Showing 78001 words to 81000 words out of 142497 words
Chapter 27 - NI DA YAYA SADAM Complete Document by Binta Umar Abbale.txt
yi miki 'karya ko."? Ta girgiza kai tana murmushi taji dad'i sosai da taji wannan labari.
Mammah tace"Ikon Allah to meyasa mu idan mun kirashi a waya bata shiga ." ? Yace."mybe don kuna gidane babu network me kyau amma ni kinga lokacin dana kirashi ina can wajan gari shine dalili."
Mammah tace"To Alhamdullahi tunda ka kirashi kuma yace yana cikin koshin lafiya Allah ya dawo mana dasu lafiya.
Ya amsa da "ameen." mikewa yayi yana kallon Sayyada da wata siga ta daban yace."Tashi muje ja ajeki a makaranta." Sayyada ta mike tayi wa Mammah sallama suka fita.
Minti goma sha biyar da fitarsu kira ya shigowa wayar Mammah! tana kicin tana aikace aikace kafin zuwan mai akinsu sai ta fito da sauri tana goge hannu daf da zata katse ta daga wayar ganin numbar Soja ya sanya ta danna da sauri tayi sallama.
Ta jiyo muryarsa na bin iska Yana fad'in"Mammah! kina jina .'' Da sauri tace"Ina jinka Sadam! ina fata dai kana lafiya ko."?
Yace."Lafiya nake Mammah munanan cikin wani kauye dake jahar barno ranar da zamu tafi naso zuwa muyi sallama Allah bai nufa ba nayi ta kiran wayarki ba'a dauka ba nasan fushi kike Mammah ki gafarce ni."
Tace."Na yafe maka yarona yanzu ya yanayin aikin naku ina fatan akwai alamun nasara a ciki."
Yace."Mammah sai godiyar Allah wallahi tunda mukaje bamu samu abunda muke so ba amma dai insha Allahu kafin kwanakin da muka d'iba su cika zamu samu nasara."
Tace."To muma muna tayaku addua Allah ya baku nasara ya kuma dawo daku lafiya." Yace.",Ameen Mamana." Yana kokarin kashe wayar tace"Sadam! baka tambayi matarka ba fa yarinyar ta damu kullum tana cikin damuwa kafin tayi bacci kuwa sai taci kuka ta 'koshi!
Shiru yayi yana nazarin maganar mahaifiyar tashi yasan za'a rina dama tunda ta sanya masa damuwa ai dole itama ta shiga cikinta......
.Duk abunda take ciki ya sani kafin su bar garin yasan irin zirga zirgar da Sulaiman keyi akanta da hidimarsa kan makarantarta duk yana da labari cewar shine ke kaita ya daukota shiyasa kawai ya tattara ta ya watsar da ita domin wani irin mugun zargi ne ya shiga zuciyarsa kan tarrayar Sulaiman din da yarinyar yana ganin tunda kamar tafi son Sule din idan Allah yasa ya dawo to zai sawwa'ke mata tunda dai dora mata iddah ba sai ta auri Sulaiman din shima hankalinsa zaifi kwanciya don ko ya aureta zuciya bata da kashi xai iya cigaba da zarginta da Sulaiman din shiyasa kawai ya dauke hankalinsa da kanta ya mayar dashi kan aikinsa.
Amma duk don ya kwantar da hankalin mahaifiyar tasa yasa yace."Mammah ki bata hakuri insha Allahu zan dawo a kurkusa dukaninku ku kwantar da hankalinku dama yanayin aikinmu ya gaji haka."
Tace."To shikkenan Soja Allah ya dawo daku lafiya ita kuma Sayyada zan rarrasheta in tausheta ta kwantar da hankalinta."
Yace."Yawwa Mammah ni zan koma gurin aiki sai na sake kira." Tace."To Allah ya jisshemu alkairi."
****
Saliha ta fuskanci Sayyada yau na cikin farin ciki da annusuwa ba kamar kwanakin da suka gabata ba da kullum zakaga fuskarta a murtuke, bayan Malamin dake ajin ya fita Saliha tace."Kawata yau naga kina farin ciki sosai nace ko kin fara soyayya ne."
Sayyada tayi dariya a nutse tace"Saliha soyayya kuma ana zaune kalau kawai dai yau haka nake jin farin ciki a raina."
