Showing 15001 words to 18000 words out of 115099 words

Chapter 6 - Bamu kadai ba ne book Complete by Zainab Makawa .txt

16 Dec 2024

6665

akwai abin da naki jini ahine mukwana cikin wanan gidan mu kadai badashi ba.
Gashi yau anty ta dan kara tsoratani akan unguwar da labarin sauran gidajen da babu kowa a cikin su.
Karfe tara duk yaran sunyi barci nai masu shimfida na kai su daki na dawo na kashe komai na falon na rufe kofan dakin ban kwantaba na fara yiwa yara addua saina dawo a kaina.
Can banyi barci ba saidai barcin ya fara daukana a lokacin sai naji kamar gaba daya kwanon ruffing din dakin ya kware naji wani irin kara kamar an sauke wani abu mai nauyi a kwanon gidan.
Mikewa nayi zaune tare da kara jawo yarans kusa dani sosai muna nan shiru banji komai ba sai kallon yaran nakeyi suna barcin su hankalin su akwance.
Addua nakeyi duk wanda ya fado min arai kasancewa na diyar babban malami tun muna kanana mun san adduoi masu karfi.
Can dai naji shiru har tsawon lokaci na koma na kwanta shiru barci bai dauke ni ba can naji kamar anja tsoki mai karfi na kara mikewa zaune zubur.
Can naji ba komai na kwanta nace araina kila dai tsoron da naji ne da farko yasani jin hakan.
Barci ya dan dauke ni zuwa wani dan lokaci kadan musalin uku na dare sai ji nayi ana ta buruntu da kayan kitchen din kamar ana wurgaza kwanon dake gidan duk.
Motsin yai yawa da burun tu na mike zaune tare da fitowa falo cikin sanda gabana sai faduwa yake yi ban san may zan gani ba a falon ko kitchen din.
Amma ina shiga babu komai komai yana nan yadda yake a gurin a jere nai ajiyan zuciya tare da jawo kofan na koma na kwanta.
Ina nan shiru ban kara jin komai ba can naji kara kamar anbuga kofa da karfi cikin hasala.
Sai karfe hudu da wani abu na daina jin motsin komai a gidan lokacin ne kuma wani barci mai nauyi ya dauke ni ban falkaba sai bakwai a razane na tashi da sauri don na makara saida na dora ma yara idomie na,shiga nai sallah saboda na makara.
Ina idar da sallah da sauri na karasa addua nai masu wanka na,shirya su duk a gurguje suka tafi saura ni da Nisaiba dake barci a lokacin.
Sai bayan tafiyan su ne na fara tuna abinda ya faru jiya da dare a gidan tiryan tiryan nake tuna komai a raina.
Gyaran gida nayi na saka kamshi na koma kitchen na dora abincin rana sai lokacin na shiga wanka.
Ina ban daki naji ihun Nusaiba da karfi kamar sani abu ya samay ta da sauri nafito zuwa dakin yarinyar dake kwance saman gado na samu ta fado kasa har bakin ta ya fashe da kain ta.
Da sauri na dauke ta ina jijigata sai ihu take tsalawa tana kalon bangon dakin a firgice.
Ina nan na samu tai shiru naje nai mata wanka na gyara mata jiki saida nima na shirya na goya ta a bayana.
Sai dai ban kawo komai ba don azatona fadowa tayi daga gado ta samu wanan raunin haka.
Tun ranan ta firgice min ba dama na ajeta ita kadai sai tata tsala ihu duk na gigice.
Yaran suka dawo gida zuwa sha biyu nan na dan samu ta sake jikin ta tana wasa a cikin su.
Aliyu bai dawo gida ba sai bayan karfe hudu na yamma yashigo ya sayo muna kayan abinci da sauran abubuwa har da kayan yara ya sake sayo masu.
Sai da yai wanka ya fito falo ya zauna daga inda nake zaune nake ce mashi abinci fa ?
Yace No maryam ki bar abincin nan sai zuwa dare idan Allah ya kaimu zanci yanzun kan iam ok gaskiya.
Kallon mamaki ne mashi amma bance komai ba nan suka fara bashi labarin sun ga monkey banana jiya da zasu dawo daga school.
Aisha tamike tana mashi rawan wai monkey banana tace daddy har fa da cizo yakeyi inji maman mu.
Nan shima yake basu labarin irin na birai nashiru tun ina sauraren su har nai zurfi ga tunanen abinda ya faru jiya da dare.
Yana magana amma banji may yake fadi ba sai da yace maryam may kike tunane haka.
