Showing 72001 words to 75000 words out of 115099 words
Chapter 25 - Bamu kadai ba ne book Complete by Zainab Makawa .txt
Nan suka gaisa dashi ta gabarta da kanta gareshi yai mamaki don sunan ta ba bace yake ba a gari don kowa yasan ta sosai.
Take fada mai suna son ganin matar shi ce maryam mamakine sosai yakama shi ida na san wa yan nan mutanen nan haka.
Yace da ita bissimillah ko sai ta danyi murmushi tace sai dai tare da yarona muke ko zan iya shigowa dashi gidan nan.
Dan jim yayi kafin ya daure yace bissimila ba matsala ku shigo daga ciki a tare dashi suka karaso har zuwa cikin falon mu.
Ina ganin ta na sheda fuskan ta nake cewa sannu da zuwa Umma.
Muka gaisa dasu gaba dayan su suma suka gaida Umma cikin mutunci.
Nan ta fara magana maryam sai kika ganni a bazata a gidan ki ko ?
Kiyi hakkuri yakama dole ne nazo don na nuna maki jin dadin abinda nai nasara ta dalilin ki nai maki kuma godiya.
Yau dai ga dana Nasir Allah ya dawo min dashi gida bayan tsawon lokacin daya dauka baya gidan.
Jin abinda ta fada ne yasa na daga kaina nadan saci kallon wanda ta gabatar da sunan dan ta daya bata da dadewa.
Yau gashi da taimakon Allah a sanadinki mun samu Allah ya dawo muna dashi gida lafiya duk ta sanadiyar ki hakan ya samu.
Haka yasa na wanko kafata nazo har gida nai maki godiya tare da baki dan sadaka da fatan bazaki raina dan kyauntan da nazo maki dashi ba.
Sai ta mika hannun matar da sukazo tare ta miko mata key daga hannunta.
Hajiyan ta dan zakudo daga saman kujeran da take zaune tana miko min key din tana fadin gashi motace sai dai ba wata babba bace 406 ce kika samu.
Naso ace akwai kalar data dace dake ta mata sai wanda zai dace daidai, dake na kawo maki amma babu ita a kasa yanzu.
Wanan da kike gani tare dani shine Nasir din daya bata tun mahaifin shi yana da rai yau kimanin shekara goma sha biyar ke nan bamu san inda yake ba.
Munyi neman shi duk inda ya kamata amma Allah baisa andace ba sai da naji albishir din dawowan shi daga bakin ki kuma ban yarda da zacen ki ba a lokacin.
Amma Allah da ikon shi sai gashi jiyan ya dawo gare mu daidai lokacin da kika fada muna dawowan nashi.
Haka yasa idan da hali zanso nadanji wani karin bayani daga bakin ki akan batar nashi ko akwai abinda zamu iya sani akai.
Kaina nadago a hankali nace hajiya kyautar mota haka kan wanan maganan kawai.
Mamakin furci na tayi don cewan da nayi kan wanan maganan kawai a ranta take cewa yarinya baki san halinda na shiga bane yasa kika fadi haka.
Naci gaba da cewa nima fa banice nai hakan ba ikon Allah ne sai sakon da baba malam yace na fada maki kawai yasa nane mi gidan ki na fada maki.
Murmushi tayi tace maryam wanan ba komai bane idan da zaki san ko miliyan nawa muka kashe bazakiyi mamakin ba don na baki wanan motar kawai kinfi haka a gurina maryam.
A daidai lokacin ne nafara wani hamma na ina yi ina dan murza hannaye na guri daya a lokaci guda take murya na ya canza zuwa sabuwar murya.
Ina fadin salamu Alaikum hajiya duk suka karba min sallamata, gaba dayan su a falon.
Nace da farko muna tayaki murnan dawowan jinjirinki a cikin ku da fatan zaki kwantar da hankalin ki ki saurare mu.
Nasan kin na zargin wata da aikata maki wanan aikin akan danki wanda zarginki ba anan yake ba.
Wanan matar da kike zargi har kan aiki ne kawai a tsakanin ku da ita abin baikai haka ba
Bazan so fada maki wanda yai wanan aikin ba kai tsaye amma maishi zata fada da kanta.
Mahaifin jinjirinki yana gwadawa jinjirinki so da kauna wanda har yakai bai iya boyewa kowa a fili cikin jinjiran da Allah ya bashi.
Wanan ne dalilin da tsanarsa tai yawa a zukatan mutane da dama saboda suna ganin duk wani dama nashi zai kare ne akan danki.
