Showing 102001 words to 105000 words out of 142497 words

Chapter 35 - NI DA YAYA SADAM Complete Document by Binta Umar Abbale.txt

09 Dec 2024

50492

baki da police din mutane suka soma taruwa a gurin.......Cikin gadara da nuna na fika ta fanni komai Police din ya d'aga katuwar bundugarsa ya kai masa duka da ita a tsakiyar kansa........."Yaya Sadam!!!!!!!! Muryarta ta karad'e ko ina a gurin.....a guje ta dinga buge motane tana kutsawa inda suke.......Waige-waige! yake yana son sanin daga ina ne! a kiransa sai ya sake jin wani wawan! duka a saman kansa a take ya soma ganin dishi dishi! ya rirrike kansa da hannunsa yana salati tsuganawa yayi a gurin.......Kunnansa nayi masa wata iryar kud'a!!! Ya sakejin sautin Muryar dake ambaton sunansa "Wayyo Allah na zai kasheshi Yaya Sadam!!!!!! Kirif! ya kife a gurin ya daina motsi!


Ta 'karaso gurin tana wani irin ihu! da kururuwa ta zube a gabansa tana tatta'ba jikinsa tana salati da fad'in" Wallahi shine! shine! ya dawo ashe bai mutu ba! Shine!!! Yaya Sadam! ka tashi ga Sayyadarka nice Sayyada matarka."!!!! Tana kuka take fadin maganar jama'a duk sun firfito daga mota sun kewaye su shi kuwa police din nan yana tsaye da bundugarsa a hannu babu abunda ya sha masa kai.....Ta mike a fusace! ta kai masa wani irin duka a ciki tana ihu! majina sha'be!sha'be! hawaye kace-kace! a fuskarta take fad'in"Nima sai na kasheka tunda ka kashe mun mijina wallahi nice ajalinka shege tsinanne me bakar aniya." !! Kamar mahaukaciya ta dinga dukan police din nan ya fusata! ya daga kasan bundugarsa zai kai mata duka daga bayansa aka fuzge ya juya a fusace! kawai sai yaji kyakkyawan mari a kuncinsa!!!! Wani mutum ne mai zuciya irin ta Sadam din yayi wannan aikin....Ya fuzge taurarin dake saman kafad'ar Police din ya watsar a kasa yana kallon jama'ar gurin yake fad'in"Wannan mutumin bai dace da jami'in tsaro ba sunansa azzalimi mugu don haka mu 'kaddamar masa."!!! Sai kowa ya tawo suka rufe shi da duka ko ta ina suke kir'barsa da zaginsa ta uwa ta uba.....Gurin ya hargitse sosai wasu sai take Sadam suke wanda yake kwance bai san halin da yake ciki ba.....Sayyada kuka take tana kareshi da hannunta da taga dai sun'ki daina takeshi sai kawai ta kwanta a jikinsa ta rungumeshi 'kam-'kam! tana wani irin kuka mai gunjin tsiya.......Wannan gunjin kukan da take da kuma hayaniya ta jama'a ya sanya a bud'e idonsa a furgice! ya mike zaune da ita a jikinsa.....Kallon kallon suka shiga yi ita dashi ta dinga tatta'ba fuskarsa da kiran sunansa shi kuma sai kallonta yake yana kuma nazarin gurin da suke da karfi! yace."Suna inaaaa."! Sai ya watsar da ita a gurin jikinsa na kyarma sosai ya fara kutsawa cikin mutane yana fad'in"Suna inaaa! Da kiran sunan Habu da Saleh. Binsa ta dingayi a baya tana kiran sunansa....Ya juyo yana kallonta hannunta ya rike yaja da karfi! da fadin"Sayyada ina muke a gurin nan!? ina Captain Habu da Saleh! ina kayan aikina ina sauran abokanan aikina suke."


