Showing 6001 words to 9000 words out of 115099 words

Chapter 3 - Bamu kadai ba ne book Complete by Zainab Makawa .txt

16 Dec 2024

6631

Nan nake fada mata abin da ya faru tsakani na da Laure daga neman gishiri ya zama min alkakai a gurin ta.
Innan sahura dake ta kofa a duke take cewa aiko da kashin ta ya bushe idan ta taba diyan malam a garin nan.
Ita batasan kunfi karfin ta bane wai da zata jinjina ki haka mama dake sauraren mu tace wasa dai amma watan jin kunyata ko na tsayawa in takai gare ku.
Mama tace kwanaki mijinki yazo yana gayawa malam yana son ya tafi daku can gurin aiki ko ?
Na dan tabe bakina ce eh haka yaso mama sai anty tace wai dako nai maki murna maryam.
Nace amma ai Umma ta hana anty lokaci daya suka hada baki suna fafin ta hana fa ta hana may zakiyi mata in kin zauna nan.
Na marairaice nace to nima ban sani ba sai dai ina ganin kaman saboda yaran nan ne bata son mu rabu kawai don shakuwa.
Don ko yanzun da zamuzo saida tace dukkan mu zamu kwashe mu bar mata gidan.
Oh lalai shi takewa amma banda abin Ige ai hakan da yayi shine dai dai ko nace haka dai Baba yace yanzu ai.
Kawai gaskiya baba yai mata magana inji anty na tace ta yaya zatai maku haka idan kin zauna nan ba wata zai karo muku can ba tunda yana da muradin zama da iyalin shi kusa dashi.
A marairaice nace ni dai yanzu wallahi duk a rude nake don gaskiya kodan karatun yaran nan a can zaifi.
Gaskiya dai idan tai maku haka bata kyauta maku ba dai wallahi dole ne ai mata magana ko zata sake shawaran ta.
Nace yanzun dai yace idan ya dawo idan ta yarda damu zai tafi idan kuma bata yarda zai samu wata a can ya zarga da ita.
Kai ba za akai ga haka musan bamu hana shi aure idan ya tashi amma aikece zata cuwa gaskiya haka ba adalci bane.
Nan dai muka wuni muna zancen akan batun tafiyan har sisters dina suna cewa wallahi ke ta samu anty maryam da mune ai sai dai ta wayi gari kawai mun tafi abin mu.
Wanan mara kunyan zata iya shi inji Innan sarahura tanacewa sahuran dake magana to bake bace dadin abin ke nan ita tana da ta ido.
Sai da la,asar mukai masu sallama muka tafi lokaci daya mula fito da anty na daga gidan tana kara jadda min cewa na fa dauki mataki kada na yarda da zancen Umma nace haka za,ayi ai anty takama hanyan gidan su nima nabi nawa.
Mun samu har umma ta aza min girki ko ina cire hijjab dina na fito don na
karba a hannun ta.
Nan nake fada mata mun hadu da laure ai da zamu tafi take cewa aniyar ta dai yabita wallahi.
Nagama na kwashe kamar yadda muka saba yi kafin magariba na gama komai muka shige daki saboda tsaro.

****** ********* ******
Yana gurin aiki yake fadawa abokin shi zancen son ya dawo da iyalin shi da yakeyi garin.
Mutumin yace kai amma kan ka kyauta gaskiya zama kusa da iyali shine kamalan namiji wallahi kuma zasu samu inganttacen rayuwa bisa ga zaman kauyen da suke a can.
Yace sai dai gidan dana samu ba mutane sosai a gurin don can sabon easte din da aka gina ne a yakubu gawon road na samu gida.
Aiko gurin ba laifi kaga ma ba nisa sosai da nan office din namu zai maka sauki sosai zuwa office.
Kawai ka kama abinka idan gurin yai maka kyau da sannu zakaga mutane sun cika gurin ai.
Akwai wani a malali yafi cikin mutane sosai amma dai wancan sabon easte din yafi kyau sosai gaskiya.
Mutumin yace yafi kyau mana kasan an dade da gina su amma ba bude shi ba dai yanzun aka fara shiga.
Yace kawai dai maganan shi zanyi da na bar nan gurin zanje gurin inchage din gurin muyi magana dashi.

