Showing 66001 words to 69000 words out of 142497 words
Chapter 23 - NI DA YAYA SADAM Complete Document by Binta Umar Abbale.txt
masu daukar murya nayi kowane dan jarida yafi so yaji ta bakinsa......Su kuwa 'barayin suna d'aure daga su sai gajerun wanduna suna zaune cikin kwaleliyar rana sai daukarsu ake video domin haskasu a television........... Sadam! basu samu nutsuwa ba sai wajejan uku da rabi na rana sannan kowa ya nufi gurin iyalinsa....Mafi akasarin su a cikin bracck din suke da zama da iyalinsu Mutum uku ne basu zaune a barkin cikinsu harda Sadam! da ya nufi can family house dinsu.
A ranar Sayyada yini tayi tura masa test tayi ya kai sauk goma ko daya bai duba ba ballanta ya bata amsa, ganin labaran sha biyu na rana an nuno shi yana jawabi kan nasarar da suka samu ya sake kwantar mata da hankali ta 'kagu ya dawo gida ta ganshi ko taji sanyi cikin ranta.....Duk mai kaunar Sadam yaji dadin abunda ya same shi banda Sulaiman wanda lokacin da yaga Sadam! din a tv 'yan jarida sun kewaye shi suna daukar rahoto yaji wani bala'in kyashi da hassada ya kamashi yaso ace wannan fitar da yayi an kawo musu gawarsa mikewa ma yayi ya bar gurin ranshi idan yayi dubu to ya baci......
Ana kiran sallahr la'asar ya shigo gidan bai zame ko ina ba sai sashensa wanka yake so yayi saboda jikinsa yayi bala'in tsami duk ya daddauje gwiwoyinsa a lokacin da ya fad'a tarko......Zama yayi gefan bed yana kwance takalminsa a hankali ya zare ya cire safar sannan ya kwance blet din ya zare wandon a hankali ya zauna yana duba gurin sai yanzu yake jin zafin ciwon duk da a ido idan ka kalleshi zaka dauka ba wani gagarimun ciwo bane to shi kadai yasan yanda yake masa ciwo a jikinsa ....Hannu ya daga yana kokarin cire riga Ta shigo dakin gabanta ne ya fad'i ganinsa zaune! itama ta shigo ne tayi wanka ta sanja kaya.......Da sauri ta 'karaso inda yake "Yaya Sadam! yaushe ka dawo."!? tafada cike da kulawa Yace."Yanzu." Kallonsa take cikin nazari taga yana lallaba jikinsa ta kalli gwiwarsa taga ta kumbura kad'an da sauri ta tsuguna zata sanya a hannu akai ya rike yana girgiza mata kai."
Murya na rawa tace"Ciwo kaji." Girgiza kansa yayi alamun "A'a." tace"Ba gashinan na gani ba." Yace."Ke! ba wani ciwo ne na kuzo a gani ba daujewa ce."Tace"Sannu to." Shiru yayi yana yunkurun mikewa....Ta rike hannunsa wai zata taimaka masa kallonta kurrum yake yarinyar ta damu dashi sosai.....Toilet suka nufa tare ta had'a masa ruwan zafi tace"Yaya Sadam na ganka an nuno a tv kana magana." Yace."Eh." Tace."Gaskiya kayi kokari Allah ya tsareka daga sharrin masu sharri." Yace."Ameeen Sayyada." kama hanya tayi zata fita yace."Zo ki gasa min jikina." Ta juyo tana kallonsa sai ya mika mata towel kar'ba tayi a hankali shi kuma ya hau cire shart din jikinsa ya shiga kwamin wankan daga shi sai karamin wando....Tace"Ya za'ayi na gasa maka jikin....? Hararata yayi yace."Ba gashinan na kwanta ba ko ina da kika sani a jikina ki danna min da ruwan zafi ciwo yake min."
Tace."To." Ruwan ta shiga tsanowa da towel ta fara danna masa a kirji ya lumshe ido yana jin dadi yace."Ki dinga dannawa da kyau." Tace."To." Gwiwowinsa ta dinga matsawa ruwan zafi tana dannawa yana jin dadi.....Ta dauki kusan minti ashirin tana wannan aiki ya bude idonsa yana kallonta a hankali ya rike towel din yace."Ya isa haka nagode." Ji tayi kamar ta fashe masa da kuka tausayi yake bata.... "Hada min wani ruwan mai zafi." Yafada yana mikewa zaune....Ruwan ta hada masa yace."jeki zanyi wanka." Tace"Ko inyi maka." ? Da sauri ya kalleta yace."Ke! ni zakiyi wa wanka." Girgiza kai tayi da sauri! Yace."Oya fita ki bani guri.'' Simi- simi ta kama hanya ta fita tana kumshe baki Yaya Sadam kenan to wai wane dare ne jemage bai gani ba hummm!
