Showing 87001 words to 90000 words out of 142497 words

Chapter 30 - NI DA YAYA SADAM Complete Document by Binta Umar Abbale.txt

09 Dec 2024

50475

kallonsu kan Sadam! dake ta faman kallon Sulaiman din yana murmushi.....Hansatu tace"Babu shakka baku kama ko kusa ko alama kai dagani bafulatani ne shi kuma daga ni babarbare ne domin ma fatarku ba daya bace kuma baku kama suna ne yazo iri daya."


Sulaiman yace."ni nawa dan uwan kamar mu daya dashi tamkar an tsaga kara haka muke kama da juna maganar kuma kunga numbar ta a wayarshi hakan na iya faruwa mybe daga company ne don haka ni bani da wata ala'ka da wannan bawan Allah. amma kuma na dauki alkawarin zan taya ku cigiya ko Allah zai sanya a samu danginsa." Duk jikinsu yayi sanyi sosai Mussaman Munkaila dukaninsu kuma sun amince da maganganun da Sulaiman din ya fada musu cewar Sadam ba dan uwansa bane sam! basu hada wata ala'ka dashi ba.
NI DA YAYA SADAM


NA
BINTA UMAR ABBALE


37
Da jin abunda Sule ke fada sai duk jikinsu yayi sanyi suma sai suka gazgata maganar tasa ta cewar bashi da wata alaka da Sadam din kawai dai sunane yazo daya.......Sulaiman ya mike tsaye yana kad'a key din motarsa ya d'an kalli Sadam din dake zaune gim! kamar gunki sai kallonsa yake yi, Dauke kansa yayi ya mayar kansu Munkaila yace."To ni zan koma Allah ya sa damu da alkairi shi kuma wannan bawan Allah Allah ya bayyana masa danginsa."


Hansatu tace"Ai ka tsaya kaci abinci gashi a kan wuta bamu sauke ba." Yace."Nagode da karamci na barku lafiya." Takalmansa ya zura ya kama hanyar futa Munkaila ya rufa masa baya.....Sadam ya bisu da Kallo fuskarsa ta nuna alamun alhini da damuwa ya dinga kallo Sulaiman din kamar ya mike ya bishi babu tunanin haka, har sai da Sulaiman ya fice daga gidan sannan ya dauke kansa kwanciya yayi lamu kan tabarmar ya takure jikinsa idanunsa sun kada sunyi jawur!! Harira taji tausayinsa ya kamata sai ta soma kuka tana cewa ka tashi na cigaba da yi maka ta tsuniyarka." Sadam ya d'ago idanunsa yana kallonta Ta sake cewa "Ka tashi na cigaba da yi maka ta tsuniyarka." Ya bude baki a hankali ya maimaita maganar da tayi "Ka tashi na cigaba da yi maka ta tsuniyarka." Harira ta d'aga kai alamun haka take nufi sai ya mike zaune yana kallonta tayi murmushi tace"A'ina muka tsaya."? Shima murmushin yayi yace."A'ina muka tsaya."? Dafe kanta tayi tace"Kai matsala ta da kai kenan komai mutum ya fad'a kaima sai ka fad'a." Wannan magana tayi masa tsayi shiyasa bai iya maimaitawa ba sai yayi shiru yana kallonta tamkar wata hallita da ya sani a cikin kwakwalwarshi.....Harira ta cigaba da yiwa Sadam tatsuniya ta gizo da 'koki ya saki jikinsa sosai yana murmushi sai da lokacin cin abinci yayi sannan ta mike daga gurin taje ta dauko masa abinci da ruwa ta zauna gabansa ya bude ya ciko hannu zai kai bakinsa duk sai ya zuzzube a kasa....Rike hannunsa tayi tana fad'in"A hankali a hankali zaka ci dinga d'iba....Ya d'aga mata kai tamkar wanda ya fahimci abinda take nufi. Ma dai-dai ci ta d'ebo a hannunta ta kama hannunsa ta zuba masa abincin tace "Kamar haka zaka d'iba sai kasa a bakinki." Ya d'aga mata kai yana kai abincin bakinsa......Haka ya dinga d'ibar abincin kad'an-kad'an yana kaiwa bakinsa har sai da ya koshi sannan ya daina diba ta dauko masa ruwa a buta da wani 'koko ya wanke hannunsa......Sai sannan itama ta samu lokacin zama taci abincinta tana ci tana masa hira shi kuma ya 'kura mata ido yana murmushi aikinsa kenan murmushi, Wasila ce tayi sallama ta shigo gidan hannunta rike da fanteka suka gaisa dasu Hansatu tace"Harira zakije rafi jidon ruwa." Harira tace"Anya kuwa zani yau hira muke da Soja." Wasila ta kalli Sadam dake ta zabga murmushi tace"Tabd'ijam."! Harira tace."Meye wani tabdijam! akwai magana a bakinki." Wasila ta gumtse bakinta tana murnushi tace"kawai ki tashi muje mu jido ruwa malama." Hansatu ta le'ko daga daki tana fad'in"Harira tashi mana ku tafi kina ganin gidan babu ruwa ko."? Harira tace"To Baba waye zai kula da Soja shi kadai ne fa zaune a tsakar gidan." Hansatu tace"Gamu muna shige da fuce a gurun babu abunda zai same shi." Harira ta mike ta gyara d'amarar dake 'kugunta ta dauki fantekarta ta jidon ruwa suka kama hanyar fita daga gidan.