"Yaya Sadam! ka nutsu nan ba filin ya'ki bane Captain Habu da Saleh suna Kaduna muna cikin jahar kano ne a yanzu." Ya juyo yana kallonta cike da tsantsar mamaki! ya dinga kallon garin yana mamakin me ya kawoshi garin kano shi da yake kan aiki cikin garin barno amma kuma za tace masa yana jahar kano shin wai me yake faruwa ne.?Sai ya fara tunanin abubuwan da suka faru shekara daya da rabi data da wuce ya dinga tunanin karan battansu da artabun da suka dingayi da mutanan kwakwalwarsa ta shiga tunano masa irin bugun da suka dinga masa a tsakiyar kanshi har ya silale ya fad'i! a gurin yana ganin dishi dishi a idanunsa to tun daga lokacin bai sake gane kansa ba sai yanzu da ya ganshi tsaye kan saman gada ana hayaniya.....Hannunta ya rike tsam! tsam! suka dinga kurd'awa tsakanin motoci yana so su bar cikin jama'a.....
A dai-dai lokacin kuma Jatau! da Munkaila suka hangoshi ya nufo inda suke Munkaila yayi saurin tararsa yana fad'in"Soja sannu abunda ya faru kenan Allah ya kiyaye gaba kaga tsaikon da'a ka samu a bakin titi ya sanya Harira ta haihu cikin baburi An samu 'ya mace."


Tun sanda Munkaila yake maganar ya zuba masa ido yana kallonsa sam! bai fahimci me yake nufi ba Fuskar Munkaila na tayi masa gizo a fuskarsa.....Ya tsurawa Jatau! ido yana kallonsa yace."Ban gane maganar da kuke ba ni Sunana Sadam Auwal d'an asalin garin jigawa cikin wata karamar hukuma mai suna *Dabi* nan ne tushena amma kuma yanzu haka ina zaune a jahar kaduna ina mamakin abunda ya kawoni garin kano tare da matata gatanan a hannuna."


Jatau! Yaji wani irin farin ciki ya Lullubeshi babu shakka Soja ya dawo cikin tunaninsa sai ya soma fadin kalmar "Alhamdullihi ala kulli halin Allah nagode maka daka nuna min wannan rana da wannan bawa naka ya gane wanene shi a rayuwa."


Munkaila ma yana cike da farin ciki mara misali ya kalli Sadam din yace."Soja wannan al'amari yana bukatar nutsuwa domin abubuwa masu wuyar sha'ani sun faru da kai yanzu mu shiga mota muje asibiti kaga kyautar da Allah yayi maka." Sadam ya cika da mamaki da maganar Munkaila to saboda kwarjin da dattijon yayi masa ya sanya baiyi gardama ba domin shima a jikinsa yana ji akwai babban al'amari da ya faru da rayuwarsa........Babur din suka shiga dirben yaja suka nufi asibitin murtala.


Abunda ya faru bayan futar Sadam daga cikin babur a lokacin da gosolw ya tsananta a gurin......Sai ciwo ya tsananta ga Harira ta dinga mukususu tana kiran sunan Allah da ka kalmar shahada ga wani irin jini daya tsinke yake zuba a jikinta sai su Hansatu suka tsorata take suka gigice ganin 'yar tasu na neman rasa ranta ya sanya suka rirriketa suna salati....Hankalin me babur din ya tashi ya fito yana neman Sadam din to fitowarsa ke da wuya Harira ta haihu cikin babur din sai dai tunda ta haihu ta sume don mabiya ma bata fad'o ba Hansatu ta fito daga babur din tana share hawaye da kiran sunan Allah......Jatau! da Munkaila dake cikin nasu babur din suka hangota da sauri suka fito suka isketa da tambayar abunda ke faruwa ta sanar dasu halin da ake ciki tare suka isa inda babur din yake ganin halin da Harira ke ciki ya daga musu hankali Munkaila ya dinga neman alfarmar mutane suna matsawa da abun hawansu har direban ya samu hanyar da ya juya domin sauya hanyar zuwa asibiti........Hansatu ta koma cikin babur din yaja da sauri suka bar gurin.


Munkaila da Jatau suka kasa bin bayansu sun tsaya suna so su san halin da Sadam din ke ciki.....Wannan shine abunda ya faru.


Duk inda zasu shiga kafarsa kafarta hannunta na cikin nasa a damke ko ina sukayi sai ya bisu a baya yana mamaki da tu'ajibun wannan al'amari Sayyada dai bakinta mutuwa yayi sai zare ido takeyi zuciyarta na mata wasi wasi kan maganganun da mutanan sukayi kan Sadam din to ganin shi bai ce komai ba ya sanya kawai take binsu zugwi zugwi a baya.


