Showing 93001 words to 96000 words out of 115099 words
Chapter 32 - Bamu kadai ba ne book Complete by Zainab Makawa .txt
shi na juya na dauko ruwa ina ajewa ne naji muryan shi yana fadin wake da mota a kofan gida kuma.
Kai tsaye na bashi amsa da cewa nawa ce kawai daga haka ban tsaya ba na shige dakin kwanan mu na dauko kudin nakawo mai.
Cikin mamaki yake kallona don son jin karin bayani daga bakina sai bayan ba aje kudin ne nake cewa wanan mutumin da kazo dashi ranan ne ya turo matar shi da wanan kayan don hasken daya samu ga abinda akai mai.
Cikin mamaki yace wai da gaskiya kina nufin kudi da mota ya bayar a matsayin tukwaici a gare ki haka ?
Nace gasu ai a gaban ki kai ya girgiza yana cewa lalai ma al, amarin naki maryam bana wasa bane ashe don kin wuce sani yanzu kan.
Ai har kin fi wani ma, aikaci samun riba a cikin wata don a iya lissafi na abinda kika samu faruwan wanan alamarin naki ba karamin abu bane gaskiya.
****** ********* ******
Hajiya saratu na komawa gurin su Alhaji take fada masu duk yadda abin ya faru sai dai ta boye masu wasu daga ciki.
Nan suka ja mata kunne akan ya kamata su bar wanan zance iyasu don kada wasu su gane gurin azo a bata masu sa, an su nan gaba.
Sai dai sin sha alwashi zasu dinga taimaka min idan hakan ya taso ta hanyan hajiya saratu tunda ina da aure ba gani na zasu dinga yi ba anytime.
Itako zuciyar ta yaki aminta akan maganan dana fada mata kan zancen abinda take shirin aikatawa.
Cikin sati kamar yadda tai niyya haka ta kudiri shiga da kayan ta kasan saudiya din.
Aiko aka cafke kayan case yai kamari akace sai an kamata an tuhumay ta.
Ta kira su Alhaji sada hankali a tashe take sheda masu komai kan su taimaka mata su ganni ayi magana asan mafita akan zancen.
Haba hajiya saratu yanzu da hankalinki da wayon ki har kika bari wanan abin ya faru dake don kawai idon ki yarufe akan abin duniya ?
Kece fa da kanki kizo muna da karin bayani akan wanan boyar Allah da irin abinda kika gani da idon ki a gareta.
Sun cikin wanan case din sai kuma ga zancen yan matan data tura waje an kamasu a iyakan boarder ya taso nan abubuwa suka taru suka rikice mata a lokaci daya.
Sunzo gurina da zancen kan asan yadda akayi ta kubuta nace ba na wanan aikin don ba, a bisa tubalin gaskiya aka dorashi ba.
Duk yadda suka so gani naki yarda akan maganan sai da suka hafa da baban Abba shine yasani a gaba akan ataimaka mata ko don su Alhajin da suka saka bakin su ciki.
Dole ba don naso ba na bukaci ganin baba malam akaro na farko da kaina kamar yadda ya umurce ni danayi indan ina da wani bukata a gareshi.
Sai ko gashi ya taka akaina da kan shi nasha matukar wuya a ranan kafin akai ga mafitan zancen nata.
Yadda duk aka fada haka akayi sai gashi ta samu kubuts sai dai su wa yanda aka kama an dan sasauta masu don ba wasu kaya masu aibu bane sosai goro ne sai su kayan mata da sauran tarkace aka yanke masu hukuncin shekara daya da rabi aka kashe zancen a cikin sauki.
Na dan samu sararawa yanzu bana komai kuma sai harkan aiyukan gida da suka shige min gaba kawai.
Hajiya Aisha kamar yadda tai alkawarin zamu Abuja a tare da ita sai gata da zancen ya taso mata don an kammala aikin komai a can.
Kafin baban Abba ys yarda da tafiyan nawa tare dasu, sai da Umma ta saka baki ya amince da hakan .
Amma ya nuna rashin yardan shi da hakan wanan tafiyan da nayi dasu naga duniya a furin wa yan nan mutane sosai.
Gida wanda tsayawa fadan tsarin shi bata bakine gurin tsaruwan shi ga mai karatu.
Muna shiga gidan naji kaina ya wani sarawa nan dai na samu daya daga cikin kujerun falon na kai zaune sama.