Saliha tace"Gaskiya kam na lura dan tunda muka hadu ban ta'ba ganin irin wannan walwalar a fuskarki ba." Sayyada dai murmushi tayi tana jin dadi a ranta jin cewar Ya Sadam sunyi waya da Ya Sulaiman yana lafiya kuma yace zai dawo cikin satinan shine dalilin da ya sanya take ta farin ciki da annushuwa.....Farin cikinta ya sake nunkuwa lokacin data dawo gida Mammah ta shaida mata cewar suna fita a dazu da safe Sadam! din ya kira waya tace sun jima suna hira har yace a baki hakuri yananan lafiya kuma in Allah ya yarda yana kan hanyar dawowa."
Sayyada ta dinga jin wani farin ciki a ranta ashe dai Sadam! ya damu da ita tunda gashi har hakuri yake bata tabbas itama ta dauki al'kawarin idan yazo zata bashi hakuri kan abunda tayi masa kuma sannan zata bashi hakkinsa na aure mutukar ya nema dama maganar karatu ce ta sanya take gudunsa amma tinda yanzu ta fara zuwa makaranta to magana ta wuce shima Ya Sulaiman din ba zaice komai ba dan ta yarda da Sadam! din tana so ya dawo su fara rayuwa irin ta ma'aurata.
NI DA YAYA SADAM
NA
BINTA UMAR ABBALE
33
Misalin 'karfe biyu na dare duk suna kwamce 'karkashin boda wasu daga cikinsu bacci 'barawo ya kwashe su Sadam! kam idanunsa biyu daga zarar yaji motsi zai haska fitila a shirye yake da shirin ya'ki....Harbin bunduga suka soma ratatata!!! da sauri duk suka mike suka firfito a guje suka nufi wani gajeriyar gatanka suka 'boye jikinsu duk sun saita bundugunsu.....Suma suka soma saki har'bi ta ko'ina.
Gudu suka soma ji na sawayen mutane suma suka fito a guje! suka bi hanyar da suke da tabbacin nan suke suna gudu suna sakin harbi Sadam! ne kan gaba! sai nausawa yake cikin daji......Can ya hangosu suna haure wata duguwar katanga Ya dinga saita bundugarsa yana sakar musu harbi a kafafunsu sai da ya samu nasarar harbin mutun uku a kafa.....Captain Saleh na ganin aikin Sadam! na kyau sai kyashi da bakin ciki ya kama shi shammatar Sadam! din yayi ta bayansa ya tad'e masa kafafu....Sadam! ya fad'i! ragwajab a gurin to da yake dare ne kuma akwai duhu babu wanda ya dauka shine ya fad'i........Sai suka dunga tsallakeshi suna wucewa Sadam! ya yunkura domin mikewa ya kasa yana ganin abun kamar wasa yayi yayi ya mike ya kasa sai ya fara jan jiki yana binsu a baya......Can yaji gudu! sun dawo da baya suka dinga tsallakeshi suna komawa boda wasu daga ciki ma har takeshi sukeyi basu sani ba su dai kokarinsu su tseratar da ransu....Dalilin da ya sanya 'yan ta'addan suka samu galaba akansu kassaruwar Sadam! din dama shine 'karfin aikin to Captain Saleh yayi masa illah! ya durkusar dashi kawai saboda yana ba'kin ciki kada Sadam din ya taka wani matsayi kan aikinsa....Cikin masu takeshi su wuce har shi dan da yazo ya samu murfin gwiwarsa ya take sosai da wannan kwantarerean takalmin nasu Sadam! ya rintse ido yana salati tare da rike hannunsa Saleh ya fuzge a guje ya bar gurin.....Sadam! yayi kwamce a cikin ciyayi cikin tsananin azaba! hannu yasa cikin ciyayi yana laluben fitilarsa bai ganta ba dole ta sanya ya cigaba da jan jikinsa domin nausawa ciki har yanzu zuciyarsa a dake take burinsa kawai ya samu galaba kan abokan ya'kinsu......Hasken fitilar da ake haskowa ne ya dallare masa ido ya sanya bayan hannunsa ya kare fuskarsa, Can ya soma jin takun tafiya..
Lamfu yayi ya kwanta, 'Kafar wani tazo giftawa ta kusa dashi ya sanya 'karfi ya tad'e 'kafafun sai ya fad'i a gurin!!!! Da saurin ya mi'ke cikin zafin nama ya ciro 'karamar bundugar dake hannunsa ya saita masa ita a ma'kogwaro.........Sauran suka dawo da baya da baya suna haskasu da fitila.