Tana fita tayi ar'ba da wayarsa kan bed da sauri ta zauna tana dubawa test din da dinga tura masa ta shiga dubawa taga ko d'aya bai duba ba....Tayi mamaki sosai ko da yake ina yake da lokacin duba wani test yanzu amma dai tasan tunda ya shigo gida zai duba wayarshi ajiyar zuciya ta sauke tana tunanin ko wace iriyar amsa zai bayar idan yaga test din sa'konnin soyayya masu zafi ta tura masa wanda tasan duk wanda aka turawa irinsu tilas ya magantu kuma ya yabawa wacce ta tura..............................
NI DA YAYA SADAM
*BINTA UMAR ABBALE*
29
Tana jin motsin fitowarsa tayi saurin ajiye wayar ta tsurawa kofar toilet din ido ya fito sanye da gajeran wando da towel rataye a wuyansa, kirjinsa data kalla shine ya bata sha'awa jikinta ya mutu murus! cikin kasala da mutuwar jiki ta dauke kanta....Mikewa tayi a hankali ta shiga toilet d'in, ruwan wanka ta had'a ta jima a tsugune kafin ta fara wanka haka kawai take jin sha'awar Sadam din na taso masa ganin faffad'an kirjinsa ya tafiyar da hankalinta sai ta dinga tunawa da zazzafar soyayyarsa da ya gwada mata a kwanaki biyu da suka wuce,
Da kyar tayi wankan ta fito daure da towel me kauri ta ta lullube jikinta da wani ma dai-dai ci yana tsaye gaban mirror yana gyara sumar shi tazo ta tsaya a bayanshi....ta mudubin yake kallonta fuskarsa babu yabo babu fallasa yace." Yace."Wannan kifta idanun da kikeyi ya nuna min cewar baki da gaskiya."
Tayi kasa da kanta duk bakinta yayi nauyi ganinsa a haka na bala'in tayar mata da hankali yace."Ke! wai meye kike ta sunkuyar da kai nifa bana son gulma." Dariya tayi tace"Ni tsoro kake bani wallahi duba jikinka a murd'e kamar irin 'yan dambe na tv." Yace."Ba wani nan ke dai kawai kice ina baki sha'awa ne shiyasa naga kina ta kallona."
Ta'be baki tayi tace."Wallahi ni baka bani sha'awa ba." Murmushi yayi kawai ya basar tun tana gasa masa jiki ya lura da irin kallon kurrular da take masa shine yanzu zata basar....Shi kansa yasan babu macan da zata kalli zatinsa tace bai mata ba yana mutukar alfahari da kyawun jikin da Allah ya bashi.
Yana matsawa daga gurin ta matsa mai ta shafa sama-sama ta gyara kwantaccan gashinta ta daureshi kana ta sanya wata duguwar riga mai hula duk da ba tayi wani make up tayi kyau sosai da sosai karamin hijab ta sanya a maimakon hular rigar......Shima cikin wata bud'ad'diyar t_shart da shout nickar ya shirya jikinsa ya zauna gefan gado tare da daukar wayarshi yana dubawa.....Sayyada ta samu turarashi masu karfi ta ambula a jikinta take dakin ya d'ume da kamshi Ya dago yana kallonta da 'baci rai! Yace."Saboda baki da hankali shine zaki yi min asarar turare ko dan baki san mahimancin sa bane." Kanta a kasa tace"Yi hakuri." Girgiza kai kurrum yayi ya cigaba da duba wayarshi....Gabanta ya fadi ganin wayar a hannunsa sai tazo ta zauna kusa dashi tana le'kawa....Bai hanata ba ya cigaba da duba test messages din da suka fi guda goma....Karantawa yake yana mamakin wace yarinya ce wannan ta turo masa da wannan haukan...."Ya Sadam! Wacece."!? Tafad'a fuskarta a murtuke."! Kallonta yayi ta gefan ido ganin tasha kunu yasa shima yace."Me ya dame ki budurwata ce." Tace"Bangane budurwarka ba." Yace."Eh ko zaki hanani kula 'yan mata ne buduwarta ce tayo min test gashinan tun jiya tana tambayar lafiya ta."