Sai na kada kai a cikin takaici nace kai bil, adam baku da kyau baku da tausayi a rayuwan ku.
Ki godewa Allah jinjirinki yana rike da Allah a tare da shi sosai da ba iya abinda zai faru dashi ba ke nan.
Ko zaki iya tuna matar da takawo maki tallan tufafin yara a office dinki a shekarun da suka wuce ?
Har kukai sa,ainsa da ita kafin ki sayi kayan idan ma baki tuna ba bari na tuna maki yau .
Kawar kice amma sai tana hurda da wata da baki yarda da ita ba haka yasa zargi ya shiga a tsakanin ki da ita.
Wanan tufafin dakika sayawa jinjiranki agurin ta ne farkon sanadin batar danki don kin saya masu kayan dake da sihiri a cikin sa.
Gaba daya yayanki hudu sun shiga tsana a zuciyar mahaifinsu wanda ke baki kawo komai a hakan ba a ranki.
Hajiya tace anyi haka gaskiya amma ni ban san cewa Gajiye zata iya min haka ba gaskiya.
Zata iya fiye da hakan don itama a lokacin tana son ta auri maigidan naki sai dai tana ganin baida kowa a gaban sa sai ke da zurian ki.
Cikin mamaki hajin tace ita gajiye din ke nan ko ?
Kwarai kuwa don haka yasa take hurda da abokiyar zaman ki wacce itama bata san cewa rudin ta takeyi ba a lokacin.
Tare suka hada kai sukai mashi kurciya wanda ba zaku kara ganin sa ba a duniyan nan gaba daya.
Allah ne ya taimaka yana barin nan bai tsaya ko ina ba ya fada dajin kashimil inda ya fada a hannun wani musulmi hafizi yake taimaka mashi.
Wanan matar da yazo da ita wanan bawan Allah ne ya taimaka mai saboda sun yaba da hakalin shi sosai suka bashi yar su aure.
Kurciyar da akai sihirin da ita ta mutu a daji cikin sahara acan muka nemo layan sihirin muka warware shi shine har hankalinsa ya dawo gida sosai kikagan shi.
Idan da bamu samu dauko wanan layan ba danki ya bata daga gare ki ke nan har abada.
Sai dai kuma anan gida ana bata mai sunan cewa ya saci makuddan kudin mahaifin shi ne yasa ya gudu ya boye dasu ko ?
Hajiya tace haka ake fadi gaskiya amma ni nasan ba haka bane maryam.
Murmushi nayi nace ni ba maryam bace zaki iya kirana da malam sulaimana ko Alhaji malam uba nake a gurin maryama, godiyar mu ce ita da muke aike kawai a gurin ku bani adam.
Saboda ita tamuce jinin muce muna da alaka maigirma a tsakanin mu da ita cikin bil,adam.
Za,a kawo wa danki abubuwa da dama da sunan murnan dawowan shi gida cikin ku , bashi ba koke kada ki taba ko daya daga ciki komai sha,awan da abin ya baki.
Har zuwa wani dan lokaci bazaki fahinci danki ba don haka kibishi a sannu har komai ya daidaita akan shi.
Na barku lafiya lokacin sallah ya gabato sai wani lokaci idan Allah yakaimu kuma.
Shiru nayi na dukar da kaina yayin da kowa na falon ya numfasa don jin abin al, ajabin da sukaji daga bakina.
Hamma na sake yi again ina dan murza hannaye na dana hade a guri daya a hankali.
Matar da suke tare da hajiya take cewa kamar fa bai tafi ba sai murya sukaji ana fadin baba yatafi mukkadarasiya ce dai tazo tayaki murna dawowan jinjirin ki.
Hajiya babana ya tafi bai maki bayani ba amma ni yanzu zan maki idan kina son ji.
Da sauri hajiyan take cewa idan zan samu zanso naji komai gaskiya akai don nasan inda zamu dosa.
Hajiya da farko kada ki bar dakin a garin nan don makiya sun maki yawa a tare da ke ba gida ba ba, a waje ba.
Hajiyan ta amsa da fadi gaskiya ne haka maganan take makiya kan akwai su wallahi karma siyasan nan da nakeyi a yanzu.
Dawowan shi zai jawo idon mutane akan shi donke kin yi sakaci sosai ga iyalin ki.
Boko kawai kika saka a gaban ki baki damu da yi wa jinjiranki komai ba akan zaman duniyan nan da rayuwan su.
Wanda haka ba hali ne da ya dace duk uwa tagari tayi watsi dasu ba a rayuwan ta cikin wanan zamanin da muke a ciki.
