya cigaba da zubar da hawaye yana nadama mara amfani yanzu ko ya rayu ba zai yi rayuwa mai dadi ba babu kafa daya sannan duk duniya tasan abunda ya aikatawa dan uwansa.


Shi kuwa Saleh har yanzu babu wani nasa da yazo kansa danginsa kaf na can Ptarcout matarshi kuma dama tuntuni ya saketa itama 'yar can ce bashi da yaro ko daya shiyasa yake cin karansa babu babbaka.....Kuka ya keyi sosai domin shi al'amarin ma yafi tsananta ta 'bangaransa dan dukanin kafafun aka cire duka sun tashi daga aiki bakidaya kullum da daddare haka yake zaita zumduma ihu! babu salati da kiran sunan Allah.


Sunji dadi da suka ga yanda jikin Captain Habu yayi sauki alhamdullahi tunda har yana iya magana 'yar wacce ba za a rasa ba kuma yana gane kowa sauki dama sai a hankali.


Abbah ya sanya direbansa ya dauki su jatau da kayayyakinsu sukayi sallama da juna suka dauki hanyar kano cike da kewar 'yarsu Harira.


****
Satin su Baba Ladi biyu suka tafi sai gidan ya dawo shiru daga Sayyada Sai Mammah da baby Asalamiyya dake hannun Mammah idan Sayyada na makaranta sai Mammah da me aikinta....Sadam kam baya zama tun bayan tafiyarsu Jatau ya koma aiki ka'in da na'in dan ranar dasu Baba Ladi zasu tafi bai sani ba sai bayan ya dawo yake samun labari.


Yau kunsan kwanansu goma basu hadu ba dake wani sa'in da asubah yake futa kuma baya dawowa da wuri kai wani sa'in ma baya kwana a gida shiyasa basa haduwa da juna, itama zurga zurgar makaranta ta dauke mata hankali ga jarrabawarsu data taso ta a gaba amma dai duk da haka kullum da tunaninsa take kwana take tashi ta fuskanci mutuwar matarsa ta dokeshi shiyasa tayi masa uziri amma tana saurare ko zai kirata a waya ko yayi mata tes shiru babu wanda yayi mata ranta yana 'baci sai dai kawai babu yanda zatayi ne.


Motarshi na kokarin fitowa daga cikin gidan ita kuma tana kokarin sauka daga a dai-adai ta sahu gabanta ya fad'i ganinsa cikin kayan aiki da alama futa zaiyi sai take mamaki ashe dama bai futa ba.....'Kasa tayi da kanta ta fito da kudi ta mikawa me babur d'in ta gyara jakarta tare da gyara hijab dinta ta kama hanya zata shige.


Har ya gota ta sai kuma ya tsayar da motar ya sauke glasa din motar yana kallonta tana sauri yace."Ke! daga ina kike."!?
Kamar ta shareshi sai ta juyo a nutse tace."Makaranta mana." Ya zuba mata ido "Dama baki 'kare karatun ba."!?
" Eh" kawai tace ta juya girgixa kansa yayi ya figi motar ta bishi da kallo tana ta'be baki tunda matarsa ta mutu yake wani cin kunu sai basar da mutane yake itama taji ciwon mutuwar ai kuma ba zata ta'ba mantawa da al'amarin ba tunda itama Allah ne yasa tana da sauran kwana da tuni sai dai labari.....Gidan ta shiga tana tunanin irin zaman da za tayi dashi ya 'karo wani miskilancin wanda yafi na da yawa.


*Littafin na
NI DA YAYA SADAM


BINTA UMAR ABBALE*


53
Bayan kwana uku da faruwar haka rannan sai Abbah yace idan ya dawo daga aiki yazo ya sameshi yana son magana dashi, to bai shigo gidan ba sai bayan sha biyu da rabi na dare yasan duk gidan sunyi bacci shiyasa ma bai tunkare su ba ya wuce gurinsa cike da gajiya gami da kasala da sha'awar dake damunsa. Ya samu yayi wanka ya kwanta ko towel din bai samu damar cirewa ba bacci ya daukeshi.....Dake asabar ce babu aiki sai ya koma bacci bayan yayi sallahar asubahi, Alhaji Auwal ya'ki fita kasuwa yana zaman jiran shigowarsa sai da yaga goma da rabi ta gota sannan ya kira Sayyada itama tana gida lokacin yace."Taje ta kira Sadam a gurinshi......Hijab ta sanya kan riga da wandon dake jikinta na bacci ta tsaya gyara wardrobe dinta yasa ba tayi wanka ba.....Gabanta na faduwa ta fara buga kofar dakin nasa.


