Showing 138001 words to 141000 words out of 142497 words
Chapter 47 - NI DA YAYA SADAM Complete Document by Binta Umar Abbale.txt
dawo sallahar asubahi ya tura kofar dakin nata ya shiga ya tarar da ita zaune kan dadduma tana lazimi......Zuwa yayi ya kwanta kan bed din yana lumshe ido har yaji wata sa'ida saboda ganinta.....Tana idar da laziminta ta bar masa dakin.
Kicin ta nufa ta fara hada musu break fast ya shigo kicin din yana tattaba ta kamar yanda ya saba tureshi take tana zumbura baki taki cewa dashi komai sai sambatun surutu yake yi da babynsa...."Momy na fushi dani ka tayani na bata hakuri kaji ko........Fushi take dani ni kuma bana so ina shiga damuwa jiya har rufe mun kofa tayi." Sai kace da babban mutum yake magana yanayi yana zura hannunsa karkashin rigarta yana shafo cikin
Ji tayi kamar yana mata tafiyar tsutsa a jikinta a kumbure tace"Ka bari bana so." Ya dora ha'barshi kan kafadarta dai-dai kunnanta yace"Babu gaisuwa sai tsiwa ko ni dai nace ayi hakuri jiya ni kadai nasan irin wuyar dana sha ina neman alfarma yau kar a rufe min kofa."
Shiru tayi masa tana aikinta yana taya ta ganin ba tace masa komai ba kuma fuskarta ta saki sai ya saki jikinsa sosai yaji dadi da ta sauko.
Tsaf ta shirya masa dainnig ta shige daki abunta wanka take ya shigo dakin kawai sai ya fada toilet din tayi kici kici da fuska ya dinga ya'ke yana so ya janye mata hankali ta hanashi dole sai ta nuna masa matsayinta sannan ita ba 'karamar mace bace da zai dinga fadawa magana daban daban.
Ta rigashi ta fitowa ta shirya cikin pakisatan tana gyara dogon gashinta ya fito daure da towel isa yayi inda take yana gogar jikinta....
Ta shareshi ya karaci neman maganarsa yayi shirin aiki.....Ko gurin brek fast din ma bata sakar masa fuska ba duk ya damu sai nan nan yake da ita kamar ma kar ya futa gurin aiki sai dai yaga babu haza ya kama hanya ya futa amma kuma yini yayi kiran waya karfe shida shaura kuwa ya dawao gidan
Mamaki tayi amma bata nuna masa ba yayi kwance a duguwar kujera yana kallon shige da ficenta daga daki zuwa kicin....knocking akayi yace."Waye." daga can waje Saliha tace"Nice."jin muryar mace tasa ya kwala mata kira ta fito tana goge hannunta a kasalance yace."kinyi bakuwa." kofar ta nufa ta bude Saliha ta shigo tana dariya da fadin"Uwar biyu ganin sadam din zaune a palo sai ta nutsu suka gaisa dashi shi ya amsa a sake yana san kawance su da saliha saboda ya fahimci yarinyar ta san abunda takeyi.....Mikewa yayi ya futa ya barsu.
Goron bikinta Ta kawo mata Sayyada tace"Lallai Saliha ashe abu ya matso duk haduwar da muke baki fada ba." Saliha tace"Ashe babu dadi kenan ke meye bakiyi mana ba sai nice mara sirri." Dariya kawai tayi tace"Amma banso ba bikinki ya had'e dana Amina Ranar litinin zamu tafi *Dabi* Saliha tace"Aikuwa dai sai ki ajiye na Amina ki dauki nawa kin sandai irin zumuncin dake tsakanina dake." Sayyada tace"Na sani zan duba yanda za'ayi amma ko wane bangare ya shafeni."
Hira suka shigayi ta makaranta da kuma yanayin yanda karatun nasu ke tafiya gangara.....Saliha tayi sallah magariba sayyada ta kawo mata abinci taci ta koshi sannan sukayi sallama da juna.
Yana zaune saman motarshi da waya a hannunsa sai tafka rigima suke da Halima Saliha ta fito tayi masa sallama Sadam mutum ne mai kyauta ya dauko kudi ya bata kimanin dubu biyar godiya tayi ta wuce ta tafi.