Muna zaune a dakin umma da yamma ya bugo waya suka gausa da faranta ga fuska suke gaisuwa da umma din can ban san may yace mata ba sai ji nayi umma na fadin kai kana ga zancen tafiyan ne wai har yanzu.
Na fada maka ban da ra,ayin wanan tafiyan nasu can wani uwar duniyan na daban.
Nafison ina ganin su a gidan nan a tare dani idan ka kwashe su ni dawa zan zauna a gidan nan.
Ka tausaya min mana Baba kai dai fa Allah yabar min nake gani sai yanzun da kadamu iyali kuma suke debe min kewan ka.
Ina ganin ce mata yayi to shikan sai dai yai aure don ba zai iya zama shi kadai ba don yagaji da hakan.
Sai cewa umma tayi kaje kayi mana idan haka kaga yafi maka daidai a rayuwan ka.
Wani irin mugun faduwan gaba naji a raina nace may umma take nufi da nine wai so ne haka ko dai kiyayya take min .
Ranan ban mata ko sai da safe ba na mike abina na bar dakin tare da daukan Nusaiba a kafada na.
Daki na koma sai kuka na kulle kofana ban sake fitowa ba again sai faman tunane nakeyi kawai a raina ni kadai a daki.
Washe gari ma ban fito ba ina daki kwance har rana ya haska sai jin muryan umma nayi tana fadin oh yau maryam bazakiyi muna ko abin karin bane ?
Gidan ko shara babu ban amsa mata har takai ta kawo kofan daki ta daga labule ina kwance na kunna redio ina saurare zabi sonka da akeyi a tashan redio kwantagora.
Daga labulen da tayine tana fadin maryam yau ko lafiya kike ne na dan zauna kadan saman gadona nace lafiya nake Umma.
Toowoo ko maganan da kika ji inayi da,Baba na jiyane kike wa fushi haka hmmm maryam baki gane manufa tane ke.
Ke da,yaran nan fa kukadai nake gani inji sanyi ina zan barshi ya,kwashe ku zuwa wata uwar duniya can.
Ni yadda duniya takoma yanzun ne nakeji wa baka kwana da mutum ba ya tashi dakai a ranshi.
Ga kaduna ba karamin gari bane tun can baya don mu acan ne muka,fara jin labarin yankai kai da sace mutane .
Nace Allah ya tsare mu umma amma dai ai bamu kadai zamu zauna ba aiko?
To abun har yakai can to fito kiwa yaran nan girki su karya rana tayi ni na gama magana ta.
Yaje can yasamu yar barikin da yace su zarga a tsakanin su yafi min sauki nikan.
Wani iri naji a raina haka na mike banda yadda zanyi don ban iyayiwa umma rashin kunya naje na dora masu girki abin karyawa.
Haka muka wuni ina share umma a gidan sai magana take sake min idan yyara sunyi abu nai masu fada sai tace kai ku kama kan ku kada a fashe haushin daba naku ba akan ku yau.
Bayan kwana biyu anty na tazo don taji yaya mukayi akan zancen tafiyan namu nake cewa cikin kuka wallahi anty tana akan bakan ta ta hana.
Don a gaba sukai waya dashi take cewa yaje ya nemi wata can a,bariki ya aura.
Kai ashe haka matar nan take wallahi ni har ta zube min Allah ashe bata da imani bari zanje gida zan fadawa baba halin da ake ciki ai.
Shiya hankalina bai kwanta ba nace bari nazo naji may ake ciki akan zancen don mu sanan abin yi kafin ku tafi don naga wata ya kusa karewa nasan zaizo ke nan.
Nace wallahi anty babu zancen don ta hana tafiyan tace bazamu tafi mu barta ita kadai ba.
A,a tace dai dama ita kike aure ba Aliyu ba ke nan da zata fadi haka kai tsaye.
Ko da anty na zata wuce umma taga canjin fuska sosai a gurin ta don batai mata yadda ta saba ba inda tazo gidan.
Direct anty na gidan mu ta wuce can take fadawa iyayyen mu yadda mukayi da Umma kan zancen tafiyan mu kaduna.
Aiko sukai ta yanka fada suna aibanta umma da halin da ta tsiro suna fadin bata sona ashe duk sallon yaudara ne kawai.
Sai da baba ya shigo gida ake fada mashi abin dake faruwa dani murmushi yayi yace kubarta ai zan ganta muyi maganan naji hujjan ta.
Haka dai baba ya kashe maganan ya hana kowa ya kara magana sai yaga umma din.
Aliyu ya bugo waya ban iya dauka ba sai kukan da nakeyi kawai hankalin shi ya daga ya shiga tambayana may akayi may ke faruwa ne wai.
Na kasa magana sai dakyat nace mai ni abinda umma ta yanke a kan mune bai min ba ai wanan ba so bane ko gata gare mu.
Maryam may ye abin tayar da hankali ga zancen nan ba ina zuwa gurin kuba duk karshen wata yanzun fa haka jibi ma zab shigo idan Allah ya yarda.
Kada ki bari ajiku da umma ai maku dariya don son da Umma taje min ne ya koma a gare ku ai.
A raina nace wani so ko kiyayya dai da yarta ne ni aida batai min haka ba wallahi.
A fili cewa nayi ai baza aji mu ba amma ni dai gaskiya naso mu dan zo ko ma dai don miga gari kawai.
Hakuri yabani yace mu bar zancen har yazo zai san yadda za,ayi idan bata yarda ba sai a hakkura mu zauna kawai.
Nikan sam umma takasa gane kaina duk kwanakin nan harda dan kwaliyan da mukeyi idan zayazo yanzu wanan zuwa da zaiyi duk banyi ba hakana na zauna komai ban anyana ba akaina har yaran dagidan ido kawai tasamin tana kallona .






