Showing 135001 words to 138000 words out of 142497 words

Chapter 46 - NI DA YAYA SADAM Complete Document by Binta Umar Abbale.txt

09 Dec 2024

51209

masa hankali yarinyar tayi wayo sosai.....Ganin goma ta kusa ne yasa Mammah korarshi ya sanya rigima wai sai ta bashi baby Asalamiyya tace"Sai ta sake wayo sannan da kyar dai ya fito yana kokarin bude mota ya hango Sule na turo kekensa zai fito shine yaje ya karasa fito dashi Sulaimam ya dinga godiya yana share hawaye, can gurin masu gadi ya kaishi shi kuma ya koma inda motarshi take.


Lokacin da ya isa gidan tayi bala'in galabaita tayi amai har ta gaji ga wani uban zazza'bi daya rufeta tana kujerar palo tana makyarkyata, Har ya wuce ya dawo.


tsayuwa yayi kanta yana kallonta ta dago kai tana kalloshi hawayen da ya gani na fita a idonta shine ya daga masa hankali.....Tsugunawa yayi yana kokarin riketabta fuzge jikinta sai jikinsa ya soma kyarma jin yanda jikinta ya dauki zafi rau!! A rikice yace."Baby menene baki da lafiya."? Shareshi tayi ta cigaba da matse fuskarta ya sanya hannunsa ya tallafo fuskarta duk ya shiga damuwa" Me damunki me yasa baki fada mun baki da lafiya ba."


"Ni ka kyaleni sau nawa ina kiran wayarka kana sharewa ni za rainawa hankali." Tafadi maganar tana buge hannunsa.


"Sorry ina aikine shiyasa ban dauka ba ayi hakuri kinji." A marairace ya fadi maganar.


Yunkurawa tayi zata mike ya rike hannunta "Baby baki da lafiya sosai ga jikinki nan ya dauki zafi muje clinic a duba ki."


"Ni ka kyaleni." Tafada cikin jin zafin ciwo.....Yace."So kike na mutu kenan ai koma nawa ya tsaya yanzu sai naga kin samu baby kece fa rayuwata."


Taji dadin maganarshi yace."ba zan mayi wanka ba tashi kawai muje a duba minke idan na dawo sai nayi."


Girgiza kai tayi tace"Kawai kayi shirinka a tsanake kaci abinci tukkuna."


Yace."Kin amince da hakan."? Daga masa kai tayi sai a mike ya nufi dakin tabi bayanshi tana taimaka masa yace."Ki zauna yau na huttasheki baby."


"A'a ka kyaleni na samu ladana." murmushi yake yana kallonta a hankali yace."Allah yayi miki albarka.


Wanka yayi ya fito ya shirya cikin kananun kaya dama tana sanye da hijab sai kawai suka rike hannun juna suka fita shine ya bude mata motar ta shiga ya zauna mazauninsa kana yayiwa motar key suka nufi wani pravite hospitl dake kusa dasu.


Gwajin fitsari akayi mata wanda ya nuna positive ma'ana tana da ciki gashinan ma ya kwana biyu zaiyi wata biyu da kwanaki.....Da jin wannan magana Sadam ya rikice a gaban dr din ya 'kam! 'kame ta yana murna sai washe baki yake kamar wanda akayiwa albishiri da gidan aljanna.....Dr ya dinga masa dariya shi ya dauka ma bai ta'ba haihuwa sai da Sayyada tace masa ai suna da wata 'yar sannan......abunda yakeyi ya sanyata mamaki itama duk ya rasa inda zai sanya kansa sau godiya yake musu ita da dr din kamar sune suka bashi haihuwar...... Dr ya bata shawarwari wanda zasu amfaneta kana sukayi masa sallama


A cikin mota fad'i yake."Kome babyana yake son yaci ki fada mun zan siya masa kai gaskiya naji dadin wannan albishiri babyna zata haifa mun yaro Allah ya ingata baby Allah ya rabu lafiya."


Tausayi ya soma bata babu shakka Ya Sadam na son haihuwa ta inda suka sha bam! bam! da Sulaiman kenan.......Har suka isa gida yana mata addua da kuma fatan Allah ya rabata da cikin lafiya.


Yafi sati biyu bai take ba yana dai ta hakuri ba wai dan baya bukata ba asalima kullum da bukatar yake kwana yake kuma tashi ko gurin aiki yaje sai yayi da gaske yake tabuka abun kirki sha'awar Sayyada na nema ta kasheshi.


