Showing 75001 words to 78000 words out of 142497 words

Chapter 26 - NI DA YAYA SADAM Complete Document by Binta Umar Abbale.txt

09 Dec 2024

50490

na lura bakwa jituwa da mijinki amma dai bari mu gama magana dashi a waya sai naji me ya hadaku."


Lubabatu ta daga wayar suka gaisa da juna tace"Kana ta kiran waya sai kace wanda yayi ajiya a gidan ko ka manta wani abun ne."?
Tana sane tayi masa maganar ta dauka zaice Sayyada ya manta sai taji yace."To ina ruwanki don na kira wayar mamana ina so naji muryarta ne kuma naji lafiyarta."


Tace."Ko dai kana so kaji lafiyar matarka shine kake wani 'boyewa kawai kace kana son magana da Sayyada.


Yace."Wacece Sayyada kuma a wane gari take."!? Aunty Luba ta bude baki kamar yana gabanta tace"Lallai ma Sadam baka da kirki Matar taka guda.


Yasa dariya tare da fad'in"To ai mantawa nayi don na tambaya kuma sai ya zama laifi."


Tace"Ba zai ma laifi ba Soja Mammah dai na daki shiyasa kaji bata dauki wayar ba nan nida Sayyada ne bari na bata wayar."


"No ki bari kawai zan kira anjima." Sai ya kashe wayarsa ya barta da waya a hannu.


Sayyada ta goge gunti hawayen fuskarta tace"Aunty Luba kinga rashin mutuncin da Ya Sadam ke min ko? saboda kawai nace ina so in cigaba da karatu Abbah ya amince shine yake jin haushina, wayar da Yaya Sulaiman ya siya mana ya kwace yau kwana hudu kenan.


Aunty Luba tace"Gaskiya Sadam! bai kyauta ba ai ba'a haka kuma ni banga laifinki ba don kice kina son ki cigaba da karatu, kawai dai don yayiwa abun mummunar fahinta ne amma kiyi hakuri insha Allah komai zai dai-dai ta fushi yake idan ya gama dole zai dawo yana neman shiri."


Sayyada tace"Lallai aunty Luba kamar baki san waye Sadam! ba gurin zuciya Ai ni nasan ba zaizo yana bani hakuri ba shifa komai nasa shine dai-dai yanzu ma dan Abbah yasa baki ne da tuni ya tafi dani bracck din su."


Aunty Luba tace"Kinga kuma ni inda nice ke yarda zanyi Mu tafi tare domin in kula dashi da bukatunsa gaskiya an shiga hakkinsa da yawa karfa ki manta da cewar ke amaryace kina kan lokacin ki ne."


Sayyada tayi shiru tana naxarin maganar aunty Luba gaskiya kuma da wannan don itama kwanaki ukun da tayi tayi sune cikin kad'aici da damuwa ta riga ta saba kwanciya a jikinta kuma kafin suyi bacci sai sunyi rungume rungume da tsote-tsotsensu kad'aici da sha'awa sune kawai suke damunta.


Sadam! Na sane ya'ki sauraran Sayyada duk dan ya nuna mata 'bacin ransa yasa yake shareta amma kullum da sha'awarta yake kwana yake tashi aiki yanayinsa ne da tunaninta duk daran duniya cikin mafarkinta yake gashi har ya rabata da budurcinta akwai ranar da yayi mafarki gashi Sayyada ta haifar masa yaro mai kama dashi sak! Ranar yini yayi a kwance yana tunini ko yaje can family hause nasu ne ya lalla'ba ya kusance in da rabo sai ta haifar masa wannan yaro ....Sashe na zuciyarsa yace."Ka saurara tukkuna ka dauke kanka daga kan yarinyar ka bari har sai tasan muhimancinka tukkuna.


