Showing 30001 words to 33000 words out of 142497 words

Chapter 11 - NI DA YAYA SADAM Complete Document by Binta Umar Abbale.txt

09 Dec 2024

50459

jikina har yayi sanyi da jin wannan magana." murmushi yayi yace."Mamah mutukar kikaga banje wannan jihadin ba to bana numfashi a doran duniya ke dai addua kawai zaki cigaba da yi min." Tace."To Ubangiji Allah ya baku nasara ya kuma dawo mana daku lafiya."Alhaji Auwal dashi Sadam! din suka amsa da "Ameeen Ya rabbi."!


***
Amarya Sayyada fa sai gyara take sha ta ko wanne fanni domin can 'bangaran mahaifinta ma kullum sai sun kirata sun turara mata jiki da had'in turare sannan sunyi mata dame-dame na maganin gyara tasha sun shafe ta da lalle tare da bata rubutu na tsari a cewarsu wannan lokacin ne ya kamata su nuna mata kaunar da suke mata, Mahaifinta yayi mata siye-siye sannan ya bata shanu biyu saniya da sa yace amma za'a ajiye mata a garin duk zuriar da ta samu nata ne Sayyada taji dadin kyautar da mahaifinta yayi mata Kakanta maigari ma yayi mata kyauta ta ban mamaki! kowa ya kula da Sayyada a cikin gidan Maigari banda matar babanta Allah ya sanya alkairi ma ta kasa cewa saboda tsabar bakin cikin dake damunta


*Wannan kenan*


Cikin 'yan kwanakin da Sayyada tayi tana shan magani gami da kar'bar gyaran jiki sai ta ciko sosai tayi kwarjini kyawunta ya sake fitowa fatar jikinta ta goge sosai ta zama abin sha'awa in ka ganta sai ka rantse da cewar cikin birni akayi mata gyaran amare saboda yanda ta koma, Kullum tana gidan Mariya tare da Ummi da sauran kawayen su suna shirya yanda al'amarin biki zai kasance.....Amina ta 'karfi da yaji ta shiga cikinsu ta saki jikinta ana hidima da ita tun suna zaginta suna mata dariya har suka kyaleta domin ta kiyin zuciya.....Ummi ce ta yankawa Sayyada salatif mai tsari da burgewa suka hada lalle yanda zaiyi kyau yayi kamu! aikuwa Sayyada ta fito ras da ita jan lallan yayi masifar kyau abinka da farar fata.
Kitsone Sayyada tace bata so saboda tsan ko anyi ba zaiyi wani tasiri ba, sai Mariya ta dinga tsokanarta tana fadin ai gwara ki kitse kanki wallahi don kin san kullum sai ya jike da ruwan wanka." Dariya suka sheke da ita suka tafa Sayyada tace"Ke nifa yanzu na fara jin tsoro wallahi."Mariya tace."Duk tsoranki baki kaini ba gashi ni na hakura na zama 'yar gari." Haka suka 'bata lokaci suna hira kafin suyi sallama da Mariya su nufo gida.


****


Yau Juma'a uku ga watan bakwai shekara ta dubu biyu da bakwai aka daura auran Sadam! da Sayyada, Kan sadaki dubu hamsin wanda Sulaiman ya bada da aljihunsa wannan al'amari yayi masifar 'batawa Sadam! rai da kansa ya bada sadakin auran sa naira dubu talatin amma saboda tsabar son a sani yayi gaggawar mi'ka nasa sam bai wani burgeshi ba ya fi son komai yayi da kansa tunda har ya fara goranta masa kan aikinsa to baya so ya gaza ta ko wanne fanni.


