Showing 105001 words to 108000 words out of 142497 words
Chapter 36 - NI DA YAYA SADAM Complete Document by Binta Umar Abbale.txt
akwai magautan da zasu sake wani yunkurin akaina ki bari kawai dukaninsu zan basu mamaki."
Ta dinga kallonsa da wani irin yanayi a fuskarta tace"Yanzu ace iyayenka na cikin halin damuwa ta rashinka wanda nasan har yanzu basu fitar da rai ba akanka sun dai hakura sun barwa Allah yanzu kuma Allah ya bayyanaka kana raye a duniya sannab kace sai nan da wani lokaci zakaje garesu saboda wani dalilinka a gaskiya idan kayi musu haka bakayi musu adalci ba."
Yace."Nasan da haka Sayyada amma ai nima kinji uzirina ko? kuma daga dawowata sai gujewa wad'anda sukayi min hallaci hakan ba kana bace Wad'annan mutanan sun cancani komai a gareni kuma na fad'a miki mahaifiyar yarinyar nan bata da lafiya tasha wahala sosai gurin haihuwa Allah ne yasa tana da sauran kwana a duniya dole in tsaya inga ta samu lafiya tukkuna koma meye sai ayi."
Taji wani kutun ba'kin ciki ya tokare mata a kirji lallai Matar tasa nada babban matsayi a gurinsa tunda har yake kokarin watsar da iyayensa akanta to idan hakane kuwa itama ba taga amfanin zamanta cikin asibitin ba gwara kawai taje tayi abinda ya kawota garin.
Ta mike tana karkad'e zaninta ta rataya jakarta kallo ya bita dashi ya mike hannunsa rike da yarinyar......"Ina zakije kuma."? Ba tare da ta kalleshi ba tace"Zan nufi masaukina ne." Sai sannan ya shiga tunanin abinda ya kawo ta garin.
"Wai shin me ma ya kawo ki garin kano ne."? yafad'a yana me tsura mata ido da tuhuma....Ta tare da takalleshi ba tace" Aiki ya kawoni." Gaba tayi ya bita da kallo cike da mamaki!!! Ya juya ya iske inda su Hansatu ke zaune suna maganar data shafesu....Ya mikawa Abu babyb tare da fad'in"Bari in samarwa Sayyada abun hawa." Sukayi saurin kallon inda take zaune sai suka hangota ta kusa fita daga gate din asibitin suka cika da mamakin yarinyar ta tafi babu sallama kome yake faruwa oho.''
Yana fita ya isketa ta tare babur zata shiga ya hana mai babur din daukarta rai a 'bace yace."Ina miki magana kinyi gaba Sayyada ashe dai har yanzu kina nan da halinki ko."?
"To Yaya Sadam! wai me kake so nace maka ne? tafada cikin kosawa yace." Na tambayi me ya kawoki garinan kin'ki tsayawa kiyi min cikakken bayani saboda kin rainani kinyi gaba kin barni ai ko mutanan nan kyayiwa sallama kafin ki tafi."
Tayi kokarin danne damuwar dake damunta tayi masa bayanin abunda suka zo yi a garin yace."Kina nufin kece kike takaitaccen labaran nan na barka da hantsi."? Tace."Eh." Yayi jim! yana tunani da 'batacciyar murya yace."Okey waye ya za'bar miki wannan karatun."? Ta kalleshi tana cin kunu tace"Nice na za'bawa kaina." Girgiza kai yayi yace."Idan na isa dake wannan takaitaccen labaran da kikeyi kina ma'kale murya to daga yau karki sake aiki kuma inda irin wannan ne mutukar nine mijinki ba zakiyi ba."
Ba tace masa komai ba ta cigaba da tsayar da abun hawa ranta in yayi dubu ya 'baci wai shin wane irin hukunci ya dace tayi masa ne.......!
"Wace Unguwa kuka sauka keda abokanan naki."? Shiru tayi bata bashi amsa ba
" Ko bakiji bane."! ? yafad'a da kaurarriyar murya......."Ja'in Yamma." Shiru yayi yana kallonta wai ashe dama Sayyada ce keyi wannan labaran da yake saurara yana jin dad'in muryarta yanzu wa yasa iya adadin mazan dake sauraran muryarta yasan dole wasu suji dadi su yabe ta babu shakka ba za'ayi wannan shashancin dasi ba.
