Showing 24001 words to 27000 words out of 115099 words

Chapter 9 - Bamu kadai ba ne book Complete by Zainab Makawa .txt

16 Dec 2024

6668

mata aka diba aka kara mata zuwa karfe uku mukai ma mutanen godiya suka tafi.
Nan ya zauna damu yace ranan a gurin mu zai kwana tare da mu nan ya kwana asibiti da biyu ga tsoron gida ga jikin yarinyar dake wahala sosai.






ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
[10/27, 10:48 PM] Zuraiyah Zuzu ๐ŸŒŸ: ๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ง ๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ฆ
BA MU KADAI BANE,,,
๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ฆ ๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ง
9โƒฃ




An sallamo mu daga Asibitin likita yace bayan sati daya mu dawo akara dubata a gani yadda ta kara ji.
Makwabta suna ta shigowa gaishe mu da dawowa har da wanda bamu hurda dasu.
Halin rayuwan barki ke nan sai ku zama yan uwa a tsakanin ku da kuke a shiya daya.
Yanzun tun dawowa na na ga Baban Abba sai yawan ce min yakeyi kifa rika yiwa yaran nan addua idan zaku kwanta.
Na kance mai ai ina masu addua yaran da yasa mu raba daki dasu yanzu naga ta koma cewa na dinga masu shimfida a kasa su kwanta daki daya damu.
Ni dai ban tambaya ba na dauka dai duk wani abune yasa yake hakan.
Kwanan mu hudu da dawowa gidan ranan cikin dare gidan arna kun nan kusa da mu wani sabon al,amari ya faru kuma.
Muna barci da dare ihun su ya tayar da mu nace kai a fili amma kafirci baiyi ba wallahi wanan ai daukan alhakine.
Nakai kallona ga agogo karfe sha biyu da rabi na dare nace ikon Allah yau kuma komay ya faru haka dasu.
Can dai na dinga jin hayaniyan yai yawa nafito falo don duk yara sunyi barci a lokaci ga maigidan bai gida sun tafi operation wani baki ruwa can wani gari.
Window din falon mu na dan daga naga mutanen quarters din sai zuwa gidan zukeyi daya bayan daya duk da dare ya farayi sosai a lokacin.
Can na hango yar sokoto da anty ta window shine ya sani fitowa daga gidan nima amma ban isa kusa ba na tsaya daga kofan mu ina kallo.
Wai ashe matar gidan ce duk kwanakin nasai wasu kyankyaso guda biyu sun cije ta idan tana barci sai taita ciwo ba gaira ba dalili.
Shine ranan ta kwanta da abu a kusa da ita batai barci ba kyankyason na fitowa Allah ya bata sa,a takai masu bugu suka fara shure shure.
A can dakin da yaranta suke a kwance taji ihu tana zuwa tasamu yaran kamar yadda kyankyason data buge suma suna shure shure a dakin shine ta saka ihu.
Ganin na fito yasa Anty da yar sokoto suka dawo inda nake tsaye muka tsaya a tare dasu don mazajen su suna cikin gidan a lokacin.
Muna gurin aka dauko pastor din su na kiristan yazo gurin nan ya shiga irin saddabarun su take yaron nan John ya fara bayani kamar haka.
Yana cewa shi da kaunan shi yan cult ne sune suke zukewa uwar su jini duk dare saboda an saka suyi hakane daga kungiyar su.
Yace yar uwar shi Stephener ta daure baban su shiyasa kullun baida lafiya.
Pastor din yace a ina suka samu wanan abin yace a school ne abokin shi ya bashi sweet yasha shine ya ga kanshi a cikin group din.
Ita kuma kauna shi anty din class din su ce ta saka ta a group din cult ta basu biscuits shi ta shigar dasu.
Duk wanda ke gurin sai da hankalin shi ya tashi a lokacin nan yaron ya shiga bada labarin abubuwan sherin da sukeyi wa mutane yace harda accident din da makwabci su na farko yayi ya mutu sune suka kashe shi.
Kwanaki ma ciwon da yayi yaje ne ya kashe sabuwar makwabciyarsu da take saka wakan musulmai a gidan ta wanda abin yana matukar damun su .
Shine ya samu ashe tana da sprint masu karfi a tare da ita agidan har suka kusa kashe shi.
Yace yaso ne ya kashe matar har yaran ta don tunda suka shigo quaters din nan yake jin haushin su don yaran ta sunfi su sa,a.
Pastor yace saboda may kake son kashe su basuyi maka komai ba yace ban son sune yaranta suna da baiwa da yawa wanda shi baida irin shi.
Pastor ya tambaye shi yaya sukewa baban su yace sun daure shi ne sosai don yaso ya gane su shine suka mayar dashi hakana.
Hankalin mutane yai matukar tashi sosai dajin yadda karamin yaro da baikai ko goma sha ba yake irin wanan ketan har da mahaifan shi.
Mata don Allah mu saka ido akan yaran mu mu hana su cin abin hannun wanda ba jinin su ba,ako ina.
Yaron yace wa pastor din ai idan suna son suyi cuta sukan zama babban mutum ne su dinga rabawa yara sadaka gurin amsan sadakane suke jayewa yaro destiny din shi gaba daya.
Basu kadai ba har da,wasu witches suna hakanan yaron yace.
Da kyat da addua aka samu hankalin yaran ya dan dawo gare su aka kwashe su zuwa church su da daren nan don yin irin abin su can.
Nan mijin anty da suka fito suka samay mu suke bamu labari nace mun shiga uku may mukai wa yaran nan haka kawai su tsane mu har suna batun kashe mu.
Labari ya kai ko ina dasafe zancen ne ko ina akeyi wanan abin mamakin da Baban su Abba ya dawo ne mijin anty yake bashi labari hankalin shi yai matukar tashi sosai da garin ma gaba daya.
Yace wai maryam kodai don mun zo ba dason ran Umma bane muke ganin wanan jerabawan haka wai ?
Nace nima nayi wanan tunanen a baya shiyasa ake cewa duk abin da yaron ka zai yi inda ba wanda ya sabawa addini bane kabishi da adduan fatan alheri kawai.
Nace da yardan Allah ubangiji ba zai bari wani abu ya cuta muna ba na,sheri Allah yana tare da mu insha Allahu.
Mun kai wani lokaci muna maganan wanan irin rayuwa yai ma yaran fada sosai tare da tsorata su akan duk wanda ya basu abu kada su karba kada ma suyi hurda da mai shi kawai.
Duk suka tsorace kowa na fadin ni dai ba zanci bama zan karba ba gaba daya.
Washe gari zamu koma kai Nusai ba ganin likita don haka na tashi da,wuri na kammala komai da zanyi muka wuce asibitin.