Labarin daurin auran na isa cikin gidan Sayyada jikinta yai 'kwata'kes! salo-salo taje ta kwanta kan gado gabanta na fad'uwa! gayyar 'kawayenta ne da suka zo suka sanya ta saki jikinta duk sunci kwalliya dai-dai gwargwado amma kuma kana ganinsu zaka gane akwai banbaci da 'yan cikin gari......Itama amaryar tana sanye da Swiss les purple anyi mata dinki stone work dake duk Hjy Fatsima ta bayar an dinka mata rabin kayan lefan dinki irin na 'yan birni Sayyada tayi kyau sosai ta gyara gashinta ya sauka gadon bayanta ta yafa dankwalin les din kana sanya takalmi plete da pose irin ta amare tayi kyau sosai sai dai kana kallonta zaka gane bambamci da ita da amaryar cikin gari sannan kuma akwai yarinta a tare da ita tunda yanzu ba tafi shekaru goma sha hudu zuwa sha biyar ba........Jama'ar da suka cika gidan suka dinga janta da wasa tana dai daurewa tana gaishesu da abun yayi yawa kawai sai ta fashe da kuka ta rungume Baba Ladidi to itama Baban ashe 'boye kukan take ganin Sayyada nayi sai itama ta fara nata aka rasa me basu hakuri su hakura....Cikin wannan hali suka shigo gidan....Sadam! da Sulaiman kaya iri daya ne a jikinsu shadda ce galila dinkin babbar riga, Sulaiman fuskarsa a sake ya dinga gaisawa da jama'a shi kuwa gogan bai wani tsaya sosai ba a gurin tunda yaga abinda yake faruwa takaici yasa ya bude dakin da suke sauka ya shige har da turo kofa....Sulaiman kam wayarsa ya fito da ita ya dinga musu hoto yana dariya sai da yaga abun nasu yana nema yayi yawa sannan ya soma rarrashinsu da kyar suka daina kukan Jama'a kuwa sai dariya ake musu.


Yana daga kwance cikin dakin yana jiyo abinda yake faruwa juyi kawai yake yana mamakin zubar da girma irin na Sulaiman yana jiyo muryarsa yana tsokanar Sayyada ji yake kamar ya tashi yaje ya kwad'e shi don takaici......."Yaya Sulaiman bamu wayarka muyi selfie." muryarta ya jiyo cikin taratsi tana wannan maganar.....Kafin ya ankara yaji sulaiman din na cewa"Muje inyi muku keda 'kawayen naki." Firgigt! ya mi'ke zaune rigarsa da ya cire ya dauka ya sanya ko botiran bai mayar ba ya fito fit!!! ai tuni sun fice daga gidan.....Kai tsaye hanyar fita ya nufa, yana jin yan biki na fad'in"Ango kasha kamshi Allah ya sanya alkairi." bai ce komai ba yayi gaba........Can baban soro ya riskesu suna ta hauka shi kuma Sulaiman din sai biye musu yake yana dariya harda Mariya da take matar aure ta cire mayafi tana gantsare-gantsare wai ita dole hoto takeyi tana so tayi kyau........."Wannan wane irin hauka ne."!!!! muryarsa ta sanya suka juyo da sauri....yana tsaye da fuska a daure ya hard'e hannunwa a kirji yana watsa musu dan iskan kallo....Ya kalli Sulaiman cikin takaici yace."Wannan dai ba girman ka bane wallahi karfa ka manta da cewar wa d'an nan yaran ba irin 'yan matan cikin gari bane babu abinda suka sani bayan haka kuma akwai matata a cikinsu dai-dai kenan kazo kana daukarsu a hoto kana dariya."


Sulaiman yayi shiru ransa ya 'baci Sadam bashi da mutumci kuma baya jin kunyar ya tozarta shi a gaban ko waye.....Ba tare da yace masa komai ba ya wuce ya barsu a gurin.....Cikin tsawa! yace."Dallah! malamai ku wuce ku bawa mutane guri in banda hauka kawai kun tsaya gaban gardi irin wannan yana muku hoto wai ku kyawawa! mtsssw!!!! Su Mariya suka shige cikin gidan jikinsu duk a sanyaye Sayyada taji haushin wulakancin da yayiwa kawayenta sai ta dinga zumbura baki tana hararasa! tazo zata wuce yace."Dube ta sam bata dace da amarya ba."! "To ai kai ma baka dace da ango ba." Yace."Ke waye ya fad'a miki dama ni ango ne."!? Hararsa tayi yace."Ni kike harara mara kunya." Ta juya tare da fad'in"Duk inda ango yake yana farin ciki amma banda kai kowa yace ka sanja hali ka'ki ji! Ni ba zaka takura min da kawayena ba tunda ai ba da wayarka muke hotonba." Yace "Zo nan ki 'karbi wayar tawa kuje kuyi hoton." Cikin rashin wayo ta dawo shi kuma ya zura hannu kamar zai dauko wayar caraf! ya rike damtsenta! suka kalli juna ita dashi saurin dauke kansa yayi jin wani irin maganad'isu na fizgarsa zuwa gareta....Cikin kasalalliyar murya tace"Sakar min damtse."!
"Idan na'ki fa."? yafad'a cikin wani irin voice hucin numfashinsu ne yake had'uwa sai jikinta ya soma kyarma! shi kuma ya kurawa bakinta ido yana kallo a hankali yace." Su Sayyada amarya." Dauke kanta tayi tana shan kunu. Ya saki murmushi tare da cizan lipls dinsa na kasa yace."Ina fatan kin shirya kar'bar angon naki." Zumbura baki tayi tana dauke kai! murmushi yayi ya sakar mata hannu yace."Ki shirya da kyau! ni ba ragon namiji bane kuma bazan d'aga miki 'kafa ba."
Murguda baki tayi tace"Ai a shirye nake kuma waye ya fad'a maka nima raguwa ce."!? ido ya zare ya bude baki yana kallonta cike da mamaki! fari tayi masa da gadar-gadar din idanunta wanda yasa ya kusa faduwa a gurin ta juya ta shige cikin gidan......''Iyeee! ashe dai 'yan matan 'kauye suna da abun mamaki yanzu ya tabbatar da cewar Sayyada tasan aure tasan abinda akeyi a zaman aure, lallai akwai badakala kenan.....Shifa baya jin zai taki yarinyar a yanzu sai ta zama cikakkiyar mace a ganinsa a sannan ne zata iya d'auke masa dukanin bukatarsa a yanzu yana ganin idan ya kusanci yarinyar zai iya sanyawa ta had'u da yoyon fitsari tunda yawanci masu irin shekarunta ke haduwa da lalurar ya girmi Sayyada da kusan shekaru ashirin kuma karfinsu ba daya bane jarabarsu ba daya bace shiyasa kawai ya yanke shawarar bari ta kara shekuru sai suyi zaman aure mai tsafta


