Showing 33001 words to 36000 words out of 142497 words
Chapter 12 - NI DA YAYA SADAM Complete Document by Binta Umar Abbale.txt
ka dawo gari."? Yace."Jiya na shigo da daddare munyi waya da Luba ashe bata fada miki ba." Luba tace"Mamah naga dare ne shiyasa ban sanar dake ba." Hjy Fatsima ta zauna suna gaisawa yace."Luba tayi min waya da safe wai bata jin dadi dole sai taje asibiti." Hjy Fatsima tace"To in banda abinka mace me tsohon ciki kamar wannan yaushe zaka sameta da lafiya." Yace."Allah dai ya raba lafiya."Ameeen suka ce gabad'aya. A gurguje suka kammala karin kummalon sannsn suka wuce asibitin Sayyada ta gyara gurin ta koma ta zauna Hjy Fatsima tace"To ai sai ki had'a kayan karin ki kaiwa mijin naki ko Sayyada." Tace."Ai bacci yake."Tace"Eh ki had'a komai ki kai masa kinga idan ya tashi sai ya gani." Tace"To Mamah." Kicin ta shiga ta hada komai cikn kwando ta dauka ta nufi bangaran nasu.
Koda ta shiga dakin har yanzu bacci yake ya rungume pillow 'kam! ya sanya wani a tsakiyar 'kafafunsa daga ni baccin a takure yakeyinsa.....Kwandon ta aje ta matsa jikin bed din tana jan pillows din ya ri'ke 'kam! yana sauke ajiyar zuciya......"Yaya Sadam!!!! Yaji muryarta ta daki dodon kunnensa firgigit ya mike zaune yana kallonta da jajayen idanunsa wanda suke dauke da tsabar fitina mafarki yake gashi yana sex da ita yana jin wani irin nishadi wanda har yake mamaki ashe zai iya samun gamsuwar da yake so da ita.
Ita kuma ganin yanda kwayar idonsa ta sauya sai taji tsoro ta dauke kanta da sauri.....A hard'e! yace."Waye yace kizo ki tashe ni ina baccina mai dad'i!!!! Tace."Mamah ce tace in zo in tasheka ka karya." Yace."karya kike mamah tasan ba'a tashina idan ina bacci."
Sai ta d'auke kai tana turo bakinta wannan d'abi'ar tace zu'baro baki......Girgiza kai yayi yace."Wuce ki bawa mutane guri." Matsawa tayi ta jingina da bango(garu) "Cewa nayi ki fita a dakin malama." 'Kin fita tayi ya dinga magana tana jinsa tayi shiru dalilin da yasa baya so ya tashi a gabanta saboda yasan sandar girmansa a mi'ke take shiyasa baya so ta gani ya lura yarinyar 'yar bin 'kwakkwafi ce......Yace."Bakiji abinda nace ba ko."!? "To wai me na tsare maka ne ga hanya nan fa na baka ka wuce dole sai kace sai na fita daga dakin."!! 'Kwafa yayi ya yunkura ya mike!!! aikuwa karaf! idanunta ya sauka kan abinda yake 'boyewa, hannu tasa ta toshe bakinta sai kace wacce taga gagarimin abu........Sai ta dauke kanta tana d'an kumshe dariya Takaici tamkar ya kasheshi wai shi wannan yarinyar takewa rashin mutunci ko da yake to me zai 'boyewa sayyada dama ta riga ta gama ganin girmansa......Yana daf da shiga toilet din ne ya jiyo muryarta tana fad'in" Gaskiya Yaya Sadam! ka nemi magani baka da lafiya ta'b!!!!!!."""" bai ce mata komai ba ya shige amma ya cika da mamakin jin furucinta wato shine ma bashi da lafiya kenan aikuwa sai yaci ubanta zai nuna mata garau! yake zata gane shayi ruwa ne.....Wanka yayi ya fito fuskarsa a daure tamau!! tana ta kallon fuskar tana kumshe baki.....Ya mutsika basilin turare ya fesa ya kawo sabuwar jallabiya yasa still yana jiyowa yaga tana masa dariya hade da gumtse baki......Cikin fusata yayo kanta da gudu ta ruga palon tana kyakyatawa......Ya tsaya tsakiyar dakin hade da rike kugu yana mamaki! gyada kansa yayi ya koma ya zauna kasan kafet da kansa ta hada abincin yaci ya koshi ya ture kwanikan kana ya mike domin gaida iyayensa.
