Showing 84001 words to 87000 words out of 142497 words

Chapter 29 - NI DA YAYA SADAM Complete Document by Binta Umar Abbale.txt

09 Dec 2024

50469

saboda gudun wad'annan mutane gashi mutane na rad'e rad'in cewar shi yaron Ma'akaici ne na tsaro haka kawai ba za ka sanya azo ya tashi garina da ya'ki ba.....Ina mai baka Umarni kayi maza ka fitar min dashi daga garina idan ba haka ba kuma to kaima zan kore ka daga garina."


Jatau! Yace."Yallabai a gafarce ni nasan nayi kuskure ayi hakuri a dan bani lokaci kankani insha Allahu zan sallami wannan bawan Allah dake gidana."


Mai gari yace." Anyi maka uzuri Jatau! dalili kaima kana hidimtawa gari na baka wata uku kacal ka futar min da wannan bako daga garina."


Jatau yace."Insha Allahu ranka shi dade godiya nake." Sallama yayi da fada ya kama hanyar gida yana zancan zucci akan Sadam din.........


Ranar litin da sassafe suka shirya tsaf Munkaila ya shirya Sadam! cikin yadin toyobo ya sanya masa hula irin ta fulani.....Bakin kasuwa ya fita ya samu texi irin wanda suke zuwa sarin kayan miya na gwari ya nemi alfarama gurin direba ya futar dasu cikin gari in yaso sai su biyashi......A take suka tsadance dashi Yaje ya tawo dasu hannunsa rike dana Sadam! suka karaso gurin.....Ya bude mota ya turashi ciki Sadam sai kalle kalle yake yi tunda ya shiga gidan Jatau bai fito ba sai yau kallon garin yake sosai da sosai kana ganinsa zaka gane fai san inda yake ba bai ma san me yake ciki ba.....Jatau ya shiga ya zauna direba ya kunna motar suka bar gurin.....
NI DA YAYA SADAM


NA
BINTA UMAR ABBALE


36
'Kwararran likita wanda ya danganci 'bangaran 'kwa'kwalwa shine ya tsananta bunkicensa a kan Sadam! a take ya gano Sadam! din ya samu matsalar 'bacewar tunani sakamakon buguwar da kanshi yayi yasa ya mance kansa ya mance waye shi ya mance komai da komai na rayuwarsa ya dawo tamkar yaron da aka haifa yau wanda komai ya gani sabo ne a gurin sa.....Dr Abdullahi yayi wa Malam Jatau bayani kamar haka.


"Malam wannan bawan Allah bashi da ta'bin hankali kamar yanda kuke zargi lafiyarsa kalau sai dai ya samu 'bacewar tunani sakamakon wani abu da ya faru dashi na buguwar kai ko kuma makamancin haka, yanzu babban abunda zaku mayar da hankali akansa shine ku dinga yi masa labarin abubuwan da suka gabata a lokacin da yake da tunaninsa kana kuma ya zamana kullum wani na kusa dashi na nuna masa abubuwan da yake yi yau da gobe wanda ake so ya kasance tare dashi makusancinsa in yana da mata to ita zata daukin wannan nauyin insha Allahu kuna nuna masa abubuwa da yawa zaku wayi gari guda tunaninsa da hankalinsa sun dawo dai-dai."


Jatau! yayi shiru yana nazarin maganar likitan yace."To yanzu babu wani magani da za'a bashi wanda zaiyi saurin dawo dashi hayyacinsa da wuri."


Dr Yace."Akwai magani amma gaskiya mu nan bamu dashi dole sai an fita 'kasar waje za'ayi masa aiki in da yiwuwar ya dawo dai-dai sai ya dawo amma babban maganin wannan matsala shine wannan shawarwarin dana baku."


Jatau! Yace."To shikkenan Likita mungode kwarai insha Allahu zamu yi iya bakin kokarinmu."


Likita ya had'awa Sadam! magani masu kyau na sanya kuzari da cin abinci Jatau! ya biya kudi Munkaila ya riko hannunsa suka fito Sadam! sai kalle kalle yake a gurin tamkar wani wawa ya koma komai nashi babu kuzari sai dai ido.