****


Yau ta kama Asabar ranar hutu ga ma'aikata Sayyada ta tashi da farin ciki da walwala yau suna sanya ran ganin Sadam yazo week end gida domin haka yace duk ranakun asabar da lahadi zaizo ya kwana biyu sai ya koma Sayyada tun safe tayi kwalliya cikin wani swiss baki da ratsin ja les din yayi mata kyau sosai ta gyara gashin ta ya sauka bayanta yari da sar'ka pashon ta sanya ta fesa turare mai dadin kamshi a jikinta ta fito palo ta zauna nan aunty Luba ta dinga tsokanrta Wai taci kwalliya tana jiran Sadam! to zata gaji da jira don ya kirata a waya ba yace ba zai zo ba. Sayyada dai dariya takeyi ba tace komai ba Mammah na jinsu tana musu dariya......To har kusan karfe biyar na yamma babu labarin Sadam babu dalilinsa Sayyada tayi kamar ta fashe da kuka saboda ba'kin ciki Hajiya Fatsima sai fad'a takeyi tace"Aunty Luba ta kirashi a waya taji shin zai zo ko ba zai zo ba.....aikuwa ana kiranshi ya tabbatar musu da cewar bai zuwa gabad'aya mana sai wani satin.....Sayyada taji wani dunkulelen abu ya tokare mata a kirji mikewa tayi ta shige daki ta fada kan bed tana kukan bakin ciki.
NI DA YAYA SADAM


NA
BINTA UMAR ABBALE


32


A hankali Aunty Lubabatu ta tura 'kofar d'akin ta shiga, Sayyada ta mike zaune da sauri ta hau goge hawayen fuskarta aunty Luba ta zauna tana fuskantarta a nutse tace."Sayyada d'aki kika shigo kina kuka."!? Sayyada ta hau ya'ke tana girgiza kai. Aunty Luba tayi murmushi tace"Nifa Sayyada tun farko laifinki na gani wallahi kan me yasa za'ki nunawa su Abbah ke cewar ba zaki bi mijinki ba? kika san dalilin da ya sanya yace zai tafi dake gurun aikin su ko babu komai shi namiji ne dole akwai bukatar mace a tare dashi mai zai sanya ki tauye masa hakki dole kema hakkinsa ya kamaki tunda gashinan naga kin kasa sukuni sai damuwa kikeyi kina kuka ni dai shawarar da zan baki shine idan yazi hutu wani satin ki lalla'ba ki bishi kawai ." Ta dago kanta da sauri tana kallon aunty Luba tace''Aunty makarantar fa kinga Ya Sulaiman har yaje can *Dabi* ya kar'bo takarduna ya gama komin komai zan fara zuwa."


Aunty Luba tace"Ina ganin tunda Abbah ya sanya baki kan karatunki to ko kin koma bariki da zama zaki cigaba da zuwa ai zafi biyu kuka had'awa Sadam! ni dan yayi fushi bai bani haushi ba kin'ki binsa gashi kuma kin had'ashi da Abbah ya amincewa bukatarki a sanda bai shirya ba kinga kuwa dole yayi fushi dake." Sayyada tayi shiru tana nazarin maganar aunty Luba gaskiya hakane dole Sadam yaji haushi abinda tayi to yanzu meye shawara gaskiya tana son mijinta kuma tana kewarsa tana sha'awar jin d'umin jikinsa kuma tana son makarantar ta shin wane zata dauka a ciki miji ko karatu......Sulaiman ne ya shigo d'akin Aunty Luba ta amsa sallamarsa tana masa barka da zuwa Sule mai ido a tsakar ka ya dinga binta da kallon sha'awa Aunty Luba tayi bul-bul da ita tayi cika irin ta masu jego fatarta tayi luwai sosai yaji sha'awar matarshi ta kamashi....Kusa da ita ya zauna jikinsu na goggaya Sayyada ta dauke kanta tana gaisheshi ya amsa yace."Wace shawara Dukeyi ne kuka kulle daki." Aunty Luba tace."Muna magana ne kan rashin zuwan Sadam a wannan satin Sayyada ta damu shine nake rarrashinta nace kawai wani satin idan yazo ta hakura ta bishi." Sulaiman ya watsa mata harara yace."Ke kin san illah zaman wannan gurun kuwa.? Luba tace"Na sani to amma su sauran matan dake zaune a gurun meye ya kamasu." Yace."Sayyada ba zataje bariki ta zauna ba, suma wad'anda suke zaune a cikin bariki mafi yawancinsu ba 'yan gari bane suke dauko iyalinsu su zauna ita kuwa tana damu a kusa mai zai sanya taje ta zauna cikin kafurai shi Sadam! din shine zai dinga zuwa mata duk sati shine magana.