Koda ya isa bangaran iyayen nasa abin da ya gani ya 'bata masa rai Sayyada da Sulaiman kujera d'aya 2sitar suna zaune suna hira ita kuma Luba na kwance tsakiyar kafet tana kallonsu jefi jefi tana sa musu baki....Da kyar ya daure ya isa inda suke hannu ya mi'kawa Sulaiman d'in suka gaisa babu yabo babu fallasa, ya zare hannunsa tare da watsa mata wani irin kallo....Jikinta ne yayi sanyi sai ta rage dariyar da takeyi ta shiga hankalinta.... Dakin mahaifiyar tasu ya nufa suka gaisa sai ya lura da ita kamar bata son su hada ido don haka bai ja wata doguwar magana ba ya fito.....Ba tare da ya kalli inda suke ba ya kama hanyar fita yana ji Luba na masa wasa bai tanka mata ba mugun haushin mijinta yake ya rasa gane me yake damun Sulaiman son matansa yayi idan da yana daukar Sayyada 'yar uwarsa to yanzu kuma da take auransu ai ya kamata ya kama kansa tunda yanzu kamar a matsayin suruka take a gurinsa. amma saboda tsabar zubar da girma ya zage yana dariya da ita.........Harabar gidan ya zauna gurin hutawa yana duba sa'kwanni abokanshi, Captain Habu ya kira shi a waya cewar ya fito yanzu yanzu yanzu labari ya same su cewar an samu wani d'an boko haram! ya shigo kasuwar bacci kuma ana zargin anan ya kwana cikin tasha." Daga jin wannan magana sai yayi zumbur ya mike bangaransa ya nifa domin shiryawa....Tsaf ya shirya jikinsa da kayansu na sojoji ya fito, Sayyada na ganinsa cikin kayan aiki sai gabanta ya fad'i! Sulaiman yace."Ya dai naga kayi shirin fita aiki kai ko d'an hutun amarcin ma baka dauka ba." Wani irin kallo ya watsa masa kamar ya gargad'e shi sai kuma ya fasa.
Hajiya Fatsima tace"Da'alama aikine ya tashi yanzu." Yace."Eh mamah nan ya zauna ya fada mata halin da ake ciki.....Sayyada dajin wannan magana sai ta fashe da kuka"Yaya Sadam! don Allah kar kaje kar su kashe ka."!! Palon yayi shiru.....Aunty luba tace."Wallahi nima jikina yayi sanyi Sadam! ya mike da fad'in"Addua kawai zaku dinga yi mana." Ganin ya nufi hanyar fita ya sanya sayyada ta ruga a guje ta rungumeshi ta baya tana kuka........Wannan lokacin Sulaiman ji yayi tamkar ya harbe Sadam! saboda kawai sayyada ta rungume shi wai shin shi me Sadam! yafi shine ? da Sayyada take sonsa, hakika yana jin bala'in ciwo a cikin zuciyarsa son da yakewa Sayyada yayi yawa kuma yanzu ya tabbatar da cewar tayi masa nisa tunda ta kasance matar 'kaninsa.
Kuka takeyi sosai! har sai da ta bashi tausayi yaja hannunta suka fita motarsa ya nufa da ita ya bude suka shiga"Goge hawayen ki."Ya fada tare da mika mata hankici mai kamshi
Bayan ta goge sai ya mika hannu ta bashi makale kafad'ata tayi yace."Saboda me."? "Saboda ina son 'kamshinka Don Allah Yaya Sadam! kar kaje gurin nan kaji ina sonka bana so wani abu ya sameka."!
Ajiyar zuciya ya sauke a hankali yace." Kin gane ko Sayyada shi wannan aikin namu daban yake da sauran, muna taimako da tsare rayuka da dukiyoyin talakawa ne kuma kafin mu kar'bi aikin sai da mukayi rantsuwa da al'kawari kan cewar komai wuya rana zafi ruwa sanyi zamu fito a duk lokacin da wata tarzoma ta tashi zamu taimaka koda zamu rasa ranmu saboda haka ki kwantar da hankalinki babu abunda zai sameni sai alkairi."
Hawaye take tace"To Ina rokon Allah ya tsareka kuma ya baka nasara mijina." Murmushi yayi irin wanda bai ta'ba yi mata irinsa ba ya "karbi hankicin ya goge mata hawaye kana ya mika mata ta kar'ba tana murmushi.....Shina murmushin yake yana kallon fuskarta.
