Showing 99001 words to 102000 words out of 142497 words
Chapter 34 - NI DA YAYA SADAM Complete Document by Binta Umar Abbale.txt
yunwa ka samemu ba sannan kayi tolal din kudin da ka kashe kan hidimar da kayi mana insha Allahu za'a biya ka abunka matsiyaci ne yake kyautar 'yan wuta......Aikuwa da jin wannan magana ta Lubabatu sai ya fusata yayi kanta ya jefar kan kujera ya hau bugunta da kafafunsa yana fad'in"Ni kike kira da matsiyaci."!!! Ihun! da take ne ya sanya Sayyada shigowa palon a guje ta isa gurin tana janye Lubabatun yana 'kara haurinta da kafarsa.
"Haba Yaya Sulaiman wannan ai rashin imani ne baka bata abinci ba ka hau dukanta wannan zalinci ne wallah......." Wani wawan duka ya kai mata a baki a gigice ta 'kwallara 'kara tana me rike bakinta.....Ya sake kaiwa bakin nata duka yana fad'in"Don Uwarki da Ubanki daga ina kike shegiya ni zakiyi wa nasiha baki san haushinki nakeji ba dama." Sai ya hau kwance blet a guje! tayi hanyar dakinta ya kwarfo kafafunta ta fad'i 'kasab tayal yace."Fad'an ya dawo kanki dan uwarki yau sai naci ubanki sai na huce 'bacin ran da kike 'kunsa min na shekara da shekaru.....Ya d'aga blet din zai labta mata a jiki aunty Luba ta rike blet din ta bayansa.....Wannan damar ta sanya Sayyada arcewa daki a guje ta zura sakata tana kuka.
Aikuwa a fusace! ya soma shimfid'awa Aunty Luba blet din a jikinta kamar wani mahaukaci ya dinga dukanta tana ihu!!! Da kyar tasha daga hannunsa ta afka kicin ta banke kofa ya mayar da blet dinsa yana huci yake fad'in"Daga yau kya sake yi min maganar kudin abinci ko kuma in baku abinci ai tunda ban samu biyan bukatata ba to kuma ba zaku samu biyan bukata ba daga gurina.....Fita yayi daga gidan a cikin motashi.
Sayyada na jin ya fita da mota ta bude kofa ta fito a guje ta nufi kicin tana kuka take fad'in"Aunty Luba bude kofar ya fita."
Aunty Luba dake raku'be jikin lokar kicin ta mike da kyar jikinta duk yayi tsami ta bude kofar.....Sayyada ta rungume ta kam tana kuka tana tattaba jikinta da bata hakuri.
Lubabatu kasa daurewa tayi itama ta fashe da kuka tana fad'in"Sayyada wannan wace irin kaddara ce Allah ya dora min innalilhi wa'ina ilahi raji'un." Ta karashe maganar tana fadin wannan kalmar......Sayyada ta jata suka zauna kan kujera tana share mata hawaye tace"Aunty Luba kiyi hakuri don Allah nasan nice na jawo miki duka ki gafarce ni."
Tace"Sayyada ba ke bace dama dai Sulaiman nada niyyar dukana kawai daga ya shigo nayi masa maganar abunda yake baya kyautawa shikkenan fa ya hau zagina a kunnanki dai kinji irin gori da cin mutuncin da yake min ashe hakan bai isheshi ba dole sai ya ta'ba lafiyata akwai Allah." Hawaye ya biyo kumatunta.
Sayyada ta sanya hannu tana goge mata hawayen tace"wallahi ni yayi duka saboda bai sameni ba sai ya juya kanki kinga dole ince nice na janyo miki don Allah kiyi hakuri."
Aunty Luba tace"Sayyada na hakura ki daina yi min magajiya na bar Sulaiman da Allah mutukar ya zalince ni Allah sai ya sakamun." Hawayen fuskarta ta goge Sayyada tace"Koda baki fada ba aunty Allah sai ya saka miki zalincin Ya Sule a kanki."
Kudin dake jakarta ta fito dasu ta lissafa dubu talatin ta bata "Aunt gashi ki hada dana hannunki yanzu nan Abbah ya turo min 50k sai ki hada dana gurin Asiya nasan dai sun isa ki siya abinci ki rage cefane kafin na dawo."
Aunty Tace"Sayyada ba zan kar'bi dubu talatin ba tayi yawa dubu goma kacal zan kar'ba sai in hada dana hannuna."