Yana tsaka da bacci yaji budun kofa ya mike firgigit yana duba agogo da sauri! mike yana gyara towel din jikinshi ya nufi kofa yana fadin"Waye ne yake bugu."?


Shiru tayi sai da ta bude suka had'a ido ya 'bata fuska yana mata wani irin kallo "Menene."!? Ya fada yana 'bata fuska.


Kallonsa tayi tana jin wani fleeng na taso mata tace" Abbah ke kiranka yace lallai muje tare."


Ya juya cikin dakin yana fad'in"Kije ganin nan zuwa." Ba tare da tanka masa ba ta bar gurin.....Jallabiya ya zura a jikinsa ya sanya gajeran wando ya nufi sashen domin amsa kiran Abban.


Bayan sun gaisa da juna Sadam ya nemi gafarar mahaifinsa kan rashin zuwansa da Wuri Abbah yace."Nasan a gajiye kake ai shiyasa ban damu ba abunda yasa ni nemanka shine nace wannan zaman da kuke a gida babu fa'ida yaushe zaku tare ne kai da matarka."


A nutse ya kalli mahaifin nasa yace."Abbah da bari nayi kwanaki su sake turawa bayan haka kuma inaso inyi dan gyare gyare a gidan da zamu zauna tunda kace baka sha'awar mu zauna a bariki."


Alhaji Auwal yace."Kaine kake abunka Sadam ni tuntuni na sanya an gyara ko ina na gidan da zaku zauna guda biyu ne ma amma dai nafi do ku zauna na Kinkinau zaifi.''


Yace."Shikkenan Abbah zamu tare cikin satinan insha Allahu."


Alhaji Auwal yace to alhmadullahi Allah yayi muku albarka kuma ku samu masu yi muku biyayya." Sadam ya amsa da ameen."


Alhaji Auwal ya mike da niyar tafiya nema Sadam din ya rakashi harabar gidan har sai da direbansa ya daukeshi sannan ya koma sashensa, yana tunanin al'amura da dama.


****
Sulaiman ya zama abun tausayi kullum idan Sadam yaje dubashi yayi ta bashi hakuri yana share hawaye Sadam din na nuna masa cewa ya kwantar da hankalinsa indai tashi ne to ya yafe masa.


'Iyayen Lubabatu kuwa takanas suka sameshi kwance a asibiti suka bashi takarda da biro ya rubutawa yarsu saki babu yanda ya iya yana ji yana gani ya rubuta saki daya a takar dar ya mika musu suka tilasta shi dole sai ya kara wani sakin ya karba ya kara daya ya zama biyu babu ruwansu suka futa suka barshi cikin tsananin damuwa.


Saleh kam al'amarin nasa ya tsananta ashe yana dauke da cutar HIV ba'a sani ba yana shan magani ne a boye shiyasa bata nuna ba kwanciyarsa a asibiti tasa cutar ta bayyana a jikinsa dalili ya kwana biyu bai sha magani ba sai kowa ya sake guje masa haka yake yini shi kadai a daki yana nishin wahala babu kiran sunan Allah sai dai ihu!


***


Gidane plate mai kyau Abbah ya mallakawa Sadam dan gidan yafi na Sulaiman kyau da kayatuwa komai an sanya a gidan mussaman palonta ya tsaru bedroom biyu ne manya manya ko wanne da bed shima Sadam din da yaga gidan da tsaruwarsa sai yaji sha'awar zama a cikinsa.....
a ranar da yaje gidan ya dawo sai ya kirata a waya, lokacin suna tare da Saliha a makaranta taga kiranshi kamar ta shareshi sai ta dauka.


Gaisheshi ta farayi ya amsa a dakile kamar yanda ya saba shiru tayi yace."Kina jina."? ''Uhm."! tafada tana kumburo baki.


Yace."Ranar juma'a ta jibi kiyi duk wani shirye shiryen da zakiyi zamu tare a gidanmu." Farin ciki da fad'uwar gabana suka sameta a lokaci guda sai ta kasa magana ba sai murmushi take.