Kowa na harkan gaban shi ina guri daya zaune sai lokacin hajiya ta hankalta da irin zaman da nayi take cewa, a, a diyata yaya komai baki taba ba daga ciki.
Dan dago kaina nayi da idanuwa na da suka sauya min kalla a lokaci daya nace hajiya na koshi.
Ta fahinci idan nace kalman hajiya agare ta bani kadai bace a lokacin hankalinta ta mayar gare ni tana kallona take cewa ko zan shiga daga ciki na dan huta ko ?
Ina dai zaune gurin ban motsa ba ban yi magana ba kuma na dai yi shiru Nusaiba da nazo da ita tana makale a jikina.
Nabila diyar hajiya ta biyu ce tafito daga saman steps take takawowa a hankali zats sauko kasa ta sauya kayan jikin ta zuwa kanan kaya wanan karon.
Zubur na mike daga inda nake a zaune cikin wani kakausar murya nake ce mata tsaya anan kina kara tako daya sai dai kiga ana tafiya da kafa nan gaba.
Cak taja ta tsaya guri daya a hankali nake hawa saman matakalan benen kamar zan fadi kasa a lokacin.
Daidai step daya da ya rage ta taka na tsaya tare da dukawa agurin gaba daya wanda ke falon sun mayar da hankalin su a gare ni.
Daben gurin nake bugawa da hannu na kai kasan idon tanice bazan ko iya banbaran shi da diga ba balle hannun da nake amfani dashi.
Bugu biyu gana uku gurin ya tsake haka nasa faratana ina tonon gurin sai ga gurin ya bude hamza kanin hajiya ya karaso da sauri yana cewa wanan ma sabon shafi ne ba tarazo bane ai akai.
Can na zaro wani kwalba a daidai gurin tare da wani laya da suma an nade a cikin shi.
Take duk hankalin su yadaga gurin kowa na mamaki bin ginan gidan nayi da kallo kamar yadda dabba yake sun sunan wani abu don ya gano inda yake.
Mikewa nayi a hankali nake bin matakalan har zuwa sama ban tsaya ko ina ba sai wani daki na shiga ina shiga na nufi daidai gurin gadon.
Yaran sukace dakin mummy ta shiga hankalin hajiya yai matukar tashi sosai a lokacin jin dakin ta na nufa.
Duk da karfin gadon dagawa daya nai mashi na dago shi sama gaba daya .
Kasan gadon ma anyi kafi a cikin sa na ciro shi banyiwa kowa magana ba tunda nafito daga dakin hanyan fita daga gidan na nufa na fice zuwa waje.
Sai da nai tafiya mai nisa sosai na samu guri na tsaya ina sake kwalllaben suka kama da wuta gaba dayan su wani bakin hayaki yatashi sama yabi iska.
Na juya na dawo ina shigowa nai zaune ba umm, ba umm, umm haka na zauna kawai dani.
Kusan awa daya ban tanka ba suma duk a tsorace suke a lokacin kowa yai tsuru tsuru a falon sun mayar da hankalin su a gare ni.
Can da Allah zai bude min baki nace da karfi cikin dan zabura kamar zan mike tsaye, WALE.
Wale wale kowan su ya fadi idan ba su ba sun san ban taba sanin wani walle ba can a duniya.
Nace saike fadin Wale karo na biyu ina nuna gurin hamza yace walle ke nan ya saka abin nan ko ?
Kai na daga masu kawai ban iya magana ba sai ga hawaye ya soma biyowa a fuskana wani bayan wani shar shar shar.
Nace anba walle ya cutawa bayin Allah bayan yarda da amincin da akai mashi don may zakaci Amana Alhaji bashir ya cuta ma marayun Allah.
Ran Hamza ya baci yace yaya kinga abin da nasha fada maki kan wanan kafirin amma sai ki ce min babu komai ko ?
Nace cikin kakausar murya walle ya cuta maku ya zalunce ki zai zo yau din nan basai gobe ba zai fada maku komai da bakin shi.
Ina fadan haka na kife a gurin ina sake wani irin hamma da atishawa duk a lokaci daya nake sake su tare.
Hamza kabi sannu don gab suke dasu gama dakai don sun gane baka bari aiwa kowa gidan nan yadda suke son yi.
Nan dai nake fada masu labarin inda Hamza ya tafi batare da sanin yar uwar shi ba don nema masu taimako da kuma yadda suka gane sukabi baya suka tone abin don Alhaji bashir shuumi ne hajiya ta hana shi yin yadda yake so da dukiyan su.