'Karamar wayarshi ya fito da ita daga aljuhunsa yace."Bani numbar wayarki anjima zanzo inga gidan........Ba tare da ta kalleshi ba ta kar'bi wayar tasa ta sanya numbar ta mika masa.....Babur ya tsaya gabansu ba tare da ta fad'a masa inda zai kaita ba ta shiga da sauri tace"Muje."! Mai babur yaja da sauri Sadam! dake serving din numbar ya dago kansa da sauri ya ganta zaune cikin babur din har yayi nisa......'Kwafa yayi ya koma cikin asibitin.
Tun a cikin babur din take kuka takasa daurewa kuka take sosai har mai babur din ya gane abunda ke faruwa yace."Kiyi hakuri komai yayi tsanani maganinsa Allah Allah ya basu lafiya." Shi duk a tunaninsa ko wani ne bashi da lafiya suka kawoshi asibiti shine take kuka........."Tace"Ja'in Yamma zamu shiga dai-dai gidan mai na d'an marna ka shiga layin." Yace."To shikkenan Hajiya."
Tana sauka ta bashi kudinsa ta tura kofar gidan ta shiga da sallama Saliha ce ke musu girki a kicin ita kuma aunty Rabi'atu na cikin daki akwance 'yan mazan duk sun futa ganin gari.
Saliha tace"Sayyada sai yanzu sannu ya mai jiki."? Tace"Da sauki Alhamdullahi yanzu ma shine ya rakoni na samu mota ina aunty Rabi'' ? tace"Tana ciki tana bacci ai da nayi mata bayani sai ta daina fad'a ta shiga jajanta al'amarin." Tace"Aikuwa dai wallahi alamarin sai addua."" Ciki ta shiga ta ajiye jakarta ta fito ta dibi ruwa ta shiga wanka wai ko zataji sanyi a ranta to cikin bandakin ma kasa daurewa tayi sai da tayi kukanta son ranta kana tayi wankan ta fito.....Tana shiga dakin suka hada ido da aunt Rabi tace"Sayyada kin dawo ashe ya me jiki."? Tace"Jiki da sauki aunty." Aunt Rabi ta dinga kallonta tace"Naga idanunki sunyi jawur kuka kikeyi kenan."? tace"aunt ba kuka nake ba."Tace"Haba Sayyada gashinan idanunki sun nuna."Murmushi tayi tace"Aunt tausayi ne kawai ya sani kuka wallahi wasu jami'an tsaron na yin abunda suke so kuma basa aiki kan 'ka'ida yanzu aunty da da tsautsayi fa da tuni shikkenan Ya Sadam zai iya rasa ransa dan bayan fa ya daddakeshi da bundugar mutane suka dinga tattakeshi dan dai kawai Allah yayi yana da sauran kwana a duniya."
Aunty Rabi'a tace"Hakane dama Sayyada ai yanxu ba ko wane ma'aikaci ne yasan aikinsa ba kowa nayin abinda ransa yake so amma kuma naji dad'i sosai shima da mutane basu kyaleshi ba suka dagargarje shi.'' Tace"Aikuwa yasha duka dan jina jina akayi masa."
****
Cikin ikon Allah Harira ta dawo hayyacinta har tana iya gane wadanda ke kusa da ita.....
Sadam! Jatau dasu Hansatu na dakin suna mata sannu da jiki daga kai kurum take tana kallonsu ita kadai tasan irin yanda takeji a jikinta kamar ba nata ba likita ya shigo ya dubata yana tambayarta yanayin jikibta a hankali tace"Da sauki." Ya kalli su Hansatu da fadin"Ku bata taga abunda ta haifa." Abu ta mika mata babynta ta 'karba a hankali tana kallonta sai ta saki murmushi ta dago kai tana kallon mahaifinta tace"Baba yarinyar na kama da Soja." Suka sanya dariya harshi Sadam din yayi murmushi yana kallonta gwanin tausayi yana mamakin! wannan 'kankanuwar yarinyar ya haikewa wai har yayi mata ciki ai dole tasha wahala sai ya sake jin wani irin tausayinta na ratsa shi......Sabida fa irin wannan wahalhalun da mata kesha gurin haihuwa ya janyo ya dinga tsaikon kusantar Sayyada saboda baya so ta wahala gurin haihuwa.......Jatau yace."Ai wannan yarinya duk wanda ya ganta yaga ubanta yasan suna kama dama haka akeso kyan da ya gaji ubansa." Harira murmushi kawai take tana kara jin kaunar yarinyar a cikin ranta.....Narse ce ta shigo dakin tace" yanzu tunda kunga halin da take ciki kuna iya futa domin za'a gyara dakin kuma sannan zan nuna mata yanda zata shayar da 'yarta."