Sayyada tace"Allah aunty Sai kin 'karba ai ke kinfi ni bukatar kudi yanzu aunty ki karba kawai bayan wannan kudin ina da sauran 'yan chanji accont dina nasan zasu isheni har na dawo."
Aunt Luba ta kar'bi kudin daga hannu sayyada tana fadin"Dan dai kin matsane Sayyada da sai ince ki bar kudinki kema zasuyi miki amfani."
Sayyada ta girgiza kanta kawai ba tace komai ba tunanin zalincin Sule takeyi a zahiri mutane da yawa ba zasu dauka Sulaiman nada wannan halin ba saboda fuskar salihai gareshi......Wanda basu san waye Sadam! ba sune zasu dauka shike da irin halin Sulaiman saboda shi kullum fuskarsa a murtuke take babu fara'a amma ta 'bangaran halaye kwata kwata Sadam da Sulaiman basu tarayya ba.
*****
A hankali a hankali take tafiya kana kallonta kasan cikinta ya tsufa daf take da haihuwa hannunta rike da katin asibiti ta fito daga cikin asibitin ta tsaya tana waige waige nemansa takeyi can ta hangoshi ya tsallako titi ya isketa inda take tsaye.
Tana dan ya mutse fuska tace"Sunce wai muje a sake yin scanning. " Tafada tana mika masa katin asibitin.....Kar'ba yayi ya duba katin jikinsa duk yayi sanyi yace."Yanzu ya kikejin yanayin jikin naki? sannan ina fatan jinin ya daina zuba ko."?
Murya na rawa tace"Yana zuba amma ba sosai ba dana fada musu sai sukece dole sai na sake scanning wai zasu duba ni."
Yace."Karki damu kinji ko muje inda akayi miki scanning dinki na farko sai ayi." Umma Bayaro suka nufa Harira na cire 'kafa da 'kyar da 'kyar! mutane sai kallonta suke da mamakin yarinya 'kankanuwa da uban ciki a gaba.
Allah yasa basu tarar da layi ba matar da take ciki na fitowa Harira ta shiga minti goma sha biyar ta fito daga dakin scanning din tana cije baki......Da sauri ya kamota ya zaunar kan kujera yana lallabata da rarrashinta.....Hawaye suka soma zubo mata Harira na da saurin kuka tace"Soja marata ke yi min wani irin ciwo da kyar nake iya tafiya cikin sai motsi yake duk ya dameni."
Cikin kulawa yace"Kiyi
hakuri Inasha Allahu zaku rabu lafiya ai motsin da yaron yake shine lafiya ki huta anan yanzu ki fada min me kike so kici naje na siyo miki bakin asibiti."
Tace"Bana son cin komai mu koma gida na kwanta jiri nake ji." Yace."Sai ki dan huta tukkuna sai muje mu mika musu scanning din kana mu koma gida ki kwanta ko?" Kai ta daga yace"Me zan siyo miki yanzu."? Tace"Akwai masu kulele ko awara ka siya mun ina sha'awar ci." Yace."Bari in dawo yanzu." Mikewa yayi ya fita daga gurin da sauri.......Harira ta bishi da kallo ita kad'ai tasan abunda takeji a jikinta.
*****
Koda Sulaiman yaji labarin tafiyar Sayyada kano sai yace bai yada ba suka dinga kai ruwa rana da ita dashi hakan ya janyo ya mammauje ta da duka tana kuka taje ta sanarwa da iyayensa halin da ake ciki......Aikuwa Alhaji Auwal yace bai isa ba sai da karatun yazo gangara ana tunanin nasara sannan zai kawo wata matsala to Sayyada sai taje ta 'karo ilimi kan wanda take dashi........Ganin ran mahaifin nasa ya 'baci ya sanya ya janye 'kudirinsa amma ya dauki aniyar kwabonsa ba zatayi ciwon kai ba tafiya kuma ko birnin sin! Sayyadar zata tafi taje tayi shi babu abunda zai daina na rayuwarsa.
Ranar littinin Sayyada tayi sallama da gida da aunty Lubabatu wacce tayi tamkar kar su rabu 'yar wannan tafiyar da Sayyadar zatayi ji take tamkar ta shekara ce haka dai sukayi sallama cike da begen juna Sayyada taje ta had'u da abokanan tafiyarta suka dauki hanyar kano cike da fatan samun nasara bisa abunda aka tafi nema.