Tace."Wannan budurwar bata da hankali wallahi kace mata gwara ma ta hakura domin baka da gurin ajiye ta."
Maganarta ta bashi dariya amma baiyi ba yace."Ni nace miki bani da gurin ajiye ta."? shiru tayi tana kallonsa Yace."Ni ko yanzu na tashi aurena banda matsalar gurin zama koda kuwa mata hudu zan aura saboda haka ki daina fadar haka."
Sai idanunta ya cika da kwalla ta dake bata bar ta ta zubo ba tace."Ni kuma na rantse ba zan zauna da wata mace a gida ba kuma in dai kace aure zakayi to sai na fadawa su Baba dole ne kuma ka bari na koma makaranta."
Yace."Wannan ne kuma baku isa ai tun farko sai da nace su bari kiyi karatu suka 'ki sai yanzu kuma ki kawo min wata magana ai kin cuci kanki."
Kuka ta fashe masa dashi tana burgima kan bed din tace"Wallahi ba zakaje ka auro wacce ta fini ilimi da waye wa ba nima dole sai nayi karatu me zurfi kana so ka auro wacce tafi ilimi kuji dadin kirana da 'yar kauye ko."
Ya dinga kallonta yana mamakin iya shege da sangarta ta yace."To idan na tashi auran sai ki hanani makaranta kuma nace ba zakiyi ba."
Mikewa tayi tana kuka tace"Aikuwa sai na fadawa Abbah wallahi ba zan zauna ka auro wacce ta fini ilimi ba." Kallo kawai ya bita dashi har ya fita daga dakin....Girgiza kansa kawai yayi gaskiya a tsarinsa sam! baya son matarshi na yawon zuwa makaranta shiyasa tun farko yace su bari ko NCE su bari Sayyada tayi suka'ki Yanzu shaidar kammalar secondary shoocl ne kawai da ita yana ganin hakan ma ya isa ba sai ta koma wani karatun ba.
Sayyada kam a palo ta tsaya ta goge fuskarta ta dai-dai ta kanta kana ta fita tana mamakin Sadam! wato tun bai san wacece budurwar ba har ya dauka ya soma muzguna mata da bakar magana, aikuwa zata zuba ido taga ko zai bada amsa.
Bata dad'e da shiga sashen ba shima ya shigo da wannan shigar ta kananun kaya Sayyada taji kunya ta kamata sai ta lura shi ko a jikinsa haka ya shiga dakin jegon aunty Hauwa tana ji tamkar ta hanashi shiga saboda kishi tasan akwai baki a ciki kuma har da 'yan mata kai koda matan auran ma wata ba zata iya kauda kanta daga barin kallonsa ba, Mikewa tayi ta bi bayansa.....Sai taga ya dogare a bakin kofa wanda shima jama'ar dake dakin su suka hanashi shiga ciki da yasan zai riski mutane da yawa da shiryo jikinsa......Gaisawa sukayi da jama'ar dakin Sayyada ta ra'ba ta jikinsa ta wuce ta zauna kusa da Asiya....'Kawar Asiya mai suna Labibi ta dinga satar kallon Sadam! tana bala'in son cikakken namiji mai kwarjini da suffar mazantaka duk inda cikakkenan namiji yake to sadam ya kai inda ake so sosai taji ina ma mallakinta ne shi......Sayyada takaici duk ya cika ta tanaji tamkar ta mangare Labibi dake kalle mata miji tamkar zata cinye shi.
Shi kam! bai san sunayi ba yana can yana tsokanar aunt Luba itama tana tsokanar sa dama sun saba duk sanda suka had'u sai sunyi irin wannan wasan amma fa na mutunci sukeyi babu hauka a ciki.
Juyawa yayi zai fita sai kuma ya juyo yana kallon Sayyada yace."Ke! ki kawo min abinci ina palo." Tace."To.'' Yana fita Labibi ta kalli Sayyada tace"A gaskiya Sayyada kinyi sa'ar miji ba zan munafurce ki ba wallahi ki kamashi ki rike da kyau idan kikayi sake akwai 'yan mata a gari marasa imani zasuyi wuf dashi." Dariya suka sanya Asiya da Labiba ita kuwa Sayyada shan kunu tayi tana d'an hararar Labibin kamar tace Cikin wad'anda zasuyi wuf dashi d'in ai har dake mayya kawai! sai kawai ta share tace"Bari in kai masa abinci in dawo." Sukace "To shikkenan."