Hannu yasa ya d'ago fuskarta a hankali yace." Bani nasha."! ta lumshe idonta tare da budewa sai taga fuskarsa daf da tata, rintse ido tayi gabanta na fad'uwa.....Murmushi ya saki ya sakar mata fuskar ba tare da yayi mata komai ba yace."Kije gida kiyi min addua amaryata."
Ta bude kasalallun idanunta tana kallonsa hannu ya zura ya bude mata kofar motar ta fito ya daga mata hannu kana yaja motar mai gadi ya bude gate ta figi motar a guje ya fice!!! ta jima a tsaye a gurin tana kallon hanyar da ya wuce jiki a mace ta koma bangaransu ta kwanta inda ya kwanta jiya ta dauki jallabiyarsa da ya cire ta rungume a kirjinta tana hawaye. haka bacci ya dauketa.
Sulaiman kuwa ganin Sayyada bata dawo ba sai yaji duk xaman gurin ya isheshi tashi yayi zai fita aunty Luba tace"Darling yaushe xamu koma gida ne.? ba tare da ya juyo ba yace."Duk sanda kika shirya komawa." Ta mike da kyar tana fadin "Yanzu ma a shirye nake." Tsaki yaja ya fita sai ta bishi da kallo cike da mamaki! auran soyayya sukayi da juna amma tunda ta samu ciki ta rasa gane kansa da gidinsa wulakancin yau daban na gobe daban, kwata-kwata bashi da lokacinta sai aukin hira da 'yan mata a waya.
Ta wagar sojojin na shiga cikin kasuwar jama'a suka soma watse masu sana'a da suka karkasa kayansu suka soma kwashewa Sadam! ya kar'bi abin 'kara karfin murya yace."Kowa ya zauna ya nutse kuma ku daina kwashe kayan sana'ar ku bunkice muka shigo zamu tafi idan mun gama mu barku ku cigaba da sana'oinku.'' To sai da sukaji wannan magana sannan hankalinsu ya kwanta....Su kuma sojojin sai suka watsu dana already wasu sun rufe gate din gaba da baya kuma tsun tsare hanya......Sadam! ya dinga kutsawa cikin rumfunan jama'a ya duddubawa su kuma sauran suna zazzage buhunhuna! na kayayyakin sana'a duk wasu daurarrun kayan sai da suka kwance suna dubawa babu wata alamar ganin mutum......duk fad'in kasuwar sai da suka bunkita basu ganshi ba....Sadam! ya ri'ke 'kugu yana kallon tarin jama'ar da sukayi tsuru-tsuru suna jimami d'an boko haram! ya shigo cikinsu basu sani ba wasu daga cikin ma har sunyi alkawarin cewa daga yau ba zasu sake fitowa kasuwa ba har sau gwamnati ta shiga al'amarin......Dai-dai inda yake tsaye karkashin wata katuwar kwata ce da aka rufe ta da silaf kwatar tun daga farkon kasuwar take har karshenta kuma duk rufe take da Silaf.....Babu zato! Sadam!! yayi 'yar hantsle!!! Ya ganganra can! gefe kafin kice kwabo guri ya hautsine da hayaniya kowa naso ya tsira da ransa......Cikin zafin nama ya mi'ke.....da gudu! ya nufi gurin kafin ya 'karasa an jefo wani abu!!! jama'a na dubawa suka ga bomb!!!!! Sai ihu! gudu karce! marasa karfi sai faduwa sukeyi ana tattake su kowa dai na neman ya ceci ransa.......Ba tare da wani tunani ba ya afka cikin kwatar, Can ya hango shi yana gudu!!! cikin kwatar bakajin komai sai motsin ruwa!!!! Sa'ilin da gurin ya hargitse ne aka samu wani wanda yayi saurin mayar da silaf d'in da wannan d'an boko haram d'in ya cire ya rufe gurin alhalin yasan Sadam! na ciki......Jama'a sunyu dafifi bakin gate suna ihu! ga gate a kulle marasa hakuri kuwa ai har sun soma haura katanga suna dura 'kasa, Captain Habu ne yazo cijn zafin nama ya bude gate din aikuwa jama'a suka dinga turareniyar fita......Captain Aminu shine yayi jihadi ya d'auki bomb din a guje ya fita dashi can cikin bishiyo ya jefa shi ya bar gurin da saurin gaske.........!
