Showing 111001 words to 114000 words out of 115099 words
Chapter 38 - Bamu kadai ba ne book Complete by Zainab Makawa .txt
yake kamar maijin sanyi a lokacin haka nan ya kwana a firgice kuma ya kasa cewa dani uffan jikin shi yai wani irin mugun zafi radau na rufe shi da bargo amma sai rawan sanyi yake yana sambatu.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
[11/27, 9:32 PM] Zuraiyah Zuzu ๐: ๐ฉโ๐ฉโ๐งโ๐ง ๐ฉโ๐ฉโ๐งโ๐ง
BA MU KADAI BA NE A, , ,
๐ฉโ๐ฉโ๐งโ๐ง ๐ฉโ๐ฉโ๐งโ๐ง
3โฃ3โฃ
SALAMU ALAIKUM YA MASOYA DAFATAN MUN WAYI GARI LAFIYA ALLAH YA SADA MU DA RAHAMOMINSA ALLAHUMA AMEEN.
INA MAI KARA SANAR DAKU SABON NOVEL DINA DAKE TAFIYA A GROUP DINA WANDA KEDA MATUKAR AFANI AGARE MU MATA, MAISO ZATA IYA KIRAN LAYINA DON JIN KARIN BAYANI DON BA KOWA ZAI SAMAY SHI BA SAI IDAN KINYI REGISTER
08036959257 SAI NAJI KU, , ,
Kafin gari ya waye yai matukar wahala sosai koda gari ya waye idan ka ganshi zakace yai wata daya yana ciwo duk ya zabge ga baki daya.
Gashi nayi tambayan duniya may ya samay shi ni da Umma amma ba baki sai sauke ajiyan zuciya yakeyi da ya fara dan barci zai zabura ya mike yana leken window kamar yana duban wani abu.
Haka yasa hankalin mu yai matukar tashi sosai ga halinda yake ciki don akwai matsala gaskiya.
Muna ganin haka nake cewa Umma ya kamata mu tafi asibiti dashi gashi sai rawan sanyi yake rufe a cikin bargo.
Shiryawa nayi bayan na daure na hada abin karyawa a gida umma tana zaune tare dashi a dakin mu.
Na ce bari na tadashi ya karya mu tafi na dan taba shi kadan yai wani irin firgita ya zabura zaune yana kallon mu.
Nace a hankali tashi ka karya mu tafi asibiti yanzu, wani kallo ya watso min tare da girgiza kan shi.
Umma tana ganin haka tasha jinin jikin ta ta fice daga dakin daga falo naji muryan ta tana kira na nafito zuwa inda take.
Na samay ta zaune tayi tagumi da hannun ta daya nace Umma gani ta dago kai a cikin damuwa tana kallona ido da ido tace.
Anya maryam baki ganin kamar mutanen boye ne suka shafi yaton nan ?
Naji gabana yai wani irin faduwa nace Umma muranen boye kuma kuma ?
Tace baki ganin irin yadda yanayinsa yake ne kamar mai neman wani abu can ?
Nace amma sai nake ganin kamar zafin zazzabine yake sashi yin haka kin san wanda bai ciwo bai iya yin ciwo ba sai ya tada hankalin na tare dashi randa yayi.
Nace bari dai mu tafi asibiti dashi kawai don hankalina ya daga kwarai ban taba ganin yai ciwo haka ba ?
Umma tace nima dai haka din ne gaskiya na juya da nufin na koma daga cikin dakin abinda ban san yadda akayi ba na yake jiki na fadi a kife a gurin tare da sake wani irin ihu mai karfi.
Umma tace yau na shiga uku may zangani haka ni kadai a gida Abba maza kira min yar sokoto.
Yaron ua sheka dagudu sai gidan yar sokoto yana saye cikin shirin makaranta sai hakki yakeyi.
Yace mama wai kizo inji Umma baban mu da maman basu da lafiya daga yar sokoto har mijin ta suka nufo gidan mu da saurin su.
Yanayin da suka samayni ciki yasa ta fahinci mutanen ne suka hau kan na.
Yar sokoto ke fadin sannu da zuwa yau kuma shigowan safe haka kukaiwa godiyar taku ?
Wani irin juyi nayi sunajin yadda kassan jikina ke ba da sauti kas kas tace don Allah ko waye yayi magana musan may ya kawo shi nan.
Sai zuwa can babu magana tsawon dan wani lokaci nace cikin wani murya haba haba haba bil, adama yaya kuke son muyi ne wai?