Ganin ogansu a kwance a 'kasa ga bunduga a ma'kogwarsa sai hankalinsu ya tashi da sauri suka zube makamansu......Suna zare ido! Sadam ya dinga kokarin tashi tsaye ya kasa wannan shine ga koshi ga kwanan yunwa....Wani usur! ya fito dashi daga aljuhunsa ya hura da karfi! sheda ce da duk inda 'yan uwansa sukaji to zasu tawo gurin....Ya dinga hura usur! din da karfin gaske yana sake saita bundigar wuyan ogan......Shiru babu wanda yazo....Takaicin duniya ya ishi Sadam! gashi yayi nasarar kama babbansu amma kuma bashi da kafafun da zai mike ya tasa 'keyarsu.....Yayi kiran 'yan uwansa dake malalata ne sunaji sunyi shiru ha'kika dukaninsu basu san meye aikin soja ba."
'Daya daga cikin 'yan ta addan ne ya lura da halin da Sadam! din ke ciki na rashin kafafu sai ya lalla'ba a hankali ya dauki daya daga cikin bindigunsu masu tsayi da 'katuwar 'kota ya sanya 'karfi ya daki! kan Sadam! da ita!!!!!! Sadam! ya d'ora hannunsa duka biyu a kanshi yana rintse ido....Wannan damar ta sanya Ogan ya mike tsaye da saurin gaske ya rarumi bundiga daga cikin bundugunsa ya sake kai masa duka aka! Sadam ya silale ya fad'i a gurin....Dukainsu suka dauki bundugunsu suka dunga bugun kan Sadam! da ita tun karfinsu suke dukansa akansa sai da suka ga ya daina motsi tukkuns suka kyaleshi daukarsa sukayi jina jina suka nufi wani 'katon ruwa dake da maraba da garuruwa suka jefa shi a ciki.....Ba tare da wata damuwa ba suka kama gabansu.
A can Boda kuwa Captain Saleh yayiwa Habu jini jina da duka dalili bayan sun dawo suna mai da magana Captain Saleh ya shaida musu cewar shine ya tad'e Sadam! ya fad'i a gurun dukaninsu suka cika da mamaki jin abunda Saleh yayi Habu ya nuna masa rashin dacewar abunda yayi shikkenan sai ya hau zaginsa har ds cire riga wai suyi dambe da kyar aka rabusu.....Sai kuma suka jiyo usur na tashi hakan ya tabbatar musu da cewar Sadam ne ke neman taimako Captain Saleh ya sanya wani 'katon katako ya tokare hanya yace."Babu wanda zaije Captain Habu yace."Bai isa ba idan shi ba zashi ba to bashi da hurumin hana wani zuwa sai suka soma cacar baki daga haka fad'a ya kaure a tsakaninsu Captain Saleh mugu mai bakar aniya ya fito da wata shegiyar aska daga aljihunsa ya dinga yankar Habu da ita Sai da yayi masa jina jina sannan ya kyaleshi......Wannan rashin imanin da ya gwada kan Sadam da Habu ya sanya suma sauran abokanan tafiyar suka samawa kansu lafiya saboda suna jin tsoron muguntar Saleh dama babu wanda yake shakka sai Sadam! to yanzu baya gurin zaiyi abunda yaga dama ne.
****
A furgice ta tashi zaune zaune hannunta ta d'ora kan kirjinta tana dannewa dakin take bi da kallo tana zare ido......Can kuma ta fashe da kuka mai tsanani jikinta na kyarma! ta diro daga gadon ta fita daga dakin.
Dakin take bubbugawa tana kuka da fad'in"Mammah! ki bude sun kashe shi innalililhahi wa ina ailaihi raji'un!!!!....Hajiya Fatsima ta dinga jin bugun kofa cikin baccinta tana kuma jin sautin kuka.....Da sauri ta bude idonta tana sake jin gunjin kuka da kalmar innalilihi wa'ina ilahi raji'un! da Sayyada ke maimamtawa.
Da sauri ta bude kofar dakin tana fad'in"Sayyada lafiya kukan me kikeyi ne me ya faru?"!
Ta rungumeta 'kam! tana wani irin kuka tace"Mammah shikkenan sun kashe shi shikkenan Sun kashe min mijina."!!!!
Jiki na rawa Hajiya Fatsima ta jata suka zauna kan gado tace."Sayyada yi shiru ki fada min meke faruwa ne kar ki tayar min da hankalina."
Kafin tace komai Abbah ya shigo dakin......Ya karaso inda suke hankalinsa duk a tashe yace."Meke faruwa ne naji koke-koke."!
Hajiya Fatsima ta nuna masa Sayyada dake jikinta a kwance tana kuka tace"Nima ina tsaka da bacci naji bugun kofarta tana kuka tambayarta nake abunda yake faruwa."
Abbah ya zauna kan kujerar mudubi Yace."Sayyada nutsu ki fada mana me ya faru.?