*****
Harira ta dawo gidansu da zama sakamakon matsaltsalon da take fuskanta tun sanda cikinta ya tsufa ta shiga watan haihuwa take ta faman shan wahala zubar da ruwa sai kuma ta dawo zubar da jini koda sukaje asibiti likitoci suka dubata suga abunda ke faruwa sai sukayi mamaki sosai domin dai har yanzu akwai sauran lokaci kafin ta haihu amma abun mamaki jinin dake zuba a jikinta sai suka hanata aiki da zurga zurga suka duba lafiyar yaron dake cikin normal sannan suka dorata kan magani wanda zai hana jinin fitowa kana sukace daga zarar taji ciwo na haihuwa to maza su tawo asibiti da jin wannnan magana da likitoci sukayi sai hankalin Hansatu ya tashi ta nemi izini gurin Sadam kan ya amince mata Harira ta dawo gida har lokacin da Allah zai sauketa lafiya."
Sadam baiyi wata gardama ba ya amince da bukatar Hansatu Harira ta koma gaban iyayenta da zama tana jiran lokacin haihuwa.
***
Sayyada sun sauka wani ma dai-daicin gida wanda hukumar makaranta ta basu suka zauna na tsawon kwanakin da zasuyi su koma garinsu Su shida ne kacal maza biyu mata hud'u sai Malama Rabi'atu wacce ta kasance jagorarsu........Kwanansu biyu da zuwa suka fara yin abunda ya kawo rana ta farko tashar express redio suka fara zuwa....... sosai Sayyada ta sanya ido kan yanda ake gudanar da aiki da kuma sanin makama.....A rana ta biyu ne suka nufi tashar freedom redio nan taga yanda ake aikin jarida komai a nutse a tsare abun ya bata sha'awa sosai ganin yanda wata ma'aikaciya *Halima Umar Sani* tana labarai rai-rai-rai babu wata tangard'ar murya ko ta na'ura har sanda Halima ta gama gabatar da aikinta Sayyada na kallonta bayan ta gama ta fito Sayyada tace"Aunty Halima gobe idan Allah ya kaimu ki bani aikinki nayi wallahi kin bani sha'awa sosai." Halima tasa dariya tace"To ai bani zaki tambaya ba muje na rakaki ofis din shugaba."
Koda suka samu Daraktan dake 'bangaran gudanar da labarai da maganar yace."Babu komai ai da koyo akan san gwani Gobe Insha Allah Sayyada zata gudanar da takaitaccen labaran da sukeyi bayan shirinsu na barka da hantsi......Sayyada ta dinga murna ta fito tana sanar da 'yan uwanta yanda sukayi.
Washe gari da safe suka wuce gidan redion lokacin ana daf da kammala shirin barka da hantsa Sayyada na zaune kan wata kujera da wata duguwar takarda a hannunta tana duba abunda zata fad'a cikin labaranta,
Ma'abocin jin shirin barka da hantsi ne na kullum baya wuceshi domin shirin ya kan sanya shi ya 'karu da abubuwa da yawa shiyasa da lokaci yayi zai kunna redionsa yana saurara yana harkar cinikayyarsa......Bayan an kammala shirin ne yana kokarin kashe rage vollom din redion yaji muryar ta doki dodon kunnansa.
_*Assalamu alaikum warahamatullahi ta'alah wa barakatuhu jama'a barkanmu da sake saduwa daku a wannan lokaci da muke kawo muku ta'kaitaccen labari wanda Halimatu Umar Sani take gabatar muku a irin wannan lokacin to sai dai yau labaran zai zo muku ne daga bakin SAYYADA LAWALI 'YAR MUTAN DABI! to jama'a a yau ne gomna Abdullahi Omar ganduje ya sanar da cewar wannan watan zai rage kaso biyu daga cikin al'bashin ma'aikata a fad'in jahar nan gwamna Abdullahi Umar ganduje ya tabbatarwa da masana labarai cewar zai kwashi kudin ma'aikata domin ya bada tallafin korana ga wad'anda cutar ta ritsa dasu...................!!!!!!!*_ Tiryan tiryan Sayyada take ba tare da tangard'ar ba......Al'amarin ya bawa kowa mamaki! Mussaman Sadam! Wanda ya mi'ke Tsaye da redio a hannu ya ware murya sosai yana sauraran muryar tar!!!!! yana sake nanata! sunan mai murya a cikin zuciyarsa......
