Showing 36001 words to 39000 words out of 142497 words
Chapter 13 - NI DA YAYA SADAM Complete Document by Binta Umar Abbale.txt
bana so ki sanya wani abu a cikin ranki."
Tace."Wallahi al'amarin ke bani mamaki shiyasa nake magana Allah ya dai-dai ta tsakaninsu." Ya amsa da ''ameeen ya rabbi."!
***
Kallonta yake itama tana kallonsa idanunta yayi fululu saboda kuka babu yabo babu fallasa yace."Ya kamata ki daina wannan kukan ya isa haka."
Ta goge hawayen fuska mirya a dashe tace."Tausayinka nakeji don girman Allah ka daina wannan aikin kaji."
Shan kunu yayi yace."Ke! bana son shirme! Wannan aikin idan kinga na bari to bana nuffashi."
Hawaye ya sake kwaryo mata, tausayi ta bashi ya sanya hannu yana goge mata hawayen fuska a daure yace."Idan baki daina min wannan kukan ba yanzu zansa Captain Habu ya mai dake gida."
Zum'bura baki tayi....Yace."Ni dai na fad'a miki." fuskarta ta hau gogewa da hannunta tana kallonsa shima yana kallonta zuwa yanzu ya gama fahimtar yana da babban matsayi a zuciyar yarinyar yana ganin tsananin sonsa da kaunarsa a cikin kwayar idonta.....Suna cikin wannan hali Captain habu ya shigo da take away a hannunsa, Sai yasa dariya yana fad'in"Kaga laila majnun ko."!! Sadam yayi saurin dauke kansa yana dan harararsa, Yana dariya ya zauna a wata kujera yace"Sayyada lallai kina son abokina da yawa nifa yau na dauka hawayenki ne zai kare." murmushi tayi ta sunkuyar da kanta kasa.
Yace."Ga abinci na kawo miki kici." Girgiza kai tayi alamun bata ci. Yace."Me yasa."? A hankali tace"Bana jin yunwa." Kai tsaye yace."Ban yarda ba dole kici wani abu idan kuma kin fiso angon naki ya baki a baki to." Tayi saurin kallonsa yana kwance idanunsa a rufe ya bude yana harar Captain habu din da jin abinda yace.....Captain habu ya mike yana fad'in"Bari in baku guri tun kafin in sha naushi." Dariya tayi tana kallon mutumin nata....Bayan fitar captain habu da minti biyar likita ya shigo da sauri ya kalle ta domin yaga yanayin da take ciki har yanzu hijab dinta na jikinta.....Ta gaishe da dector din shi kuma ya tambaye ta mai jiki tace da sauki....Ya hau duba jikin Sadam! suna hira sama-sama bayan ya bashi magani ya fita ya juyo yana kallonta da d'aurarriyar fuska yace."Kar wanda ya 'kara shigowa kika gaishe shi ranki sai ya 'baci!." Da mamaki ta kalleshi yace."Kinji abinda nace miki ko."? d'aga kanta tayi....Ya mai da idanunsa ya rufe yana jin wani irin kishi a cikin ransa ai dole ne ma ta bar asibitin nan,
Muryarta ya jiyo tana fad'in"Ka tashi kasha maganin to."! banza yayi mata tace"Kaji." ya bude idonsa yana kallonta sai ta sunkuyar da kanta...."Sayyada."! ya ambaci sunanta cikin wata iriyar murya.Ta kalleshi yace."Bana bukatar damuwa yanzu kuci abinci ki kwanta ok."
"Nifa bana ci."! Tafada duk ranta a 'bace! yace." Kanki kikayiwa ai." Dakin yayi shiru na tsawon minti goma ta mike ta shiga bandakin dake cikin dakin minti uku ta fito tazo ta ra'ba kusa dashi zata kwanta....."Ke! meye haka tashi ki koma kan kujerar can ki kwanta." Abinda ya fada yasa ta maka masa harara! ya kuma ganta ta gyara kwanciyarta a gefansa....."Wai kina so ki dauje min ciwo na ne? idan takura min Zakiyi zan fita in bar miki da'kin." Kuka tasa tana shashshake takaici ya isheshi ya mike zaune da kyar yana kallonta kudundune a cikin hijab tana kuka yace."Kiyi min shiru malama dukanki ko zaginki nayi da zaki cika min kunne da kuka mtswww!.