Fita sukayi daga d'akin Narse din ta gyara abunda zata gyara a dakin kana ta zauna tana nunawa Harira yanda zata baiwa babynta nono cikin ikon Allah yarinyar na kama nonon ta zu'ko ruwa aikuwa ta kama sosai tana sha tamkar ba bakuwar duniya ba wai tasan dadin nono narse din da ita Hariran suka cika da mamakin wayon yarinyar.
To Dr yace."Ba zai sallami Harira ba sai ta kwana biyu tukkuna yaga yanayin jikin nata sannan sai ya basu sallama....Abu ta zauna tare da ita Jatau da Munkaila Sadam! suka nufi gida.
Duk abunda Uba yake dansa Sadam ya siyawa 'yarsa akwati guda ya cika da kayan baby ya siyawa Harira turamen atampopi uku da mayafi da takalmi dama ta tanadi manya manyan ragunansa guda biyu........Misalin karfe shida na yamma ya shiga gidan Jatau din lokacin Hansatu ta kammala abinci bayan sun gaisa ya dauki kwanukan abinci ya nufi asibitin dasu dama tuntuni Jatau da Munkaila sun rigashi yin gaba dalili shi ya tsaya 'karasa sauran siye siyensa da baiyi ba.....Yana cikin babur din a dai-dai mta sahu ya kira wayar Sayyada ta dinga ringing ba'a daga ba, ya kira ya kai sau biyar bata dauka ba ransa ya 'baci sosai ya mayar da wayarsa aljihu yana shan toka wato dai idan zaka shekara baka ga mutum ba to duk sanda ka ganshi to ka tambayi halinsa.....Ransa a 'bace ya isa asibitin.....
*LNI DA YAYA SADAM
*BINTA UMAR ABBALE*
44
Yanayin yanda yaga Harira da babynsa cikin 'koshin lafiya sai hankalinsa ya kwanta sosai ya zauna kusa da ita yana tambayarta yanayin jikinta tace"Da sauki sai dai ciwon kai da takeji kadan kadan amma dr ya bata magani dazu." Yace."Insha Allah zai daina miki ciwo." Ya karbi yarinyar yana dubata Harira kallonsa kawai take sai taga kamar bashi ba kamar ya sake wata nutsuwa akan a tada kuma ba irin wannan mu'amular take dashi ba taga sai wani d'ari-d'ari yake da ita baya so su had'a ido.....Ta'bangaran sa kuma sam baya son kwallon yarinyar gani yake tamkar ya kwareta ya haike mata tana 'kankanuwa kamar haka shiyasa yake jin nauyin had'a ido da ita......Sama sama suke hira da ita dashi nan ya gane yarinyar nada sanyi da saukin hali ba kamar Sayyada ba masifaffiya tabbas akwai yiwur zaman lafiya a tsakaninsu tunda dai Allah ya sa'ba halaye ta bangaran ita Haririn....Abunda yake ayyanawa kenan a cikin ranshi.
Lokacin da ya kira wayar Sayyada tana bandaki Sai aunty Rabi a dakin ita kuma ka'ida bata d'aga wayar mutum mutukar baya gurin shiyasa wayar tayi ta ringing ba'a dauka ba.
Koda ta fito taga kira da sabuwar numbar sai jikinta ya bata ko shine da kamar tabi numbar sai kuma ta fasa ta cigaba da saurare ko zai kirata,
Sai kusan tara na dare ya fito daga cikin asibitin ya tsaya bakin asibitin yasa kati ya sake neman numbarta
Hira suke dukaninsu na zaune a tsakar gida Saliha Harun da kuma Isa aunty Rabi'a tuni tayi baccinta sune dama suke zama duk dare suna hirar abunda ya shafi harkar karatunsu.....Ringing din wayarta ya katse mata maganar da take numbar dazu ce ta dauka a hankali tayi sallama, ya sauke ajiyar zuciya a hankali yace."Kina ina d'azu nayi ta kira baki dauka ba."? Tace."Lokacin ina bandaki ne."
"Okey ganin nan kan hanya sai ki bani kwatanccen gidan idan na shigo layin." Tace"Yaya Sadam ka bari sai gobe mana yanzu dare yayi." Yace."Yanzu nake so nazo ko akwai laifi ne."?
Girgiza kai tayi tana mamakin sauran hasala irin nasa tace"Idan ka shigo layin sosai akwai wani inji na wuta dai-dai nan zaka sauka sai ka kirani a waya."