Nai firgigit nai ajiyan zuciya ina ce mashi ba komao yaya kamar kada na fada mashi amma sai can na nisa nace wallahi Baban Abba gidan jiya da matsala.
Ya duka yana dauko Nusaiba zuwa jikin shi yace matsalan may kuma maryam?
Na fada mai duk abinda naji daren jiya sai kawai naga yana ta dariya yace kai maryam to ko Laure ce tabiyo ku nan din kuma ?
Tsoro maganan shi yaban don ko ance maye har bangon duniya wai yana iya zuwa da dare.
Munan nai shiru nama kasa maganan komai dan tsoro shiko ko a jikin shi naga bai damu ba ko kadan.
Daren ranan lafiya kalau muka kwana banji komai ba a gidan haka yasani sake jikina nabar zancen komai.
A gida yai weekend a tare da mu muna cikin farin ciki da so da kainan junan mu muda yayan mu.
Ranan Monday suka fara kokarin shirin fita zuwa gurin aiki masu makaranta kuma suka shirya zuwa makarantar su.
Yarage kamar kullun dagani sai Nusaiba a cikin gidan tana falo tana wasan ta nikuma ina yan aiyuka na nagida.
Can naji ihunta da sauri nazo falon yarinyar ta nufo ni cikin dan tsoro na dauke ta na saka a baya don ko nono taki kamawa a lokacin.
Da kyat na samu tai barci sai dai hankalina yaki kwantawa da yawan razanan da Nusaiba take yawan yi yanzu.
Kafin wani lokaci jikin yarinyar yai wani irin zafi radau tausayi tabani gashi ko paracetamol banda shi a gidan.
Na zauna nai addua a ruwa na bata tasha na shafe mata jikinnta dashi sai ta koma barci sai dai kuma taki yarda na kwantar da ita a falon kuma .
Kiran wayan shine ya sani fitowa falon na dauka muka gaisa nai mashi yaya office yace Alhamdullahi.
Ina Nusaiba ko tayi barci ne ?
Nace eh gata nan a baya bata jin dadi jikin tane yai mugun zafi sosao tun dazun .
Yace subbahanallahi kin bata magani tasha ko nace ba magani a gidan ai yaya nadai yi mata addua kuma ga jikin nata yana dan sanyi yanzu.
Yace bari na sayo magani yanzun zan bayar akawo maku kibata nace to mun gode ya kashe wayan.
Nan naci gaba da wankin da nakeyi a lokacin sai wani lokaci mai dan tsawo dan sakon ya kawo maganin na bata sai dai duk a lokacin ma jikinta yayi sanyi ko.
Yaran na dawowa ta dan kara gyagijewa a tare da su sai da zasu islamiya ne na saka hijjab dina na rakasu har gidan su anty don da yaran ta suke tafiya islamiyan kullun.
Zan dawo gurin gida jen nan biyu naji wani irin tsam ajikina nace la,ilaha illa anta subahanaka inni kuntu minal zalumin.
Nan na shige gida cikin tsoro gyaran gida nayi da yaran suka bata kafin su fita don na riga da na gama girki tuwone ya rage na tuka kawai.
Can dai naji har lokacin tsoron bai fita min a raina ba nadauko waya na kira lamban wayan babana muka gausa dashi.
Yake tambayana muna lafiya dai ko nace mai lafiya muke ba sai dai kawai akwai yan matsala ne.
Yace subbahanallahi maryam matsalan may kuma nace wallahi baba gidan da muke sabon guri ne babu mutane sosai.
Kuma akwai gidaje a kusa damu wanda babu kowa a cikin shi nan dai na koro mai duk abinda ya faru bayan zuwan mu gidan.
Yace umm umm maryam Allah ya sawaka yanzun dai dai kiyi hakkuri zan duba al,amarin na gani amma shi mai gidan naki kin fada mashi ko ?
Nace Baba na fada mashi amma bai dauki maganan tawa da muhin manci ba yace wai na saka tsorone kawai a rayuwana shine nake wahala.
Yace babu damuwa maryam.insha Allahu koma may nene zan duba na gani sai nai maki bayani akai ke dai ki rike addua a bakin ki ko yaushe nace insha Allahu baba anayi yace dakyau.
Mukai sallama dashi nace ya gaida mutanen gida yace zasu ji insha Allahu.
Yaran suka dawo daga islamiya nai masu sannu tare da karban kayan su na wanke na shanya kafin mu kwanta sun sha iska.
Da wuri ya dawo gida don Nusaiba da bata da lafiya tana zaune suna cin abinci da yan uwanta mukai mashi sannu da dawowa ya amsa muna idon shi na akan Nusaiba dake zaune a tsakan falo ita da Aisha suna cin abinci.