Yau zamani yazo muna da sabon rayuwa da abubuwa iri iri a cikin sa wanda mu ada bamu daukan su da wani muhinmanci sosai.
Amma yanzu ya zama dole duk uwa ta gari ta mike akan yayan ta tana masu addua tana kuma dan nema masu tsari daga cikin tsarin da ba sai an kaucewa mahaliccin mu ba.
Koda ta hanyar yin sadaka ga mubukata da marasa lafiya da tsuntsaye zaki iya neman tsari ga jinjiranki.
Akwai taimako da dama daba sai kin kauce hanya ba wanda sai dasu dole rayuwa take tafiya dasu a yanzu.
Tun yaro yana karami yanzu iyayye basu hana shi yawan amsan sadaka daga makwabtan su wanda akasarin mutane a yanzu bawai sadakan Allah da Annabi ne sukeyi ba.
Akasari sunayi ne da wata manufa da wasu miyagun mutane ke basu , sa,an kwashe baiwan yaro da yake dashi tun yana karami.
Sai wanan baiwan da sa, an su koma ga wanan mutumin idan har sadakan gaskiya ce ai ga mubukaci ake son mutum yaba da sadakar shi.
Amma zakiga mutum ya tara yara kanana a kullun yana mika masu sadaka da hannun sa wanda ba komai bane wasun su sukeyi sai sihiri a hakan.
Bance duk masu sadaka haka suke ba sai dai gaskiya akasarin masu yi a yanzu da wani manufa suke yin hakan.
Wani zai shafa kan danka da sunan so ko kauna wanda ba komai ne zai diba a cikin sa ba sai bawan da Allah yaiwa yaron ka kawai zai rabashi dashi har abada.
Ko zaki iya tuna kin tafi kauye da yarki Nafisa to hakane ya kasance da ita kike ganin ta wata kala a cikin diyan ki.
Ranan auren Binta yarki akwai matar da ba, abawa wanan abin da kuke rabawa ba na ledan buki.
Wanan matar tun wanan lokacin take rike da mahaifar yarki Binta da yau shekara bakwai da aure amma ko batan wata bata taba yi ba a gidan mijin ta.
Mamaki ne sosai ya kama hajiya jikinta ya shiga karkadawa cikin nazarin magana ta.
Na girgiza kai nace dan adam ba kyau gaskiya zaku iya yin abinda mutum bai taba zaton zaku iya ba don ba imani ke gareku ba duka.
Wanan rabon abinda kukeyi idan kuna buki yana iya kawo maku matsalolin aure da dama wanda ku baku sanda hakan ba a gurin ku ba.
Zaku iya zama a gaban yaro karami kuna cin abu ba tare da kun bashi ko da kadan ne daga ciki ba shima ya lasa yaci wa ran shi koda kadan ne
Wanda haka zai iya kawo sanadin da yaro karami zai iya tsiyaye zurian da Allah ya bashi gaba daya lokaci daya ga fitsarin sa.
Wanda ke hajiya hakan yana daga cikin halinki a baya kina ganin ba yaro abu zai saka shi a kwadayi ko wani abu can da ban.
Ba hakka abin yake ba ga zahiri gaskiya yaro yana tare da wani bawai ta musan man amma sakaci irin ta iyayyen yau yana kawo matsalar da dama ga yaran mu na yanzu.
A da can baya idan mace tai ciki sai manya kawai ke iya gane hakan daga gareta su fahinci tana dauke da juna biyu basu magana sai dai su bar zancen ga zuciyar su kawai.
Amma yanzu tun ciki yana mako biyu wata daya zuwa yan watanni kowa zai sani kamar an busa sarewa.
Wanan shine matsalar dake damuwar yarinyar ki da kikaiwa aure a baya Aminatu yar wajan wanki da kika tayar abaya.
Da sauri hajiyan take kallona da mamaki don jin abindana fada don tasan yarinyar nata na fama da yawan miscarage .
Nace dazaran ta samu ciki gaba daya sai kowa ya gama sani kafin agama hallita shi a cikin ta, wanda yawan, bakin mutane ne ke yawan lalata shi koma da haihuwan tayi dan zai iya zuwa a lalace ko wani kala can daban.
Baki ke nan, irin taku na yan adam duk yake haddasa hakan wani lokaci ga mataye masu haihuwa.
Idan Allah ya bata wani cikin idan zata iya jan bakinta tai shiru ta dinga karanta malikki yumiddim, kafa goma sha daya da safe da yamma tana shafe cikin dashi, insha Allahu cikin zai zauna ajikin ta har ta haife shi lafiya insha Allahu.