Bayan Fitar su Jatau! likita ya cigaba da aikinsa tv dake manne a bango na ta aiki ya d'aga kanshi ya dan kalli tv sai ga fuskar Sadam! da kayan Soja mai labarai yana fad'in" Jama'a wannan shine Captain Sadam! Auwal 'Daya daga cikin sojojin da aka tura aiki Maiduguri wanda 'Yan bindiga suka kashe shi suka kuma jefar da gawarshi yau tsawon kwanaki bakwai kenan da afkuwar al'amarin Idan da wanda yaga wani abu daya dangance shi to sai ya kira wannan numbar domin karin bayani."


Da sauri Dr din ya mike ya isa bakin tv din yana so ya tabbatar Anya wannan fuskar ba fuskar mara lafiyar nan ne da suka fita ba.......Hotonan Sadam! ake haskowa wani da uniporm wani kuma da kayan gida a take Dr ya gazgata shine da sauri ya dauki wayarsa ya saka numbar da suka bayar......Ya hau kira minti biyu aka daga wayar baki na rawa yace."Yallabai barka da aiki." General ya amsa da barka dai....Yace."Yanzu ina kallon labarai naji ana cigiyar soja mai suna Sadam."! General ya mike tsaye da gaggawa yace."Eh kwarai hakane shin kaga wani abu da ya dangance shi ne."? Dr yace."Yallabai shi kansa na gani wani mutumin kauye ya kawoshi asibiti na dubash."


General Yace."Da gaske kake dr wane gari kake kuma wane asibiti ne."? Dr yace."Babban asibitin dake plateau ni likita ne dake duba marasa lafiyar kwakwalwa Mutum ya kawo min shi kan in duba shi suna zargin bashi da hankali to sai da na tsananta bunkice a kansa na gane ba rashin hankali yake ba kawai ya samu matsalar shafeear tunani sakamakon buguwar da kansa yayi shine tunaninsa ya koma na yara 'kanana na basu shawarwari sosai dangane da yanda zasuyi lafiyarsa ta dawo."


General Yace."Babu shakka jikina na bani Sadam! ne dama ni tuntuni nake zargin yana raye bai mutu Allah yasa kasan wani abu da ya danganci mutanan da suka kawo shi." Likita yace."Yallabai wallahi ban san komai ba sai bayan sun fita da kusan minti talatin sannan naga abunda ke da akwai amma ina zargin kamar mutunan daga yanki wannan gari suka fito wato jos idan an tsananta bunkice ba za'a rasa su a cikin 'kauyinka dake garin ba."


General Yace."Hakika ban ta samun labari mai dad'i irin wannan ba likita mungode kwarai da gaske za kuma mu shirya zuwa garin domin mu tsaurara bunkice ko Allah zai sanya a dace.."


****
Jatau! ya tara iyalinsa ya shaida musu yanda sukayi da maigari mutukar bai sallami Sadam nan da watanni uku ba to babu shakka zai bar masa garinsa sannan ya shaida musu maganar da Dr yayi kan Sadam din dole a dinga kula dashi ana sanya shi nishadi saboda haka kowa sai ya daura d'amara dawo da hankali da tunaninsa."


Harira tace"Baba ni zan dinga yi masa tatsuniya." Munkaila yace."Ni kuma zan dinga zuwa gona dashi ina koya masa ayyuka." Abu da Hansantu suka ce mu kuma zamu dinga masa kula dashi insha Allah." Jatau! yace."To masha Allah Allah ya taimake mu kan abunda mukayi niyya."
Munkaila ya mike ya nufi bukkar da suka sauki Sadam! din ya futo da kayan sojojinsa ya zube masa a gabansa yana d'addaga masa su.....Sadam ya tsurawa kayan ido yana kallonsu shima sai ya sanya hannu yana dad'dadagawa yana murmushi.


Munkaila yaji wani abu a cikin aljihun wandonsa sai ya zura hannu ya fito da kayayyakin ciki walet dinsa ce da wayarsa sai agogonsa suma duk ya zube masa a gabansa Sadam! ya d'auka yana duddubawa yana ta so ya fahimci wani abu dangane da kayan amma ya kasa sai ya dauka yana wasa dasu kamar yaro karami.


Munkaila Yace."Baba wannan wayar tashi zata taimaka mana sanin daga ina yake duk da cewar bai zam lallai wayar tayi aiki ba amma zan je bakin kasuwa idan masu chaji sun kunna inji sai su sanya in gani ko zatayi idan ba tayi ba sai a cire layin akwai abokina Haruna dake amfani da waya sai in bashi ya sanya a wayarshi tanan zamu samu numbar wani daga cikin danginsa sai mu kira mu sanar dasu halin da ake ciki."