Yace."Okey ganinan kan hanya." tace"To." kashe wayar yayi.......Saliha tace"wai waye zaizo ko dai kinyi sabon saurayi ne."? Harun yace"Ai Sayyada kamar kifin rijiya haka take ta'ki bawa mutane fuska wallahi koni ta 'bangarena akwai masu sonta ganin babu fuska yasa nace suje su tunkareta da kansu." Isa yayi dariya yace."Kwarjini takewa maza amma bandani." Sayyada dai murmushi take tana fadin"Ku dai wallahi kun fiye shirme, wannan da yayana ne zai zo yaga inda nake zaune." Saliha tace"Kina nufin har ya fito daga asibitin."? tace"dazu fa nace miki shine ma ya samar min abun hawa ai magani kawai aka bashi ba wani abun ba."
Saliha tace"Hakane fa.....Suna zaune suna hira Sayyada dai jinsu take domin gabanta ne yake faduwa Allah yasa kar yazo mata da wata maganar da zata daga mata hankali.
Ringing din wayar ya katse mata tunaninta tana daga wa yace."Gani a gurin."Tace."To." Kashe wayar yayi ya tsaya rukunin company dake gurun yana nazarinsu, yana kuma dakon zuwanta gurun.
Sayyada ta zura hijab dinta har 'kasa ta kalli Harun tace"Wallahi tsoro nakeji in ba dole ba me zai sanya ni futa cikin daranan ga unguwar tsit! sai uban karnukan tsiya don Allah zo ka rakani." Harun ya mike Isa ma yace."Muje nima." Saliha tace"Kuje ku dawo ni inan."
Fita sukayi tare suna tafiya suna hira sun sanyata a tsakiyarsu......Tun daga nesa yake hangosu dake gurun akwai wadatar haske sosai albarkacin kamfaninka dake gurin......sai da suka iso daf dashi sannan idanunsa suka gazgazata masa abunda yake zargi, Yayi kici kici da fuskarsa wanda itama na ganin yanayinsa sai tasha jinin jikinta....Suna isa su Harun suka bashi hannu ya karba sukayi musabah, kana tace"Ya Sadam! muje kaga gidan." Yaji tamkar ya maketa a gurin! wad'annan 'kartin mazan da take tare da ita su waye.? amma bai ce mata komai ba yace."Muje." suka fara tafiya yana binsu a baya a hankali ta tsaya su Harun sukayi gaba ita kuma ta dawo gefansa suna tafiya.
"Wad'annan 'kartin dake tare dake fa."!? Taji muryarsa na fad'ar wannan maganar......." Tare muka zo dasu ai." tafada cikin sanyi.....da gefan ido ya kalleta yace."Kina nufin kice min tare kuke kwana gida daya dasu."!?
Sai gabanta ya fad'i! tasan halinsa da ba'kin kishi gami sa mugun zargi shiru tayi tana addua cikin ranta.
A dakile yace."Kin saba nayi mika magana kiyi min shiru ko."? Tace"Ba haka bane ni ai ban san abunda zance maka ba."
Yace."Kawai kice "Eh ko A'a shikkenan." Ta saki ajiyar zuciya a hankali tace"E tare muke dasu a cikin gidan sai dai su suna kwanane a stroom dake gidan."
Yace."Lallai ashe kin zama bayahudiya kina kwana da 'kartin maza a gida d'aya bayan kin san kina da aure hakane ko ba haka ba."!?
Shiru tayi masa ranta ya soma 'baci! da irin maganganun da yake ya'ba mata amma sai ta daure tace"Kasan fa harkar karatu yanda yake ai ba laifina bane nima kuma bani kad'aice matar aure ba shugabar tafiyarmu ma da aurenta.
Yace."Ai wannan dalilin ne ya sanya nace ni ba zakiyi karatu da aurena akanki ba dalili ni mutum ne me kishin tsiya mussaman kan abunda nake so wato ni ina can hankalina na wani guri ana shiga hakkina ko."? Tayi shiru tana tafiya zugwi zugwi yace."Tom muje inga yanayin gidan idan be yi min ba zamuje can gidana tare magana ta kare."
Wani irin kallo tayi masa lallaima ai wallahi babu inda zata bishi ai wannan bayi bane kawai ya ganta tare da abokanan tafiyarta rana tsaka yace wani abu wai gidansa ita bata fatan shiga gidan da yayi rayuwar aure da wata ba ita ba.
Koda Sadam! ya shiga gidan sai su Harun suka sake ganinsa a take su gane fuskarta Isa yace"Idan ba idona ke yi min gizo ba sai nace kamar "Yallabai Sadam! Sojan da ya 'bace shekara d'aya da rabi ana nemansa da sanin wanda yaga abun da ya dangance shi " Harun yace."Wallahi nima tun dazu idona keyi min gizo."