Ta dago kanta tana kallonsa hawaye ne kawai ke shatata a fuskarta Cikin rauni tace"Abbah sun kashe shi! sun kashe min mijinaaaaa."!
Dukaninsu suka zuba mata ido suna kallonta da mamaki. Mammah ta kalli mijin nata tace"Alhaji ko dai mafarki tayi ne."?
Yace."Gaskiya kam wannan dai ina tunanin mafarki tayi." Sayyada ta rike hannunna tana makyarkyatar jiki tace"Wallahi Mammah ba mafarki bane da gaske nake sun kashe shi wayyo ni! wayyo na shiga uku na lalace."!!!! Ta kurma wani uban ihu! tana burgima a kasan gurin.
Hankalinsu duka ya tashi Alhaji Auwal ya fito da waya yana neman numbobin jama'a duk wacce ya kira is swic up abunka da dare kowa ya kashe wayar Sai ya fara kiran wayar Sadam! din abun mamaki ta hau ringing.....Hamdala yayi cikin ransa yana jiran yaron nasa ya dauki wayar sai dai kash! har ta katse bai daga ba.
Kiran wayar ya cigaba dayi babu 'ka'kkautawa! tana shiga amma ba'a daga ba ya kira ya kai sau ashirin da ya gaji ya hakura ya dago kansa yana sharce gumin goshinsa.
Sayyada kuka take muryarta ta dashe surutai kawai takeyi tana fad'in''Ni na gani sun kashe shi sunata dukansa suka daukeshi suka jefa a kogi......! shikkenan nima mutuwa zanyi sun kashe min mijina na shiga ukuna Wayyo Yaya sadam d'ina!! Innalilahi wa'ina ilaihi raji'un!!!!! Ganin kamar tana nema ta zautu ya sanya suka rufu akanta suna tofa mata adduo'i To suma dai zuwa wannan lokacin jikinsu yayi sanyi jira kawai suke gari ya waye suji abunda ke da akwai.
Da asussubah Abbah ya kira Sulaiman yace maza yazo gida babu lafiya.....Ba da son ransa ba ya shirya ya nufi famly house din nasu.......Ganin irin tashin hankalin da iyayen nasa suke ciki ya sanya ya nuna damuwarsa kan al'amarin......Gari na waye wa suka nufi barikin sojojin domin samun cikkaken labarin abunda ke faruwa.
T34
Gari na soma haske Captain Habu ya silale daga cikinsu ya nufi inda yake tunanin zai samu sadam! d'in, kutsawa ya dinga yi yana lalube hade da kiran sunansa shiru sai kukan tsuntsaye ke tashi babu inda bai duba ba baiga Sadam ba jikinsa yayi bala'in sanyi ya nemi guri ya zauna yana zubar da hawaye......Shikkenan sun samu galaba kan jarumi shikkenan sun kashe Sadam! sun jefar da gawarshi innalilihi wa'ina ilaihi raji'un!!!!!!!! Ya dinga maimata kalmar yana goge hawaye hakika yayi rashin abokinsa dole yayi kuka ya jajanta al'amarin yananan zaune suka dinga shigowa gurun da dai-dai da dai-dai ganinsa ya hada uban tagumi ya sanya jikinsu yayi sanyi kowa da tambayar da yake masa Captain Habu ya kasa cewa komai,
Captain Saleh na zuwa gurin ya fara lalube yana fad'in"Ina gawar tasa take ne."!! A fusace! Habu yayo kansa cikin zafin nama ya rike ma'kogwaronsa ya shake masa wuya.
Captain Saleh ya dinga kakari idanunsa duk suka firfito waje.....Kokarin 'bam'bare Hannu Habu ake daga wuyan Saleh abun yaci tura wannan karon Allah ya bashi nasara kan Saleh sai da ya galabaitar dashi sannan ya sake shi ya fad'i kasan gurin yana rike ma'kogwaro
Habu na wata iriyar tsuma! yace."Hakika ba kowa ne ya janyo mana wannan asarar ba sai wannan mutsiyacin mugu mai bakar aniya shine ya janyo mukayi rashin gwarzo jarumi a fagen ya'ki! Yanzu sun kashe mana Sadam! sun dauke gawarshi wannan shine babban tashin hankalinmu."
Musulman cikinsu suke salati suna jajantawa har da masu share hawaye na bakin ciki basu ta'ba fita ya'ki da Sadam! anci galaba a kansu ba sai dai su suci nasara tabbas ba karamin rashi sukayi ba.