Jatau Yace."Babu shakka wannan shawara taka tayi kyau Munkaila yanzu ka tashi kaje bakin kasuwar ko Allah zai sa a dace."


Munkaila ya yunkura da wayar a hannunsa Sadam! ya dam'ke masa hannu yana kokarin kwace wayarsa.


Yace."Ka bari yanzu zan dawo maka da ita."
Shima yace."Ka bari yanzu zan dawo maka da ita." Munkaila ya kalli Jatau yace."ka gani ko baba ya'ki sakin wayar." Sadam! ya maimaita abunda munkaila ya fada


Jatau! ya dinga rarrashin Sadam ya saki wayar Sadam! ya sha kunu ya'ki sakin wayar Harira tace"Baba ku kyaleshi mana watakila ya soma dawowa hayyacinsa tunda ku kaga ya'ki sakin wayar." Abu tace"Kawai kai Munkaila yi dubara ka cire layin sai ka bashi wayar." Aikuwa haka akayi Munkaila ya cire layin ya bashi wayar.....Ya 'karba yana murmushi sai shafa fuskarta yake.


*****


"Haba Sayyada wannan wace iriyar rayuwa ce kike so ki jefa kanki a cikinta? Wannan yaro dai da kullum kike kuka akansa ya riga ya mutu ba zai dawo ba, shi da ya tafi baiyi gaggawa hakanan mu damu ke zaune a duniyar ba muyi jinkiri ba muna jiran lokaci ne mutuwa rigar kowa ce Allah ya dauki ran Sadam a sanda yaso sai kiyi hakuri ki bishi da addua itace magani ba ki zauna kina kuka kina kara masa azabah ba." Baba Ladidi ce ke yiwa Sayyada wannan maganar.


Hanci ta sha'ka! ta goge hawayen fuskarta tace"Baba ku daina cewa Ya Sadam! ya mutu nifa kullum muna tare dashi sai yazo munyi hira munyi wasa da dariya kuma yace."Zai dawo insha Allahu."


Baba Marka ta sanya salati tana tafa hannu tace"Anya Sayyada anya kuwa karfa kije ki zauce! ta ina kikaga wanda ya mutu ya dawo.! ai in an mutu ba'a dawowa sai a darul salam za'a had'u."


Tace."To wai ku da kuke wannan surutan kunga gawarsa ne? ku bari kuga gawarsa sai ku tabbatar da abunda kuke zargi Ko jiya naji Abbah suna waya da shugabansu su Sadam! din na gurin aiki kan cewa an samu labarin an ganshi tare da wasu mutane a garin jos ko fitar da kukaga Abbah yayi can suka nufa domun bunkitawa."


Baba Ladidi tace"Kaji wata magana ko? ai dama yanzu mutane zasuyi ta yad'a jita jita m saboda kawai su samu kudi ni dai nasan wannan yaro ya rasu tunda dai ita mutuwa ba'a wasa da ita shima Abban naku wahala ce bata ishesu ba shiyasa suke daukar maganganun mutane kawai ya zauna a gida ya cigaba da yiwa yaronsa addua domin itace ta dace dashi, Jiya da na kusa raba dare ina yi masa addua ina kwantawa bacci nayi mafarki dashi yana cikin walwala da farin ciki yayi tayi min murnushi alamu sun nuna yana cikin rahamar Ubangiji."


Sayyada tace"Addua dai ba'ace ki fasa yi masa ba amma ki daina cewa mijina ya mutu yananan a raye bai mutu ba." Baba Ladidi tace"Kece mahaukaciya ai da kika kasa tawakkali Iyayensa ma sunyi sun hakura amma ke kin'ki kullum kuka da rashin cin abinci kanki zaki cuta shi yana can Allah ya sadashi da matan aljanna hurul'ini."
Takaici ya sanya Sayyada fashewa da kuka ta kwanta bata sake cewa komai ba Baba ladidi da baba marka suka dinga yi mata fad'a da kawo mata misalai Sayyada na jinsu tayi shiru da bakinta Haka Mammah ta shigo dakin taji abinda ke faruwa itama ta zauna tana mata nasiha Sayyada jinsu kawai take itafa da ba dan tasan hukuncin wanda ya kashe kansa ba to da itama ta kashe kanta ta huta da wannan kunci da damuwar da take ciki.......Sule ne ya shigo dakin hannunsa rike da key yana sanye da kananun kaya yayi kyau sosai kamshi sai tashi yake a jikinsa.


