Showing 141001 words to 142497 words out of 142497 words
Chapter 48 - NI DA YAYA SADAM Complete Document by Binta Umar Abbale.txt
fad'in"Babu amfani na bar wannan shirmen a waya ta kuma duk sanda kika sake mun magana Halima ranar sai munyi fada dake."
"To ai shikkenan dama ni bance dole ba na daina." Tafada tana masa wani sihirtaccan kallo wanda kana ganin kallon kasan na tsantsar soyayya ne....
Halima kuwa na ganin Sadam a Online sai ta turo masa voice note......."Sweet Hart barka da yamma ya aiki yau naji dadi da farin ciki iyeyanmu sun tsaida maganar auranmu ga pictures dina nan nasan zasu d'ebe maka kewa."
Takaici ya kamashi da jin voice note din......Sayyada ma taji haushi amma sai tayi shiru kawai tana sauraran amsar da zai bata.
_"Lafiya Ke Halima ashe bakiji gargadin da nayi miki ba ko? kina so muyi rabuwar rashin mutunci dake ko? shin wai ni kadai ne namiji a duniya da zaki makale kice dole sai ni wallahi wallahi wallahi! kiyi gaggawar zuwa ki warwarw matsalarki da kanki domin kika sake suka daura wannan aure kece zaki sha wahala ranar da suka daura auran a ranar zan sake ki!!! Kin san halina dai sannan kina maganar pictures dinki bana so domin nayi deleted dinsu ina da mai d'ebe min kewa wanda fuskarta kawai na kalla ta isa na manta da cewar akwai sauran mata irinku a duniya saboda haka ki samawa kanki lafiya."_ Yana gama maganarshi ya tura mata kuma bai kashe data ba sai da ta bude ya tabbatar ta gani kana yayi blocking din numbarta ya kashe datarsa.
Sayyada jikinta ne yayi sanyi sai kuma ta soma jin tausayin Halima ance ciwon 'ya mace na 'ya mace ne tuntuni ta fahimci irin son da takewa Sadam shekara da shekaru taki aure saboda shi sam bai dace suyi irin wannan rabuwar ba kuma ita laifinta ne data nace tunda mutum yace baya sonka ai sai ka hakura amma saboda rashin zuciya kayi ta naci haba! halin wasu matan sai su wallahi.
Halima ta gama sauraran voice note Sadam sai kuka ya kece mata ta dinga dukan hannun kujere tana fad'in"Idan kaine autan maza Sadam na hakura da kai koda zan dawwama banyi aure ba zan zauna haka daga yau na futa daga rayuwarka." Kuka take sosai jikinta na kyarma nan mahaifiyarta ta sameta ta tsaya tambayar abunda ke damunta karya ta kirkiro tace kanta ne ke mata ciwo Hajiya Fulera taje ta kawo mata magani tasha.
****
To bayan sati biyu da faruwan al'amarin Halima taje ta samu mahaifinta da maganar cewar ita sai maganar auren dake tsakaninta da Sadam ta janye bata sonsa ta hakura.
General ya shiga mamako sosai yace taje zai samu Sadam din zasuyi magana.........Waya ya kira Sadam din yaje gida ya sameshi sai yake fada masa abunda Halima tace kan maganar auransu...
Sadam yayi shiru bashi da abun cewa
General Yace."Ai idan fada kukayi ba irin wannan hukuncin zaku yanke ba yanzu bari na kira Haliman tazo sai nayi muku sulhu." Sadam yayi shiru baice komai ba.
General ya dauki waya ya kira Halima minti uku sai gata tw shigo palon general yace."To gaki ga Sadam din sai ki fada min abunda ya hadaku har kika fadi wannan magana.
"Dady ni dai nace na janye maganar aure dake tsakaninmu dashi insha Allah zan kawo maka mijina sannan babu wani abunda ya hadamu dashi kawai na daina sonsa ne."
General Yace."To ai kanki kika cuta shashasha da har kike wani kumbure kumbure babu laifin tsaye bare na zaune kice kin janye maganar aure ni ba zanyi miki dole ba abunda kike so shi za'ayi shikkenan maganar auranki da Sadam ta ruguje sai ki kawo wanda kika sake za'bowa." Tace."Insha Allah."
General Ya kalli Sadam da yake ji tamkar anyi masa albishir da gidan aljanna saboda farin ciki yace."Kayi hakura Sadam haka Allah yaso kaji ko Halima Allah ya kaddara ba matarka bace amma naso ta aureka nasan sa tayi dacen miji."
Sadam! yace."Babu komai Yallabai Allah ya sa haka shi yafi alkairi." Ya amsa da "ameen." Kana sukayi sallama da juna.
Tun a mota Sadam ya turawa Halima kalmar godiya yaji dadi da bata sanar da mahaifinta cin kashin da ya dinga yi mata ba da da wane idon zai kalleshi......Cike da farin ciki yake draving har ya isa gidanshi
Sai da yaci abinci ya huta tukkuna, tana kwance a jikinsa yake fada mata yanda sukayi da general da 'yarshi..........Sayyada taji wani farin ciki na zuryatar ta tace"Yanzu dai maganar aure ta rushe kenan."!? yace."Kwarai kuwa sai ki sake mike kafafunki a gidan Sadam ni kuma nayi miki al'kawarin zama dake ke d'aya." Ta sanya hannu ta sakalo wuyanshi tana sumbatar bakinsa "Nagode Yayana Ubangiji Allah ya bani ikon daukar nauyinka." Ya amsa da "ameen." Yana kokarin kamo bakinta tayi saurin bude masa yasa nasa suka fara tsotsar bakin juna.