Sayyada na shiga cikin gidan suka ke'be da Mariya tace"Mariya kinji abinda yake cewa kuwa."? Mariya tace"Sai kin fad'a." "Humm! wai cewa yake yi dafatan na shirya masa kaina ni wallahi tsoro nake ji fa." Mariya ta dinga dariya tace"Ke mijikin wayayye ne don Allah ki saki jiki kusha soyayya." Sayyada tace"Mariya kenan baki ga abinda na gani bane shiyasa kike cewa in kwantar da hankalina." Sayyada duk sanda ta tuno da sandar girman Sadam! sai gabanta ya fad'i! domin ba zata ta'ba mance ranar bankadashi a bandaki ba."


To haka aka cigaba da gudanar da sha'anin biki da al'adar garin....Kwana uku bayan daurin aure suka shirya tafiya Sayyada ta cika gidan da kuka tana kukan rabuwa da Baba Ladi baba marka suma kukan suke da kyar dai aka taushe ta tayi shiru aka kaita can gidan iyayenta nan ma sai da tayi kuka sun jima da mahaifinta nayi mata nasiha hakanan maigari ma yayi mata nasiha da fatan zaman lafiya sannan sukayi sallama da juna.


*****


Biyu shaura na rana sun isa garin Kaduna garin gwamna Nan ma jama'a ce cike da gidan 'yan uwan hajiya Fatsima da makota da abokanan arziki sai hidima sukeyi Ango da Amarya na shigowa suka cika gidan da bud'a suna tsokanar Sadam! sai sannan taji muryarsa yana ramawa harda dariya....'yar autar su Hjy Fatsima ce mai suna Zuhura ita ta ja hannun Sayyada suka shige can bedroom dinta ta bude mata lullubin sayyada ta dinga jin kunya tana kauda kai sai da taga zuhuran ba wata babba bace sai ta saki jikinta suna hira haka 'yan uwan hjy fatsima suka dinga shigowa d'aya bayan d'aya suna ganinta tare da sanya albarka Sadam! na kowa ne shiyasa suke kaunar matarsa.


Aunty Luba ce ta shigo tana cire 'kafa d'akyar kana kallonta kasan ta kusa haihuwa tazo ta rungume Sayyada tana fad'in"Sannu da zuwa amaryamu." Sayyada na jin muryar aunt Luba ta bude mayafi rungumeta tayi tace"ashe baki haihu ba." Luba tace"Ina kan hanya Sayyada ku tayamu addua." Tace."Insha Allahu aunty.....Tare suka ci abinci suna hirar yaushe gamo sayyada ta sake da ita sosai dama tuntuni sun saba tunda Sulaiman na kaita *Dabi* tun kafin auransu sannan duk sanda yaje *Dabi* yana bata waya su gaisa shiyasa sukayi sabo da juna.
Anan ne take jin labarin tafiyar Sulaiman din bayan daurin aure tafiya ta kamashi 'kasar larabawa *Qatar* sati biyu zaiyi ya dawo....Sayyada tayi masa fatan alkairi da dawowa lafiya.