Yana shiga palon kiran Halima ya sake shigowa wayarsa ya cije bakinsa cikin tsantsar bacin rai ashe Halima ba taji waning din da yayi mata ba ashe shi kam bai taba ganin mace mara zuciya ba kamarta gashi kiri kiri ta janyo masa rashin zaman lafiya a gidansa.
Sayyada ta kalleshi ganin yanda duk ya wani daburce tace"To meye na wani daburcewa kawai ka amsa wayarka menene."
Cike da kokarin bagararwa yace"Wai ke daga kinga an kirani a waya sai ki tsargu abokina ne fa.
Tace"To idan ba tsoro ba ka amsa wayar mana." Yace"Bani da lokacinsa ne." Karamin tsaki taja tana dauke kai.......Zuciyarsa ta sosu da tsakin da tayi masa ya ambaci sunanta cikin kausashiyar murya ta kalleshi da idanunta da suka soma tara kwalla......"Kar in 'kara magana kiyi min tsaki." Yafada cike da shan toka....Fashewa tayi da kuka ta mike da gudu ta nufi daki
Ya zauna kan kujera ransa a bace ya lura idan ya biye mata sai ta sanya masa ciwo gashi ta rainashi kamarsa kuma a gabansa take masa tsaki .......kyaleta yayi kawai ya futa daga sabgarta.
****
Haka suka dunga zaman doya da manja a tsakaninsu Bangaran Halima kuwa ya bude mata wuta duk sanda ta kirashi a waya ya ci ubanta ya farfada mata bakaken maganganu amma dake bata da zuciya gobe ma sai ta sake kiranshi.
Kuma yana sane yaki sanar da mahaifinsa sa'kon general din sai dai duk sanda suka hadu da general din yace."Abban baya gari amma da ya dawo zaizo.....General dai har ya soma fahintar wani abu sai kawai ya yanke shawarar kiran Alhaji Auwal din domin yaji abunda yake da akwai.
****
Haka sukaje *Dabi* bikin Amina Sayyada sai shareshi takeyi shine ma mai mata magana gaisuwa kam sai ta ga dama take gaidashi......Kai har su Baba Ladi suka so su fahimci wani abu dangane dasu sai suka bari tukkuna a gama shagalin biki mutane su watse sannan.
Allah Sarki Amina yanda taga Sayyada tayi kyau da kwarjini uwa uba ilimi da ya wadace ta sai jikinta yayi sanyi ta kara tabbatarwa da cewar duk zakaran da Allah ya nufa da chara ko ana muzuru ana shawo sai yayi ga dai Sayyada ta zama shamkiyar mace sai kace matar sarakai tayi kyau ga cikin Sadam a jikinta sai duk ta muzanta kamar ba amarya ba haka ta dinga rabe rabe karshe ma gold din da Sayyada tazo dashi shi ta bata aro taci bikinta dashi ta futa kunya Baba Iya kuwa sai nan nan take da Sayyada saboda yanzu taga akwai mamora a jikinta ganin yanda take ta baiwa yara kudin siyan alawa......Ummi kawarta tayi aure inda ta auri Malam bashir 'yarsu daya ita kuma Mariya 'yayanta uku duk maza suka had'u a dakin Baba Ladidi suna hirar yaushe gamo da labarin abunda ya wuce a baya.
*Litttafin na kudi ne....!*
Kika futa
NI DA YAYA SADAM
*BINTA UMAR ABBALE*
59
Anyi bikin Amina lami lafiya an gama shi lafiya Amina ta tare a gidan mijinta dake can karamar hukumar kazaure dake mijin nata dan can ne babu laifi gidanta dakuna uku ne da kicin da bandaki sai madaidaicin tsakar gida dai-dai gwargwaro mijinta nada rufin asiri ma'aikaci ne kuma yana ta'ba harkar kasuwanci, Sadam ya bada kudi yace a siya mata abun sana'a aikuwa sai aka siya mata keken dinki da firji Baba Iya tayi ta murna a wannan zamanin a siya maka abun sana'a ai angama maka komai.
Bayan gama buki da kwanaki biyu har yanzu bata sauya zani ba tsakanin Sayyada da mutuminta yanzu abunda take masa ma yafi na baya yawa sai yayi shigowa goma bata daga kanta ta kalleshi ba wataran ma idan tana zaune tare dasu baba suna hira idan ya sako baki tashi take tabar gurin....