Rana takuce kuyi yadda kuke so a cikin sa daren ma da Allah ya zaba muna mufito muyi yadda mukeso bazaku bar mu bane ?
Yar sokoto tace hakane mun sani amma muna kiyayye daren gare ku ai don a lokacin muke hutawa muna.
Kun kun kun nace cikin kada hannaye na idan haka ne yaya akayi marikin godiyar mu yagan mu daren jiya.
Yagane mu yaga yaran mu yaga tsohon mu sarkin mu malamin mu yana shan iska.
Bamuyi mashi komai ba don albarkacin godiyar mu yaci amma min razana shi sosai don bai kyauta ma jin dadin mu ba.
Umma tace Allah sarki kuyi hakkuri don Allah rashin sani ne aida baza a aikata haka ba.
Nace kunce asibiti, asibiti, asibiti, asibiti suna da maganin jinnu ne sai dai idan kuna son kashe kudin ku ga banza ne.
Sui,ufil hayat jinnu oud, sui ufil hayat jinnu oud, suka tambaya cikin son karin bayani nace masu eh, ai godiyar mu ta san shi.
Godiyan mu ga Allah ta san shi, sosai shi zata ta shafa mai shi a jiki zai samu waraka daga kaidin yaran mu da ya batawa rai.
Sarkin mu yana shan iska ya gane shi ya haska mai hasken mota a fuska haka ya batawa yaran rai suka shafe shi.
Ku kiyaye fitan dare don dare ba naku bane sai idan fitan ya kama dole na dago kai gurin mijin yar sokoto nace hayatudeen sai nai murmushi.
Nace kayi a hankali da kudin mutane don ka kusa fadawa cikin hau, ilwala,I.
Yace subbahanallahi ni kuma ya gyara zaman shi nace kwarai kuwa don akwai wani arne dake son ku hada halaka dashi kada ka soma arne ba abin yarda bane makiyan ku ne basu da tsoron Allah ko kadan atare da su.
Matar da iyayyen ka ke son ka aura kayi a hankali babu babu babu lafiya ba alheri a tare da ita ko kadan.
Gidan da kake son saye a garin ku an yaudare ka na guri bane mai kyawo shiyasa maigidan ke son sayarwa akwai huwa,i gurin bai bari kowa ya zauna don shi keda gurin sa.
Tsohuwa tsohuwa kin bar gida har gidan ya zama maboyan shedanu makwabciyar ki ta samu gurin aje ruhin yan adam yan uwanki ko zaku koma cikin gidan nan yanzu sai anyi burgan sa sosai.
Don ta samu dama da furin boye sirin ta a gidan ki don gidan yai mata dadi agidan ki suke meeting din su na mayu unguwar ku.
Abba yaron kirki saidai kassh akwai shedanun yara dake sa ido gare ka amma bazasu iya ba don kafi karfin su da tuni sun gama da kai don akwai baiwa a gareka nan gaba mai tarin yawa.
A garinku makwaciyar ku tasan da wanan tarin baiwa taso ta gama da yaron tun yana a cikin godiyan mu .
Sai dai hakan bazai yiyu ba don abubuwan dake a tare da godiyan mu bazasu bari a lokacin a cuci jinin su ba.
Godiyar mu mu tana da matukar kirki amma ke tsohuwa mai kalwa ta cusa maki mumunan ra, ayi a kan ta haka yasa muka gwada maki ba ai wa godiyar mu haka.
Yanzu kin ganan wa idon ki gaskiyar alamarinta don haka sai dai idan halinku na yan adam ne ya taso maki kuma don har gobe baki daina hassadan ta ba a ran ki .
Don kina ganin kamar ta taushe maki baiwan danki ne tafi shi arziki yanzu kin manta abin daga Allah yake.
Zamu koma don haka ke yar sokoto gare ki don godiyar mu ta yarda dake amma kina kyashi akan ta kina yada magana wanda bai dace ba akan ta, kiyi hankali da fushin mu watarana kada mu waiwaye ki akan hakan.
Sai watarana ku ceci rayuwan marikin godiya don shi yai muna katsalandan a rayuwan mu ba komai ba.
Tsit falon yayi yayin da nake sake wani irin atishawa mai karfi har sau uku daga inda nake kwance.
Sun tafi yar sokoto ta fadi haka nan tare da kiran sunana maman Abba sannun kinji.
Na gyada mata kai kawai alaman amsawa tace bari na baki ruwa ki wanke fuskan ki.
Ina tashi da kamar minti uku Umma tace dani maryam kin san sui, ifil hayat jinnu oud na kada mata kai alaman nasan shi.