Sai da sukayi nisa sosai Wasila ta kalleta tace"Harira sai naga kamar son mahaukacin gidanku kike wallahi ki raba kanki da auran mahaukaci wanda ba'asan daga inda yake ba duk ga samarinki nan masu asali a gari ki zabi guda a cikinsu ya fiye miki."


Harira tace"Wasila ban ta'ba tunanin zakiyi min wannan maganar ba wallahi wannan bawan Allahn da kuke kira da sunan mahaukaci ba haka bane tsautsayi ne kawai ya ritsa dashi lafiyarsa lau tunda har asibitin cikin gari an kaishi kuma likita ya tabbatar da cewar 'kwa'kwalwarsa kalau take kawai ya dan samu matsala ne ta shafewar tunani amma nan da wani lokaci kadan tunaninsa zai dawo amma duk kun dauki magana kuna kiransa da mahaukaci to idan ma sonsa nakeyi ina ruwanki ni wallahi bana son gulma da kinibibi kuma karki 'kara ce masa mahaukaci." Wasila tace"Allah ya baki hakuri Harira asha soyayya lafiya." Haka suka isa rafi babu wanda ya sake kula dan uwansa Harira fushi take ankira Sadam da suna mahaukaci .


***
Kusan lokaci guda Abbah da Sulaiman suka isa gida dukaninsu a gajiye suke Abbah na zaune a palo duk sun kewaye shi yana musu karin bayani Sulaiman yayi sallama ya shigo dai-dai lokacin da Abbahn ke cewa"Duk iya kacin bakin kokarinmu munyi mun sanya anyi bunkice kana munshigar da cigiya kafofin yad'a labarai na garin al'amarin dai babu wani cigaba yanzu dai mu bar komai hannun 'yan jarida zuwa sati guda zamu koma muji halin da ake ciki amma dai in an samu cigaba dangane da al'amarin to su sanar damu ta waya domin mu san halin da ake ciki."


Baba Ladidi tace"Ni dai in dai na isa da kai to nace ka daina wannan biye biyen wannan yaron fa ya mutu to meye dole sai kun hanashi kwanciya cikin kabarinsa lafiya ku ba addua kuke masa ba komai ba amma kullum sai kun ambaci sunansa yafi sau dari da wannan kud'ad'en da kuke 'batarwa ai gwara ku gina massalaci da sunansa ladan ya isa kabarinsa wanda ya mutu baya dawowa saboda rashin tawakkali kun kasa hakura."


Alhaji Auwal ya bude baki zaiyi magana Tace"Ni dai na gama magana in dai nice na haifa to wannan abu da kake ya isa shi General din yaje yayi tayi idan ya gaji ya daina." Alhaji Auwal yace."Shikkenan Baba magana ta wuce insha Allahu.


Sulaiman yace."Wallahi nima kullum sai na fita mutukar naji wani labari da ya dangece shi zanje in duba dazu ma ina fita wani mutum ya kirani wai an tsinci gawar wani soja karkashin gadar 'yan kura dake jahar kano babu wani 'bata lokaci na dauki mota na nufi kano koda na isa gurun sai na iske ba Sadam din bane haka na dawo da rashin karfin jiki wannan al'amari sai dai kawai mu barwa Allah shine kadai yasan abunda ke da akwai."