*Sayyada Lawali Dabi!!*
Ji yayi kansa na wani irin ciwo sakamakon muryar tata dake masa kuwwa a cikin kunnansa da sauri ya kashe redion ya sunkuyar da kansa 'kasa wani irin gumi na d'iga daga saman goshinsa.
NI DA YAYA SADAM
NA
BINTA UMAR ABBALE
42
Wani irin sarawa kansa yake masa yaji komai na duniya yayi masa zafi in banda muryar me labaran nan babu abunda ke amsa kuwwa a kunnansa mutane na ta shigowa shagon nasa domin siyayya sai dai su gaji da magana su juya domin kwata kwata hankalinsa da nutsuwarsa basa jikinsa suna can tunani da son tuno a ina ya san me irin wannan sunan *Sayyada Lawal Dabi!* Ya zurfafa a cikin tunani wanda ya sanya masa ganin duhu a idanunsa babu shiri ya kulle shagon nasa ya nufi gida ya kwanta tare da rintse ido sosai kwakwalwarsa ta dauki charge dangane da son tunano wacece wannan yarinya mai irin wannan suna da murya......Bacci ne ya daukeshi mara dadi wanda ya dinga wasu irin mafarkai marasa ma'ana da kan gado cikin mafarkin nasa ya dinga ganin wata rayuwa da yayi a baya mai dadi da 'yanci yaga fuskoki irin wad'anda ya sani a dacan baya amma kuma abun mamaki koda ya farka daga baccin sai yayi ya so ya tunano wane irin mafarki yayi ya kasa tunawa mafarkin ya shafe daga tunaninsa ya tashi da mataccen jiki ya shiga wanda koda ya fito daga bandakin ana ta shirin shiga masallaci domin sallahar la'asar gashi shi ta azuhur baiyi ba dole ya tsaya a gida ya gabatar da sallolinsa
***
Gaskiya Sayyada kinyi 'kokari kwarai abunda abokanan aikinta ke fada kenan ita kuma duk farin ciki ya cikata ta kusa zama cikakkiyar 'yar jarida shi kansa daraktan sai da ya jinjina mata kwarai da gaske yace."Nan gaba kad'an zaki zama cikakkiyar yar jaridar da za'ayi alfahari da ita a ko'ina." Sayyada tayi godiya tana cike da farin ciki sai dai kuma 'karkashin zuciyarta damuwa ce fal wacce ba kowa ne yasan da ita ba sai wanda ya kasance makusancinta duk yanda suke da Saliha ba tasan halin da take ciki ba har yanzu tana nuna mata ita din budurwa ce ba matar aure ba.
*****
Kwana biyu yana cikin wannan halin na tunanin son sanin ainihin yarinyar nan mai takaitaccen labarai amma duk iya kwakwarshi da tunaninsa ya kasa gane inda ya san murya dole tasa ya hakura da takurawa 'kwakwalwarsa sai duk lokacin da zata gabatar da labaran redionsa a kunne take baya matsawa ko ina har sai ta kammala tukkuna zai fara sauraran mutanan dake shige da fice a gurin sana'ar tashi......A duk sanda take gabatar da labaran yakan tsinci kansa cikin nishadi mara misali ya dinga murmushi kenan yana lumshe ido muryar yarinyar nayi masa bala'in dad'i a ranshi.
*****
Sayyada kwanansu goma a kano suna zaga gidajan redio alhamdullahi sun samu nasara da cigaba kwarai da gaske wanda har tashoshi biyu suka nemi bukatar daukarta aiki duk sanda Allah yasa ta kammala karatunta.....Tace za tayi shawara idan da yiwur hakan sai tayi musu magana tunda ita ba 'yar jahar bace al'amarin na bukatar nazari da shawarwari.
****
Da wani irin ciwon mara Harira ta tashi a daddafe ta mike tsaye tana bin bango ta fito tsakar gida Hansatu da Abu na aiki suka ganta ta fito tana rintse ido da cije baki duk sai su saki abunda suke suka nufeta suna tambayarta.....Kafin ma tace wani abu suka ga jini na bin kafafunta Hansantu ta saka salati tayi daki da sauri ta dauki hijabi tana fad'in "Abu yarinyar nan haihuwa za tayi bana son wata matsalar ta faru tunda likitoci sunce daga zarar ta fara ciwo a tafi gurunsu to gwara mubi abunda suka fada tunda dai yanzu komai yazo da zamani."
