Showing 96001 words to 99000 words out of 115099 words
Chapter 33 - Bamu kadai ba ne book Complete by Zainab Makawa .txt
dan soma kamata amma dai shigan ta na kananan yara ne ba mutunci tare da ita.
Dariya sosai maganan Umma ya bani nace kai Umma ho ai sunan birni ne ba babba ba yaro a gurin kwalliya sai wanda Allah yasa yagane gaskiya kawai.
Umma tace ikon Allah ni dai sunan na shigo kaduna ne bubu inda na sani sai asibitin da muka tafi ranan.
Umma kina son shiga garin ne kigani na tambaye ta cikin kallon fuskan ta don son jin may zatace min.
Tace maryam idan ma nace zan fita ina zan tafi tunda ba kowa na sani ba a garin.
Haka yasa na fahinci tana dai son zuwa ta danga gari kuma tana da gaskiyan ta ai.
Itace ta kawar da zancen take ce min taji baban Abba yana zancen wai ya kamata ta koma gida hakana don kada abar gida babu kowa a can.
A fahinta na Umma bata kaunan komawa gida yanzu don haka ya zama wajibi nasan yadda zanyi akan zancen .
Yar sokoto ce ta shigo gidan muna hira take ce min gaskiya maman baki kyauta min ba yanzu ashe Abuja kika tafi shine baki gaiyaceni ba ni na ci arzikin ki.
Yar sokoto haba dai yanzu ace mun kwashi jiki sa auren mu zuwa wani gari ba wani babban sha, ani ya faru ba ai sai a zarge mu ni dake.
Tace kai haba maman Abba ina ruwana da zancen mutane idan zan tafi gidan harka irin wanan duk abinda wani zai fada ya je yai ta fadi ina ruwan ta ita.
Aiko mun baje sai hiran rayuwa ake don tana jin dadin zuwa suna hira da Umma ko yaushe.
Mukaji dirin mota har Umma na cewa ga babana nan yadawo gida.
Sai mukaji an tsaya daga waje ana nocking din kofan shigowa daga falon mu.
Haka ya tabbatar muna da cewa baki ne a tafe a lokacin sallaman da akayi ne tare da nocking a lokaci guda yasa muka gane mace ce take sallaman.
Kusan amsa sallaman mukayi gaba dayan mu nida yar sokoto da Umma a lokaci daya.
Fara ce ba doguwa can ba, shekarun ta ya dan kora kadan tana da alaman sakin fuska a tare da ita.
Tufafin jikin ta kawai zai sa mutum ya fahinci ba karamar mace bace ita bin mu take da kallo daya bayan daya cikin son ta tantance gaskiyan abinda ya kawo ta gare mu.
A bayan ta wasu mata ne dogaye baka da fara suna take mata baya sannu da zuwa Umma take masu a cikin fara,a ita da yar sokoto, sai dai ni ina bin su da kallo kamar ina nazarin su.
Zama sukayi sai cikin yaren su na yan Niger dayan ke fadin wai kuwa gidan ne nan kuwa ita fa bata ga alaman abin kwarai ba anan.
Daga inda nake zaune hannaye na a hade guri daya wanda ban san lokacin dana rufe su ba ina murzawa nake fadin.
Ai kyawon guri bashi ne nuna sa,an guri ba don haka idan zatayi abinda ya kawo ta tsaya tayi.
Nace cikin yaren zabarma wai ita yanzu tana nufi ra biyo Anarba ne zuwa karban taimako ko dai ta biyo ta taji abinda za, afada ne kawai.
Na juya gurin mai suna ANARBA wace ina ga matan wani ne daga wani guri nace mata kina tafe da makiyiyar ki ne don mahaifan ki na a hannun su ita da uwar ta .
Da Mamaki suke kallona suna cewa wai dama na iya zabarmarci ne haka ko yaya na basu amma da cewa yare guda gudane bana ji a rayuwan.
Sam hamshakiyar bata yarda da magana ta ba sai dana fara bata labari ina fada mata duk yadda akayi ta auri mijin ta da sukayi auren gida dashi.
Kallon mamaki take min tace yaya akayi nasan da zancen nan nace nasan har abinda bata sani ba akan zancen.
Tiryan tiryan nai mata bayani yadda akayi auren ta da mijin ta da kuma irin gwagwamayar da yafaru a tsakanin yan uwasu a lokacin.
Na nuna mata wanan ta farko tare da sake maimaita mata cewa maitat su na hannun kakansu Dijagal itace ta saka a daure maki mahaifan ki bazaki taba haihuwa da HAMMA MANDE ba.