Sadam! harbi kawai yake saki! ta ko ina! cikin ikon Allah yayi nasarar samunsa a kafarsa...aikuwa a take ya zube a gurin.....! yana rike kafa Sadam! ya 'karasa inda yake cicci'barsa yayi ya sa'ba a kafad'a ya dawo baya sai da yazo yaga babu hanya ko ina a rufe......Ya cika da mamaki a jiye mutumin yayi ya fara kokarin ture silaf d'in domin ya samu hanyar fita inda anan mutumin ya samu nasarar zare bindigar dake jikin wandonsa ya saita kafad'arsa ya sakar masa bulet!!!!!! Ya juyo a fusace! ya dauke shi da mari! faduwa yayi cikin kwatar ya sanya takalminsa ya take masa wuya yana cije baki!! hannu daya ya ture silaf din kana ya sunkuya ya d'auko shi jikinsa jage-jage! da jini ya fito.......Gurin tsit!!! Can Captain Habu ya hangoshi ya fad'i ga jini a jikinsa a guje ya 'karaso gurin yana kiransa idanunsa yaga suna lumshewa jiri ne kawai yake d'ibanshi hannunsa ya rike yana goge masa zufa.....Da bayan bayan daya sojojin suka dawo nan sukaga halin da Sadam din ke ciki gashi dai an samu nasarar kama mutumin amma kuma wanda suke alfahari dashi yana cikin matsanancin hali.
NI DA YAYA SADAM
NA
BINTA UMAR ABBALE
Pege18*
Da sauri Captain Habu ya bar gurin, Captain Saleh yazo yazo ya tsaya kawai a kansa yana masa wani irin kallo yaso ace ha'kansa ya cimma ruwa yaso ace bukatarsa ta biya a kansa amma babu komai watarana ya tabbatar da cewar bukatarsa sai ta biya a kansa ya dauki alwashin sai ya salwantar da ransa mutukar suna aiki a guri guda.
Mota Captain Habu ya shigo da ita da sauri Captain Saleh ya sunkuya domin taimaka masa sai ya d'aga masa hannu goshinsa duk ya tsatstsafo da gumi hannunsa a kafadarsa ya rike gurin harbin jini kam duk ya jika masa jiki.....Captain Saleh ya matsa gefe guda yana kallo Captain Habu ya rirrikeshi ya kaishi mota, sannan suka tasa 'keyar d'an boko haram! din wanda suka rufe masa fuska da wani ba'kin abu suka daure duk hannayensa da ankwa....Gurin cika yayi da mutane 'yan jarida har sun hallara a gurin mutane sai dauka suke a wayoyinsu da kyar motar ta fita daga gurin.....Cikin brecck din akwai asibiti dake kula da sojoji da iyalinsu kai tsaye can aka nufa da Sadam! wanda tsabar dauriya tasa idanunsa ya kada yayi jawur jijiyar kansa duk ta tashi kana kallonsa a lokacin zaka fahimci yana jin jiki sosai....Lokaci guda likitoci suka rufu a kansa har sai da suka samu nasarar cire bulet! din sukayi aikin gurin yanda ya kamata kana sukayi masa allurar bacci domin ya samu hutu.
Rundinar sojoji ta Najeria tayi mutukar jin dadi da faruwar wannan al'amari tabbas sun dad'e suna so su kama koda d'aya ne daga cikin wad'anan mutane domin su kafa hojjoji kana kuma su tsaurara bunkice akansa domin ya sanar musu inda sauran 'yan uwansa suke.....Saboda haka hatta da mataimakin shugaban 'kasa sai da yazo ya duba Sadam! kuma ya jinjina masa a bisa namjin kokarin da yayi....Sannan ya sanar dashi sakon mai girma President yace."Yana gaishe shi da kyau kuma yana jinjina masa hakika ya cika gwarzon maza.......Wannan al'amari yayi masifar 'batawa 'yan adawa rai mussaman Captain Saleh wanda shine mutumin da ya rufe kwatar da silaf din duk dan kar ya samu hanyar fitowa, Sadam! na da ma'kiya a gurin aiki sosai da sosai don wasu ma basu zo duba shi ba sai kananun maganganu ne ke tashi.......A can 'bangaran gida kuma tun misalin karfe takwas na dare suke kiran wayar shi sai dai Captain Habu ya dauka yace."Baya kusa Hjy Fatsima data gaji sai tace Ya fada mata gaskiya idan wani abun ne ya faru Captain Habu ya boye mata....Tun sannan suka sha jinjin jikinsu Sayyada kuka ta hau yi! Hajiya Fatsima ke rarrashinta da ta kwantar da hankalinta babu abinda ya faru.....Alhaji Auwal na kasuwa labai ya riske shi cewar sojoji sunyi nasarar kama dan boko haram! cikin kasuwar bacci amma kuma daya daga cikinsu ya jikkata domin dan boko haram din yayi nasarar harbinsa a kafada.....Ba tsaya wasa ba ya nemi numbar d'an sa to shima dai captain habu ne ya dauka nan yake tambayarshi ya ake ciki Captain Habu yace babu wata matsala insha Allah ya nemi da ya bashi Sadam! din sai ya hau kame kame! kashe wayar kawai yayi ya nufi gida....Yana isa ya tarar dasu cikin tashin hankali da damuwa domin suna zaune suna kallon labarai tashar Bbc news suka nuna Sadam! din akwance kirjinsa daure da bandeji yana jawabi da yanda abun ya faru.........Duk suka tashi hankalinsu Sayyada sai kuka takeyi sai an kaita gurinsa, Sulaiman ne ke rarrashinsa idan ka ganshi sai ka dauka ya damu da al'amarin amma a cikin ransa dad'i yake ji sosai yaso Sadam din ya she'ke barzahu sai ya samu damar auran matarshi Sayyada.