Baba Ladidi tace"Ai ka gama magana Sule mu barwa Allah lamarin babu tsumi babu dubara dukanin abunda Ubangiji ya hukunta to shine dai-dai."


Sayyada na zaune kasan kafet a takure tunda suka fara maganar ba tace komai ba sai hawaye ne kawai yake ambaliya a fuskarta ta rasa ma wane irin tunani za tayi kawai sai ta mike ta nufi daki tana kuka , dukaninsu suka bita da kallo suna tauyasa mata tabbas dole ne tayi kuka rashin miji ba wasa bane.


*****
To kwanaki suna ta shud'awa har aka daina lissafin kwanaki aka dawo lissafin wattani yau kimanin watan Sadam! Hudu da rasuwa ta 'bangaran wad'anda suka dauka ya mutu kenan......Zuwa wannan lokacin Sayyada ta koma makaranta amma dai walwarta ta ragu kuzarinta ya ragu kai komai nata ma ya lalace shi kansa karatun sai tayi da gaske take fahinta domin shi sai da ta dawo baya sosai saboda wannan alhini da ta shiga, Kullum bata iya bacci da daddare sai ta tasa hoton Sadam a gabanta taci kuka ta koshi kana take iya bacci shima da hoton a rungume a kirjinta.....Tayi wata iriyar rama mara kyau Mammah da Abbah sunyi fada har sun gaji sun sa mata ido su kam basu ta'ba ganin mai kulafuci irin Sayyada ba, Su Baba Ladidi kuwa dama baram-baram suka rabu da juna domin Sayyada sai da ta kai ta kawo tana musu rashin kunya duk sanda zasu bud'i baki suce mijinta ya mutu to a ranar yini take tana nukufurci da kuka idan sunyi mata magana ta gaggaya musu duk maganar da tazo bakinta. Babu arziki suka tattara yanasu yanasu suka tabi inda suka fi wayo *Dabi* To sai Sayyada ta samu saukin wasu abubuwa wanda da lokacin sunanan ko tagumi suka ga tayi sai su hau kiranta mara tawakalli yanzu kuwa sai ta yini a daki babu mai cewa da ita komai don Mammah bata san takura mata ganinta take tamkar tana ganin Sadam a raye.........Sulaiman da kansa ya nufi *Dabi* bayan tafiyarsu baba da sati biyu yaje musu da uwar siyayya kamar mahaukaci yayi musu kwance kwance ya fada musu abunda ke tafe dashi kan maganar auran Sayyada nan kuma ya tabbatar musu da cewar duk tsawon watannin auran Sadam din da Sayyadar bai take ba har yanzu Sayyada a matsayin budurwa take domin Sadam din bai amshi sadakinsa ba.


Baba Ladidi ta dinga kuka tana fad'in"Gaskiya Yarinyar nan bata da imani wallahi ashe! Sayyada haka take yaron nan wani zuwa da yayi yake fad'a mana cewar bata bashi hakkinsa na aure ashe ko da suka koma can kadunar bata bashi hakkinsa ba ya tafi da kwad'ayi da bukata banta'ba ganin mara imani irin Sayyada ba amma shine saboda tsabar munafurci take damun mutane da kukan banza da wofi ai dama dole ne Allah ya jarrabeta."


Sulaiman Yace."Tabbas hakane Baba domin ni ana saura kwana bakwai Sadam ya bar garin yake shaida min abunda yake faruwa tsakaninsa da matarsa da kaina sai da naje nayi mata fad'a amma ba taji ba to har yayi wannan tafiyar ma sai da ya tabbatar min da cewar bai samu yanda yake so da ita ba wannan ya sake tabbatar min da cewar har ya mutu bai kar'bi sadakinsa ba." Sai na samu Abbah na shaida masa halin da ake ciki ya sanar da Mammah sai muka yanke shawarar kawai ta cigaba da zuwa makaranta kamar yanda ta fara to yanzu haka tana zuwa makaranta ni kuma da naga rashin dacewar zamanta a haka na yanke shawarar tunkararku da maganar auranta nasan dai dukaninku zaku bani goyon baya kan al'amarin."


Baba Marka tace"Sosai kuwa zamu baka goyan baya d'ari bisa d'ari domin wannan shawara daka yanke itace dai-dai Sayyada dole ne ta xauna da kai a madadin dan uwanka kuma dole ne tayi maka biyayyar aure tunda shine ya had'aku maganar daurin aure a tsakaninku ba za'aja wani dogon lokaci ba za'a daura don haka kana komawa gida ka sanar da mahaifin naka muna nemansa mu kuma daga nan zamu nufi gidan iyayenta wato gidan maigari kenan zamu shaida musu dukanin halin da ake ciki."