A wata rumfa suka iske su Hansatu da Abu duk sun zauna sunyi jugum-jugum! Hansatu taci kuka ta koshi sosai ta fitar da rai da 'yar tata domin da suka iso asibitin babu irin wulakancin da bayi musu ba kafin a kar'bi Harira sai da suka sha kyara da hantara da fadin"Dama mutumin kauye bashi da hankali tunda an fada sun fada cewa daga zarar ciwon nakuda ya kama to su garzayo asibiti sai bayan da suga abun yayi tsanani sannan zasu kwaso jiki su tawo Hansatu ta dinga basu hakuri tana kawo musu uziri ko sauraranta ba suyi ba suka sanya aka dauki Harira kamar wata matacciya aka tura ta dakin 'yan haihuwa.......Suka nemi guri suka zauna suna jiran tsammani to cikin wannan hali suka samesu.


Wata narse ce ta fito farfajiyar gurin tana fad'in"Ana neman iyayen Harira Jatau suna ina."?


Jatau yace."Gani malama nine mahaifinta tace"Okey ina mijinta yake."? Jatau ya nuna Sadam! dake tsaye yana kallon ikon Allah." narse din tace"To ku biyoni akwai bayanin da dr zaiyi muku."


Jatau! yayi gaba Sadam ya saki hannun Sayyada yabi bayansa.


Gefe guda ta zauna gumi sai d'iga yake a jikinta ta sanya gefan hijab dinta ta goge duk ta rasa wane irin tunani ma za tayi wai shin me yake shirin faruwa ne ga rayuwarsu.......Wayarta ke 'kara ta sanya hannu ta zaro ta ko dubawa ba tayi ba ta kara a kunnenta Saliha tace"Sayyada wai ina kika shiga ne? gamunan hankalinmu duk ya tashi Aunty Rabi'atu bakiga fad'an da takeyi ba."


Cikin mutuwar jiki da sanyin murya tace"Saliha ganinan asibitin Murtala wannan mutumin da police din nan ya daka da bunduga dan uwana ne gani tare dashi ana dubashi." Sayyada ta fadi wannan maganar ne saboda bata so kowa yasan sirrinta."


Saliha tace"Allah sarki to babu damuwa zanyi musu bayani yanda zasu fahimta." Kashe wayar tayi tabi hanyar dasu Sadam din suka bi da kallo.


"Malam kaine Mijin Harira Jatau."? Likita ya fada yana kallon Sadam dake fuskantarsa Yace." Eh nine." likita ya kalli Jatau yace."Kaine mahaifinta."? Jatau! yace."kwarai kuwa likita."


Likita Yace."Ya akayi kuka bari yarinya 'kan'kanuwa ta galabaita haka? ya akayi kuka bari ta dinga zubar da jini ba ku tawo asibiti ba gashi duk naga irin dokokin da aka fada muku a katin ta ana awo amma kuka tsallake kuka jefa yarinya cikin halin rai da rayuwa a gaskiya baku kyauta ba."


Jatau yace."Wallahi likita ba laifinmu bane wannan al'amari Allah ya kaddarashi yarinyar nan na fara nakuda mahaifiyarta ta matsa aka tawo asibiti, tiryab tiryan Jatau ya warwarewa dr abunda ya faru a tsakanin titin Yahya gusau da gadon 'kaya.....Dr yace."Yanzu dai muna bukatar jini lede hudu wanda za sanyawa yarinyar domun ta zubar da jini sosai Allah ne ma ya sanya tana da sauran kwana a duniya da yanda ta zubar da jini nan sai sai kuji mummunan labari muna bukatar jini da gaggawa."


Jatau yace."Idan babu matsala a gwada nawa sai a d'iba ga d'an uwanta can a waje shima a gwada nasa in yayi dai-dai a d'iba."


Sadam! ya girgiza kansa cike da tausayin dattijon da matar da ake ikirari da cewar tasa yace."Baba baza a d'ebi jininka ba saboda kai kanka a yanzu kana bukatar jini da kulawa sosai saboda haka nawa jinin za'a gwada idan yazo d'aya a d'ebi yanda ake so." Dr yace."Okey tom babu damuwa."


Sadam ya kwanta wani gado idanunsa a rintse yana tunanin rayuwa Dr ya fara aikinsa........An samu dace Jinin Sadam yazo daya dana Harira don haka ba tare da 'bata lokaci ba Dr ya d'ebi leda biyu ya kira wata narse yace suje su fara sanya mata wannan d'in.....Babu yanda Sadam! baiyi da Dr din ba akan ya d'ebi duka leda hud'un a jikinsa Dr ya nuna rashin yarda yace"Tunda Allah yasa yarinyar nada dan uwa sai a gwada nasa a gani kaima kana bukatar hutu a yanzu domin na lura kana cikin rud'u da tashin hankali saboda haka ka kwanta ka huta kawai."