Tana Fita Labiba ta kalli Asiya tace"Kin san Allah Asiya da badan akwai sanayya a tsakani ba da tuni an wuce gurin dan wallahi guy nan yayi masifar kwanta min a rai."
Aunty Luba tace"Wallahi kar inji kar in gani Labiba ke Asiya Sayyada ba cancanci haka daga gurunmu ba."
Asiya tace"Haba Aunty Luba ni me kikaji nace? Nasan Sadam! yafi karfina ballantana ke! Labiba itama Sayyadar don dai za'bin iyayensa ce shine dalili amma 'yan matanshi duk 'yayan manya ne masu fad'a aji a najeria."
Labiba tace"Ke dai ayi sha'ani kawai yo ni ina ruwana da wasu 'yan matanshi kawai ni in ina san abu nasan duk yanda zanyi na same shi...........!
Mammah bata nan taje kasuwa had'o kayan barka a cewarta komai da akewa maijego to sai anyi wa Lubabatu........ yana zaune a palo da waya hannunsa yana jiran ta kawo masa abinci ta fito daga kicin hannunta dauke da tire kayan abinci ne a jere....."Na jera maka a daining ko na kawo maka nan."
Yace."Kawo min nan." Ta isa inda yake ya dauke kafafunshi daga kan tevur din dake gabanshi ta jera abincin a nutse ta had'a masa komai a plate Macoroni ce da miyar kifi da kayan lambu sai farfesun kan rago wanda Mammah! tayi wa Luba sai kamshi yake lemo mai sanyi ta dauko masa da ruwa duk ta aje.....Ya fara cin abincin ita kuma ta kama hanya zata bar gurin yace."Ke! dawo in gama ki kwashe kayanki ko sai naje na sake kiranki sannan.'' Dawowa tayi ta zauna kujerar dake gefansa......A wayance ta dauki wayarsa tana dubawa yana kallonta ya kyaleta.....Test ta turawa kanta da kanta na zagi da cin mutunci ga abinda ta rubuta.
_Ke! ki fita da harkar mijina domin ba sa'anki bane idan kuma kin'ki ji to wallahi ni Sayyada sai nayi maganinki banza karuwa mai bin maxan mutane ni kad'ai ce matarsa har mutuwa kuma nice uwar 'yayansa! nice za'binsa kina wahalar da kanki ne domin ba auranki zaiyi ba mahaukaciya kawai na barki lafiya_
Sai da ta tabbatar test din ya tafi sannan hankalinta ya kwanta ta cigaba da duba wayar numbars ta shiga tana dubawa numbar mace guda ta gani yayi serving da *Hali dubu* Halima ce baya ga ita ba taci karo da numbar ko wace mace ba duk maza ne abokansa dana aiki........."Ke! wai me kike dubawa ne a wayar bani wayata."! ya fada yana mika mata hannu.
Mika masa wayar tayi tana zumbura baki yana cin abinci yana dube-dube a wayar test din data tura ya karanta tsaf!!! ranshi ya 'baci ya juyo a fusace! yace."Don Ubanki! waye ya saki."!? Shiru tayi domin jikinta ya bata yaga test din....Ya aje cokalin a zafafe! Yace."Ba magana nake miki ba? waye ya saki zaginta."? "To itama waye yasa ta tace." Tana sonka."? Ya kawo mata wani bahagon mari!! a firgice! ta kauce! tana mamakinsa sai huci yake ya mi'ka mata wayar tare da fad'in"Maza rubuta mata ban hakuri ko kuma yanzu in ragargaza ki."!! 'Kin kar'bar wayar tayi ta buge rigar ta ta juya ta nufi dakin jegon aunty Luba.....Binta yayi da kallo cikin mamaki....Sayyada kam! tana sane tayi masa haka so take taga ni shi zai bata hakuri ko kuwa.