Tsabar farin ciki ya sanya Sulaiman washe baki ya dinga godiya tare da yi musu al'kawarin insha Allah wannan shekara za suje su sauke farali kasa mai tsarki,


*****


An samu mutukar cigaba ta fannin samuwar lafiyar Sadam! zuwa wannan lokacin Sadam yasan lokacin sallah idan yayi yaje yayi yasan a dadin sallah asubah da sallahr azuhur


da la'asar da magariba da isha'i ko wace sallah idan lokacinta yayi zai tashi yaje ya daura alwala mussaman lokacin sallahar asubahi kusan duk gidan shi yake tashinsu....Yana hira da mutane amma ba sosai ba kana suna zuwa gona da Munkaila suyi ciyawa da sauransu Sadam! ya saje da mutanan 'kauyen dan marke idan ka ganshi a kan jaki ba zaka dauka yasan wani abu ba sabuwar rayuwa yake yi mai dad'i da ma'ana komai a saukake babu tsawwalawa zuwa kuma wannan lokacin soyayya mai 'karfi ta kullu a tsakaninsa da Harira yana masifar sonta ta inda har rafi yake rakata d'ebo ruwa, duk 'kwayenta sun guje ta saboda kawai ta nuna musu muhimancin Sadam din a gurinta shikkenan shima da ya gane saboda dashi suka daina huld'a da ita sai ya zama me d'ebe mata kewa mutukar baije gona ba to suna tare bakin bishiya suna hirar soyayya.....Wannan sha'kuwar tasu ta sanya Jatau! farin ciki sosai yana ganin zai iya aurawa Sadam din Harira suyi zamansu lafiya ba wata matsala bace a gurinsa.


****
Ko da Alhaji Auwal yaje *Dabi* yaji abinda ke faruwa sai shima yayi farin ciki sosai yace hakan yayi dai-dai da kuma ma'ana amma a fara tuntun'bar Sayyadar sai aji ta bakinta.....Baba Ladidi tace"Babu wanda zai tsaya tuntu'bar Sayyada da wata magana domin idan an tsaya ana tambayar ta to zata dagula al'amarin kawai a daura aure in yaso daga baya sai a fada mata."


Alhaji Auwal yace."Wai da a bata hakkinta a matsayinta na bazawara."


Baba Marka tace"Ai har yanzu Sayyada budurwace muke da ikon za'ba mata mijin da ya dace da ita saboda haka batun ma a tsaya tambayarta duk bata taso ba."


Alhaji Auwal ya kalli Mahaifin Sayyada dake zaune a gurin wanda tunda ake maganar bai sanya baki ba Yace."Kayi shiru bakace komai ba kaima kana da damar da zaka tofa albarkacin bakinka kan 'yarka kana da ikon kace E ko a'a mu duka 'yan bi ne tunda dai yarinyar nan 'yarka ce."


Baba Lawali sunan mahaifin Sayyada kenan yace."Ni bani da wata magana kan wannan al'amari duk hukuncin da kuka yanke dai-dai Sai dai ince Allah ya sanya alkairi."


Duka suka amsa da "Ameeen" Kana suka tsayar da maganar daurin aure sati biyu masu zuwa.


****


Mai gari ne ya aika a kira masa Jatau! i zuwa fada....Jatau ya shirya tsaf ya nufi fadar mai gari a take na kusa da maigari ya bashi guri ya zauna yana fad'in"Ai yanzu ka zama suruki Jatau! kana kusa da maigari yanzu."


Jatau! ya mika gaisuwa fada kana yace."Ranka shi dade ka aika kirana nace Allah yasa lafiya ba wani laifin nayi ba."


Mai gari Falalu yayi murmushi yana kallon Jatau yace."Muhimiyar magana ce ta sanya na aika a kira min kai." Jatau! ya gyara zamansa sosai yace."To ina sauraranka ranka ya dade."


Mai gari yace."AbulHalim ne yaga yariyar gurinka Harira jiya yazo min da maganar kan cewa yana so a nema masa auranta."