Abun duk ya dameshi ya tsinewa Halima yafi sau dari duk itace ta janyo masa wannan masifar......Yau suke shirye shiryen tafiya dama ba guri daya suke kwana ba ya shirya tsaf ya fito ta shiga dakin baba ladi sai ya tarar da ita kwance kan gado ko alamar shiri babu a tare da ita.
Sassauta murya yayi yace"Baki shirya bane kinaga lokaci naja bana so muyi tafiyar dare." Kamar da dutse yake magana yace"Wai ba magana nake miki bane umm!? kawai kin tsiri gaba dani ina a matsayin mijinki ke bakiga anyi auran nan ba amma duk kinbi kin daga hankalin ki kin takura min zuciya kin takura kan...."Ya Sadam! ni dai ka kyaleni kayi tafiyarka babu inda zan biki sai na haihu." Ya kalleta da bacin rai a tare dashi "Baki isa ba haihuwarki a kwai saura saboda haka kawai ki tashi ki shirya mu tafi.
Kuka tasa tana fad'in" Ni wallahi babu inda zanje kawai kayi tafiyarka bana bukatar ganinka." Baba ladidi ta shigo dakin tana fadin"Kukan me nakeji haka ke Sayyada dama ina ciki dake wallahi so nake komai ya dai-dai ta inyi miki magana ina lure dake da yanda kike zama da mijinki sakarya kawai sai ki fada mun abunda yayi miki kike gaba dashi zai shigo ya futa ki kasa gaishe shi ko shine yayi miki magana bakya kulashi......"Baba ai gashinan a tsaye a gabanki ki tambayeshi mana." Tana kuka tayi maganar Baba Ladidi tace"Ni baxan tambayeshi ba ke na tambaya saboda na lura ya fiki gaskiya." Sai kukanta ya tsananta tace"Dama ai shi kullum me gaskiya ne a gurunku ni kun tsaneni dama." Baba tace"Halinki muka tsana in banda sakarci ina ke ina gaba da miji."
Sayyada bakin cikin duniya ya isheta sai ta juya musu baya ta cigaba da kukanta..........Baba Ladi ta kalleshi a nutse tace"Wai mai ya hadaku ne na lura itace fitinanniyar mara kaunar zaman lafiya."
Hular kanshi ya cire ya dan gogo gumin fuskarshi yace"Baba ba wata fa shahararriyar magana ba ai kin san General AbdulSalamu shugabanmu na gurin aiki ko." ? Baba Ladi tace"Ni kuwa nasan wannan mutumi mutumin kirki ne yana kaunarka da kaunar cigabanka."
Sadam ya shiga fada mata abunda ke faruwa tsakaninsa da Halima kana ya fada mata abunda general din yace ya bashi Halima ya aura.
Baba Ladi tace"To ai wannan abun farin ciki ne ni a ganina kai kana nufin da Sayyada kadai zaka zauna ka tauye rayuwarka haka kurrum dan ubanta haka ta taso ta gani anayi muma mu biyu ne nida Marka hakanan ubanta Lawali matansa biyu yanzu sannan tace baza'ayi mata kishiya ba, wane irin hallaci ne mutumin nan bai maka kai kuma sai ka watsa masa kasa a ido to ni kam ina goyon bayan wannan al'amari Allah ya sa damu za'ayi."
"A'a Baba nifa ba son yarinyar nan nake ba wallahi ta dade tana sona bana so in aureta in kasa adalaci a tsakaninsu shiyasa na bata shawarar ta nemi miji tayi aure abunta.
" Oh! kajini da surkududun namiji a baka kyautar mace kace baka so saboda kawai waccan galafirin nayi maka fushi duk ka wani susuce kana sanyi jiki to maza ka tsaya kallon ruwa kwado yayi maka kafa ai na dauka tsayayyan namiji ne jarumi ta ko wane fanni a she a gida lusari ne wai har kake fadin"Kana tsoron kar kayi rashin adalci oh ni Suwaibatu." Takare maganar tata tana rike ha'ba....Baba Marka ta daga labule ta shigo dakin tana fad'in"Hayaniyar me nake ji ne."? Baba Ladi tace"Shigo ki tayani jimamin wannan lamari." Baba Marka ta shigo ta zauna nan Baba Ladidi ta shiga wassafa mata yanda al'amarin yake
Cike da mamaki! Baba Marka ta kalli Sadam tace"Aikuwa kaji kunya yarinya kankanuwa na juya akalarka har tanayi maka fushi kana bata hakuri a wannan zamanin ai kaine za kasha wuya, Haba Sadam! wane irin hallaci ne wannan mutumi baiyi maka ba shine zaka saka masa da wannan abu ka zauna kayi nazari da tunani mana......"Baba ku rabu dani da wannan magana don Allah ni ba tsarina bane idan dole sai anyi auran ma sai a daura da Sule ni ina da mata ta isheni rayuwa."