Yace yaya jikin nata yana dan taba wuyan ta a hankali nace taji sauki ai tun dazun jikin yai mata sanyi.
Wanka yashiga yayi ya dawo falo nan yai sallah ishai a gurin yaran suks samay shi saman sallaya suka haye shi Aisha da,Nusaiba.
Shiko Abba ko ajikin shi sai kallon da yakeyi baban yace yaje daki ya dauko mai wayan shi saman gado.
Yaron na,shiga sai gashi da gudu yafito yana hakki da sauri muna hada baki muna tambayan shi kai maynene wai jikin shi har kyarma yakeyi yana nuna dakin baban ya daka mai tsawa yace wawan banza kawai matsoraci kana zuwa ka dauko min wayana daki saman gado.
Ganin da nayi yana kuka yana dan buga kafan shi a kasa yasani mikewa nabi shi narike mai hannu muka shiga dakin tare.
Nadauko mai waya sai dube dube yaron keyi yana shishige min ajiki alaman yaga wani abu.
Yakawo wa iban wayan ya amsa a hasale yana fadin kaidai wawa ne wallahi Aisha tafika wayo.
Ganin yadda yaron ya takura yasani cewa kabae fadin hakana kasan ko may ya gani a dakin ya tsorata.
Bai bari nakai karshe ba yace ai duk kece wallahi kika tsorata yaran nan yanzu kamar Abba zai ce wai yana jin tsoron shiga daki a wanan lokacin.
May kike nufine wai maryam da kike son tayar da hankalinki ga gidan ne wai idan ma wani abu kike nufi to kisani ni banda karfin kama wani gidan dayafi wanan kyau.
Mamaki maganan shi yabani don ban tsammaci jinhaka daga bakin shi ni ina nafito gidan mu dai ginan kasa ne iri rihewan na da ma gimshikin kasa har sama,
Gidan shi kuma da nai aure ai gina ne akaja daki biyu sai baranda da kitchen da makewayi ni ina daya umma tana a dayan dakin.
To may zaisa ya fada min haka da yake ban saba mayar mai da magana ba sai cewa nayi Allah yabaka hakuri amma ni ban nufin komai da gidan na ni ina nafito da zan raina wanan gidan kuma.
Daga haka nai shiru shima shirun yayi ran shi a bace yana dan amsa ma yaran magana sama sama kawai.
Shi kan Abba inda nake zaune ya dawo ya zauna sai dai hankalin shi baitare da shi kallon da yakeyi ma ya daina haka barci ya dauke shi abu ga kurciya.
Ashe yana shiga dakin yaga mace tsaye a tsakiyan dakin da fararen kaya tana dube dube shine yaji tsoro ya gudo sai dai na godewa Allah da baice komai ba alokacin.
Tun ranan Abba yake tsoron shiga daki shi kadai koda kuwa da ranane nikuma ban tambaye shi ba don ban son ya tayar da hankalin shi idan ya tuna.
Da yake yaro ne kwana biyu sai ma ya watsar da zabce ya dawo normal din shi yana wasan shi kamar farko.
Har aka gama weekends aka koma aiki na koma zama ni kadai sai nusaiba kawai a gidan zuwa sha daya babana yakirani muka gaisa natambayi lafiyan shi.
Can bayan mun gama gaisawa ne yake ce min maryam nace na,am baba tace ataikace dai zance maki kidage da addua akanki da diyan ki don gidan yana da dan matsala kadan amma bai mai dorewa bane.
Kada ki sa tsoro komai a ranki kema ki jajirce kifitar da tsoro a zuciyar ki don kina tare da,Allah ga kuma naku iskokan na uwar ku dake tare daku.
Nace da sauri baba ko shine suke damuna suna son dawo wa akaina ?
Yai dan murmushi yace kai haba Maryam ai iskan Amina bamasu cutarwa bane bakin da suka shige tane daga baya suka cuta mata akan wani bukatan su can da bamu yarda dashi ba amma aike naki ma yanzu sunfi karfin na uwarku nisa ba kusa basu yarda a cuta maku ko kadan.
Addua dai zaki tsanan tayi Allah ya kareku ku baki daya kuma sai kin fitar da tsoro a ran ki.
Na amsa a sanyaye da to baba insha Allah zan kula zan dinga yi yace zan kara dubawa idan na samu wanda zaizo zan bayar da sako sai akawo maki.
Nai godiya mukai sallama na kashe wayan na zauna ina dan tunane don na fahinci baba ya boye min wani abu a dunkule wanda ban sani ba.
Naci gaba da gudanar da rayuwana kamar ko yaushe ban sake maganan ba da Aliyu kuma.






ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
[10/27, 10:48 PM] Zuraiyah Zuzu ๐ŸŒŸ: ๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ฆ ๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ง


BA MU KADAI BA NE,,,
๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ฆ ๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ง
7โƒฃ


Ina tsaye tun safe nake wanke wanke sai abincin dake saman gas na yaran da,zasu tafi makaran ta dashi.
Na dauraye hannaye na nafito falo na hada kayan break fast inda na saba ajewa komawa daki nayi na samu Aisha zaune tana saka socks a kafanta.
Abba yana binciken wani abu a cikin school bag din shi abinda gagani cikin school bag din nashi ne ya ba kowan mu mamaki.
Dabino ne da ruwan zamzam cikin wani leda light blue dagani zaka gane cewa kamar tsaraban kayan saudiya ne.
Yana jin nashigo dakin ya juyo gare ni da sauri yana fadin mama wannan fa nace maynene haka tun ban karbi ledan ba .
Yaron yace a cikin school bag dina na gan shi yanzun nan ai, nakarba ina dubawa dabino ne dan kasar saudiya da dan goran ruwan zamzam karami fari.
Ledan na dauka na nufi dakin mu dashi yana zaune a bakin gado yana daura takalmin su na yan kaki.
Jin na shigo yadago kai ina ce mashi ina kwana baban Abba ya dan saki murmushi a fuskan shi yana cewa ai na zata yau bazaki iya moriya ba da safe ?
Dan murmushi na sake nace akan may kamar jiya farau haba dai nace Baban Abba kaine ka saka wa Abba wanan abin ga school bag din shi.
Ledan dake hannu na yabi da kallo yana fadin may nene wanan din a ciki nace dabino ne da ruwan zam zam kamar tsaraba ne na kayan makka fa ?
Ledan ya karba yana dubawa yace ina wanan kuma yafito nace yanzu Abba din ya gani acikin jakar shi.
Abba din ya kwalawa kira sai gashi ya shigo yana goye da jakkar shi uban yace ina kafito da wanan kuma yace baba ban sani ba yanzu nagan shi a cikin jakata.
Yace kodai wani ne yabaka a school ka manta dashi a school bag din ka Abba.
Yaron yai sauri yana cewa a,a baba ba wanda ya bani jiyama ai da dare sai dana juye duk kayan jakan ina neman sharfiner na amma banga wanan ciki ba.
Uban ya murde fuskan shi yace wai ba na hanaka karban abu a hannun mutane ba ko.
Yaron ya marairaice yace wallahi baba ba wanda ya bani yanzun ne dai nagan shi a ciki.
Ya juyo inda nake yana fadin Abba Abba wallahi ban san irin halin yaron nan ba da shegen shiru shiru haka.
Yaya zaka aje abu kace wai kuma kai ba naka bane to idan ba naka bane nawaye ?
Nan yai mai fada ya fita dakin ranshi a bace ubban ya aje dabinon saman side drower dakin .
Suka fita suka karya kumallo sai da suka gama ina kallon yaron har lokacin bai sake jikin shi ba .
Na dauko masu abincin su nakai masu suka fita suna min bye bye sai na dakatar da yaran nakaraso har inda suke nace masu duk wanda ya baku wani abu kada kuci shi kunji suka amsa da to mama.
Nan na dawo cikin gida na ci gaba da aiyu kana ga zaman kadai cin dake damuna a lokacin.
Falo na kwanta da niyar ba Nusaiba nono sai barci ya fara dan daukana sai naji kaman ana diban ruwa a cikin roban dake ta baya muna tara ruwa a cikin shi.
Bude idanuwa na nayi a hankali ina ganin kamar mafalki ne nake yi ba mafalki bane haka din nake ji.
Yadda kasan kana sheka ruwa a bucket yana bada sauti haka nake ji na mike zaune a hankali don nusaiba tayi barci ko a lokacin.
Har yanzun ina jin sautin diban ruwa a cikin roban sai na nufi hanyan bayan a hankali.
Tafiya naji a tsakar dan filin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login