Aunty Luba tace."Sai nake ganin kamar an shiga hakkin Soja wallahi mutum da matarshi amma ku hana ya dauka....Sulaiman yace."Nima ai kin shiga hakkina zaman me kike a nan tunda dai kinji sauki ba sai ki koma dakinki ba." Tace"Ka cire wannan magana ni ai haihuwa nayi kuma ka'ida sai nayi kwana arba'in sannan shi kuwq Sadam fa amarya guda aka dauke masa an shiga hakkinsa da yawa." Yace."Rabu dashi idan ya damu da ita zaizo ai ke Sayyada kar ki wani daga hankalinki na riga na gama miki komai insha Allah sati mai zuwa zaki fara zuwa poly technical sai ki za'bi abinda kike so ki karanta." Sayyada tace."Nagode sosai Ya Sulaiman."Yace."Karki damu dama na fada miki zan tsaya miki kiyi karatu ke dai ki rike al'kawarin da kika daukar min." Tace."To Ya Sulaiman." Mikewa tayi ta fita daga dakin....Sule na ganin Sayyada ta fita sai ya rungumo Luba yana tatta'bata aikuwa ta tureshi tana hararasa tace"Kai da baka san haihuwa ina kai ina wannan harkar ai sai dai kaga anayi." Ta kama hanya tayi ficewarta ya bita da kallo cikin tsantsar sha'awa lallai in dai sai ya haihu sannan zata bari ya ta'ba jikinta to kuwa sai dai ya hakura domin shi kam baya bukatar haihuwa a karkusa yafi so ya tsikari duniyarsa da tsinke yaci zamaninsa sosai in yaso idan ma zai haihu sai ya haihu.


*****


To haka rayuwa tayi ta tafiya Sayyada ta soma zuwa makaranta wanda Sulaiman yake sintirin kaita ya kuma daukota sosai Sayyada taga bambancin waye wa da mutanan *Dabi* da *Kaduna* 'Yan mata masu aji da gayu dasu ta dinga karo magana d'aya sai an sanyo mata turanci shiru takeyi idan bata fahinta ba wata maganar kuma idan ta gane abunda take nufi sai ta bada amsa Sayyada tana karantar aikin jarida domin shine burinta taji ta gidan redio tana labarai ko kuma taga ana nunata a tv tana labarai wannan bangaran na mutukar burgeta.....To ganin yanayi Daliban makarantar da wayewarsu ya sanya itama ta mayar da hankalinta gurin ganin ta cimma burinta karatu sati guda da fara zuwanta makaranta ta soma sauyawa hankali da nutsuwa ya soma zuwa jikinta Ta had'u da wata Saliha wacce jininsu yazo daya da ita tare suke zama guri guda suyi karatunsu haduwarta Saliha yasa tasan abubuwa da yawa domin dai Saliha irin matanan ne masu sauki kai bata da mugunta tana koyawa Sayyada abubuwa da dama.......To ammafa Saliha bata ta'ba sanin Sayyada nada aure ba itama Sayyadar bata ta'ba fad'a mata ba, ita kuma Salihar kullum cikin hirar saurayinta take Abdul wanda saura wata hudu kacal a daura musu aure dashi dan wataran ma shine yake zuwa daukarta daga makaranta.


***


Yau kimanin sati shida kenan da tafiyar Sadam! ko da wasa bai tako kafarshi gidan ba Mammah har ta gaji da fad'a ta hakura idan ya kira waya ma sai taki dauka ta kyaleshi sai dai ya turo test messengers wannan ma bata dubawa Sayyada ce mai lalube wayar tayi ta karanta test dinshi cikin dukanin test din da yake aikowa Maman nashi bata ta'ba cin karo da wanda ya ambaci sunanta ba idan ba'kin ciki ya ciyo ta sai ta kulle kanta a d'aki taci kuka ta koshi ga aunty Lubabatu me d'ebe mata kewa ta koma d'akinta sai ita kad'ai da Mammah don mai akinsu idan ta gama komai tafiya takeyi......Sayyada sai ta fara rama a tsaitsaye saboda tunanin Sadam! din da kewarsa ya soma ta'ba lafiyarta.


Mammah dai duk tana hankalce da ita tagaji da wannan abu dole ta sammu Abbansu ta shaida masa halin da ake ciki saboda kada yarinyar mutane ta shiga cikin wani hali......Alhaji Awal na dawowa daga kasuwa bayan yaci abinci Mammah ta shaida masa cewar tun fa tafiyar sadam din yau tsawon sati shida bai zo ba gashi matarshi na kokarin shiga wani hali.