Rage sautin kukan tayi tana goge hawaye yace."Ki kwanta inda kike tunda kin nace! kar ki matso kusa dani balle ki sanya ni a wani hali." Ita dai bata ce masa komai ba ta kwanta......Cikin karfin hali ya mike yaje ya kulle dakin ya dawo ya kwanta minti goma bacci ya daukeshi.....Ta bude idonta tana kallonsa kauna da sonsa da tausayinsa na 'kara nunkuwa a cikin ranta.
Itace ra riga tashi taga gari har ya soma haske tana kallon agogo ya nuna mata lokaci karfe shida da kwata na safe da sauri ta sauka taje ta dauro alwala ta fito motsinta shine ya farkar dashi ya mike zaune alhamdullahi jikin da sauki ya mike ya nufi toilet din Alwala yayi ya fito ya tada sallah, kusa da ita........A hankali ta juya tace."Ina kwana ya jiki"? Ya amsa mata babu yabo babu fallasa, mikewa tayi ta zauna gefan gadon hijab din ta cire ya kalleta da d'aurarriyar fuska "Ki shirya idan anjima za'a mayar dake gida ko kuma idan su Mamah sunzo ki bisu."
"Saboda me."?tafad'a tana kallonsa....." Ke! ni nake magana kina tambayata." ! ya fada yana kwalalo mata manyan idanunsa....Ba taji tsoro ba sai ma zumbura baki da tayi...."Ko ba kyaji ne."!? banza tayi masa. Duk tausayin kanta ya cikata Yaya Sadam! baya sonta sai wulakantata yake sai idanunta suka soma kawo ruwa, Idanunsa a tsaye a kanta ya gani da sauri yace."Karki kuskura hawayen nan ya zubo." Ai ya 'bata bakinsa don tuntuni hawayen ya tsinke sai kawai ya saki baki yana kallonta Dr ne ya shigo tayi sauri ta 'boye fuskarta cikin hijab, Ganinsa kan dadduma yasa dr fad'in"Alhamdullahi Yalla'bai da alama ba zaka dade a kwance madam ta iya jinya." Hannu ya bashi suka gaisa dr ya duba jikin nasa kana ya bashi magani yana fad'in''Ni zan dinga baka magani da safe Madam kuma ta kula da kai da rana da dare ." Yace."Kai ma na huttashe ka ai ba yaro bane ni zan sha magani da kaina." Dr na dariya yace."A'a Madam ya fi kamata ta baka zakafi samun sauki da wuri." Murmushi kawai yayi dr yayi masa sallama ya fita.
Mi'kewa yayi ya isa gadon ya zauna yana kallon bayanta shiru babu wanda yayi magana ya sanya hannu yaja hijab din ta baya ta rike wuyanta da sauri ta juyo tana kallonsa, Sai ya saki hijab din ya kwanta rigingine ba tare da yace mata komai ba ita kuma hakan da yayi sai ya sake tunzura ta ta mike zata fita daga d'akin!....."Sayyada."!!! Ta jiyo muryarsa na kiranta ko kallonsa ba tayi ba ta bude kofa ta fita, sai suka ci karo da Captain Habu da Saleh zasu shigo dake kofar a bude take duk yana hangosu yana kallon tana gaishesu har shi Captain Saleh din da yake mata wani irin kallo.....Ransa ya 'baci! yarinyar nan ta raina shi wato yace kar ta fita sai da fita! ga matsiyacin nan yana kallonta Captain Saleh anyi d'an akuya......Habu yace."Sayyada ina zakije." ? inda inda ta hau yi yace."Muje ciki." gaba tayi suka rufa mata baya........Xaune suka same shi fuskar nan a murd'e fatar goshinta duk ta tattare kana kallonsa zaka fahimci ransa a 'bace yake.
NI DA YAYA SADAM
NA
BINTA UMAR ABBALE
Pege19*
Jiki a sanyaye taje bayansa ta zauna tare da rufe jikinta da hijab idanun saleh na kanta sai ya soma zargin wani domin shi duk abinda akeyi bai sani ba bai san cewar Sadam din yayi aure ba tunda ba shiri suke da juna ba, ammafa ganin farko da yayiwa yarinyar ya kwadaitu da ita tabbas idan ta kasance matar Sadam! ce ita to kuwa duk yanda zaiyi sai yayi ya biya bukatarsa ko dan ya kashe sadam din da bakin ciki Sakin fuska yayi tamkar ba mugu ba ya duba sadam din yana tambayarsa jiki duk gurin sai da sukayi mamakin sauyawarsa lokaci guda Sadam kam baiyi wani mamaki savoda yasan Saleh ba karamin makirin mutum bane.