Captain Habu ya ciro wayar da suke amfani da ita ya fara traying din numbar shugabansu wato General Abdulsalam. Wanda shima nashi bangaran yana can hankali a tashe domin maganar dasu Abbah suka zo masa dashi ta daga masa hankali mutuka........Da kyar ya samu wayar ta shiga Gen Ya daga wayar yana Fad'i"Habu Yanzu ya ake ciki ne ina fatan komai na tafiya dai-dai."
Habu ya goge gumin goshinsa cikin sanyin jiki yace."Yallabai al'amura sun dagule! Al'amura sun 'baci!!!!!! Gen Yace."Innalilhi waina ilahi rajiun!!!! Captain Habu yace."Yallabai mun nemi Sadam mun rasa a gurin tun bayan da ya'ki ya har'ke a tsakaninmu da su sun samu galaba a kanmu, ta dalilin goyon bayan Captin S.......Ai kafin ya 'karasa yaji saukar 'katon dutse a kanshi! a take kansa ya fashe! jini ya hau zuba ta ko ina silalewa yayi ya fad'i a gurin yana salati!! Hankalin General yayi masifar tashi da jin wannan al'amari sai ya fara fadar kalmar innalillahi wa'ina ilahi raji'un!
Abbah dake zaune a kujera gumi! duk ya ji'kashi yaji dukanin abunda ke faruwa An kashe d'ansa gurin ya'ki an rasa gawarsa La'ila ha'illahu Muhammad rasulilihi Sallalahu alahi wasalam!
Kafin kice me labari abunda ke faruwa ya karad'e gari cewar sojojin da aka tura aiki Maduguri suna cikin hadari don har yan ta'addan sun samu nasarar kashe guda daga cikinnsu ba tare da 'bata lokaci ba yan jarida suka nufi garin domin daukar rahoto
****
Captain Saleh ya jefar da gingimeman dutsen dake hannunsa yana wani irin huci! da gumin hanci! yace."Har ni zaka sha'ke wuya na kyaleka Habu baka isa kayi ajalina ba ni ne zanyi ajalinka."" Captain Habu na kwance cikin jini yana matagugu Saleh ya hana kowa zuwa inda yake Wayar sailular dake tarwatse a 'kasan gurin ya dauka ya had'ata guri guda ya kunna....Aikuwa tuni kiran General Ya shigo Saleh ya daga yana wani salau salau da murya yace."Yallabai gamu cikin tashin hankali domin sun sake kawo mana hari! sun samu nasarar raunta Habu a lokacin da kuke waya dashi Yanzu haka dukaninmu muna mafaka muna bukatar d'auki daga gurunku."
General Yace."Ku zauna inda kuke kar ku sake fitowa gamunan zuwa gurin." Saleh yace."Godiya muke Yallabai." Kashe wayar yayi yana kallon abokanan nasa yace."Wallahi duk wanda ya budi bakinsa ya fadawa Yallabai da sanya hannuna kan afkuwar lamarin nan sai na kashe shi ina fatan baku mance waye Saleh ba." Shiru sukayi masa suna kallonsa kawai yana ta tsara musu karyar da zasuyi idan General da yan jarida sun iso gurun.
Can gida kuma Mammah duk ta rasa ya zatayi da Sayyada ta fita daga hayyacinta kuka kawai take tana fadin sun kashe mata miji ita kawai a kaita inda mijinta yake duk dauriya irin ta Hajiya Fatsima sai da tayi hawaye saboda tashin hankali, lallabata takeyi da fad'in"Mafarki ba gaskiya bane ta kwantar da hankalinta insha Allahu mijinta na nan a raye cikin koshin lafiya.
Tafiyar jirgi sukayi shiyasa suka isa garin cikin kankanin lokaci.........General Da Abbah Sulaiman da 'yan jarida da sauran sojojin suka nufi inda abun ya faru suna bunkice ko Allah zai sa suga wani abu da ya danganci Sadam! din cikin ikon Allah suka ga hularshi bakin wata bishiya General ya dauka yana dudduba gurin.....Wannan hula ta Sadam! 'Yan jarida suka rufu a kanta suna ganin kamar Sadam! din ne sai daukar hotonta sukeyi to duk wani bunkice da ya kamata ayi anyi babu Sadam a gurin babu labarinsa Hankali a tashe Gen ya sanya aka dauki Habu da bai san inda kansa yake ba suka sanya shi a jirgi suma suka shiga gabad'ayansu suka bar gurin cikin alhini na babban rashin da sukayi.
Tun a mota Alhaji Auwal ke kukan zucci idanunsa sunyi jawur babban tashin hankalinsa na rashin gawar dansa