Jatau! gabansa ya fad'i jin abunda maigari yake fad'a AbdulHalim ya tsallake 'yayan kowa yace 'yarsa yake so yaron da kowa ya san cewar lalatacce ne shaye shaye da yiwa yaran mutane fyade babu abunda ba yayi shine zai ce yana son 'yarsa......Maigari yace."Jatau! kayi shiru ko kana da wani uziri ne."?


Jatau! yace."A gafarce ni ranka ya d'ad'e yarinyar nan tuntuni na dad'e da yi mata miji."


Maigari ya 'bata fuska sosai yace."Kamar ni na aika ayi kiranka kan wata bukata tawa ka kawo suka akai lallai babu shakka Jatau! wuyanka yayi kauri a garin nan."


Jatau! yace."Iya gaskiya ta na fad'a ranka shi dad'e ayi hakuri."


Maigari ya gyara zamansa kan kujerarsa yana karkada kafafu yace."Wai tukkuna ma shin yaron da ka bawa yar taka dan wanene a cikin garin nan."?


Jatau yace."Wannan yaron ne da na tsinta a cikin rafi watanni hudu da suka wuce alhamudullhi ya samu lafiya yana mu'amula irin ta mutane kuma sun shaku da yarinyar har suka kulla soyayya a tsakaninsu ni kuma nayi musu alkawarin aure."


Maigari yace."Wato kana so ka shaida min cewar wannan yaron yana cikin garina baka sallame shi ba kenan."?


Jatau! yace."A gafarce ni ranka shi dade ban sallameshi ba domin sanin da nayi ko na sallemeshi babu inda zashi tunda bai san kowa ba sai na cigaba da zama dashi sai dai kullum muna adduar Allah ya kawo wanda zaice ya san daga inda yake."


Maigari yace."Babu shakka! Jatau! wato har ka soma yanke hukunci da kanka a cikin garina to kuwa babu shakka zaka tattara kayanka kaf kaf ka fice min daga gari wallahi wallahi wallahi nayi rantsuwa da Allah kwana uku kacal na baka ka tattara yanaka yanaka ka fice min daga gari tunda ni ban isa na zartar da hukunci a garina ba sai an'ketare wannan hukuncin da na zartar dashi akanka ya zartu a har abada."


"Wannan gaskiya ne ranka shi dad'e! gaskiyar magana kenan ai wannan hukunci shine dai-dai."!!!! Surutan da mutanan fada keyi ya cikawa Jatau kunne yace." To kamar yanda ka zartar da hukunci a kaina nima zan dauki hukunci zan bar maka gari kamar yanda ka bukata amma ka sani wannan duniya ba matabbata bace kuma mulki da Allah ya baka baice ka zalinci jama'a ba irin wannan ni na barku lafiya." Jatau ya mike yana sanya takalmi jama'ar fada suka hayayya'ko kansa da zagi da cin mutunci Jatau! yayi musu shiru ya kama hanya zai tafi a take Falke wani mutum ne mara mutunci a fadar ya tasa 'keyar Jatau! da zunguri ya kuma sanya yara suka rakashi har kofar gidansa suna yi masa ihu! da zaginsa wai tunda ya zagi maigari shima sai sun zageshi har an soma samun wasu daga cikin yaran sun fara jifansa......Tun daga nesa Sadam dake bakin bishiya ya hango abunda ke faruwa ya mike da sauri yaje ya watsa yaran ya ri'ko hannun Jatau! suka nufi gidan yana tambayarsa abunda ke faruwa Jatau! Yace."Mu shiga gida sai in fada maka abunda ke a da akwai." Sadam ya rike hannunsa sosai suka nufi cikin gidan.
NI DA YAYA SADAM


BINTA UMAR ABBALE*


38
Jatau ya nemi guri ya zauna yana goge gumin dake saman goshin sa Hansatu ta karaso gurin hannunta rike da kofin silba cike da ruwan randa ta ajiye a gaban mijin nata zama tayi gefansa ta dauki maficin tana masa firfita tare da fad'in"Malam yau garin nan ana zafi sosai wallahi sai zufa kake kamar wanda yayi tafiya mai tsanani!


Yace."Hasantu wannan zufar da nake bata lafiya bace." Jatau! ya warware musu yanda sukayi da maigari kan kiran da ya aiko yana masa.


Sadam! da kansa ke sunkuye a kasa ya dago ido jawur yace."Baba saboda ni maigari ya kore ka daga cikin gari me zai hana ni ka sallame

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login