Tace sunce ki shafawa mijin ki tare da hayakin shi yanzu wai ba na asibiti bane gamo yayi da su a daren jiya.
Da sauri na dago kaina na kalli Umma nace gamo kuma Umma a ina ya gamu dasu.
Sai na fashe da kuka tace haba nace Umma ni ina fama da haka ace kuma yau baban Abba shima abin ya shafe shi kuma.
Tace basu shige shi ba sun dai bashi tsoro ne kawai sukace don ya gan su ya haska masu haske akan su.
Lokacin wai akwai tsohon sarki a waje yana shan iska shi kuma ya biyo gurin su.
Da sauri nace baba ke nan ba kanin baba malam mahaifin mukkadarasiyya.
Kallo na suke da mamaki nace tabbas yana kasan nan yazo ziyar na san da hakan nasani kuma sunce mu kiyaye su har ya wuce.
To yanzu dai idan kina iya tashi ki tashi ki dauko maganin kiwa mijin ki yadda suka ce.
Na yunkura zan tashi naji wani irin jiri ya kwashe ni da sauri na koma na zauna inda nake zaune da farko na dafe kaina.
Yaya dai kuma suka tambaye ni kusan a lokaci daya nace babu komai jiri nake ji kawai sannu suke min.
Sai bayan dan wani lokaci na mike zuwa daki na shiga neman maganin wanda sune suka bani shi dama.
A hankali na yaye bargon da yake rufe dashi nakai hannu a jikin shi jikin nashi yai wani irin mugun zafi sosai.
A hankali na soma shafa mai na daba mai ta gurin hancin shi da kunnuwan shi da saman kan shi.
Bai fi minti goma ba ya sauke wani irin ajiyan zuciya mai karfi cikin murya kamar ihu yace maryam maryam nagan su tabbas BA MU KA DAI BA NE A GIDAN NAN.
Nace haba ya Isa mana haka kayi shiru Allah yabaka lafiya ya koma ya lumshe idanuwan shi a hankali sai kuma ya koma barci mai nauyi.
Haka yasa muka barshi ya samu barci da kyau muka dawo falo sai lokacin ne yar sokoto da mijin ta sukai muna sallama suka tafi gida.
****** ********* ******
A gidan su maigidan ke cewa murjan wai kin san ban taba yarda da zance wasu jinnu ba can sai yau din nan.
Mata kamar ibishiya komai da ta kalli mutum tasani akan shi haka ?
Kai dai ka fadi haka ni babu ruwana wallahi kadai ji warning din su kai min yanzu don haka koda gigin barci ba zan kara maganan ta bani.
Dama Anty hauwa ce mai kawo maganan niko nake zakewa na yi daga yau kuma na dai na indai ni murja ce.
Sai lokacin ta juya gare shi tana cewa ashe kai har aure ake nema ma ban sani ba a gida ?
Yace kai zancen anty Fatine fa wata wai diyar kanin mahaifin mijin ta shine wai ta kama min ita na kara.
Yanzu ai dai kaji in kunne yaji gangan jiki ya tsira yace ai dole sai na bincika.
Yace haba no warder ashe gidan nan sukace na kawo kudi a yadda na taya ashe sun san sherin dake gidan suke son lakaka min shi.
Yar sokoto tace to wani mutum ne ke son cutanka da suka ce yace bakowa bane Devid ne na fahinci haka tun soma maganan ta.
Dama shakiyi ne shi yana da alaman yaudara tare dashi Allah dai ya rufa min asiri ban zurma a hannun shi ba da wallahi ya cuce ni har abada.
Nan dai suke ta magana akaina har ya shirya a makare ya fita zuwa office don ya makara ranan kan case din mu.
Baban Abba bai falka ba sai guraren karfe daya na rana ya tashi daga dogon barcin da yayi.
Koda na shiga ya hada wani irin zufa sharkaf dashi kamar ba shine ke rawan sanyi ba da safe haka na.
Jin muna magana dashi Umma dake cikin matsanacin damuwa ta fado dakin tana fadin ya tashi ne ?
Nace ya falka Umna wai wanka yake son yi ko zai ji dadin jikin sa.
Bathroom na shiga na hada mai ruwa ya mike dakyat jikin shi babu lakka daganin yadda yake tafiya zuwa ban dakin.
Yana fitowa tare da alwala yai sallah nai mai maganan abinci yake cewa nabashi tea kawai yasha a lokacin.
Falo ya fito anan na samay shi nafito da kayan tea na hada mai tea mai kauri ya sha ya koma saman three seater ya kwanta sai faman sannu umma take mai a raina nace uwa ke nan.