Hajiya tace insha Allahu angama in dai wanan ne kawai zan ja mata kunne sosai ga hakan.
Nace Ni na barku lafiya lokacin sallah yayi zan bar godiyar mu ta huta haka na.
Tana wucewa sai na kama kuka wiwiwi matar tace ikon Allah wani yazo kuma fa hajiya baban Abba dai yana zaune imani duk ya kashe maijikin sa.
Wai yau maryam din shi ne a cikin irin wanan halin haka take wanan wahalan da wanan abin murya na ya koma kamar ta larabawa a lokaci daya alhalin ni ko Niger ban taba zuwa ba balle garin larabawa.
Sukace dawa muke magana don Allah yanzu larabci na fara yi cikin gwanewa Allah yasa hajiya da Nasir suna dan ji.
Suke tambaya ana basu amsa wani ma basu san may ake fada masu ba suna dai jin ana fada sosai ana kuka cikin harshen larabci ne kawai.
Fada takeyi wai an bar Nasir ya wahala sosai a duniya don haka su sai sun dauki mataki akan duk wanda keda hannu cikin wanan abin.
Don Nasir abokin karatun su ne tun suna kana a masar da sukai zama lokacin mahaifin shi yana ambasado acan.
Kuka sosai mai shi takeyi tana fada ta wuce a jikina nan na sake atishawa masu karfi har kashi uku sai na lamay a saman salayan da nake zaune akai.
Sai sannu kawai suke min da sannu maryam da kyat cikin daga kai nake karba masu na koma bayan kujera na dan jingina kaina a hankali.
Shiru falon yayi ba mai magana daga cikin mu sai zuwa can hajiya Umma da duk imani ya cika ta shiga nazarin maganganun da taji yanzu take cewa.
Wai nace ko ku mutanen garin nan ne ko baki ne ku ?
Baban Abba yace cikin sauke ajiyan zuciya hajiya aiki ne ya kawo ni nan garin ok kawai tace can kuma ta kara cewa don Allah ku mutanen wani gari ne ?
Yace daga Niger state muke hajiya ok ok nagane No warnder kawai tace.
Sai dan shiru da ya kara biyowa baya a falon kowa da abinda yake nazari a ransa.
Can tanisa tana cewa ok mu zamu koma ke nan sai kun kara jin mu ke nan.
Malama maryam mungode zamu tafi zaki jini nan bada dadewa ba insha Allahu.
Suka mike shima baban Abba mikewa yayi yabi bayan su nansan saboda darajan tane da kima yasa shi binta suna sallama dashi.
Nan dai suka tafi suka bar mu da mota a kofan gida wanda wai yake a matsayin nawa.
Motar dako mijina ba irinta yake shiga ba amma yau a dalilin wani sanadi nina mallake shi.
Banso fada mai ya samo min hantiti kamar yadda akace na dinga yi sai dai yadda jikin ya matsa min dole nai mai magana akan iein yadda nake jin jikina ya damay ni.
Ya fita yaje gurin nema min kafin yamma ya karasa yi sosai a lokacin bai jima ba sai gashi ya dawo min dashi a cikin dan wani bakin leda.
Haka na kama shakawa kamar mahaukaciya kafin na samu naji dama a jikina.
Cikin karfin hali irin nawa hakan bai hanani yin girkin dare ba ina yi ina kwantawa har nagama abinda duk zanyi .
Ranan kafin tara na dare har na kwanta nai barci don duk jikina a dipge yake min bana jin dadi ko kadan a tare dani.
Kasa hakkuri yayi ya dauki waya yakira mahaifina don yasan halin da nake ciki.
Nan yake sheda mai halin da ake ciki yanzu har kyautan motar akai min kan wani matsala da ya taso na warware shi.
Baba yace ikon Allah wanan abin kuma akan maryama ya sauka kuma ?
To Allah ya sauwaka yasa ayi a cikin nasara abune na nufin Allah babu yadda zamuyi sai dai kawai musawa al, amarin Allah ido.
Don idan mukace zamu bi zancen da zafi bamu san yadda al, amarin zai kasance ba damu.
Fadan da baka ganin maishi sai a sannu addua zamu bita dashi akan Allah ya kawo mata saukin al, amarin a rayuwan ta.
Don abin nasu kamar ya zama gado ke nan don kaga haka mahaifiyan ta tayi aanan wahalan da yake bamu fahince su yadda ita ta fahince su ba sosai sai abin yazo da akasi akarshe ma muka rasa rayuwan ta