Don basu son hada zuria da jiniku sai irin nasu yan zabarma yar may kwairi kwarara.
Kuka ne ya subbace wa matar a cikin damuwa take kuka tana sharan hawaye take fadin dama ita tasan yan uwanta basu son zaman ta da mijin ta don tafito daga tsatson mahaifinta da basu so a cikin ta.
Bukatan ganin ta nayi ita kadai don haka kowa ta barni dagani sai ita a falon wanda hakan bai ma yan uwan ta dadi ba don basu so haka ba a ransu.
Na fada duk yadda matsalolinta suke da hanyan da za, a magance su cikin sauki take matar ta riko min hannu tana fadin idan Allah ya nufe ta ta samu haihuwai tayi min alkawarin abubuwa da dama a rayuwanta nace a, a basai kin min komai ba bani da dogon gurin rayuwa akan alamurana.
Ina dai taimakawa wanda Allah yabani ikon taimakawa ne a duk lokacin da hakan ya taso .
Nace sun fada min wata mai iska ce ta turo su gurina tun daga yaimai na kasar Niger matan da ta turo su tafada masu ikokaina ne kawai zasu iya warware kullin da akai mata.
Dalilin da yasa ke nan suka nemi da ai masu kwatancen ida nake iskan matar yai masu shine suka shigo daga Niger don su ganeni idan gaskiya akefa a kaina.
Da zata zo ne sai tsohuwar gidan dake zaman kakan su ita da mijinta ta hada ta da wata daga cikin jikokin ta don tai mata rahoton abinda duk ya wakana tsakani na da ANARBA din .
Gashi daga zuwan su na fara fasa masu kwai duk da sun san cewa za, a iya aikata abindana fadi din ga yadda yan uwa suka saka ta a gaba don matsalan rashin haihuwan da basu samu ba da maigidan nata.
To amma kuma tsohuwar kakan su tasan duk inda matsalan nasu yake tayi hakane don ta aura mai daga cikin jikokin ta da take son ya aura daga jinin ta.
Hankalin Anarba yai matukar tashi sosai yadda taji bayanin komai ta tausaya wa rayuwan ta da kyat na kwantar mata da hankali ta samu natsuwa a tare da ita.
Tace cikin sanyin murya maryama kina ganin guri na zai samu cika nace da ita sanin gaibu sai lillahi yayata amma ki jaraba maganin dana baki nan da wata daya mu gani.
A warwaron dake a hannun ta naga tana kokarin cirewa ido kawai na tsura mata sai bayan ta cire ne take cewa tare da miko min tana fadin maryam ki karbi wanan a warwaron bazan fada maki kudin shi ba amma nan gaba zaki sani.
Nabaki shi ne a matsayin sadaka tsakanina dake ta bude jakkar ta tafitar da damin kudi masu yawa ta aje a gabana tana fadin.
Wanan sako ne daga maigida yace nazo maki dashi sauran bayani idan Allah ya biya muna bukata zaki jimu.
Nace kudin nan suyi yawa gaskiya da zaki rage su zanfi jin dadi a rayuwana.
Murmushi tayi tace kada kiji komai yar uwa matsayin bukatan mu zai biya zakiga fiye da hakan a rayuwan ki daga gare mu.
Tabani matukar tausayi na bita da ido nace da ita kiyi hankali da rayuwan ki koda ace kin haihu bawai zasu daina bibiyan ki bane daga ke har abinda zaki haifa nan gaba.
Sai da ta share hawayen daya zubo mata take cewa tasani tasan da hakan a yadda take zama dasu gata marainiya a cikin su.
Wani maganin nakara bata na fada mata yadda zatayi amfani dashi take cewa dani nai matukar kwanta mata arai yadda ta dan fahince ni.
Nace babu komai Allah dai ya karba muna bukatun mu na alheri tamike tana fadin zasu koma don yau take son komawa Niger Republic din su don akwai taron da zata halarta a gobe insha Allahu.
Take cewa da motan gidan gwanatin wani gwauna na kasan nan suka zo nan ida nake ga kwatancen da akai masu ne yakawo su inda nake.
Munyi sallama dasu suka tafi inda taba anty hauwa da yar sokoto da Umma alheri mai yawa saida suka kadu.
Bayan tafiyan su ne yar sokoto ke fadin ikon Allah, yanzu muma alherin ki maman Abba yana shafuwan mu.
Yanzu sam na daina jin komai idan nai wani abinda ya shafi aiki wanan yana nuna alamane na cigaban alamarina da nake ciki.