Jatau! ya kira Munkaila ya shigo aka gwada jininsa yayi dai-dai dana harira aka d'ebi leda biyu a jikinsa shima ya kwanta kusa da gadon Sadam yana hutawa.........To wannan kusancin nasu ne ya sanya Munkaila ya dinga warwarewa Sadam! abubuwan da suka faru dashi a baya da yanda suka tsince shi a ruwa da irin wulakanci da tozarcin da maigari yayi musu a kansa da yanda akayi suka siyar da komai nasu suka bar gari suka dawo garin kano da zama......Nan ya warware masa yanda akayi suka 'kulla soyayya mai 'karfi shida Harira da yanda aka daura musu aure komai Munkaila bai rage ba sai da ya shaidawa Sadam!
Kana yace."Domin ka sake gazgata magana ta akwai kayayyakinka da muka tsince ka dasu sunanan a ajiye idan muka koma gida zan nuna maka su."


Siraran hawaye masu zafi! suka shiga zirarowa ta gefe da gefan fuskarsa Ya kama hannun Munkaila ya rike tamau! yana fad'in"Ba sai ka nuna min komai ba Munkaila ni da kaina 'kwakwalwata na hasaso min wannan rayuwar da nayi tare daku tabbas hakane! Munkaila tabbas wannanan al'amari ya faru na tuno komai yanzu Harira matatace Uwar 'yata babban burina yanzu ta samu lafiya mu cigaba da zama da juna tare ha'kika kunyi min abunda ba zan ta'ba mantawa dashi ba har'karshen rayuwata.
NI DA YAYA SADAM


*BINTA UMAR ABBALE*


43


Munkaila yace."Alamu sun nuna mana cewar kana da iyali bayan faruwar wannan al'amarin dazu ka shaida mana cewar wannan yarinya matarka ce shin yaya kake ganin iyayenka zasu dauki wannan al'amarin da ya faru da kai da Harira kuma kana ganin babu wata matsala ta bangaran iyalin naka."


Sadam! yace."Haba Munkaila waye bai san kaddara ba ai cikar mutum shine yarda da kaddara mai kyau ko mara kyau ballanta ni wannan kaddarar tawa me kyauce a gurina da duk wani masoyina kaddarar haihuwa ai kaddarace mai kyau mutukar an samu dan ta hanyar halas."


Munkaila yace."To Alhamdullahi Ubangiji Allah ya had'a maka kan iyalinka yaba ikon yin adalci a tsakaninsu." Ya amsa da "Ameen." Yana mamakin lamarin Ubangiji wannan al'amarin da ya faru ga rayuwarsa yayi mutukar bashi tsoro da kuma sake jin tsoron Allah a cikin zuciyarsa, sun kai kimanin awa guda a kwance kafin likita ya shigo dakin yace."Yanzu kuna iya tashi amma yana da kyau idan kun fita ku samu maltina kusha saboda samun kwarin jiki." Suka amsa da ameen ya basu wani jan magani yace su had'iye a take suka had'iya suka fito daga dakin.


Har yanzu suna zazzaune a cikin rumfar suna jiran fitowarsu Sayyada na can gefe guda zaune a kan takalminta su Hansatu sunyi sunyi da ita ta dawo gefan tabarmar da suke zaune ta zauna tace su kyaleta a inda take haka suka hakura suka kyaleta.


Idanunta a kansa lokacin da suka fito ganinsa sai ya sanya zuciyarta karyawa gabanta ya shiga faduwa hakika jikinta na bata wani abu zai sameta na rashin dad'i.....Koda suka fito bai iske inda take ba sai ya tsuguna kusa da Jatau! suna maganar abunda ya shafi Lafiyar Harira.


Narse din dazu ce ta iso inda suke hannunta nannad'e da towel wanda babyn ke ciki tace "Ga babyn angyarata." Da sauri! Abu ta 'karbeta tana murmushi da fadin"Alhamdullahi.....towel din ta bude fuskar yarinyar ta bayyanta....kyakkyawa da ita tamkar yayi kaki ya zubar domin har yanayin fatarshi iri daya ne dana yarinya komai irin nashi ne kamarsu daya da Mammah! tunda dama Sadam din shike kama da mahaifiyarshi, sai bayan sun gama ganin yarinyar ne sannan Jatau ya mika masa ita ya karbeta a nutse yana me tsurawa fuskarta ido kauna gami da tausayin yarinyar suka cika masa zuciyarsa wai yanzu wannan yarshi ta sinna ya hafeta cikin rashin sanin waye shi a rayuwa babu shakka Ubangiji babu yanda baya shiryawa bawa al'amuranshi ya jima yana kallon fuskar yarinyar yana kara gazgata kamaninta dashi da mahaifiyarsa babu wani shaida gami da 'kananun magana duk wanda yaga yarinyar nan yasan 'yarshi saboda tsananin kamar da suke da juna.