"Ko bakiji abunda nace ba." Yafada maganar jin tayi shiru ba tace komai ba....."Kina ina ne naji hayaniya tayi yawa."? Yafada yana jiran amsarta dan baya son wannan shirun da take masa.


Cikin kasalalliyar murya tace"Ina makaranta fa amma dai gamu a bakin titi zamu samu abun hawa."


Yace."Okey ku tsaya nan koma dake da waye zanzo yanzu." Cike da mamaki tace"Kana gurin aiki zaka zo daukana a wannan ranar." Yace."Ke! bana son shashanci idan aiki ne ya tashi cikin wuta ma ina shiga ballanta wannan ranar da kike zuzutawa." Tace"Oh sorry sai kazo.'' Kashe wayarta tayi tana kallon Saliha dake neman tsayar musu da me d'an sahu.


"Saliha kinji mutuminki zai zo yanzu ya daukeni ji nake kamar abun a mafarki wai ranar juma'a xamu tare a sabon gidanmu."


Saliha tace"Alhamdullahi naji dadi wallahi saura ki tsaya wannan halin naki na jan aji kije ya tsinke don Allah in kun tare ki nuna masa so da kauna kisa ya manta da mutuwar matarshi dake damunsa dan Allah kada kishi yasa kice ba zaki kula dashi ba in kin ganshi cikin kadaici.


Murmushi kawai tayi itafa zata fadawa Saliha waye Sadam baka ta'bayin abu dan ka burgeshi sai ya ga dama ma zai kalleka.


Sunanan tsaye motar sa ta tsaya inda suke ya sauke glass din motar yana kallonsu Suka mike suka isa bakin motar Saliha ta gaisheshi ya amsa da sakin fuska.......Saliha tace"Yau Yallabai ne da kanshi yazo daukarmu gaskiya munji dadi sosai kuma yanzu mun fara tunanin hankalin ya juyo kanmu.


Shiru yayi baice mata komai ba shifa wannan wasan sam bai saba ba in ba da Lubabatu ba.....Saliha ta budewa Sayyada motar ta shiga ta zauna kusa dashi Saliha ta zauna bayan motar yayiwa motar key suka bar gurin..........kad'an-'kadan sautin redio ke tashi a motar ta dan kalli fuskarsa taga a murtuke babu wata walwala sai kawai ta biyewa Saliha suka dinga hira a motar sai da Saliha zata saukane yayi magana "Ko gaishe da mutan gidan." Ya fada kamar baya so, Sayyada ta daga mata hannu bayan futar ta motar sukayi sallama.


Tafiya suke shiru dan sautin redion dake tashi a cikin motar yanzu ma babu shi da alama ya kashe redion.


Bayan sun isa gida yayi parking ta fara kokarin bude motar ta fita ta jiyo muryarsa can 'kasan ma'koshi "Karki futa malama." Sai ta saki murfin motar tayi shiru tana sauransa......."Ki juyo ki kalleni mana ya fada da irin muryar dazu.


Juyowa tayi ta kalleshi kamar yanda ya bukata yace."Kinyi min laifi amma har yanzu baki san kinyi ba ko.? Tayi kasake tana kallonsa da mamakin wane irin laifi tayi masa.


Yace."Matata ta mutu kin kasa yi mun gaisuwa baki da baki sai dai kawai gi dinga gwalalowa mutane ido kamar zaki had'iye shi."


Rai a dan bace tace"Sau nawa kuma kake so nayi maka gaisuwar dama ai ba dole ne ka fahimci cewar nayi maka gaisuwa ko banyi maka ba, tunda lokacin kana cikin jin zafin mutuwar ba zaka bambamce ba."


Yace"Ni dai nasan tun bayan rasuwar Harira baki sake kulani ba gaisuwa ma sai kin ga dama kike mun ki futa lokacin da kike so ki dawo kuma a lokacin da kike so kamar wacce take zaman kanta.


"Ya Sadam! dan Allah ka kyaleni na shiga gida na huta ni gaskiya bana son neman magana kasan inda nake zuwa to meye na wannan maganar kuma.!?


" Eh duk da haka dai dole inyi magana tunda hakkina ne ko kinga laifina."!?