Suka gaisa da mutan dakin ya kalli Sayyada dake kwance tana kuka magana yayi mata tayi masa banza yayi yayi ta kulashi ta'ki kallonsa mugun haushinsa takeji har yanzu bai mata gaisuwar mutuwar mijinta ba.


Baba Ladidi ta dinga surfa mata bala'i "Don Ubanki ba gaba yake dake ba har zai shigo daki ki kasa gaishe shi yana miki magana kina wulakanta shi shine ya kashe miki miji ko kuwa? shashasha mara tawakkali kawai." Sayyada kukunta ya tsananta a guje! ta mike ta shige kuryar daki ta afka gan gado kuka take ranta kamar zai futa........Tsayuwarsa taji a kanta ta dago da sauri suka hada ido dashi....murmushi ya sakar mata tayi bala'in shan kunu tana dauke kanta


Yace."Baby me nayi miki kika tsane ni na lura tunda Sadam ya mutu kika daina amsa gaisuwata." Hannu ta daga masa da sauri tace"Yaya Sulaiman ina ganin mutuncinka wallahi kar ka sake cewa mijina ya mutu bana so."


Ya bude baki yana kallonta tamkar zaiyi magana kuma sai ya fasa yace."To shikkenan tunda bakya so ba zan sake ba baby amma ki dinga amsa gaisuwata Sadam! kuma bani na kashe shi ba lokacinsa ne yayi."


Tsaki taja ta mike da sauri ta bar masa dakin.....Ya bita da kallo cikin mamaki tabbas zai sha fama da yarinyar nan kafin ta dawo gareshi yanzu ya lura ta dauki karan tsana ta dora masa amma yasan yanda zaiyi mata,


Sulaiman na fita kira ya shigo wayarsa koda ya duba sai yaga sabuwar numbar sharewa yayi bai daga ba har ta katse......Wani kiran ya sake shigowa tsaki yaja ya dauka ba tare da yayi sallama ba.


Munkaila Yace."Salamu alaikum Halo." Sule yace."Wa'alaisalm da waye nake magana."? Da sauri Munkaila yace."Kana magana da Munkaila Jatau mai jaki daga garin jos cikin 'Kauyen 'Dan marke." Sule yace." Okey lafiya dai ko."?


Munkaila Yace."Yawwa kana jina ko? Yau tsawon kwanaki uku muka tsince wani mutum a cikin rafi ruwa ya kawoshi bakin ga'ba koda muka duba sosai sai muka gane cewar soja ne saboda tufafin dake jikinsa.....Tsawon kwana uku ya dawo hayyacinsa sai aka samu matsala bai dawo da tunaninsa ba muka kaishi asibiti likita ya tabbatar mana da cewar tunaninsa ya shafe gabadaya a sakamakon buguwar da kansa yayi bayan mun koma gida ne muna bunkice cikin kayansa muga wayarsa to wannan damar da muka samu ya sanya muka dauki layin nasa muka sanya a wata wayar sai muka ci karo da numbar ka kacal a layin shine muka kira ka domin kayi mana karin bayani."


Tunda sanda Munkaila ya fara bayani Gumi yake tsiyaya a jikin Sulaiman kansa ya dinga sarawa Sadam! bai mutu ba yananan a raye." !? Maganar zucci yake ashe ta fito fili Munkaila yace."Eh kwarai kam yanan a raye cikin koshin lafiya sai dai kuma tunaninsa baya tare dashi."


Zufa! ta ko'ina ke d'iga daga jikin Sule baki na rawa yace."Idan nazo garin jos a ina zan same ku." ? Munkaila yace." Kana zuwa kaje tasha sai kace motar 'kauyen marke zaka shiga idan an saukeka sai ka kira wannan numbar da na kira ka da ita insha Allahu zanzo na daukeka." Sule yace."Gani nan zan shigo mota nazo." kashe wayar yayi a gaggauce ya afka motarsa ya fice daga gidan a guje.....So yake ya gazgata shin Sadam din ne ko kuma wani daban ba wai zaije garin ne don Ya dauko shi ba a'a zai gani da idonsa shin da gaske ne Sadam din na raye bai mutu ba.