****** ********* ******
Muna zuwa muka samu mutane sosai a layin nan yake ce min idan ya tsaya zai makara zuwa gurin aiki .
Don haka na karbi kudi idan mungama na dauki drop zuwa quarters din mu zan iya ko nace zan iya tunda drop zan dauka akaini har gida.
Bai dade da,wucewa ba Nusaiba ta falka ta fara min fitina duk ta rudani saboda kukan da takeyi.
Haka yasa na dan fito daga waje ina lalashin ta na dauko ruwa na bata akwai wata mata da muke zaune kusa da juna ta dan fito daga waje itama take ce min ta falkane nace mata eh wallahi gashi sai kuka take min tundazun na rasa gane may ke damun ta.
Matar tace nakawo ta tagani na mika mata ita duk da nasan halin yarinyar da kiuya ba yarda zatayi ba da ita.
Amma abin mamaki sai ta tafi gurin matar harda lafewa a jikin ta tana,sauke ajiyan zuciya a hankali.
Matar ta dago kai tana murmushi tace yaro ke nan da ace zaku kaita wurin maganin gargajiya da zaifi kila ta samu lafiya.
Don gaskiya ciwon ta bana asibiti bane wahala kawai kuke yi anan din amma gaskiya sai gargajiya matsalanta.
Nace cikin murmushi ni ban san kowa ba a garin nan don mu bakine mijina ne kawai na sani shima ba kowa ne yasani ba don bai ma da lokacin zama.
Tace da zakiyarda dani dana taimaka maki nakai ki wani guri insha Allahu za,a dace da yarandan ubangiji amma sai idan kinyarda da Allah kin yarda dani.
Abin da da mahaifi gashi naga yadda take wahala ba sauki kullun ace ba jini a jikin ta.
Yasa nace ai ba matsala tunda kince Allah gurin baida nisa sosai ko tace nan ne kusa sai muyi sauri muje kafin layi yazo kan mu mun dawo insha Allahu.
Nai mata godiya muka fita tare zuwa bakin titi a daidai wani dan kiciron naga ta tsaya saiga wani taxi yazo ta tsayar dashi tare da fada mai sunan gurin da zamu tafi din.
Muna shiga take ce min idan zaki watarana a daidai nan gurin zaki tsaya anan zaki samu taxi din da zai kai ki gurin.
Tafiya mukayi bamai dan nisa ba sai ga mu a,wani dan kauye can bayan gari.
Tace a sauke mu a wani guri muka sauka mukaidan tafiya gurine kamar kauye.
Munzo dai dai wani gida ne take ce min bari don Allah mu shiga gidan nan na,gaidasu.
Gida ne irin na kauye ga itace ankewaye a darnin gidan dake da zana ga icen zogala dana,aduruku duk ya kewaye gidan gwanin ban sha,awa dashi cikin gidan katon icen cediyane ya baje yai innuwa gwanin ban sha,awa.
Matan gidan su uku ne daya tana daka a wani irin turmi da ban taba ganin irin shi ba sai a gidan.
Daya tana sharan tsakar gida dayan tana wanki tufafi a duke jin sallaman mu ne suka daga suna cewa ,a,a maraba da mutanen saudiya ashe kun dawo garin.
Muka zauna dayan ta karaso tana cewa Mukaddarasiyatu yaushe kuka dawo ina su baba tace duk suna lafiya nima na dawo ne na gyara gida kafin su iso garin.
Sai faman kallona sukeyi na gaidasu suke tambayana yaya gida au bakuwa kika samu ne mukaddarasiya tace eh makwabciyata ce wallahi yar tace bata da lafiya muka zo ganin baba.
Sukace malam malam yana nan yanzun ma nasan yana can da yaran suna karatu don basu taso ba tukun.