Sadam! Yace."Nine ba gizo idonka ke maka ba." Aunt Rabi dake daki ta fito da sauri domin shigowarsu gidan tasa ta farka daga baccin daya dauketa aikuwa itama idonta yayi mata tozali dashi a tsaye......."Sayyada a'ina kika samo wannan mutumin ko shine yayan naki da kike maganarsa." Aubty Rabi ke wannan maganar.
Tace"Eh Aunty Shine." Haruna yaje ya rike hannun Sadam yana dariyar farin ciki yake fadin "Yallabai ashe kana raye a duniya dukaninmu masoyanka munyi tunanin ka dade da mutuwa hakika munji bakin ciki da rashinka munyi kuka sosai ashe kana raye gaskiya munyi farin ciki da bayyanuwar ka Allah ya sake tsare mana kai a duk inda zaka shiga Allah kuma ya baka rinjaye akan abokanan gabarka." Sadam! ya amsa da "Ameen Ya rabbi ina godiya kwarai da gaske......Aunty Rabi tace" Ka zauna mana ko ruwa kasha Sayyada ki dauko masa ruwansha kin barshi a tsaye." Duk sun rasa ina zasu sanya kansu ganinsa hakika ransu ba karamin dadi yayi musu ba sunaji kamar suna da wata ala'ka a tsakaninsu dashi kasancewarsa dan uwan Sayyada ya sanya suke jin kamar suma sun hada wata ala'ka dashi.
Babu yabo babu fallasa yace."Alhamdulahi ba sai nasha ruwa ba nagode da kokari." Ya kalli Sayyada yace."Ki dauko jakar kayanki mu wuce."
Tayi saurin kallonsa tana kallon Aunty Rabi'a......"Kamar yaya." Tafada tana kallonshi shi kuma ya kalli Aunty Rabi'a yace."Watakila nasan ke in Kikayi mata magana za tafi ji, a matsayina na mijinta na umarce tayi abu ta tsaya gardama wanda dama halinta ne ina ganin a matsayinki na mace mai ilimi da sanin ya kamata zaki san hukuncin macen dake bujerewa umarnin mijinta."
Duk sai sukayi shiru suna kallon Sayyada da mamaki! ita kuma sai ta sunkuyar da kai duk ta rasa ya zatayi.
Yace."Naga kun shiga mamaki shin ko bata fad'a muku matsayina a gurinta ba Matata ce kuma 'kanwata auran zumunci iyayenmu sukayi mana."
Aunty Rabi tace"Wallahi ko da wasa Sayyada bata ta'ba fad'a mana tana da aure ba ballanta musan cewa kaina mijinta, a gaskiya Sayyada baki kyauta ba na sannan kuma ba haka ake zaman amana ba meye a ciki dan kin fada kina da aure Nima ina da aure kuma ai bake kadai ke da aure cikin makaranta Saliha ma ta kusa auren nan to meye abun 'boyewa.....Saliha tace"Shiyasa mana kullum take lullube da hijab har'kasa aini banga laifinki ba Sayyada." Sadam! na tsaye yana jinsu.
Aunty Rabi tace"Ai sai kibi mijinki gobe idan kinga babu hali kiyi zamanki ba sai kin fito tunda dama sauranmu 'yan kwanaki mu koma gida."
Baki na rawa tace"A'a aunty kin manta kuma gobe zamu gabatar da shirin matasanmu a yau gaskiya zan fito." Tace"To shikkenan yanzu dai kibi mijinki sao goben idan Allah ya kaimu."
Saliha ta shiga dakin da sauri tana fad'in bari na dauko miki kayan da zakiyi amfani dashi gobe." Sayyada dai shiru tayi ranta duk yayi ba'ki'kirin kawai saboda iko daga ganinta sai ya hau wani abu itafa wannan halin nasa shike had'ata dashi.
Fita yayi waje bayan yayi musu sallama Harun da Isa suka bishi suna ta bashi labarin abubuwan da suka faru a Kaduna bayan barinsa garin yayi ta mamakin yanda al'amura suka lalace yace"Insha Allah al'amura zasu gyaru mutukar na dawo komai zai dai-daita amma kuma sai mun samu hadin kan mutanan gari." Sukace Insha Allahu suma zasuyi iya bakin kokarinsu......Ta fito hannunta rike da leda viva sai kace wata 'yar tallah.....Sadam! yayi sallama dasu Harun suka kama hanya suka wuce tafiya suke babu wanda yace uffan a cikinsu