***


Sai misalin karfe takwas na dare sannan gidan ya samu sau'ki masu aiki sun gyara ko ina na gidan kowa kuma ya kama gabanshi sai aunty Luba wacce dama tun bayan tafiyar mijin nata ta dawo gidan sai ya dawo tukkuna Hajiya Fatsima tace"Da zuhura ta zauna ta d'ebe mata kewa tunda anyi hutu......Hajiya Fatsima ta shigo dakin ta tarar dasu suna hira ta kalli Luba tace"Ya kamata Sayyada ta shirya sai ku rakata dakin mijinta ko."? aunt luba tace"To Mamah! tana fita Luba tasa Sayyada tayi wanka tas ta gyara mata jikinta kana ta feshe mata jiki da turare masu sanyin kamshi ta bata wani material mai kyau da tsada tasa ta yafa mata mayafi kalar material din takalmi sabo ta sanya suka fito a tare Hajiya Fatsima tayi mata nasiha sosai dangane da zaman aure.........Kai tsaye bangaran Sadam! din suka nufa lokacin yana daf da fitowa sai sukayi kici'bus! fuska ya saki sosai suka gaisa da Luba duk fad'an da sukeyi da Sulaiman bai shafeta ba saboda yana ganin mutuncinta sosai matace mai hankali da aiki da iliminta yace."Da kin bari ma nazo na dauki amaryarta da kaina ai ba wani abun bane." Tace"Oho dai naji ai komai zaka fada sai dai ka fad'a ni bana kishi tunda dai nasan nice uwar gida." Yace."Ai kuwa yanzu na daina yayinki tunda na samu amarya." Dariya tayi tace"Ai dama wannan halinku ne." hanya ya basu suka shige yace."To ni dama fita zanyi amma ba zan dade ba." Hararasa tayi tace"Kana da amaryar zaka fita yawo ko aiki ne da kai ya kamata ka dauki Uziri." Yace."Karki damu yanzu zan dawo insha Allah....Gurin aiki zan nufa yanzu amma bazan wani dade ba tunda nasan akwai amarya ke dai kawai ki zauna kiyi min gadinta." Tace."Baka isa ba nima ka barni da kishin dake damuna." Dariya ya dinga 'kyakyatawa ya kama hanya ya fita....Sayyada ta dinga mamakinsa dama haka yake sai dariya yake har da kyakyawata lallai ma Yaya Sadam! ita sai yayi ta sha mata kunu yana mata tsaawa.
Aunty Luba ta d'an zauna mata amma da taga dare yayi sosai sai tayi mata sallama ta koma can sashen su Hajiya......Sayyada tayi tsuru kamar mayya motsi kadan ta duba agogo karfe goma sha biyu da rabi tayi bai shigo ba sai ta kwanta kan gadonsa tana kuka haka bacci ya dauketa bata tashi ba sai asubah!!! tana kokarin sauka daga gadon ne taji motsin shigowa cikin palon ta koma ta kwanta nan taji ya turo kofar dakin ya shigo ya jima tsaye a kanta yana kallo duk a tunaninsa bacci take yaje yana jan kafafunta" Taki bude ido mugun haushinsa takeji ta dauka zaiyi ta rawar kai a kanta kamar yanda angwaye keyi shi sai yayi wanka ma yayi ficewarsa saboda bata da matsayi a gurinsa.....Da ta gaji da jan kafar ta da yake sai ta fuzge da karfi ta jiyo muryarsa yana fadin"Tashi kiyi sallah." Toilet ya nufa ta bishi da harara! Taji ciwon abinda yayi mata ya nuna bai damu da ita ba shiyasa yaje ya kwana a waje....jin motsin bude kofa yasa ta dauke kanta da sauri ya fito ya sauya jallabiya duk tana kallonsa ya dauki carbi ya fita....Nan ta mike ta nufi bandakin domin daura alwala.