"Banga laifinka ba dama ai kai baka laifi.'' Ta fada tana tabe baki.......Ido ya zuba mata yana ayyana abubuwa da yawa a kanta yace." Naga kin dauki fushi da yawa kije gida xan koma gurin aiki ki shirya yau zan dawo da wuri zamuje wani guri."


A dakile tace."To" ta bude kofa ta futa daga motar sai da yaga shigarta cikin gidan sannan yaja motarsa ya bar gurin


****


Wani supar market ya kaita yace ta za'bi dukanin abunda take so kasa daukar komai tayi ba dan cewar kayan dake cikin gurin basuyi mata ba ita yanzu ba siyayya ce a gabanta ba burinta shine ya bata dukkanin kulawarsa.


Ganin taki daukar komai sai ya shiga d'ibar mata kayan kwalliya na mata da turarrika digsinar masu kamshi da tsada ya dinda jibgar mata kananun kaya da kayan bacci shima ya samu boxes da vest da sauransu suka isa gurin biyan kudi tana mamaki tana kallo ya fito da kudi kimanin dubu hamsin da wani abun ya basu kana suka hada mishi kayan suka kai mota.


Ita dai binshi take tana mamakin shin yanzu ya soma sonta ne da ya jibgo mata uwar wannan siyayya babu mai bata amsa dole sai shi sai taja bakinta tayi shiru tana mazewa ta daina rawar jiki a kansa.


"Zamu tsaya asibiti mu duba Sule."! ta kalleshi da mamaki a tare da ita. Gira ya daga mata da fadin" Ko nayi laifi ne.'? girgixa kai tayi tayi shiru kawai tana mamakin sauki kai irin nashi a zahiri idan yana wani abu sai ka dauka cewar shi mutum ne me zafin kai amma kuma idan ka zauna dashi zaka gane sam duniya bata dameshi ba idan wani ne da tuni ya sanya gatangar karfe tsakaninsa da Sule amma dake akwai kauna irin ta jini da 'yan uwantaka Sadam din bai hofintar da Sulaiman din ba


Suleiman da ganin sun shigo dakin sai ya fara tsiyayyar da hawaye yana shashsheka aikin kenan ya shiga baiwa Sadam hakuri har sai da Sadam din ya hanashi Sayyada kam fita tayi daga dakin tana share hawaye wai Ya Sule ne ya koma haka rayuwa kenan shiyasa akeso in zaka gina ramin mugunta ka ginashi dai-dai misali dan watarana in ka gina kaine zaka burma.


Shima Sadam din cike da tausayin Sulaiman din ya fito daga dakin.


Ya tarar da ita cikin mota tana share fuska bai tanka mata ba yayi wa motar key suka bar cikin asibitin.


Yana kallonta ta gefan ido sai goge fuska take tana sha'kar hanci ya dab 'bata rai! zuciyarsa na wasi wasi akan kukan da take da sauri ya kauda zargin da zuciyarsa keyi a kanta gyaran murya yayi kad'an yace"wai ke kukan me kikeyi haka."?


"Ya Sadam Wallahi ina tausayawa Yaya Sulaiman ka duba kaga yanda ya jefa rayuwarsa cikin matsala kai innalihi Allah ya rabamu da sharrin zuciya."


Yace."Ameeen gaskiyarki Sulaiman abun tausayi ne a halin yanzu sai dai shi lokacin da yake aikata lamuransa ai ba dauka wannan lokacin zaizo ba shi Allah ai ba'ayi masa wayo."


"Allah dai ya bashi lafiya naga yayi nadama sosai Ya Sadam don Allah ka yafe masa."


Hararata yayi yace."Magana ai ta wuce a gurina ni bana rike mutum komai laifin da zaiyi min na yafe masa."


Ajiyar zuciya ta sauke tana goge fuskarta ya dinga satar kallonta tausayi take bashi yarinyar yasan duk akanta komai ya faru sam Sule bai iya sarrafa zuciyarsa ba shi kam mace bata isa yasa ya kauce hanya ba ko kuma yayiwa dan uwansa mugun abu kowa dai da halinsa dama hakane sai ku fito ciki daya hali kuma ya bambamta............. Yana parking din motar a cikin gidan ya dan kalleta tana kokarin bude motar yace."Ki kawo min abinci gurina." Tace"To." tare suka fito daga motar ta wuce sassansu shi kuma ya sanya yaron gida Audu ya kwashi kayanta ya shiga dasu ciki......Gurinsa ya wuce cikin kasala da mutuwar jiki halin da ake ciki idan bai kusanci yarinyar nan ba zai iya mutuwa dan zamanta kusa dashi ya haifar masa da abubuwa da dama shiyasa ya shirya dubara idan ta kawo masa abincin zai yi mata wayo ya rage zafi.