ZAINAB IDRIS MAKAWA
[10/27, 10:48 PM] Zuraiyah Zuzu ๐ŸŒŸ: ๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ง ๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ฆ
BAMU KADAI BANE A GIDAJEN MU,,,,
๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ฆ ๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ง
4โƒฃ


Yashigo garin yadda ya saba amma kuma shi kan shi yanayin da ya riske mu ciki ya bashi mamaki sosai don ba haka ya saba samun ba don ko wanka ma ranan ban wa yaran ba har ni ina daure da wani tsohon zanin goyon Nusaiba a jikina.
Sai bina da kallon mamaki kawai yake yi haka na shigo na dangware mai abinci tare da gaishe a tsatsaye n fita yabini da kallo har na bace mai ya sauke ajiyan zuciya kawai.
Umma tana gefe tana kallon mu sai cewa tayi ikon Allah ko wai duk fushin tafiyan ne haka fa.
Niko ba inda zasu su barni gidan nan ina nan a tare dasu idan ma ba rashin tausayi irin na maryam ba da take son kwashe yaran nan su barni da kewa.
Haka yadda ka ganta haka ta koma ba maijin dadin ta a gidan nan dagani har yaran nata.
Duk da baiji dadin maganan Umma ba amma kuma sai da yaji haushi irin hukuncin dana dauka kan dan maganan da bai kai ya taka kara ba kawai.
Da dare ma ba wanan taron da rawan jikin da na saba mashi a baya can haka yai rawan shi da kidan shi ya,barni na juya mai baya kawai .
Don yanzu daga shi har umma daukan su a makiyana nakeyi a gidan na,fahinci zaman amfani kawai dani sukeyi a nawa fahinta.
Ina jin su da safe Umma tana ta sirfa masifa wai bazata dauki irin wullakancin da na dauko yiwa jikokin ta ba.
Aliyu yana fita daga gida gidan mu ya,wuce gurin babana bayan sun gaisa dashi ne yai mashi sannu da zuwa tare da tambayan shi lafiyan mu.
Yai dan murmushi yace suna lafiya sai dai ita maryam din ne nadawo na samu a cikin wani yanayi.
Babana yace subbahanallahi na kamar may kuma ?
Yace wallahi gaba daya ta sauya baba kamar ba maryam ba saboda kawai zancen tafiyan da Umma tace bazasu tafi ba can inda nake aiki dana so zuwa dasu.
Murmushin manya babana yayi yace kai yaro dai yaro ne ita maryam ina ta samo wanan halin nata kuma haka don ban santa da halin banza ba a baya.
Aliyu yace hakane baba shine nace bari na fada ma a dan tsawata mata ta,daina kada su samu sabani da Umma nan gaba.
Babana yace ba matsala zanzo gidan yau da yamma insha Allahu kafin na zauna karatu.
Sukai sallama yakawo kudi kamar kullun idan yazo gaida baban nawa yakan dan bashi har dasu Inna wani sa in yakan shiga yadan basu su ma.
Bai dawo gida ba sai bayan sallah azahar yana,waje da,abokan shi na gida a,waje karkashin darbejiya sun shinfida babban tabarma akai.
Yana shigowa ina alwala yake cewa wai na zuba mai ruwa butan kawai na karba na zubo mai ruwan na mika mai.
Murmushi kawai yayi ya karbi butan don bai taba ganina cikin wanan halin ba sai a wanan lokacin.
Kamar yadda, baba yai alkawarin zuwa gidan namu sai ko gashi da yamma tare da,yarashi biyu a,bayan shi masu daukan karatu a gurin shi.
Umma yace ace anawa sallama baban maryam nan umma ta hau fada tana fadin yo karana akai ne gurin malam kuma?
Lalai zance yakai to ni babu mai hadani da hatimi in lalace rayuwa na ya tashi ga banza.