Tana shiga dakin ta nutsu suna ta hira ta tsalleke can inda ta aje wayarta ta dauko ta dawo ta zauna tana kunnawa test din data turo ya shigo ta karanta tana kyalkyala dariya aunty Luba tace"Ke kuma fa Sayyada tace"game nakeyi aunty." Asiya tace"Sayyada akwai kuruciya." Hirararsu suka cigaba dayi Sayyada na jiran shigowar sa'ko taji shiru bai shigo ba bini bini ta duba wayar a yanda taga ya damu ta dauka zai rubuta ban hakurin kamar yanda yace sai taji shiru bai turo ba....Hankalinta ya kwanta ta soma zargin duk hargagin karya yake dama
Sai mai aiki ya sanya ta kwashe kayan abincin bayan ya gama ci. Yananan zaune Mammah ta shigo Baban gida biye a bayanta ya aje kayan dake hannunsa ya fita domin kwaso sauran.....Sadam! yace."Mammah a maimakon ki bari shi Sulaiman din yaje da kanshi yayi siyayyarsa kika wahalar da kanki shiga kasuwa a wannan ranar akwai damuwa wallahi."
Tace."Sadam! idan na biye ta Sulaiman babu abunda za'ayi wa yarinyar sam shi kasuwancinsa ne a gabansa Yarinya ta haihu irin wannan babu d'an ai dole a tausashe ta." Yace."Hakan yayi Mammah to amma me yasa baki bari ni naje na siyo komai ba." Tace."Ina kake da lokaci bayan haka kuma kai baka san kayan mata ba shiyasa naje da kaina." Yace."Hakane." Dakin aunty Luba ta leka tace"Asiya da Sayyada suzo su kwashewa aunty luba kayanta....Suka fito tare Sayyada duk ta dauka ya bar palon ashe yana nan mazewa tayi ta hau daukar kayan tana shiga dashi dakin.....Shima bai ce mata komai ba ya mike ya fita sasshen sa ya nufa domin daura alwalar sallahar magariba.
Sai da taga dare yayi sannan hankalinta ya tashi tasan idan tace zata kwanta a sashen tilas Mammah ta tuhume ta, amma dai bari ta gwada ta gani, shimfida tayi kasan kafet ta kwanta tana duba waya Mammah ta shigo domin yiwa Luba sallama sai kawai taga Sayyada akwance cikin mamaki tace"Sayyada me kike baki sasshenku ba ko yau ma aikin kwana ya tafi."? Kamar tace"Eh sai kuma tayi shiru Mammah tace"Ni dai nasan baije aiki ba tunda dazu ma ya shigo ya dauki lemo a firji wai nashi ya kare.....To kya kwanta a nan kuma ki bar mijinki ki tashi kije sasshen naku."
Tace."To Mammah."
Mammah ta kalli aunty Luba tace"Ina fatan babu wata matsala ko."? aunty Lubabatu tace"Babu wata matsala Mammah.'' Tace"To sai da safe." Tace."Allah ya tashe mu lafiya."
Mammah na fita Sayyada ta mike tare da kashe wayarta ta mikawa aunty Luba.
Aunty Luba tace."Wai ke me yasa bakya son tafiya sasshenku da wayarki ne."?
Sayyada tace"Haka kawai aunty ke dai ajiye min a gurinki." aunty Luba ta kar'ba tana fad'in"To sai da safe." Sayyada tace."Allah ya bamu alkairi." Ta bude kofa ta fita jikinta duk ya mutu bata san artabun da zasuyi dashi ba.
Yana kwance rigingine kan bed yayi pillow da hannunwansa kafafunshi duk biyun na zube a kasa rufin dakin ya tsirawa ido yana kallo......Tunani yake yi kan abinda zuciyarsa take bijiro masa dashi dangane da yarinyar cikin 'yan tsakankanin kwanakin nan kullum kwana yake ya yini da tsananin sha'awarta yana so ya kusance ta yana jin tsoron kar yayi mata rauni da sansamu ne kullum ya samu tana yi masa abunda tayi masa a *Dabi* to yana ganin zai iya saurara mata har ta 'kara 'kwari....Yana jin kunyar yaje mata da wannan sigar ne saboda gudun raini a tsakaninsu ko wancan karon ma da abun ya faru ya sakar mata girmanshi tayi yanda take so dashi don babu yanda zaiyi ne kuma a lokacin yana ji kamar ya mutu saboda sha'awa shiyasa ya kyaleta amma ha'ki'kanin gaskiya sha'awa na nema ta kassara shi komai yake daurewa kawai yake yi......Motsin shigowarta yaji dad'in ya 'kurawa kofar shigowa ido ta shigo tana cin magani wai ita dole kar ya raina ta ko yayi mata wata maganar ta nufi toilet tayi wanka da brush ta fito tana tsane jikinta da towel kayan bacci marasa nauyi ta sanya a jikinta