Gashi wani lokaci zan iya ganin mutanen nawa cikin siffa na yan adam wanda ba mafalki ko wani imagination nake ganin su ba.
Zan zauna dasu muyi hira sosai bana jin tsoro kamar farko don ancire min tsoronsu a raina.
Ga kudi na shigo min ta yadda ma ban taba tsanmani ba haka yasa na hada kudin makka wa mahaifina da nake son ya sauke farali a bana.
Naso na biya su tafi da Umma sai dai hakan bai samu ba don wasu yan dalili da aka samu.
***** ********* ******
Ogan su babban Abba ya samu matsala dashi da wasu manyan su har ake ganin case din zai ya jawo masu adakatar dasu daga aikin su.
Ganin yadda hankalin duk yan office din nasu ya tashi yasa baban Abba ya tausaya masu don duk suna acikin tashin hankali saboda shugaban nasu yana matukar taimaka masu sosai.
Bai fada min ba sai nice a kafadawa kamar a mafalki naga damuwan dake damun su a office din su.
Yana zaune ya tasa abinci a gaba ga Umma dake mai hira ta cika shi da zancen kanin ta da take son wai ya taimaka mashi.
Yara kowa na harkan gaban shi hasken wutan lantarkin da ya haske falon namu zai iya nuna yanayin da kowan mu yake ciki a falon.
Ban san yaya akayi ba nake cewa dashi amma da Oga zai amince ya datse Jibrin hassan akan maganan nan inaga zai samu mafita akai don daga gare shi matsalan take.
Wani irin kallo ya watso min mai nuna mamaki ko tuhuma akaina na yaya akayi nasan da wani zance can.
Nace eh Jibrin Hassan shike son yi maku zagon kasa bayan shine ya tura ogan ya aikata hakan kuma takardan da kuke nema da zai yi depend di ku yana gurin shi kai tsaye Oga zaice dashi ya bashi takardan daya dauka ranan hudu ga watan shidda a table dinshi daya shigs sallah zakuga yadda zai kadu kuma zai fito da takardan ba bata lokaci.
Maryam are sure da maganan ki don wanan fa ba karamin magana bace.
Nace nasan da hakan shiyasa nake son kai ka fada mai idan ma har baka fada mai bani zan fada mashi tunda naga yana da tausayi mutumin.
Kara kallona yayi nace ina son hakan yafito daga gurin kane kawai don aikin kane kuma alherin hakan akan zaifi amfani.
Shiru yayi kamar bai dauki maganan da muhinman ci ba a ranshi sai dai can kasan zuciya shi juyayin maganan nawa yakeyi yadda har nasan haka akan su.
Washegari da zaifita na sake maimaita mai abinda na fada mai daren jiya din.
Umma tace kai kayi abinda akace dakai kawai ban son abinda zai jawo matsala daga baya.
Dariya umma ta bashi ganin yadda tai believe akan alamarin iskokai na haka.
Ya isa office ke nan ya nayin da yaga mutanen office din nasu yasa yasan da magana yau a office din nasu.
Ashe sun samu labarin manyan su zasu shigo bincike ne akan zancen takardan daya batan.
Zancen mu ne ya fado mai aran shi yaga kawai ya kundunbalan yin wanan kasada ya fadi yadda nace dashi.
Saidai idan kuma hakan baiyuyuba fa zata matukar kwabe dashi sosai don Jibrin din yana gaba dashi.
Mikewa yayi don baida zabi ya fada office din shugaban yana zaune a cikin damu shi kadai a office din.
Bayan sun gaisa ne yake mamaki shigowan shi direct haks don ba kasafai kananan ma,aikata ke shigowa gurinbshi ba anyhow.
Yace og dama wani magana ne nazo dashi kozamu samu mafita akan wanan matsalan.
Ina jinka Mr Aliyu Ogan ya fada cikin damu nan dai ya fada mai kamar yadda na fada mai din.
Yace tare da shafo kansa yana cire hulan aikinsu dake kan shi yake cewa.
Mr Aliyu ina wanan zamcen yafito haka bayan shi kan shi Jibrin din case din ta shafe shi sosai.
Yace Oga kadai gwada mugani kawai zan maka bayani daga baya yadda case din yake.
Oga dai baida zabi don haka Aliyu yana fita yakira Jibrin din yashigo cikin rashin damuwa da komai don yasan babu wanda yasan komai akan abinda ya aikata masu.
Yazauna suka gaisa Oga yake cewa Mr Jibrin may yasa zakai ma rayuwan mu haka please ?