Duk da yayi kokarin danne 'bacin ran dake damunsa amma duk da haka Habu ya fahimci yana da damuwa,Sama-sama suka gaisa da abokanan aikinsa inda ya na hankalce da inda Captain Saleh yafi mai da hankali gurin kallo sai yaji tamkar ya tashi ya Nausheshi saboda takaici, Captain Saleh mayen mata ne shi yasa kwata-kwata baya son zamanta a bracck din saboda irin su Saleh a kwai hadarin gaske......Hira sukeyi sama-sama, ba tare da ya sanya musu baki ba, Sai da ya gaji da abinda Saleh keyi masa yace."Ya kamata fa ku shiga ofis naga lokaci ya wuce." Dukaninsu suka mike sukayi masa sallama, Saleh har da waiwayen Sayyada saboda tsabar jaraba.
Suna fita ya mi'ke zaune yace."Ke! juyo nan ki kalleni." Juyowa tayi tana kallonsa kana kallonta kasan a tsorace take domin miryar da yayi mata magana kamar ba ta mutum ba.
"Baki isa kizo ki zubar min da mutunci ba." Ya fad'a yana zare mata ido! ya cigaba da cewa meye amfanin xamanki anan da zakice dole sai kin zauna tare dani me kike tsinana min ? daga anyi magana sai ki hau kuka bakyajin maganata nace dake Karki fita sai da kika fita ni da bakina nace kar in kara jin wani namiji ya shigo kin gaisa dashi saboda ban isa ba naji da kunnena kina gaisawa da Saleh! To yau d'in nan zaki bar brecck din nan ko 'kinki ko kinso idan kukan jini zakiyi sai dai kiyi na gama magana."""" Shiru tayi masa idanunta ya kad'a yayi jawur! Sadam baya sonta yanzu meye laifin wanda ya kula da kai da rayuwarka kan kawai tace zata zauna tare dashi yake wulakanta, Hawayen da take ta kokarin dannewa suka fara zuba.....Yana jinta tana shashshekar kuka yaki kallonta lumshe idonsa ma yayi bacci na daukarsa,Motsin bude kofa yaji ya bude ido ita kuma tayi saurin sanya gefan hijab dinta ta kare fuskarsa.
Sulaiman ne ya shigo cikin Shadda galila 'yar gasken anyi masa d'in 'yan birni yayi kyau sosai kamshi ne kawai yake tashi a jikinsa.
Babu yabo babu fallasa ya amsa sallamarsa Sayyada najin muryar Sulaiman ta bude fuskarta, Sulaiman ya karaso bakin gadon ya tsaya yana kallon Sadam! din A hankali yace."Ya jiki."? "Alhamdullihi." Yafada ba tare da ya kalleshi ba. "Yaya Sulaiman ina kwana ya kwanan Aunty Luba."!? Ya Juyo yana mata wani sihirtaccen kallo fuska a sake yace." Lafiya lau baby Sayyada dake haka yake kiranta tun tana yarinya ya cigaba da cewa "Ya mai jiki? ina fatan komai lafiya."
Da gefan ido ta kalleshi taga ya wani ci kunu! gabanta na faduwa tace"Jiki da sauki wallahi." Shiru dakin yayi Sadam! na mamaki wato duk hargagi da masifar da zaiyiwa yarinyar ba zata ji maganarsa ba dole ya koya mata zama.
Sulaiman ya kalleshi a nutse yace."Babu abunda kake bukata ko? Ko da yake ma naga jikin da sauki Allah ya takaita wahala." Wannan magana da Sulaiman din yayi ta tun zura masa zuciya domin shi a yanda ya fassara maganar kamar ta rainin hankali ne *Allah ya takaita wahala* Idan bai manta ba akwanakin baya Sulaiman ya sha cewa dashi ya rabu da aikin soja saboda a cikinsa akwai babban kalubale sannan mutum yazo ya mutu a banza a wofi bai cimma shekarunsa....Wannan magana da ya fad'a ta nuni da irin maganganunsa na baya....Kamar ya bashi amsa dai-dai dashi sai kawai ya kyaleshi domin baya so su raba hali a cikin mutune amma hakika abinda Sulaiman din keyi masa ya soma wuce makadi da rawa.