NI DA YAYA SADAM


BINTA UMAR ABBALE*


54
Gajiya ta sanya bata tunkari ko ina ba sai toilet wanka tayi ta fito daure da towel mai dan fadi humra kawai ta shafa a jikinta kasancewar yanayin garin akwai zafi dan hadari ma ya hado sosai yana dab da zubar da ruwa ya sanya zafin ya tsananta bata shafa mai ba ta goga humra ta dauki riga da wando irin na bacci amma cotton ne masu taushi ta zura hijab tana niyar fita wayarta dake kan mirror tayi ringing ta dawo da baya ta dauka tana dubawa shine dama kuma zancansa take a zuciyarta taje ta kai masa abinci kamar yanda yace.....Koda ta fito palon babu kowa dan tuni Mammah ta haye sama abunta kai tsaye sai ta nufi kicin ta hada masa abincin ta dauka ta nufi gurinsa.


Kofar dakin a bude take dan haka tana turawa ta bude yana zaune gefan gado jikinsa daure da towel da alama shima bai jima da fitowa daga wanka ba


Ya bita da kallo har ta karaso inda yake zaune ta ajiye kwandon abincin.


Yace."Sai da na kira waya sannan kika tuna dani ko."?


Girgiza kai tayi "Ba haka bane wallahi gajiya tasa na tsaya nayi wanka sannan.


Yace." Dubeta dan Allah wai gajiya sai kace wacce tayi yawo mai yawa." Dariya tayi tana fad'in"Lallai wallahi da gaske nake nagaji yau munyi jarrabawa me zafi sannan ka tsai damu a titi dazu kafafuna duk sun gaji."


"Dama ai raguwace ke daga nin alamarki ba zaki juriya ba wannan 'yar tafiyar kice kin gaji tafiya cikin mota ba a 'kafa ba."


Shiru tayi masa dan taga alamar magana yake ji da ita.


"In hada maka abincin ko kuma naje zaka hada." Tafada tana kallonshi


Yace."Ki hada min abinci kuma ki zauna dan yau hira zaki tayani."


Ta kalleshi da mamaki a tare da ita Girarsa guda ya daga mata yana lumshe mata ido.


Tayi saurin dauke kanta jin wani irin yarrre da jikinta keyi.


Cikin nutsuwa ta hada masa abincin yace."Kin jibgo min nama cikin abincin ki kwashe ki bar min uku kece yafi kamata kici nama ai."


"Humm Ya Sadam kenan." Tafada tana kwashe naman dake saman abincin.......Saukowa yayi kasan kafet ya zauna ta tura masa plate din abincin gabansa tana kauda kai sam bata son ganinsa daure da towel saboda sangarta boxer din ma yau bai sa ba tasan kuma towel din kawai a jikinsa babu wani abu.


Yana mata wani sihirtaccen kallo yace."Kinci abinci ko."? Ta girgixa kai sai zan kwanta zanci." Ta fada tana basarwa zamanta a gurin duk ya gundureta


"Ki sanya hannu muci tare mana." Yafada yana kura mata idonsa.


"Ya Sadam kaci abincinka kaji nima zanci nawa." Yace"Ke! bana son iyayi ki sanya hannu muci abinci."


Kamar bata so ta sanya hannu suna ci a hankali a hankali duk rabin abincin shine ya cinye yace ta kara wani ta sake zubawa Yace."Karfa dan nace ki kwashe nama ki'ki ci kici a binki." Tace."Ya Sadam nima nama bai dameni ba." Yace."Okey to sai ki fadawa yaro karami ni nan nasha murde miki kunne duk lokacin dana kamaki kina satar naman miyar baba Ladidi." Sayyada ta kyalkyale da dariya "Kai Ya Sadam! ni yaushe na saci naman miya kuma."? Cikin shagwaba ta fadi maganar.


Da murmushi a fuskarsa yace." Idan kin manta aini ban

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login