10/6/2020
NI DA YAYA SADAM


NA
BINTA UMAR ABBALE


Pege17*
Wanke bakinta tayi da brush sannan ta daura alwala ta fito ta shimfida dadduma hijab ta zura ta tayar da sallah ta jima tana addua kafin ta kwanta bacci me nauyi ya dauketa.....Sai da gari ya fara haske sannan ya shigo gidan....Ganin tana bacci yasa ya tsallaketa ya nufi toilet din yayi uzurinsa ya fito kan bed ya nufa ya kwanta rigingine yana kallon rufin dakin bacci yake sonyi yaji motsinta idanunta da alamun bacci take kokarin hawa bed din da sauri yaja gefe yana kallonta taja bargo ta rufe kafafunta da alama bacci takeji sosai.
Fuskarta ya tsurawa ido yana kallo Yarinyar tana da kyau sai da tayi 'kankanta wata zuciyar tace masa sau nawa ana yiwa yara aure irinta kuma su zauna lafiya har kaga an haihu....."Tabbas hakane " yafada a ranshi to ammafa shi duk da haka yana jin tsoron haikewa yarinyar kar yaje ya had'ata da wata lalurar shiyasa yake so tayi 'kwari tukkuna.....Le'bunanta ya tsurawa ido yana kallonsu cike da sha'awa wai yanzu wannsn 'yar ficiciyar itace matarsa wanda yana gani da wata babbar macen ce da tuni ya kawar da kwadayinsa na shekara da shekaru.


Bacci takeyi sosai amma duk ta matso jikinsa tana nani'karsa, shi kuma sai matsawa yake yana ture ta, tana sake matsowa tsawa! ya buga mata"Ke! meye hakane."!? ta bude idonta dake cike da bacci.... ganin idanunta a lumshe ya sanya duk wata sha'awarshi ta tashi yayi saurin mikewa zaune yana hararata"Idan ba bacci xakiyi ba to ki saurara haba! mutum da dakinsa anzo an hanashi ya huta."
Turo baki tayi gaba ya dauke kansa tare da jan karamin tsaki ya koma ya kwanta yana kallon cilling shi kadai yasan abinda yake damunsa mamaki yake wai yarinya kankanuwa tana nema ta burkita masa lissafi ko Halima da take cikkakiyar mace bata ya mutsa masa lisaafi ba sai wannan yar k'ank'anuwar.


Sayyada na sani ta dinga matsawa har sai da ta dangane da inda yake ta d'ora kanta a kirjinsa ta cigaba da lumshe idonta takaici da 'bacin rai suka dameshi ya lura yarinyar fitinanniya ce kuma bata jin tsoro yanzu a wannan zamanin yarinya 'kan'kanuwa kamar sayyada har ta san ta kai kanta gurin miji......kyaleta yayi kawai kanta a kirjinsa haka bacci ya daukeshi sai da taji saukar numfashinsa sannan ta bude idonta ta tsira masa ido tana kallo Allah da ya hallice ta ya zuba mata 'kaunar Sadam! tana fatan tayi rayuwa mai tsayi tare dashi sannan tana addua Allah yasa ya sota kamar yanda take sonsa.....Bacci gagararta yayi ta lalace gurin kallonsa sai da ta gaji don kanta sannan ta mike taje tayo wanka ta shirya jikinta tsaf turarasa masu tsada ta dauka duk ta feshe a jikinta mayafi ta yafa ta sanya takalmi plate ta nufi bangaran su Hajiya.


Hajiya Fatsima na kicin ita da mai aikinta suna aikin break fast ta shiga palon ta zauna Hjy Fatsima ta fito daga kicin ta ganta a zaune sakin fuska tayi sosai Sayyada ta sakko har 'kasa ta gaisheta Hjy Fatsima ta amsa a sake tana tambayar ta gajiyar biki.Murmushi kawai tayi.


Aunt Luba ce ta fito da shirin zuwa asibiti ta zauna kan kujera suka gaisa Sayyada tace."Aunty Luba da muje in raka ki asibitin ko." Tace"Karki damu Sayyada Sulaiman ne zai zo. yanzu ya daukeni." Tace."To aunty bari in kar'bo miki break fast kiyi ko." Aunty Luba tace"Nagode kanwata." Tare sukayi bresk fast din aunty luba na tsokanarta amarci ita dai ba tace komai sai dariya kawai take.
Sulaiman ne ya shigo cikin kananun kaya yayi kyau sosai hannunsa rike da key na mota, Sayyada sai fara'a take yi "Yaya Sulaiman sannu." ya zauna kusa da ita yana amsawa tare da fadin"Ina angon naki."? hannu tasa ta rufe fuska murmushi yayi yana danne 'bacin ran dake taso masa.


Hajiya Fatsima ta fito daga kicin ganin Sulaiman a zaune sai ya bata mamaki tace"Yaushe

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login