Hira sukeyi yana jinsu dama can yasan akwai shakuwa a tsakaninsu bai wani damuba tunda bai ga an wuce gona da iri ba, shine dalilin da ya sanya ya rabu dasu suke maganganunsu na can Garinsu *Dabi* Bai tanka musu ba ya dai kasa kunne yana jinsu........"Sadam! ni zan wuce kasuwa Allah ya sawake, ya ta'kaita wahala."! Sai ya bud'e idonsa da saurin gaske ya mike zaune " Dakata malam kar ka fita tukkuna sai ka tsaya ka fad'amin ma'anar wannan kalmar da kake ta nanatawa tund'azu."!! Cikin 'karfin murya yake maganar yana wani irin haci!!! Sayyada cikinta duk ya d'ori ruwa mutum ma na kwance bai da lafiya amma ba zai bar masifa ba.
Murmushi yayi yace."Saboda nayi maka addua kake tuhuma Sadam! *Allah Ya takaita wahala* yanzu ma na 'kara fad'a." Ya fad'i maganar yana d'aga kafad'a alamun bai damu ba.
Yace."Kai! baka isa kayi min addua ta kar'bu ba ka sani Allah na kar'bar adduar mai kyakkyawar niyya ne me kyawun zuciya kai kuwa fa kullum zuciyarka ba'kikkirin take baka nufin mutun da alkairi sai sharri Ni! nafi karfinka wallahi baka isa kayi min abinda Allah baiyi min ba, bana nadamar na rasa raina a aikin soja! saboda nasan nayi aiki domin Allah da mazonsa zan samu kyakkyawan sakamako gurin Allah."
"Ni kake fad'awa wannan maganar."! ? Sulaiman ya fad'a ransa a mugun bace."!
" Kai wanene!? da ba za'a fad'a maka magana ba."! shima ya mayar masa a zafafe."!!! "Yaya Sulaiman kayi hakuri don Allah." Murya na rawa take maganar."! "Kika 'kara wata magana anan gurin sai ranki ya 'baci!! wallahi."! Yafad'a yana watsa mata mugun kallo...Mi'kewa tayi tana kuka " Wannan wane irin hali ne? yanzu meye laifin Yaya Sulaiman kuma? kawai don yayi maka addua aikin soja ai ba hauka bane." Bai san sanda ya dirgo daga gadon ba ya nufeta....Sulaiman na ganin abinda yake shirin yi yaje ya tare shi!!! "Karka kuskura ka daketa wannan ai hauka ne! dama dukaninku haka kuke ku kama matanku kuna jibga sai kace bayi."! Wani wawan! naushi ya kir'ba! masa a 'kirji! Sulaiman ya ri'ke kirjinsa yana tari! azabah! na sukanshi.....Gefe ya tureshi yaja tsaki tare da fad'i " Haka sai kace namiji ashe rago ne."!!! Sulaimai ya sake yunkurin kare Sayyada...."Wallahi karka kusantoni sai nayi maka illah! ka bar ganin kirjina daure da bandaji bani da dad'i!!!! Sulaiman ya tsorota da Sadam! domin ga dukkanin alamu allurar ce ta motsa kai Soja bala'i ne.....Sayyada ta makure jikinta a bango Rumfa yayi mata ya sanya hannu ya sha'keta mata wuya"!! Don Ubanki maimaita abunda kikace yanzu, wato kema kin fara daukar hud'ubarsa ko? kina nema ki zagemu ki zagi aikinmu? hakane ko ba haka bane."!? Cikin hargagi yake maganr....Hawaye sai tsere suke a fuskarta "Kayi hakuri don Allah ba zaginka nayi ba."!? " Ni da Sulaiman waye mijinki kuma maganar wa yafi cancanta ki dauka."? da karfin murya yake maganar....Tace"Kaine mijina kuma maganarka yafi dacewa na dauka." "Ok me yasa idan nace karkiyi abu sai kinyi raini ne ko me."!? Girgiza kai tayi..." Kayi hakuri kayi hakuri kayi hakuri."! abinda take fad'a kenan....Wuyanta ya saki ya koma ya kwanta yana wani irin nishi! kirjinsa ya rike! da alama ya fama gurin harbin....
Sulaiman na tsaye yana kallonsa yana nishi!! jini daga jikin bandejin yana fitowa saman kirjinsa, bai wani damu ba ya kad'e rigar jikinsa ya fice daga d'akin zuciyarsa tas yaji dadin yanda ya tashi ciwon nasa shine wahalalle wanda wahala ta yankewa cibiya Allah yasa ma gurin ya lalace ya jima a kwance yana jinya.