Hajiya Fatsima ta sako hijab suka nufi barikin sojojin domin duba halin da d'ansu yake ciki.....Ganinsa zaune yana shan yoght sai hankalinsa ya kwanta Captain Habu ya gaisa dasu Hajiya Fatsima tace"Ka kyauta wato shine ka'ki yi min bayani abinda ya faru sai a tv na gani."
Yace."Mamah ai abun alkairi ake fad'a shiyasa ban sanar daku komai nasan da na fada miki a lokacin zakice zaku zo to ganinsa a wannan lokacin zai d'aga muku hankali shiyasa muka bari sai da aka gama komai tukkuna."
Alhaji Auwal yace."Alhamdullahi ai da sauki ma al'amarin Allah ya kare ku ya kare ya kuma baku nasara a duk inda zaku shiga." Captain Habu ya amsa da ameen kana ya fita ya barsu domin su gana.
Sayyada gefansa ta zauna tana ta kallon kirjinsa inda aka harbe shi tsigar jikinta sai tashi takeyi hawaye kuwa wannan na bin wannan...Sulaiman ya gyada kai ba tare da yace wa dan uwan nasa komai ba ya fice daga dakin ya tsani yaga Sayyada na kusantar inda Sadam! yake. Motarsa ya shiga ya bar barikin sojojin.....A nutse ya gaisa da iyayen nasa yana musu 'karin bayanin kan yanda al'amarin ya faru...Hajiya Fatsima sai da tayi kuka tace"Ni kuwa Da zaka bi shawara ta to da ka ajiye aikin nan Sadam! akwai had'ari a cikinsa." A take ya 'bata fuska yace."Mammah bana son kina irin wannan magana wallahi! tunda na fara wannan aiki bana fata in aje kuma wallahi wallahi wallahi bana yi domin kudi ko wata daukaka ko mukami inayi ne kawai saboda 'kasata Nejaria sannan inayi ne domin taimakon al'umma addua kawai nake bukata a gurunku." Tace"Shikkenan Sadam! Ubangiji Allah ya shige maka gaba Allah ya kare ku a duk inda kuke ya tsare gabanku da bayanku." Suka amsa da "ameen." dukaninsu.......To koda suka tashi tafiya Sayyada ta'ki binsu akayi akayi ta'ki sai ma ta haye kan gadon ta 'buya a bayansa .Alhji Awal yace."A kyaleta ta zauna Sadam! bai so haka saboda abokanan aikinsa na shigowa duba shi to dan ba yanda zaiyi yasa ya hakura suka tafi suka barta.
To a cikin mota iyayen maganar suke inda Hajiya Fatsima take cewa''Ni kuwa rashin jituwar Sadam da Sulaiman na bani tsoro Alhaji yara kamar ba 'yan uwa ba ka duba ka gani Sulaiman ne ya dace ya zauna yayi jinyar dan uwansa amma ka lura ko minti biyar baiyi ba ya fita kuma bai ce masa sannu ba wannan al'amari ya 'bata min rai kuma babu babban mai laifi sai Sulaiman din tunda dai shine babba."
Alhaji Auwal yana draving yace."Kin san Sulaiman akwai sabga mybe kiransa akayi a waya shiyasa kika ga ya fita bai zauna ba amma na tabbatar zai koma ya duba shi