Daga waje Baba yana jin ta sai murmushi kawai yayi aka fito da tabar ma aka shimfida masu a waje.
Can tafito tana yafe da zani irin wanda ta daura a jikin ta kamar ba itace tagama sababi a cikin gida ba.
Sun gaisa tana durkushe daga gefe tana fadin malam yau kai da kanka kazo ai da ka aika nazo koma may nene.
Malam yace a,a ba gurin ki nazo ba gurin yar ki maryama dai nazo don irin sabon halaiyar da naji ta tsiro dashi.
Sai lokacin Umma tai murmushi tana cewa kai maryam maryam ai ba,wasa.
Gaba daya ta hana zuciyar ta sakat kan zancen wai sai tabi mijin can inda yake.
Shiru baba na yayi har umma tagama kawo hujjojin ta na rashin yardan ta ga tafiyan mu.
To amma maman Aliyu bakiyi wa yaran nan ko adalci ba don yaron yanzu harkaji ya furta abinda ya dace da bakin shi to kamata yayi ayi dubaiyya ga alamarin.
Amma yadda kika yanke masu wanan danyen hukunci haka ai dole ne yarinyar nan ta dau zafi haka gaskiya.
Daya daga cikin wanda suka takawa babana baya ne ke wanan maganan haka.
Umma ta dukar dakai babana yai gyaran murya yace to walilllahihamdu ban so ace nai wanan magana yanzu ba don bashine ya kawo ni ba yanzu.
Yanzun tafiyan maryama ce ya kawo mu amma kuma sai gashi ke yanzun kin fito da zancen da kan ki.
A gaskiya maganan malam iro ne abinda zamani yazo dashi mu yanzu sai hakkuri.
Ko azananin da can baya nisanta da namiji da iyalin shi babban hatsari ne balle a,wanan zamanin da muke a cikin shi na karshen zamani.
Ai sai naga kamar a gareki wanan nufin na yoron nan Aliyu abin farin cikin ki ne sosai yau da,bakin shi yazo maki da kudirin zancen son tafiya da iyalin shi a kusa dashi .
Ai sai kawai abisu da addua da fatan alheri a gare su na gamawa da duniya dafatan albarka ga zuria.
Umma tai shiru kawai tana,sauren irin nasihan da baba na yake zuba mata har yakai karshe yace sai abar zancen tunda baki ra,ayin tafiyan.
A turo muna ita maryama din mugan ta sai mu tafi kuma don Allah aita hakkuri don Allah halin yaran yanzu sai su.
Yanzu diyan zamani diyan agwagi ne suna gaba uwarsu tana baya haka yaran yanzun suka koma .
Sai abinda zuciyar su ke so shine ra,ayi su ya zaba masu zabi suke gani.
Umma ta mike tana cewa ta gode tashiga gida ta turo ni nazo na samu su babana ina gaishe shi ya amsa min dakyat tare da fara min fada kan sauyin da nayi da mutanen gidan mijina.
Har baba ya kare min fada da nasiha ina duke sai kuka nakeyi a hankali kawai.
Bayan babana yatafi ne da dare Aliyu ya,shigo Umma ta haushi da fada wai dani dashi mun hada baki munyi karanta gurin mahaifina.
Mutumin dake ganin ta da mutunci amma saboda son zuciyar mu don bamu tausayin ta muna son rabata da jikokin ta zamu ce sai mun rabata dasu.
Duk yadda yai mata rantsuwa shi baikai karan ta ba Umma ba yarda ba sai faman fada takeyi ran ta a bace.
Nidai ina dakina ina jin su amma ban futo ba don umma ta riga da ta sure min ko.
Haka Aliyu yai muna weekend zai komana yazo sallaman ta ne take cewa su sai yaushe zaka kwashe su kutafi din.
Yace to ai umma baki yarda da tafiyan su ba don haka na bar zancen tafiyan nasu.
Da sauri umma tace ka rufa min asiri kada gaba kuma akaini

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login