Addua yayi mata a kunnenta yayi mata kiran sallah sau uku a kunnenta na dama da hagu kana ya sumbace a saman goshinta da fad'in"Allah ya raya min ke yasa ki zama cikon addinin musulunci."


Yana d'ago kansa suka had'a ido da Sayyada wacce tunda ya kar'bi babyn take kallonsu zuciyarta ta karya mutuka tama rasa wane tunani za tayi."


Saurin sunkuyar da kanta tayi tana wasa da hannunta ya mike ya isketa inda take zaune kan takalminta......Jinsa kusa da ya sanyata sake takure jikinta sam bata so ta kalleshi saboda yanda takejin wata iriyar faduwar gaba.


A nutse yace."Sayyada kinga kyautar da Ubangiji ya bani ko Bayan rabuwata daku nayi rayuwa takaitacciya tare da wad'annan mutanan da kike gani sune suka tsince ni a cikin ruwa bayan ma'kiya sun samu nasara akaina lokacin da mukaje aiki wani kauye a barno shekara daya da rabi kenan abubuwa da yawa sun faru wanda dole sai mun samu nutsuwa sosai zan warware muku yanda al'amuran suka kasance."


Jinsa kawai take da kunne amma ta rasa inda zata aje maganganunsa a 'kwakwalwarta.....Yace."Ki d'ago kanki ki kalli yarinya mai kama dani da Mammana." A hankali ta dago kai tana kallon hannunsa ya saki fuska sosai yana nuna mata babyn.''


Cikin wata sha'kakkiyar murya tace"Allah ya albarkace ta ya sanya cikon addinin musulunci ce." Ya amsa da ''ameen." Kana yace."Karbeta ki sa mata albarka." Ta sanya hannu ta kar'be idanunta na kawo ruwa tana ta 'kokarin mayar dasu.......Sosai taga kamaninsa da yarinyar da kuma Mammah babu wanda zaice ba 'yarshi bace tunda ga komai nan ya nuna lallai d'a Jamiji ba abun yarda bane......Maganar Harira yake mata da yanda take jin Jiki sosai ita dai ba tace komai ba Allah Allah take ya kar'bi 'yarsa ya matsa da kusa da ita don wani irin zafinsa takeji a cikin zuciyarta wai har shine da kwanciya da wata mace bayan tana raye a duniya babu shakka itake son Sadam bashi ne yake sonta ba.


Ganin ba tace komai ba dangane da maganar da yake mata ya sanya yace."Ki bani takaitaccen labarin abubuwan da suka faru bayan barina gida."


Ta kalleshi babu yabo babu fallasa tace"Abubuwa da yawa sun faru masu dadi da marasa dadi sai dai marasa dadin sunfi yawa domin bayan tafiyarka da sati daya muka samu labarin cewa an kashe ka kuma an jefar da gawarka sai hankalinmu ya tashi sosai.........Duk irin dauki ba d'ad'in da sukayi lokacin da al'amarin ya faru Sayyada ta shiga warware masa da irin tashin hankalin da suka shiga da irin shige da ficen da Abbah ya dinga yi kan neman gawarsa duk dai ta warware masa komai tana hawaye amma koda wasa bata fad'a masa yanda akayi aka daura musu aure da Sulaiman ba


Sosai ya shiga cikin yanayi na rashin dadi da jin labarin da Sayyadar ke bashi hakika ya tausayawa iyayensa sosai Yace."Tabbas wad'anda suka aikata min wannan akin sun zalince ni sun zalince ku amma babu komai kansu sukayi wa tunda gashi dai bukatarsu bata biya ba akaina zamu komai gida amma ba yanzu ba sai komai ya warware mun tukkuna sai naga yanayin jikin mahaifiyar yarinyar nan sai muje amma bana so ko a waya ki fad'a musu halin da ake ciki domin idan an sanar da gida cewa gani a raye to

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login