Alhaji Auwal ya cika da mamaki yace."Sati uku da suka wuce yazo har kasuwa ya shaida min da cewar zasuyi tafiya zuwa Maiduguri domin binkice kuma zasu dauki kimanin sati guda basu dawo ba duk a tunani na ya shaida muku kamar yanda ya shaida min da tafiyar."


Mammah tace",Aini fushi nayi na daina daukar wayarsa test din sa ma idan ya turo bana karantawa amma bari na duba wayar nagani......Aikuwa tana duba wayar taga test dinshi inda yake shaida mata cewar tayi masa addua suna maiduguri binkicen wani kauye abun mamaki sai taga an bashi amsa da cewar "To Yarona Allah ya tsare min kai a duk inda kake ya tsare gabanka da bayanka ya kuma dawo da kai lafiya." Mammah jikinta yayi sanyi tasan ba kowa ne zai bashi wannan amsar ba sai Sayyada a take taji kaunar yarinyar ta sake shiga ranta babu shakka Sayyada na kaunar yaronta tana masa so na fisabililahi......Sai ta daga waya ta fara kiransa Sai dai kash!!! inda yake sam! babu network kiran duniya wayar na katsewa dole ta hakura ta bari sai anjima sai ta kara gwada kiransa


Har dare Mammah na aikin abu d'aya wayar Sadam ta'ki shiga, Mammah hankalinta ya tashi sai ta soma 'kananun hawaye a fakaice takeyi tans gogewa yanzu hankalinta duk ya koma kan d'an nata ko cikin wane haki yake oho!


Sayyada kam ai tafi Mammah shiga damuwa motsi kadai kwalla zata ciko idonta ta goge sam bata so kowa ya gani......Cikin wannan yanayi Sule ya shigo ya samesu nan Mahaifiyar tasu ke shaida masa halin da ake ciki, Sam! bai wani nuna damuwarsa kan lamarin ba yace."Don Allah ku kwantar da hankalinku Sadam! dai ba yaro bane kuma hausawa nacewa lafiya itake 'buya yanzu idan da wani abu ya faru dasu to da tuni an sanar da cewar sojojin da aka tura binkice garin Maiduguri sun samu matsala sunan lafiya haka yanayin aikinsu yake."


Wannan magana da Sule yayi ita ta sanya Hajiya Fatsima ta dan samu nutsuwa ita kuwa Sayyada ganin yanda ya nuna halin ko in kula da al'amarin sai ya bata haushi ta dinga ji kamar ta kamashi da duka dan ba'kin ciki.


Misalin karfe d'aya na dare Sayyada ta lalla'bo ta fito daga d'akinta kai tsaye d'akin Mammah ta nufa a lokacin ita kuma tana tare da mijinta......Waya ta dauka tayi saurin barin dakin.


A hankali ta zauna gefan gadon jikinta sai kyarma! take ta lalubo numbar Sadam! din ta fara kira cikin ikon Allah wayar ta shiga sai dai har tagaji da ringin ta katse bai dauka ba hawaye suka wanke mata fuska ta sake kira nan ma bai dauka ba sai ta fashe da kuka sosai hannu na kyarma! ta tura masa test kamar haka.


_Don Allah ka daga wayar ka muji lafiyarka Mahaifiyarka na cikin damuwa yini guda ana kiran wayarka ta'ki shiga_


Test din ya tafi ta rungume wayar a kirjinta tana ji kamar shi ta rungume.....motsi kad'an zata zabura ta duba wayar ta gani ko ya maido amsa shiru babu labari ta sake daga wayar tana kara kira......Da ta fara shiga sai ta katse haka ta dinga yi sai kace wata mahaukaciya sai surutai take ita kad'ai.


Sadam! kam suna can 'karkashin boda suna fafatawa da mutanan wasu 'yan fashi! ne da suke da mafaka a gurin duk tsawon kwanakinsu a gurun basu ga goda gilmawar mutum ba kamar sun san da cewar sojoji sun kawo farmaki gurin shegu sun 'ki zuwa shiru gurun bakaji sautin komai sai na kukan tsintsaye rashin network din gurin ya tsananta don duk uban test messeges din da aka tura masa ko guda bai shigo ba......Shima duk sanda zaiyi kira sai yayi muguwar tafiya mai tsayi ya samu wani guri da suke da tabbacin nada service suke sannan yake samun damar tura test ko kuma ya kira waya.