Wanan abin na juya daki na dauko da niya na na kara shafa mai da sauri ya cire hannun shi da ya kare fuskan shi dashi yana cewa maynene haka kuma ?
Umma ce ta tare ni da fadin tsaya mana ta shafa don Allah ko zaka kara walwalewa.
Yace may ye shi din kuma tace kai dai bari ta shafa ma kawai badon Allah ya taimake mu tana dashi ba a gida yaushe zamu samay shi har aima amfani dashi kaji sauki haka ?
Murmushi yayi tace ke shafa mai kinji ban tsaya ba na fara shafa mai turaren maganin a jikin shi.
A hankali naji yana sauke wani ajiyan zuciya zakace ko yai nisa ne ga tunane a lokacin.
Idanuwsn mu a kan shi wani sabon barci ne ya dan kara daukan shi a gurin bai falka ba wanan karon sai karfe biyar na yammaci.
Yai sallah na gabatar mai da abinci yace maryam bar abincin nan please bakin nan nawa babu test ko kadan.
Nace ai dole ba karamin jin jiki kayi ba ai Allah dai ya kawo saukin alamarin ai.
Da asibiti muka tafi da kana can killa ma sai sun rike a can su kwantar da kai a yanayin da ka kwana ciki.
Kwanan shi biyu ya walwale ya koma kamar baiyi ciwo ba ma alokacin ya koma normal life din shi.
****** ********* ******
Kudi na tsab na hada nakaiwa hajiyan controler taban kayan da sai dana gigice don yawan su.
Na kalli yawan kayan da akace wai duk a matsayin nawa suke nan na fara kasuwanci sosai ba kama hannun yaro.
Allah ya kama min abin sosai har manyan mata suka san da zamana moton da nake shiga na sayar na tura kudin a gyara gidan mahaifina dashi.
Don na samu kyautan mota tagani ta fada daga gurin gwauna don yanzu zance na zama tankar yar gida a gurin su.
A cikin haka wata rana suka bugo min waya wai Adisatu ta haihu a Niger nai matukar farin ciki sosai da samun wanan labarin.
Ga matar gwauna tace tare zamu yafi Niger suna da ita don Adisatu tace azo dani wai.
Suna saura kwana biyu muka bar kasan nan zuwa kasan Niger a tare da aminiya ta yar sokoto da tai min rakiya.
Munga daula sosai a gurin wa yan nan mutane nayi mamaki daganin haka don a yadda muke jin labarin wai kasan basu kai kasan mu Nigeria arziki ba.
Sai gashi mu munga sabanin hakan gare su ko don gidan masu akwai ne muka tafi oho ?
Zan iya cewa wata kila su arzikin su na gado ne don duk dan wanan zurian idan ka ganshi kaga masu akwai.
Don munga karyan gwalagwalai a gurin su duk wacce zata shigo acikin dakkakiyar shedda ce ga sarka da yan kunne da munduwa duk na zinare.
Muma mun lakaci arziki don akwati guda na irin tufafin su na samu ta ranadar min na fitan suna da zan saka ajikina.
Ganin nazo da yar sokoto itama sai ga nata daga cikun nata tufafin bazakace an taba amfani dasu ba ma ajiki.
Duk wacce tazo zakaji Adisatu tana fadin ga sisters din ta daga Nigeria suka zo suna sai kaga ana mutunta mu da ta fadi hakan.
Mun saje dasu sai ka dauka muma yan kasan ne saboda irin tufafi na alfarma dake a jikin mu.
Ko wani kaya yasha aiki har kasa dashi da zani har dan kwalin su ga gwal a wuya yana muna sheki.
Washe gari ne da dare ta gabatar dani ga maigidan ta wanda da ka gan shi basai an fada ma ba kaga buzu sak dogo siriri dashi amma akwai naira.
Adusatu ce ke gabatar damu tana nuna matar gwauna yace ai yasanta yace yaya maigidanta yace yayi tafiya bai samu zuwa ba ko ?
Tace hakane yaso zuwa amma tafiya ya kamshi tare da shugaban kasa sunfita zuwa waje.
Tace hone ga malama maryam daga Nigeria da na tafi gurin ta kwanan baya kan matsalan mu.
Ya dago da sauri cikin harshen hausa mai surki da yaren su na can yake cewa au wanan ita ce kika tayar min da hankali akan ta sai kin shiga nigeria kin ganta ?
Tace kuma zuwan yai muna amfani ba don gashi yanzu Allah ya azurta mu d Abdoullah.
Nan