To ita dama haka take so kullum bata da wani aiki sai bacci idan ya fita kenan sam ta kasa gane halin da yake ciki ballanta ta taimaka masa ita dai tunda ya daina damunta shikkenan.


Yau dai ko minti talatin baiyi da fita ba ya dawo saboda ya kasa yin komai sai layi yake mararsa ta cika tayi fam! sai murd'a masa takeyi...


Bugun 'kofarshi ne ya tayar da ita ta mike da sauri tana tambayar waye......Muryarshi ta juyo a hankali yana fad'in"Baby bude nine.".


Ta bude kofar da sauri tana kallonsa.....Ganin yanda kwayar idonsa ta jirkice sai tasha jinin jikinta tace"Ya Sadam ya ka dawo ko ka manta da wani abun ne."? Girgiza mata kai yayi ya shige ciki yana fad'in"Bacci nake ji sai anjima zan koma."


Tabi bayanshi da kallo har ya shige daki.


Jikinta yayi sanyi tsaf ta gane abunda ke damunsa anya bata so kanta ba kuwa Ya Sadam mabukaci ne sosai yayi mata kawaici tsawon sati biyu bai nemi wani abun daga gurinta ba yana da kyau ta duba matsalarshi Dakin tabi shi ta tarar dashi zaune gefan gado dagashi sai boxer ya dafe kansa da hannu.


"Ya Sadam." tafada lokacin da take tsaye a kanshi....
Dago kansa yayi yana kallonta taji ba zata iya jurar kallon kwayar idonsa ba dauke kanta tayi tace"Meke damunka."?


Yace."Me kika gani."? Tace"Babu komai.." Yace."Kaina ke ciwo kadan na fada miki kuma bacci ne idan nayi zan samu sauki."


Tace"To ko in kawo maka panadol." Yace."Jeki kawo." Jiki a sanyaye ta juya ya bita da kallo yana rintse ido kamar da gayya take murguda mazaunanta, ya sake jin wani irin suka a kasan mararshi.


Ta shigo hannunta rike da maganin ta mika masa kana ta dauko masa robar ruwa.....Baiyi musu ba ya kar'ba yasha ya kwanta yana kallonta...
Itama shi take kallo sai ya saki murmushi a hankali yace."Ya babyna hope yana cikin koshin lafiya kuma bai saki amai ba ko."?


Kai ta d'aga masa tace"Da sauki dai yau."


"God haka ake so." yafad'a yana rintse idonshi hade da cije le'be ta riga ta gama fahintar sa a duk lokacin da yake cikin sha'awa ya dinga cijar lps dinsa kenan....


Zamanta kusa dashi ya sanya ya zabura! tsikar jikinsa na mikewa yace "Baby pls jeki palo kiyi zamanki kinji ko"


Kai ta girgiza masa tana marairace fuska....."Oh my gud."! hakan ma da tayi sai ya sake rikita shi yace."Kinga baki da lafiya zamanki kusa dani zan janyo abubuwa da yawa ki tashi daga kusa dani.


Hannu tasa a kirjinsa tana shafa kwantaccen gashin dake gurin tana matsa nipples dinshi......Ya sauke wata gawurtacciyar ajiyar zuciya yana nishi!!! bab....baby bakiji abun....abunda nace ba ko? kina so in danne ki yanzu."


A hankali tace"Eh." Ya bude idonsa da sauri yana kallonta....Gira ta daga masa a sangarce tace''Ka danne ni ina so."! Yace."Da gaske."? kai ta daga masa tana cigaba da shafa kirjinsa....."Alhamdullahi yafada yana shafa gefan fuskarta.


Rigar jikinta ta cire dake karama ce ta tun kafin ta cire breziyar ya gigice ya kai hannunsa kan bombos din ya matsawa 'yar 'kara ta saki tana ture hannunsa, a kid'ime! yace."Baby bari na ta'ba ko bakya so ne."? Tace"Da zafi kake." Yace."Okey bari in hura miki ya kai bakinsa kan bombos din yana hurawa ta dinga kyarmar jiki da sauri ta rungume kanshi dake gurinshi shi kuma sai ya rike bombs din da kyau yasa baki yana shan guda yana murza guda......Rikicewa tayi ta dinga wani irin nishi tana sosa masa sumar kanshi shi kuma sai lumshe ido yake yana kara rikita mata lissafi.......Sai da sukayi wassanin soyayya kana suka shiga biya junansu bukata.....bai yarda ya hau kanta ba stayel suka dinga yi iri iri har suka samu gamsuwa da junansu.