Wannan rayuwar sukeyi ta rashin dadi a gurin abinci suke dafawa da kansu dad'inta guda sun tafi da ruwan sha irin na roba da sauran abubuwan bukata da yawa daga cikinsu har sun soma sarewa da al'amarin sun fara shawarar komawa gida saboda tsawon sati guda babu wani cigaba da suka samu......Sadam! shine ya nuna rashin amincewarsa kan dole su zauna su cigaba da aiki dama ai sati biyu aka basu kafin zuwan lokacin suna saka ran bukatarsu zata biya.


Captain Saleh ransa ya 'baci da wannan hukuncin da Sadam ya yanke sanin da yayi cewar shine ke jan ragamar tafiyar ya sanya kawai ya kyaleshi amma daga zarar yaga Sadam! din baya gurin zai tsiri gulmarsa da sauran abokansu Captain Habu ne kawai baya sanya musu baki kan magabarsu sun dunga zagin Sadam! kenan da fad'in"Shi ya fiye naci da kulafuci Allah yasa sanadiyar wannan aiki yasa ya rasa ransa tunda dai an fada masa cewa mutanan nan bada suddubaru da yawa kuma suna da kayan aikin da zasu iya ya'kar su dashi amma saboda tsabar taurin kai irin nasa ya'ki yarda su bar gurin wai shi dole sai ance masa gwani sai suka had'a bakinsu kan cewa koda Allah ya sanya Mutanan sunzo gurin zasu ingizashi ya tunkaresu daga karshe su sai su watse su barshi yayi ta ya'karsu tunda yana ganin kamar zai iya......Wannan shawarar suka yanke bayan barin Sadam! da Habu daga gurin.


Wani irin bacci tayi mai cike da mafarkai barkatai ta tashi cikin mutuwar jiki da kasala dan da kyar ma tayi wanka ta kimtsa jikinta ta fito cikin hijab kafadarta rataye da jakarta ta zauna daining suna gaisawa da Mammah lokacin Abbah ya fita.


Mammah tace"Waya ta na hannunki ko."? Sayyada tace"Jiya na dauka a dakinki na sake tranying ko zata shiga bata shiga ba."


Mammah tace"Ki sake gwadawa idan kin fita ko Allah zai sanya ta shiga. Tace."To." tea ta had'a karamin cup ta sanya madara da milo ba tare data hada da Brad ba take kurba haka Mammah tace"Ruwan tea ba zai dauke ki ba Sayyada ki hada da bread mana."


Murya na rawa tace"Mammah bana jin dadin bakina tea din ma ya isa." Tace"Kiyi hakuri ki daina sanya damuwa cikin ranki insha Allahu yana lafiya zai dawo kuma cikin nutsuwa da kwanciyar hankali." Kafin Sayyada tace Komai Sulaiman ya shigo cikin wata lafiyyyar shaddar galila sai mai'ko take ya karya hula irin ta kanawa kamshi kawai yake tashi a jikinsa Tabbas Sule na birni yana kuma tsikarar duniyarsa da tsinke kana kallonsa zaka gane bashi da damuwa fuskarsa da fara'a ya karaso inda suke sai ya gansu sunyi jugum!


Ya zauna suna gaisawa da mahaifiyar tashi Ya kalli Sayyada da idanunta suka kod'e! yaushe rabonta da sanya kwalli.


Yace."Wai meke faruwa ne naga duk kunyi jugum! sai kace kuna zaman makoki."


Hajiya Fatsima ta kalli Sulaiman din tana mamaki! Ta lura sam! bai damu da halin da d'an uwansa ke ciki ba sha'anin gabansa kawai yake yi Tace"Dole ka ganmu cikin yanayi na damuwa Sulaiman har yanzu bamu samu wayar Sadam! ba.


Sajensa ya shafa as'usel Yace."Mammah Sadam fa na nan lafiya kune kawai kuke tayar da hankalinku dama ai tuntuni na fada miki cewar aikin soja nada irin wannan tashin hankalin shi yanzu yana can hankalinsa a kwance ku ya barku da tashin hankali......Kuma ni jiya na kirashi a waya ai yace."Duk ku kwantar da hankalinku yana cikin koshin lafiya kuma ku sanya ran dawowarsa a cikin satin nan."


Sayyada tayi saurin fad'in"Yaya Sulaiman don Allah da gaske kunyi magana dashi a waya."? Ya bata fuska tare da fad'in"Ashe ina

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login