Munkaila na gama waya da Sulaiman sai suka yanke shawarar zama su jirashi shi da abokinsa Haruna suka samu wani guri a cikin tasha suka zauna jiran isowar Sulaiman din duk da basu san daga wane gari zai tawo ba amma dai tunda yace musu yana kan hanya zasu zauna zaman jiransa domin kar yazo a samu wata matsalar duk da cewar akwai numbar da zai kira ya same su.


Sulaiman ya dinga sharara gudu kan kwalta burinsa kawai ya ganshi a garin jos to kun san dai tsakanin jos da kaduna babu wata tazara mai tsayi don haka cikin 'kankanin lokaci Sule ya isa jahar plateau kai tsaye ya dauki hanyar kauyen d'an marke....yana shiga tasha sai ya dauki wayarsa ya kira numbar da suka bashi ringing d'aya tayi Munkaila ya daga wayar kasancewar dama wayar na hannunsa yana jiran tsammani.


Sulaima yace."Gani na iso ina cikin tsuhuwar tasha."


Munkaila yace."To shikkenan muma muna cikin tashar sai ka tsaya inda zamu ganka."


Sulaiman yace."Babu damuwa ina tsaye dai-dau wata bishiyar mangwaro akwai mai abinci a gurin." Kai tsaye su Munkaila suka nufo gurin da ya kwatanta musu.


Ganin hamsha'kin Alhaji a jingine da babbar mota ya sanya jikinsu yayi sanyi suka karaso inda yake tsaye suna masa sannu da zuwa.


Sulaiman yace."Ba tare da wani 'bata lokaci ba ku kaina naga inda d'an uwana yake.'' Kofar motar ya bude su shiga shima ya shiga motar ya tashe ta suka nausa cikin kauyen wanda yake da taxara sosai tsakaninsa da cikin gari da bakin kasuwa.


Da kyar Sule ya samu gurin da yayi parking din motarsa suka fito gabadayansu.


Sulaiman ya dinga bin garin da kallo yana ya mutsa fuskarsa wai mutane masu rai ke rayuwa cikin wannan kauyen da ko wutar lantarki basu dashi sai uwar tafasa data cika garin dole kwarika da sauraye su addabesu shi kam ko da lada akace yazo ya zauna cikin garin ba zai iya ba.


Sadam! na zaune kan tabarma a tsakar gida Harira ta sanya shi a gaba tana masa ta tsuniya sai murmushi yake yi yana kallon fuskarta gani yake kamar ya santa sosai yarinyar tayi masa kama da wata yarinya a lokacin 'kuruciyarta.....Harira fara ce tas siririya don har tafi Sayyada sirantaka tana da idanu manya manya fuskarta a mulmula sumul amma kuma bata kai tsawon Sayyada ba kuma Sayyada ta fita yalwar gashi.........."Asalamu alaikum." Sallamar Sulaiman a cikin gida ta sanya Sadam! d'agowa a firgice! yana kallon bakin kofa.
Suka had'a ido da d'an uwansa sai ya 'kura masa ido kurrr! yana kallonsa.


Shi kuwa Sulaiman kallo d'aya yayiwa Sadam! din ya dauke kansa da sauri gabansa ya tsananta fad'uwa tabbas shine! dama ashe da gaske wad'annan mutanan suke ashe dama Sadam bai mutu ba yananan a raye.


Nan da nan ya aro wata fuskar da ba tashi ba had'e fuskarsa sosai da sosai ya zauna a shimfidar da akayi masa sam! ya'ki kallon inda Sadam! din yake.....Hansantu ta kawo masa ruwa cikin kofin silba ya dauke kansa yana ya mutsa fuska Hansatu da Abu suka zazzauna suna gaishe shi, Ya dinga amsawa a ya mutse Abu tace."Gashi kazo malam ya fita sai dai yanzu a kirashi."


Munkaila yace."Dama yanzu nake wannan tunanin.'' Ya kama hanya zai fita Sulaiman yace."Kaga dakata kar ka kirashi ina ganin da kai kad'ai ma Zamuyi maganar ya isa." Munkaila yace."To babu laifi."


Sulaiman ya kalli gefan da Sadam ke zaune ya sake tamke fuskarsa yace."wannan dai ba shine d'an uwana da kuke magana a kansa ba dama nazo ne domin idanuna su tabbatar min nima nawa d'an uwan sunansa Sadam! amma kuma ba soja bane ina so ku kalleni da kyau ku kalleshi idan munyi kama dashi sai ku fada min."


Dukaninsu suka mayar da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login