*Littafin na k
NI DA YAYA SADAM


BINTA UMAR ABBALE*


58


Da jin labarin cikin da Sayyada ke dauke dashi sai su Baba Ladidi suka dinga murna suna fad'in"Dama rabon anan yake addua suka shiga yi mata da fatan rabuwa dashi tafiya......Mammah ma tayi farin ciki sosai kullum sai sunyi waya da Sayyadar tana tambayarta lafiyarta dana babyn dake cikinta.


Cikin wannan yanayi suka fara jarrabawa haka dai take daurewa tana 'kwarara jikinta tana zuwa makaranta saboda ta lura da take takensa idan ta nuna gajiyarta zai iya cewa ta zauna a gida kullum shike jigilar kaita ya daukota watarana yayi ta mita wai tana wahalar masa da babynsa ita dai lallabashi takeyi kar ya hanata tasan zai aikata dama tuntuni ya fada mata ko ta kammala karatunta to kar tasa rai zatayi aiki tace"Eh taji." Haka suka rabu saboda sam bata son duguwar magana.


Kwanashi biyu da dawowa daga kano yaje ya kaiwa su Jatau ziyara ranar da ya dawo da yamma general Abdulsalam ya sauka dan haka bracck din ya nufa suka tar'beshi da kyau kana suka rakashi har gidanshi.


General yace ya tsaya yana son su tattauna wata magana mai muhimanci Sadam duk hankalinsa na gurin iyalinsa sai dai ya zauna a katafaran palon nashi yana sauraran fitowarshi sai kawai Halima ta fito cikin wani uban less mai ruwan zuma sai walwali take tasha make up jiki duk ya d'aye da mai sai walwali take na gwal......Ya gyara fuskarsa sosai ta karaso kamar zata zauna a jikinsa sai kuma ta fasa ta gaisheshi tana wani marairacewa.


Yace."Halima ashe baki daina wannan shafe shafen ba ko? wanin irin kallo tayi masa tana matsowa jikinsa a marairaice tace"Sweetheart sam baka damu dani ba kwata kwata na lura ma bakayi murnar ganina ba ni kadai nake haukana akan ka baka damu da halin da na shiga ba na rame na lalace dik akan sonka na kori duk masoyana akanka kai kuma hankalinka nakan matarka wai ashe har aure kayi ka haihu kuma bayan ka dawo hayyacinka maimakon ka nemi sai ka share babina ka cigaba da sabgarka da matarka ni ina can ciwon sonka zai kasheni." Tana kuka ta karashe maganar.


Tausayi ta bashi yace"To menene abun kuka kuma dama tuntuni ni banyi miki alkawarin aure ba kuma nasha fada miki cewar ni bana da ra'ayin auran mace sama da daya kiyi hakuri ban munafurceki ba ki samu miji kiyi aure."


Kuka take sosai tana kallonshi tace"Yanzu sakayyar da zakayi mun kenan ba zakayi min adalci ba annabi fa cewa yayi ku auri hudu in kuna da iko kai kana da ikon aurena amma saboda kana gudun bacin ran matarka kace baza ka aureni ba me nayi maka."


Yace."Ki fahimci wani abu halima Sayyada ba ta isa tasa na sauka daga kan kudirina ba duk abunda nakeyi insyi bisa ra'ayina ba na wani ba kuma ni banga macan da zanji tsoro ba."


Tace"To idan ka cika namiji tsayayye ka aureni shine zan gane baka jin tsoron matarka." Kafin yace wani abu general ya fito cikin kayan shan iska fuskarsa a sake ganinsu zaune suna hira sai ya dauka hirar soyayya suke yace."Kuzo muci abinci tukkuna sai mu zauna mu tattauna maganar da Zamuyi.


Sadam yasha jinin jikinsa dajin furucin General din amma baiyi masa musu ba ya sauko kasan kafet ya zauna Halima ta zuzzuba musu abincin sunaci suna hira Hjy Fulera ta fito cikin shigar alfarma ta zauna itama tana cin abincin a cikinsu sam basa kunyar Sadam! din a matsayinsa na surukinsu Eh surukinsu mana tunda su duk a tunaninsu akwai kyakykyawar soyayya a tsakaninsa da 'yarsu.