Baba Marka da Baba Ladi suka dinga salati suna juya maganar tashi da gaske dai Sadam! tsoron Sayyada yake yi.
Yace"Idan ma tsoronta nake babu ruwanku.
Sayyada ta mike zaune tana goge fuska sai galla musu harara takeyi tace"Wato saboda ku an auroku rana daya kun zauna tare shine kuke so ayiwa wata kishiya ko to ni mijina na sona komai abunku sai na zauna ni kadai iya gani iya kyalewa." Baba Ladidi ta jefa mata mafici tana fadin"Ja'ira kawai mara kunya ai banta'ba tsammanin haka kike da son kanki ba ina laifin wannan mutumin yayi muku rana kuyi masa shanya kai jama'a!!!! Tana kokarin futa a dakin tace"indai kan kishiya ne naji ina da sonkai haka kawai tazo ta takura min ina soyayya da mijina." Baba Ladi ta bude baki tana kallonta Oh! Sayyada bata da kunya wallahi.
Wanka tayi a gurguje ta fito tana jin sanyi a zuciyarta taji dadin yanda ya farfadawa su baba magana ya nuna musu auran baya gabansa ta tabbata da ya nuna musu yana so to sune zasu shige gaba har sai al'amarin ya tabbata.
Ya dinga binta da kallo kamar maye tana sanya kayanta.....A'lamarin sai ya bawa su Baba kunya simi simi suka futa daga dakin.....Aikuwa ya mike ya iske inda take ya rungumeta 'kam! a jikinsa tare suka sauke ajiyar zuciya cikin kunnanta ya rad'a mata magana" Ina fatan dai yanzu kin fahimce ni wallahi bana son Halima da ina sonta tun farko kafin ke ita zan aura itace take nacinta amma ni ba zan aureta ba." Shiru tayi masa ya dinga farfada mata kalamai masu sanyi yana kiss din wuyanta da wasu guraren na jikinta sai yawo yake da hannunsa a jikinta......."Ka bari na sa kayana." Tafada cikin sanyi ya zare jikinsa ana nata ya matsa gefe guda yana kallonta da idanunsa da suka sauya launi.....Da zata bari da ya rage zafi ko yaya ne....
Ta shirya tsaf Baba Marka ta kawo musu abun kari suka karya kana suka dauki hanyar Kaduna garin gwammana.......Sayyada bata samu damar zuwa bukin Saliha ba sai dai taje har gidanta ta yini kana ta kai mata dumuwar da tayi niyar bata.
Bayan sati daya da dawowarsu Alhaji Auwal ya kirashi a waya yana son magana dashi....Yace."Bayan ya tashi daga aiki zai zo insha Allahu.
Maganar dai da yake zargi itace ta sanya mahaifin nasa kiranshi magana ce kan Halima general ya kirashi sun tattauna maganar har sun tsayar da ranar daurin aure wattani uku masu zuwa a yanda general din yayi Abbah bayani ya nuna masa cewar tuntuni Sadam din da Halima sun riga sun gama shirya kansu shiyasa Abbahn yace to ai babu batun aje a dawo kawai su tsayar da magana hakace ta kasance kuwa suka tsaida magana a tsakaninsu.
Sadam ya rasa me zai cewa mahaifin nasa sai goge gumi yake sam baya so yayi magana shima yayi masa fassarar dasu baba ladidi sukayi masa sai kawai yace."Hakan yayi Allah ya sanya alkairi." Abbah ya amsa da "ameen." Sabida tsabar rud'anin da yake ciki ko cikin gidan bai shigaba ya shige motarsa ya tafi.