****
Rayuwa kenan Sayyada da Sadam sun zama tsintsiya madauri daya hankalinsu ya kwanta sosai suna rayuwarsu cikin kwanciyar hankali da kaunar junansu......Sayyada ta haihu lafiya ta samu da namiji shima kamar su daya da Sadam Sadam ya sanya masa sunan mahaifinsa Auwal suna kiranshi da dady, yanzu haka wattaninshi tara yayin da Asalamiyya ke da shekaru biyu tuntuni ta dawo hannun iyayenta kasancewar Sayyada ta kammala karatunta bayan haihuwarta da 'yan kwanaki sai ta lalla'ba Mammah ta basu Asalamiya da kyar ta amince ta basu domin itama ta sha'ku da yarinyar sosai......Bayan 'yan wattani da dawowarta hannunsu ya sanya ta a makaranta dake kusa dasu.
Halima kam can Nijer taje tayi aure inda ta auri dan gidan wan mamanta wanda yayi masifar matowa akanta yanzu haka har ta haihu itama kuma suna zaman lafiya da mijinta.
Alhmadullahi Girma da daukaka na Allah ne duk abubuwan da suka dinga faruwa ga rayuwar Sadam da Sayyada da sanin Ubangiji sannan tun kafin suzo duniya kaddararsu take rubuce a allonsu masha Allah dukaninsu sun dauki kaddara kuma sunyi biyyaya ga mahallici dai-dai gwargwado dama kuma hausawa nacewa bayan wuya sai dadi......Wadata gami da nutsuwa da kwanciyar hankali sun tabbata a zamantakewar auransu Allah ya albarkace su da haihuwar yara uku duk maza Asalamiya ta zama kallabi tsakanin rahuna........
*Auwal* shine na farko *Sani* na biyu *Salisu* na uku yara duk sun girma kasancewar tazar dake tsakaninsu ba wata mai yawa bace haka Sayyada ta dinga haihuwa a kufe a kufe yanzu dai ta dan samu hutu inda shi kuma gogon ya damu shi dai kai ta cigaba da haihuwa har sai tayi dozin sannan ita kuma tace bai isa ba sai ta huta rigimar da suke ta fafatawa dashi kenan.
Sadam ya samu 'karin girma a gurin aiki Ya sake samun daukaka sosai Najeria kanta tasan da zaman *Col.Sadam Auwalu Dabi* 'Kasar Najeria na mutukar alfahari dashi inda ko wane taro za'ayi na jami'an tsaro sai an gayyace shi kuma shima yakan bada gudumarwarshi da jikinsa da aljihunsa.....Ya 'kara girma da kwarjini da haiba kana ya sauya wani dan'kareran gida dake unguwar badarawa Ya biya su Baba Ladi hajji sune dakin Allah sunyi dawafi! Baba Ladidi har da kuka tana mamaki ashe dai tana da rabon zuwa kasa mai tsarki aikuwa ta dinga zabga masa addua shi da iyalinsa.
*Bayan shekaru goma*
Abubuwa da yawa sun faru masu dadi da marasa dadi cikin marasa dadin shine mutuwar Suleiman data Baba Marka wanda ya kasance ta'kin lokaci kad'an a tsakaninsu......Hakika mutuwar wad'annan bayin Allah ta girgiza su ba d'an kad'an ba......Mussaman Baba Ladidi ta rikirkice da rikicin tsufa Allah Sarki yanzu ma ba kowa take ganewa ba, Allah sarki jiya ba yau ba.
Yana zaune a katafaran palon shi loptol ce gabanshi yana dubawa idanunsa sakaye da farin gilashi ta shigo palon cikin shiga ta alfarma ta kara 'kiba dai dai misali ta kara kyau da kwarjini idan ka kalleta ba zaka ce ta haifi dan shekara goma sha biyu ba kullum kamar sabuwa take a idon mijinta.
Ta ajiye lemon dake a hannunta kan teble din dake gabanshi jikinshi ta zauna tana wani marairaice fuska ya cire gilashin dake fuskarshi yana watsa mata kallon lov......"Baby irin wannan gayu haka? kice kawai in aje abunda nakeyi akwai labari."
Gira ta d'aga masa ta lumshe idonta a hankali ta sanya hannu ta kwance igiyar pyjamas din dake jikinsa kirjinsa mai yalwace da gashi ya bayyana ta shiga shafawa tana lumshe ido......"Baby ka bar aikin nan haka ka tashi muje kaji."! a sangarce ta fad'i maganar.....Jikinsa ya soma kyarma ya dan ture loptop din gabansa ya riketa da kyau yana matsa mazaunanta a hard'e yace''Ko baki fad'a baby ba zan iya komai ba a halin yanzu 'kamshin jikinki ya d'imauta ni." Murmushi tayi ta sumbaci goshinsa tace"Muje akwai tanadin da nayi maka." Jiki na kyarma ta dauketa cak suka nufi daki, suna tafiya yana lasar fuskarta sai dariya take masa shi kuma bai fasa ba duk ya wani susuce!!! Huuuuuu! Wannan soyayya tasu sai su *Sadam Da Sayyada Alherin Allah!*
*Tammat bihamdullhi*
_*Allah ka yafe min kusakuraina dake cikin wannan book din Sa'konnin da nake so su isa Allah yasa su isa inda nake so......Allah ka sa damu da Alheri ni daku masoya ba pls ku dauki abu mai amfani ku watsar da mara amfani.....Nagode kwarai masoya