Dayar matar ta debo muna ruwa a tulu ta kawo muna sai abokiyar tafiyana take cewa ita a koshe take nikan na karba nasha kada suga bamu sha ba dukkan mu.
Ruwa ne da zance ban taba shan irin shi ba don dadi kamar ba,a randar kasa aka deboshi ba ga gardi ga sanyi kalau.
Nasha sosai nai masu godiya tare da,aje kwanon dayan tace a tana da kirki matar dole ki taimaka mata gaskiya.
Nan mukai sallama da matan muka fita suna bina da kallon mamaki wanda ni ban sani ba.
Tafiya muke da kafa sai faman gaida matar ake a cikin mutunci haka yasa na gane matar tana da daraja a garin kodon ance a saudiya take zaune ne yasa haka oho.
Wani dan lungu muka shiga wanda tun daga nesa muke jin sautin karatun yara yana tashi.
Makaranta na hango irin na allo din nan yarane bila,adadin baka ko ganin iyakar su nai mamaki yadda dan wanan kauye haka aka,samu irin yaran nan haka da yawa gurin nan.
Wani tsoho ne na hango tsakiyan su fari da fararen kaya yana zaune a saman wani kujeran katako wanda tun muna yara nasan irin wanan kujeran a garin mu yanzu babu irin shi ma nake gani.
Kujeran katako ne na da wanda tsakiya ansa mai atamfa sai ana iya nade kujeran idan an daga sama ganin yana bada karatu tace mu shiga daga cikin gidan.
Mun shiga da sallama mata su biyu a ciki kamillaun mata dasu masu daraja kamar ba,a kauye suke zaune ba in ka gan su.
Mun gaisa dasu cikin mutunci suke mata sannu da,dawowa tare da,tambayan ta sauran mutanen gida.
Sai faman kallo na sukeyi da mamaki can dayan tace ina kika fito bani adama mukaddarasiya ?
Tace cikin murmush makwabciyatace yar ta bata da lafiya shine mukazo gurin baba ya ganta.
Dayar ta mike can sai gata da,ruwa a kwano ta kawo muna matar da muke tare ta karbi ruwan tasha ta miko min duk da na koshi amma na karba na kafa kai na zuka sosai.
Zan iya cewa ban taba shan ruwa mai dadi irin wanan ba a,rayuwana sai yau gardi dadi da,sanyi naji.
Na aje kwanon cikin jin dadi nace nagode haba bako ai rahamane ga kowa ke bakuwar muce ai.
Suka ce kaman wa yancan na farkon gidan da muka,shiga a,a ba laifi tana da mutunci gaskiya dole ki taimaka mata.
Sai ga wani yaro yashigo cikin gidan yace wai ance bakin su shiga malam yana jiran su a waje.
Muka mike muka shiga ina malam din yake tsohone sosai mai farin gemu yana zaune ya hakimce cikin kamala ta malaimai.
Wani irin sanyi naji a furin kamar an,sa A C masu yawa gurin sai dai babu komai a gurin .
Muka gaisa dashi ya kura min ido cikin murmushi yake cewa ikon Alkah yau zurian Amina ne a gida na.
Nai matukar mamaki yadda yasan mahaifiyana haka kai tsaye yake cewa Mukaddarasiya ashe kin dawo yaya su wajen iyayen naki tace duk suna lafiya.
Yace yauma kinyo barnan naki ko ban san mayasa kin san kina da tausayi ba kuma ke taba diyan Bil,adama haka ?
Tai dan murmushi tare da dukan da kanta kasa tace wallahi malam akasi aka samu banice na taba taba su ba wallahi.
Kasan yaran nan basa ji aikin Zalkafllahi ne shiyayi wanan aiki duk da nai masu fada amma sai da ya yaba mata yara.
Yace ai ku din da ace kun san ko yar waye ita din da baku taba taba wallahi nijin sherck Mustafullah ne fa ita.