Shi yasa yake kokarin ganin sai ya kawar da ita a doron kasa ya mallake komai nasu daga hannun yaran ta
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
[11/27, 9:32 PM] Zuraiyah Zuzu ๐: ๐ฉโ๐ฉโ๐งโ๐ง ๐ฉโ๐ฉโ๐งโ๐ง
BA MU KADAI BA NE A, ,
๐ฉโ๐ฉโ๐งโ๐ง ๐ฉโ๐ฉโ๐งโ๐ง
2โฃ9โฃ
Door bell ke ta ringing alaman ana sallama a gidan lokacin duk muna falo a zaune abincin da hajiya ta tura kanin ta hamza ya sayo suke ci don ta hana su cin wanda aka girka a gidan.
Duk da nace mata ba matsala amma bai sa hankalinta ya kwanta ba dashi.
Uncle Hamza kamar yadda suke kiran shi dashi ne ya mike zuwa kofan ya bude wa mai shigowa gidan a lokacin.
Ganin wanda ke danna bell din yasa shi dan kaduwa kadan amma sai yai kokarin boyewa hakan a ran shi.
Tambayan shi yayi ko hajiya tana daga ciki ya bashi amsa da tana ciki yace yana son ganin tane please.
Wani kallo uncle hamza yai mai na tuhuma sai yasha jinin jikin shi shima da irin kallon da akai mai din.
Dakatar dashi Uncle Hamza yayi daga kofan shigowa cikin gidan ya juya zuwa fadawa hajiya zuwan shi.
Cikin dakiya take cewa a barshi ya shigo daga cikin ganin mr Walle ne yashigo yasa gaba daya falon yai tsit ana kallon kallo dashi.
Gaisawa ya fara yi da hajiyan amma ta amsa mai a dadare ba kamar yadda ta saba ta aminta dashi ba.
Ganin haka yasa yaranta mikewa don su bar falon zuwa dayan falon nasu amma sai uwar ta dakatar dasu hikiman ta nayin haka shine ayi komai a gaban idanuwan su.
Uncle Hamza yai setting din wayan shi batare da wani yasan abinda yakeyi ba a lokacin.
Mr Walle ne ya fara magana yace Ma, nazo ne da wani magana wanda yake damuna sosai kusan sati uku ke nan abin yana matukar damu na a raina.
Hajiya tace you can say it now tafada cikin rashin damuwa tana tsiyaya ruwa a cup zata sha.
Ya kasa fadi sai dan kamay kamay yakeyi can dai ya daure yana cewa shi holy man ne addinin shi ya hana su yiwa dan uwan su hainci tundai, ga wanda ya yarda da kai.
Yace hajiya da farko ina son ki gafarce abisa cin amanan ki da nayi bada sanin ki ba.
Tace may kai min mr walle wanda ka haince ni har ban sani ba bayan na yarda da kai fiye da tsanmanin ka.
Yace hakane hajiya na sani sai dai ni ban yi kokarin zama mai alkawari ba da rikon amana a gurin ki.
Idan ban zo nayi confenssing din kaina ba agurin ki god will not forgive me .
Mr walle may yakawo duk wanan zancen haka a wanan lokacin ban fahinci inda maganan ka ya nufa ba.
Yake cewa hajiya bazaki fahince ni ba don an hada kai dani an cuta maki ta inda baki tsanmani ba ina tsoron kada wani abu ya samay ki ko yasamu daya daga cikin member of your familly.
Dan gyara zama hajiya tayi da mamaki take kallon mr walle din a lokacin.
Yaci gaba da fadin ba komai yasa nazo ba gurin ki don na fada maki cewa Alhaji Bashir brother din maigidan ki ya bani wani abu akan lalai sai nayi amfani dashi a gidan nan.
Ban yi ba amma dai da sani ya karbi key din gidan bayan yayi barazanan ganin baya na da iyalina akan idan ban basho hadin kaiba zai cuta muna.
Haka yasa na yarda tare dashi muka shigo don nike da keys din ko ina na gidan nan kin ya shiga bedroom dinki ya dauki lokaci a ciki haka nan kan steps din da zaikai ku sama shima yayi wani abu a gurin.
Sai dai ni bazan iya cewa ga abinda yayi ba a lokacin don ina daga bayan shi tsaye.
Kin ji abinda ke damuna nakasa samun sukuni a rayuwa na ko kadan a kan hakan.