Sayyada na zaune a palo tayi kwaliyya dai-dai gwargwado cikinta ya soma fitowa yanzu amma ba sosai ba dake tana da kwankwanso da brest duk sai ya shanye anan....Ya shigo da sallama a bakinsa ta mike da sauri ta isa bakin kofar ta karbi abubuwan hannunsa tana masa sannu da zuwa kafadarta ya rungume yana amsawa suka nufi daki.......Ruwan wanka ta hada masa duk da ya hanata amma taki kullum itake hada masa ruwa yayi wanka ta kuma shirya shi ya shiga yayi wanka ya fito ya tarar da jallabiyarshi kan bed tsane jikinsa yayi ya sanya jallabiyar tare da karamin wando ta shigo dakin da sauri tana fad'in"Yau nayi yamma ban gama abinci da wuri ba wallahi." Yace."Ai kina kokari ma anyi anyi dake a dauko miki mai taimakonki kin'ki yarda.....Zumbura baki tayi tace"Bana so." Yace."To ai nima bance dole ba." Hannunsa ta rike suka fita palo ya zauna kan daddumar da suke cin abinci ta shiga kicin tana fito da abincin kala kala tana jerawa a gabanshi Yace."Wai yau har kala nawa akayi min ne? baby me yasa bakya hutawa ne."? Murmushi tayi tace"Nifa kullum so nake in faranta maka rai kullum ina 'kirkirar abunda zai sanya ka nishadi da walwala wallahi ba zan ta'ba gajiya da hidimarka ba.
Yaji ta bala'in fasa masa kai ya gyara zama a d'okance yace"Kuma wai a haka ake so nayi miki kishiya kawai tazo ta rusa min farin cikina." Kamar wawa haka ya fadi maganar.
Ta kalleshi da kyau "My luv waye yake so kayi min kishiya." kai a karye tayi maganar....Ya kuma gyara zama babu wayo yace"Yanzu daga gida nake abbah yayi kirana kan maganar Halima wai sun gama tsayar da magana shi da general nan da watanni uku zasu daura aure."
Cikin dauriya da son danne kishi tace"Kai kuma me kace musu."?
Yace."Kawai nace Allah ya sanya alkairi amma ni nasan abunda ke zuciya dangane da yarinyar wallahi ta sake aka daura auran a ranar zan saketa."
Sayyada tasa dariya tana kallonshi lallai duk girman namiji yaro ne kuma wawa ne duba dan Allah ya saki jiki sai fada mata komai yake.
*Hakane dama idan kina so kiji halin da mijinki ke ciki a lokacin da zaiyi miki kishiya sai kiyi kwance kwance ki nuna ba kya kishi, shi kuma a lokacin zai saki jiki dake ya zama kamar wawa yayi ta fada miki komai in ta kama ma ya baki kudi yace kije ki hado lefe da kanki kana kuma yayi ta sakar miki kudi yana lallabaki kinga kinci riba biyu zaita ganin girmanki itama kuma in tazo ya nuna mata muhimancinki*
Tace"Ya Sadam tunda dai har manya sun sa baki a maganar ka hakura ka aureta ni na hakura Allah ya bamu zaman lafiya."
"Nifa ko na aureta ba zan kusanceta ba dan zarginta nake kuma kin san ni mutum ne mai kishin kansa kishin ne ma ya janyo min yawan zargi.
Tace" To Allah dai ya za'ba abunda yafi alkairi." Ya amsa da amin yana duba wayarshi......"Zo kiga wani abu." Ya fada still hankalinsa na kan wayar ta matsa jikinsa sosai tana le'ka fuskar wayar.
NI DA YAYA SADAM
*BINTA UMAR ABBALE*
*60*
🔚🔚🔚
*Alhamdullilhi*
Hotunan Halima ne kala kala ta turo masa su ta whasap had'e da kalaman soyayya hotunan sun kai kala ashirin da wani abu wasu da kananun kaya wasu da kayanmu na hausawa suka dinga kallon pictures din suna dariya Yace."Yanzu ni da nake me zanyi da wannan duba fa da kyau ki gani jiki duk 'kashi babu mamora aini ko aure zanyi ba zan auri karmashashiyar mace ba kawai nazo muna kokawa da kashi." Sayyada anji daci sai dariya ake kyalkyalwa fadi take "Ya sadam ina laifin mai sonka wallahi ni dai banga makusa a jikinta ba mace 'yar gayu irin wannan." Tsaki yaja ya dinga yin deleted din pictures din yana