Abu tace"wai da mu d'an jinkirta mu gani a gida ko Allah zai sanya ta haihu wallahi ni bana son zuwa asibitinan sun fiye tsirface tsirfacen tsiya."
Hansatu tayi gaba da sauri tana fad'in"Zancan kike so Abu kina ganin yarinya nayin na'kudar jini kice mu tsaya a gida ni kam ba zan iya ba, gwara a sanar da mijinta halin da ake ciki......Waje tayi da sauri har tana tuntube Jatau na ganinta a kid'eme! ya mike zaune yana fadin"Lafiya Hansatu.'' Tace."Malam Harira ce zata haihu shine za'a shaidawa mijinta ya samo mota a tafi asibiti." Tana idar da maganarta Sadam! ya fito daga gida da shirin zuwa kauyen kura domun dauko shinkafa......Ta iske shi tun kafin ya karaso ta sanar masa halin da ake ciki.
Cikin damuwa da tashin hankali ya nufi titi domin dauko abun hawa.....Da kyar ya samu a dai-daitar da babu jama'a a ciki ya shigo dashi ciki kana ya shiga gidan ganin suna rirrike Hariran tana cijewa ya sanya ya tattare hannun rigarsa ya dauketa cak! duk kuwa da jinin dake jikinta bai dameshi ba burinsa kawai yaga Allah ya rabata da cikinta lafiya.
Hansatu da Abu suka biyo bayansu hannunwansu rike da leda viva wacce suka shirya zannuwa a ciki duk sun tana dane sune domin haihuwar........Ya sanyanta a tsakiya Hansatu da Abu suka zauna a gefe da gefen ta shi kuma ya zauna gefan me me d'an sahun yaja da sauri suka bar unguwar............Suna tafiya yana waiwayen bayanshi yana kallon yanda Harira ke cije baki tana salati da kiran sunan Allah! hankalin me dan sahu ya tashi sai yaji wani irin imani yazo masa ashe dama haka mata ke shan wahala yayin haihuwa....Ya dinga fafarar mashin din da gudu burinsa kawai ya isa asibitin Murtala kamar yanda Sadam din ya fada masa.
Sai da suka zo titin Yahya gusau! suka tadda gosolw ya'ki gaba ya'ki baya wata babbar mota ta tokare hanya, masu uziri suka dunga juya abubuwan hawansu suna sauya hanya.....Cikinsu harda su Sayyada da Saliha wanda suma suke cikin a dai-dai tasu domin zuwa gurin aiki.....Sayyada tace"Don Allah idan da hanya ka sanja mana wallahi muna da uziri sosai yanzu." Yace"To ai hajiya bakya gani ne inda zan juya mashin din nawa ma babu spece dole sai wannan dake gabanmu ya wuce tukkuna." Kanta ta zuro tana le'ken gurin.......Idanunta suka hango mata gefan fuskarshi ya fito daga cikin a dai-dai tar ana aikin a gaji dashi burinsa kawai su samu hanyar ma da zasu juya su koma baya domin sanja hanya amma babu hali ko wane me mota yazo ya tokare hanya.....Gabanta ne ya dinga fad'uwa daf! daf! daf! Fit! ta fito daga cikin babur din tana d'ad'daga kai so take ta sake hangoshi inaaaa ya shige tsakanin motoci da mashina yana gyara hanya......"Wai Sayyada fitar me kikayi ne cikin maza kina la'ka kai." Saliha dake cikin a dai-dai ta sahu take wannan maganar......Sayyada bata ce mata komai ba sai wurga ido takeyi har yanzu kuma gabanta bai daina fad'uwa ba!...... Fara shiga tsakanin motoci tayi tana sake dubawa ko Allah zai sanya ta sake ganinsa babu ruwanta da kallon da mutane ke mata ita dai burinta kawai ta sake ganinsa tana kuma adduar Allah ya sanya shi ne........Sai da tayi tafiya mai nisa tukkuna ta hangoshi saman gada suna magana da wani d'an sanda da yake ta rashin mutunci ga mutane shi kuma Sadam! din na nuna masa cewar akwai masu uziri shiyasa ya fito yana taimakawa Shi kuma dan sandan yana nuna masa ai ba aikinsa bane......Sadam! ranshi ya 'baci! matuka ya nuna masa cewar matarsa na cikin a dai-dai ta sahu zata haihu amma yake masa wata magana a take suka soma cacar