Yanzu na yanke a raina duk abinda zai min yayi min yafi min sauki akan na yarda a cuta maku don haka zaku iya duba wanan guraren dana fada maki ku gani ko zaku fahinci abinda nake fadi.
Mr Walle how comes duk yarda da amincewan da nai maka a duk fadin garin nan har ka bari Alhaji bashir yai galaba akan ka.
Yace Hajiya is god wish sai na yarda amma nima nasan ban kyauta maki ba wallahi.
Shiru hajiya tayi tana nazari kafin tace dashi taji kuma ta gode amma yana ganin zats kara amincewa dashi kamar yadda ta amince dashi da farko kuwa?
Yake cewa shi dai ko bata kara yarda dashi ba a yanzu bukatan shi, kawai, shine ya kasance ta yafe mai akan abinda aka aikata mata da sanin shi.
Shiru hajiya tayi sai zuwa tsawon dan wani lokaci kamar mai nazari take cewa ba damuwa zai iya tafiya .
Sai da yai dan jim guri daya kaman bazai tashi ba sai ya kara cewa tayi hakkuri dan Allah shima ba da san ranshi haka ya kasance ba.
Ya dai mike gwiwa ba karfi yabar gidan don yasan cewa ba zata kara amincewa dashi ba kamar farko kuma.
Yana fita hajiya take cewa ikon Allah wai may bashir yake so damu duniyan nan ne haka ?
Uncle Hamza yace dukiyan marayun Allah shine a gaban shi mana bayan wanda sukai gaba dashi bai ishe su ba, wanda ya rage maku ne yake tsune mai ido kuma.
Nabila tace mummy ni dama wallahi ban son al, amarin baba bashir din nan tun dady yana da rai kune dai kuke daukan shi da wani muhinmanci sosai a rayuwa.
Nan dai suke ta maganganu mara dadi gamay da Alhaji bashir ba dadin saurare.
Sai zuwa can nake cewa mama amma sai nake gani daga wanan abin da yayi yakai karshe insha Allahu don kaikayi zai koma kan mashekiyar ta duk abinda yake nufi daku Allah zai mayar mai dashi a kan sa.
Daki daya muka kwana da yaran hajiya don sun ce wai suna jin tsoron kwana su kadai a dakunan su.
Na fada masu da yardan ubangiji babu komai da zai faru dasu insha Allah don akwai tsarin ubangiji wanda su ba lalai bane su san dashi.
Kwanan mu biyar a gidan tare dasu naji matukar dadin kasan cewa da wa yan nan mutanen na dan lokaci.
Na shirya tare da tarin abin arzikin da na samu daga gurin hajiya da iyalinta wanda bazan iya tsayawa fadin shi ba har sai na manta da wani.
Cikin lafiyan mota tare da tarin abin arzkina na iso gida na samu iyalina a cikin kewa na don ban taba tafiya haka ba na bar yarana su kadai.
Irin abin arzikin da Umma taga na dawo dasu gidan ne yasa ta matukar mamaki irin wanan alheri haka mai yawa.
Nan dai na shiga aikawa yan uwa da abokan arziki da abubuwan alheri dana samu suma su dana rabon su daga ciki.
Rayuwan daula yana Abuja ko a abujan gida masu hannu da shuni suke cin karen su babu babbaka.
Sai ina ganin mu ai kawai dai mun rako sune kallon duniya ashe shine dalilin da kullun mahaifin mu bai son muna shiga gidajen masu hannu da shuni don gujewa ganin wani rayuwan da ba irin namu ba.
Yaro shi bai san banbancin mai kudi da tallaka ba sai yaga kamar abin duk daya ne laifin iyayyen shi kawai.
Na fahinci hakan yanzu da hankalina yaikai lokacin da zan san haka din balle akan wanan daulan duniyan dana tafi na gano gidan masu abin.
Ban ga laifin mahaifina ba da yake tsare mu daga shige shigen gidajen masu hannu da shuni.
Wanda a da nake ganin kamar wani kuntata muna ake dayin hakan ashe ban sani ba gata ne akewa rayuwan mu da hakan.
Sai washe gari ne muna hira Umma take fada min akwai wata matar da tazo har sau biyu gidan nan wai tana son ganin ki.
Cikin mamaki na bar abinda nakeyi nake cewa Umma wacece ita ko bata fadi sunan ta bane ?
Tace bata fadi ba sai dai matar kamar yar duniyace daganin ta gashi dai girma ya