Ganin yanda yake rirri'ke kirjinsa da kuma jinin dake zirarowa yasa hankalinta yayi masifar tashi da sauri ta bude kofa ta fita Minti biyar suka shigo da likita hankali a tashe ya isa inda yake ya soma duba gurin mikin yana tambayar Sayyada garin ya akayi haka ta faru ita dai ta kasa cewa komai sai kuka takeyi
Sai da taga jinin dake zuba ya tsaya sannan hankalinta ya kwanta amma dai duk da haka hawaye bai daina zuba daga idonta ba.....Dr ya kalli Sadam! dake rintse ido yana cije lips yace.."Wai Yallabai ya akayi haka ta faru ne."! Ido a rufe yace."Bacci nakeyi na danne gurin." Dr yace."Ayya Madam kina gani a maimakon ki zauna kusa dashi shine amfanin zamanki a gurin ai idan da matsala ko zamu kawo maka mai kula da kai ne."? girgiza kai yayi alamun baya bukata.
Sayyada tace"Tsautsayi ne Dr nima bacci nakeyi shiyasa ban lura ba." Yace."Ai naga alama a yanda kike son Yallabai ba zaki bari hakan ta faru ba sai da dalili." Murmushi tayi mai ciwo tana tuno rashin mutuncin da yayi mata d'azu.
Dr Yace."Idan yayi break ki bashi magani kinji ko." Tace."Insha Allah." Bayan fitar Dr din dakin yayi shiru sai saukar numfashinsu ido ya bude yana kallon inda take tana can takure kan kujera taki kallonsa haushinsa takeji sosai tana da zuciya dole tayi taka tsantsan da rashin mutuncinsa.
Ya jima yana kallonta tausayinta yake ji yanzu kuma nadamar abinda yayi mata yake....Tsaki yayi cikin ransa koma meye ya.faru itace ta jawowa kanta.
Hajiya Fatsima da Alhaji Auwal ne sukayi sallama. Sayyada ta amsa da sakakkiyar fuska tana gaishesu....Hjy Fatsima tayi ta naxarinta taga tabbas akwai damuwa a tare da ita ga idanunta sunyi jawur dasu.....Sadam! ya gaishe da iyayen nasa cikin dauriya da kokarin danne abubuwan dake damunsa Nan Alhaji Auwal yake tambayarsa ko Sulaiman yazo yace."Bai jima da fita ba....Ya tambaye shi yanayin jikin nasa yace."Da sauki bashi da wata matsala...Godiya yayi ga Allah yayi musu sallama kasuwa ya wuce kai tsaye.
Hajiya Fatsima tace"Sayyada ga abun kari nan na kawo muku ki karya sai ki had'awa mijin naki shima." Tace."To Mammah! tea ta had'a me kauri ta zuba soyayyan dankali da kwali ta dauka gadon da yake kwance ta nufa ta zauna gefansa a hankali tace"Ka tashi kayi break kasa magani." Sai da tayi magana sau biyu sannan ya mike zaune da dubara ya kar'bi kofin tea din....Ta mika masa tare da dora masa plate din dankalin a cinyarsa....Da kyar yake daga hannunsa yana kur'bar tea din saboda kafad'arsa ta dama harbin yake, kamar ta kar'ba ta bashi da kanta sai tayi wa kanta fad'a tasan hali zai iya gwaleta ko ya hantareta. mikewa ma tayi ta bar gurin tea ta hada ta zauna kusa da Mamah tana kur'ba amma hankalinta na kansa da kyar ya shanye tea din dankwalin kuwa bai fi uku yaci ba yace."Zo ki dauke plate din nan." Ta mike da sauri ta isa ta dauke masa....Ruwa ta dauko ta dawo gurin ta 'balli maganin ta mi'ka masa kar'ba yayi ya watsa a bakinsa ya kora da ruwa, Hjy Fatsima tana kallonsu cike da farin ciki a gaskiya ta yaba kwarai da yanda Sayyada take kula da Sadam!!!
Bai kai rabin awa da shan maganin ba bacci ya daukeshi....Nan Sayyada da Hjy Suka dinga hira Sayyada ta saki jikinta sosai da ita tana daukarta tamkar mahaifiyarta.
Sai kusan karfe daya sannan tayi niyar tafiya tace zasu dawo da daddare sannan tana komawa gida zata sanya baban gida ya kawo musu abincin rana." Sayyada kamar ta bita saboda abinda yace mata dazu *Banga abinda kike tsinana min ba saboda haka idan su Mamah sunzo dole ki bisu ku tafi gida* Wannan magana ta bata haushi mutuka amma duk sanda ya sakeyi mata irinta to sai dai ya nemeta ya rasa.
Sallah tayi ta koma gefansa ta zauna