Sai bayan sun kammala cin abincin ne general ya kalli Sadam a nutse yace"Masha Allah Allah ya dawo dani lafiya hakika naji dadin namijin kokarin da kayi gurin kawo gyara da kore 'barnar dake faruwa a gurin aiki Sadam a ko da yaushe ina alfahari dakai a rayuwa kuma ina maka fatan alkairi har karshen rayuwarka.


Sadam ya amsa da ameeen shima yana masifar kaunar mutumin domin duk wasu manufofi nashi da yake so ya cimma ta bangaran aikin nasu ta dalilinsa ba karamin gudumawa ya samu ba ta bangaran general din.


General ya cigaba da cewa "Alhamdullahi sai maganar da tasa na tsayar da kai gurin nan wacce tun kafin na dawo nake so mu tattauna akanta kasancewar maganar ba zatayi a waya ba bane ya sanya nace sai na dawo tukkuna......Tun ina kasar hindu Halimatu take damuna da maganarka kan tun kafin wannan al'amari ya faru dakai kuka tsayar da magana kai da ita ta aure sai kuma gashi Allah ya saukar da ikonsa akanka sai ta sake tayar mun da maganar bayan bayyanuwarka nace ta bari tunda na kusa dawowa xamu tattauna maganar ni na baka halimatu sabida bani da haufi akanka tabbas zaka iya jagoranta sama da mace daya saboda haka idan ka isa gida sai ka sanar da mahaifinka ni da kaina zan shigo gobe mu tattauna maganar.


Wani irin gumi ne yake tsiyaya ajikinsa me yasa Halima tayi masa haka? me yasa zata hadashi da wanda yake masifar jin kunya a duniya babu iri hallacin da mutumin baiyi masa ba yakan rasa tsakaninsa dasu Jatau waye yafi wani a gurinsa dukaninsu Sunyi masa abunda ba zai taba mantawa dasu ba.....Ya goge fuskarshi da tafin hannunsa cikin kokarin nuna babu komai yace" Godiya nake yallabai Allah ya kara girma kuma insha Allahi ina zuwa gida zan sanar da Abbah abunda kace."


General yace."to masha Allah ubangiji Allah ya sanya alkairi Allah ya tayaka riko." ya amsa da '"ameeen." kana ya mike yana musu sallama Halima kamar ta mutu dan dad'i sai ta mike tabi bayanshi......kamar yasan itake bin bayansa ya dinga sauri ko waiwayo Baiyi ba har ya isa inda ya aje motarshi ya shiga da sauri ya kunna wanda yayi dai-dai da karasowarta gurin "Haba Sadam! wai meye hakane sai kiranka nake kana wulakantan......Kafin ta karasa ya dallara mata wani mugun kallo yana gyada kansa da sauri ta dauke hannunta daga jikin motar ya figeta a guje ya fice daga gidan ya barta tsaye a gurin da sakakken jiki.
[7/9, 2:47 PM] Bintu: Cikin bacci taji shi a jikinta ta bude idonta dake cike da bacci gami da kasala tana kallonshi fuskarta ya shafa yace."Baby yau kin gaji da jirana ko."? Kai ta d'a masa tana yunkurin tashi zaune.


Ya taimaka mata ta zauna sosai tana fuskantarsa "Wai ina ka zauna yau ko kaje gurin budurwarka ne." ? fuska a hade take maganar.


Hannu yasa ya shafa siraran lebunanta yace"Wace budurwa kuma? bayan ina dake na fada miki ke dai ce a gabana yanzu.


"Ta sauke ajiyar zuciya tana kallonsa yace" Ina can gidan general ya rikeni wai dole sai na zauna naci abinci." Murmushi tayi tace"Kace yau abincina zai sha kashi tunda ka ciko cikinka."


Yace"Waye ya fada miki? ai ban wani ci abincin kirki ba burina kawai in dawo gida nasan ba kici abinci ba kina jirana.


Tace"Kamar ka sani kuwa wallahi na gaji da zaman palon na dawo d'aka na kwanta bacci kuma ya daukeni.......Yace "Tashi muje kici abinci tun kafin babyna ya fara kuka." mikewa tayi tana dariya ya rike hannunta suka fita.


Dake bata son zaman daining sai ta shirya musu abincin can gefe guda kan wata dadduma mai kyau.....Ta had'a musu abincin suna hira sama-sama kira ya shigo wayarshi dake gefanta.