Da sauri matar ta kalle ni tace haba naga alama tana da kafuwa sosai itama.
Yace muga yarinyar ko na mika mashi ita cikin ladabi ya karbeta yana mata wasan jika da kaka yana yi yana shafan bayan yarinyar da jikin ta zuwa kafan ta,a hankali yana yarfawa gefe can ya dago ta yana shafan kanta shima kamar yana mata wankin kai yace don Allah ki bar ta mutanen nan makkaddarasiya idan kika kara kawo min wani kin mai illa dake da mai shi bazan kara ko kallon ku ba na fada maki.
Nan dai bamu bar gurin ba sai ga Nusaiba harda rarafen ta tana,wasan ta hankali a kwance abinta mukai mai sallama na tambaya nawa zan bada tsohon yai murmushi yace kai haba aike yar muce jikan mu Allah dai ya tsare gaba kinji yakawo wasu ganyyaiyaki kuli yabani yabani wani abu kamar mai yace na shafawa duk yarana muyi amfani dashi.
Mukai mai sallama yace idan wanan ganyen yafita baki na dawo na kara amsa mata don sau biyu za,ayi matar sai faman godiya take wa tsohon.
Bamu jima ba sai ga mota a hanya muka shiga kamar kiftawa da bisimillah sai gamu a bakin asibitin.
Layi ya kusa kawowa a kan mu da layi yazo na,shiga likita yace wonderful mai kuka bata haka gashi komai nata ya dawo normal da farko fa na katsewa yarinyar nan taku ne ban dauka ma zata kai wanan lokacin bata mutu ba,wallahi a yadda naga ta koma.
Nafito ina neman matar nan muyi sallama kuma in mata godiya sai dai matar bata nan babu dalilin ta na tambayi matan dake wajen ko sun san inda ta tafi sukace su basu ga wata mata ba gaskiya bayan ni.
Nai tsuki na ce shirmay ku dai kuna ta kanku amma na shigo da mata yanzu muke nan fa da ita na shiga na barta zata shiga idan nafito.
Basu tanka min ba na fita ina bakin cikin rashin kara yi mata godiyan da banyi ba gashi naso na bata labarin abinda likita yace min.
Nafita daga asibitin ina maijin dadi nace watau dai na,Allah basu karewa a duniya ke nan.
Ina zuwa gida na dora tukuyan magani kamar yadda tsohon nan ya fada min nai mata wanka na bata tasha na shafe ta da maganin daya,bamu.
Haka ma sauran yaran suma nai masu wanka na shafe su da maganin da aka bamu.
Da baban Abba ya dawo na labarta mashi haduwana da matar da inda muka je yace kai amma maryam ban taba sanin baki da,wayo ba sai yau.
Kin kuwa san inane kaduna kuwa kaduna fa ba Auna bane don sai a batar dake da yarki har abada kuwa.
Nace nikan wallahi tunda naji tace tsakani da Allah zata taimakeni shiyasa har na yarda sai dai ban fada mai komai da ya faru ba acan da mukaje.
Tun lokacin Nusaiba taji sauki sosai sai wasan ta takeyi niko tun ruwan da nasha a kauyen duk nasha ruwa sai naji kamar ruwan toka nake sha babu dadi kamar wancan dana sha a kauyen mai dadi.
Yanzun kuma banjin komai a gidan ban kuma jin tsoro ko darr a raina na sake abina ina sha,anina.
Shima baban Abba har yana batun canza gida amma yadda yaga na sake yasa ya dan kwantar da hankalin shi.
Gashi yaga yadda muka saba da su anty da yar sokoto mun koma kamar yan gari guda muke dasu.
Wanan yawan motsin da,nake ji a dare ban fasa jin shi ba kuma ban damu ba don ban fitowa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login