Ina son ka kawo min takarda da ka dauka anan gurin nan dai yai mai bayanin komai kamar yadda akace dashi.
Kan shi ya dukar kasa batare da yasan hakan mazai faru dashi ba kaman an matsi bakin shi yace Iam sorry sir sherin shedan ne kawai yasa nai hakana.
Yace dauko min takardan baki alaikum na tura masu kafin su taso daga Abuja.
Ba musu kamar ana izashi yafita bai dauki wasu awani ba ya dawo da takardu kamar yadda suke aje a gurinshi yamika mai.
Bayan ya duba yaga komai intact yadda ya kamata ya sauke wani gwaron ajiyan zuciya a fili yace you can go.
Yafice jiki ba karfi yana fita yaji kamar wani abu yafice mai akai yace a ranshi how comes har yai saurin yin confessing da sauri haka bayan saura kiris yacin ma gurin shi akai.
Fitan Jibrin yasa oga ya kira wasu manya da abin ya shafa ya mika masu takardan sai mamaki da murna sukeyi kowa ya zama free ke nan akan takardan.
Basu bats lokaci ba suka tura takardan can headquarter su komai ya shiga kamar yadda ya dace akan su.
Sai da komai ya kammala ne oga ya nemi baban Abba a motar shi suka fice daga ma,aikatan nasu sundayi tafiya mai nisa yace.
Mr Aliyu da farko zan fara cewa Alhamdullahi don komai ya tafi daidai har an kammala komai yadda ya dace ya kawo min takardan kamar yadda ka fada min.
To amma abinda nake son sani shine yaya akayi kasan da hakan kao don Allah kada ka boye min komai please ?
Aliyi bai boye mai komai ba yace sir mamatace keda matsala irin na jinnu da suka shafe ta itace jiya kawai ban fada mata komai ba wallahi take fada min hakan.
Cikin mamaki yace matarka fa yanzu mace ce ta fitar dani daga wanan kangin balain dana shiga wanda zai iya jefani cikin rasa aikina gaba daya.
Nan dai Aliyu yake fada mai duk irin halin da muke ciki da yadda al, amarin yafara yi min.
Yace ikon Allah yanzu ashe muna da irin giftedness dinan acikin gida jen mu bamu sani ba haka.
Yace dama shi baiwa na Ubangiji akwaishi a cikin aluman mu sai dai mutane basu ganewa da irin su ne Allah yakan boye su daga aluma don gudun cutuwa a garesu.
Kagan ni nan nasan akwai jinnu a duniya dake shafuwan yan adam suna taimakawa bayin Allah irin haka saidai akwai da yawa da bana gaskiya ba daga cikin su.
Irin hakane turawa suka fi mu don su da a kasan turai kuke da yanzu goverment din su sun dauke ta don amfanin su.
Amma mu kaga anan sai a barsu a haka da tarin baiwan su sai dai wanda Allah yanufa da ya more daga garesu ne kawai Allah zaiba ikon ganin su.
Yanzun haka ni kaina ina da yarinyar da take fama da irin wanan laluran a gida na sun hana ta aure don ko zancen aure bats so ayi mata.
Zan samu lokaci muzo hargida da Iyalina don mu yi godiya ga matar taka sannan zakaji ni insha Allahu.
Don Allah ka rike wanan sirin a tsakanin mu don ko shi jibrin bazan kara cewa dashi uffan ba amma daga satin nan isha Allahu zai bar nan .
Kafara yi min godiya gurin ita mai dakin naks kafin muzo insha Allahu.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
[11/27, 9:32 PM] Zuraiyah Zuzu ๐: ๐ฉโ๐ฉโ๐งโ๐ง ๐ฉโ๐ฉโ๐งโ๐ง
BA MU KADAI BA NE A, , ,
๐ฉโ๐ฉโ๐งโ๐ง ๐ฉโ๐ฉโ๐งโ๐ง
3โฃ0โฃ
Yanayin da ya shigo gida a cikin fara, a yasa na fahinci akwai nasara a tare dashi don na dade rabon da nagan shi a cikin farin ciki irin haka a cikin irin wanan yanayi.
Ranan har yara sun sheda yana tare da farin ciki don ya shigo masu gida da abin tabawa.
Sai murna sukeyi jin hayaniyan su ne yasa Umma fitowa daga dakin ta ta samay shi a tsakiyan su zaune yana bare masu chukulet din wa Nusaiba.
Cikin murmushi da jin dadin ganin yanayin danta da jikokin ta ta zauna tana