Tana duba wayar taga sunan dake yawo kan screen din *Hali Dubu* tasan ko wacece ba tare da ya dauka halima bace yace."Miko mun wayar ya kai abincinsa bakinsa.....Sai kawai yaga ta jefar da cokali hannunta ya bar gurin....Ya bita da kallon mamaki! sabon kira ya kara shigowa wayar hannu na rawa ya dauka yana dubawa Halima ce ransa ya 'baci sosai katse wayar yayi ya mike ya bita dakin.


Zaune ya tadda ita gef bed taci kunu....Ya gyara yanayin fuskarsa babu wasa"Tashi kije kici abinci.


Ta kalleshi da idanunta da suka rufe da kishi" Bana ci." Tafada a kufule!


"Me yasa."? ya fada yana kallonta.


A hasale! tace" Me ka gama fada mun dazu ai dama na sani ba zaka ta'ba rabuwa da wannan tsinanniyar ba."


Ya kalleta da yanayi na 'bacin rai! yace"Wai ke meyasa wani sa'in baki da hankali ne uhum? kawai daga ganin numbar sai ki fassara ni."


Ta hayayya'ko masa" Nifa bana son yaudara Sadam!!! Yau ta fad'i sunansa gatsal!! ya shiga mamaki sosai ya zuba mata ido kawai ta cigaba da cewa"Idan kasan ba zaka iya rike mun alkawari ba to tun wuri ka fada mun ba wai ka dinga munafurtata ba dama wannan mautsiyaciyar karuwar ai ba zaka ta'ba rabuwa da ita ba."


"Ke! Ki iya bakinki wallahi kar kiga ina sakar miki fuska ki rainani ni kike kira munafiki ko? Tace" To idan ba munafirci ba meye garin gaminka da Halima bayan kace ni kadai kake gani a idonka ashe munafurci n......Ya kaiwa bakinta duka yana kallonta cikin tsananin bacin rai babu shakka Sayyada taci tuwo a kansa.


Hannunta damtse da bakinta ta fashe da kuka tana fadin"Kwarai kuwa ai bakayi laifi ba dan ka dakeni dama ka saba kuma dama tuntuni ka fada mun halima tani daraja a gurinka." tana gama maganarta ta fice daga dakin a fusace!


Ya zauna kan kujerar madubi yana huci! Sayyada ta 'bata masa rai sosai har yanzu ta kasa gane matsayinta a cikin zuciyarsa......Ba laifin kowa bane sai na 'yar anace haka kawai yana zaman zamansa ta tayar masa da hankalin gida.


Numbarta ya kira ta dauka zatayi magana ya katse da sauri" Yi min shiru bana bukatar jin komai daga bakinki." Halima tayi shuru gabanta na faduwa itafa tun sanda sadam din ya bar gidansu take murna jin abunda ya fadawa mahaifinta ya amince da auranta tunda gashi ma har manya zasu shiga maganar kuma yanzu sai wulakanci yake mata.


Ya cigaba da cewa"A gidan uwar wa na amince da zan aureki da har zaki fadawa mahaifinki ga zance ga magana na dade da shaida miki ni Sadam ba zan aureki ba amma saboda tsabar macewar zuciya kin nace min to wallahi tun wuri kije ki nemi miji sadam na mace daya ne insha Allahu." "Dif! ya kashe wayarshi.


Halima tayi kasa'ke da waya a hannu tana mamaki! sai kuma ta fashe da wani irin kuka mara misali wai jama'a ya za tayi ta janyo hankalin Sadam kanta ne."?


Ya jima a dakin kafin ya bita palon ya tarar da ita taci kuka ta koshi idanunta sunyi jajawur jikinsa yayi sanyi sosai ya karasa inda take ......." Kina ji ko."? yafadi maganar yana kokarin zama kusa da ita...Mikewa tayi ta shige dakin ta murza key ta kwanta kan bed tana shashsheka.


Buga kofar ya shiga yi kamar zai kurma ihu!! me yasa Sayyada ke son wahalar da zuciyarsa ne? meyesa zata dauki wannan matakin akansa har yanzu bata gazgata irin kauna da son da yake mata ba bugun kofar yake yana kiran sunanta tana jinsa tayi masa banza.


Da ya gaji sai ya bude daya dakin dake nan ma akwai kayansu a ciki yayi wanka ya kwanta ransa a bace


Dukaninsu basuyi bacci mai dadi ba.....bayan ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login