Showing 108001 words to 111000 words out of 115099 words
Chapter 37 - Bamu kadai ba ne book Complete by Zainab Makawa .txt
kawai tunda tace Abba sai na dauki abin serious na hau na zauna na dinga mata barin kudi akai.
Look ki fada min exactly yadda kukayi da wanan matan dan kamay kamay tafara yi bata son ta fada mai komai duka haka dai tai mai bayani ya fahinci lalai fa akwai matsala duk yadda akayi tunda sunan yaron yafito daga bakin mai maganin.
Yace dole ne muyi yadda aka fada muna muyi don tsira da mutuncin mu da rayuwan yaron nan saboda nan gaba.
Tace sai naga kamar ka dauki zancen da karfi kai har cikin ran ka ?
Yace haka kawai naji maganan ya tsaya min a zuciyana don haka zan sa ai min wani abu akai mu gani.
Daga haka ya mike zuciyar shi duk a jagule ya bar falon zuwa dakin kwanan shi yana jin kan shi a cikin wani irin yanayi.
****** ********* ******
Sosai naji dadi da na samun wayan hajiya balaraba yusuf matan sabon controler na custom na kasa tana nema na a gidan ta.
Ban tsaya wani tsaiko ba nake cewa da baban Abba don Allah ya bari na tafi na amsa gaiyyatar ta.
Yace idan ma zaki tafi ne tare da ni zaki tafi nima nai masu murna idan mun tafi din..
Don haka washe gari muka shirya har Umma da yara zamu tafi, kamar an jefo min mutumiyata yar sokoto a gidan.
Ganin muna shiri take cewa yau kuma sai ina haka nace zamu gidan Ogan su baban Abba ne muyi mashi murna an bashi controller nasu na custom tace ai nima baza a barni ba dani za, a tafi gaskiya.
Ina dariya nace ai sai ki shirya mu tafi, bata dauki lokaci ba sai gata ta dawo a cikin shirin ta muka kama hanya.
Nice ke jan mota muna zaune da baban Abba a gaba yar sokoto da Umma da yara suna baya a zaune.
Da kwatancen da yake muna ne muka isa gidan a GRA katon gida ne irin na manyan kusan gwaunati.
Gidan ya matukar tsaruwa gurin tsari sosai don babu ne babu a gidan zamu shiga muka hade da Amina tafito saye da hijjab din ta mai hannu da alama fita zatayi a lokacin.
Tana ganin mu ta sheda mu ta dan saki murmushi a fuskan ta na jin dadin ganin mu.
Mun gaisa da ita a cikin mutunci take cewa ashe kuna tafe amma mama bata sani ba don tafita sai dai ba dadewa zatayi ba bissimillah ku shigo mana.
Tajuya muka bi bayanta zuwa cikin gidan nasu wani katon falo muka zauna har ita ta ciro wayan ta daga cikin jakjar ta tana neman layin mahaifiyan ta.
Sunyi magana take fada mata tana da baki a gida uwar ke tambayan ta ko su waye ?
Tace mama matar nan da kuka kaini gurin ta ne na easthe din nan .
Tace ace gata tafi wata mace Aminan ta kira daga cikin gida tazo ta kawo muna abin sha.
Ba,a dauki lokaci ba uwan ta shigo gidan da alaman dama ba nisa ta tafi ba daga gidan.
Mun gaisa tana jin dadi tace kai amma baku kyauta min ba da baku sanar dani yau zaku shigo ba ai da mun dan hada maku abin taron baki.
Nace aiko haka ma mun gode take cewa maigidan ranan yai tafiya ya tafi yin reporting gurin aikin shi.
Tace ita ma tafita ne zuwa gurin masu shirya masu bukin da za, ayi na taya maigidan murna.
Nace mama da fatan ba wani shagali zaku shirya wanda zai jawo magana ba akai ?
Tace to kin san yanzu haka akeyi da zaran ka dan samu abin farin ciki sai ka gaiyaci yan uwa da abokan arziki sun taya ka farin ciki.
Nace hakane kuma fa mutane suna son abin da za, ai bida,a sosai yanzu, wanda basu ganewa ne a haka shedanu ke samun dama shiga mutane har suyi barna ba, asani ba.
Wata kila ga mai bukin ko wani wanda ya halarci bukin nashi ya samay shi a lokacin.
Don fa duk abinda zamuyi bamu kadai bane ke gudanar dashi a gurin dole ne sai an samu kasancewa jinsi daban daban wanda ba lalai bane mu gane hakan mu.
Kai maryam har kin sa jikina yai sanyi wallahi nace hakan ne ke kasan cewa yadda alumma suka kasance ne yakawo hakan ai.
Yanzu yaya za, ayi ke nan shiyasa fa dama na bukaci na ganki kafin hakan ya kasance, musanman ma akan ita wanan din kada wani abu kuma ya skasance da ita.
Don yanzu gaskiya alhamdullahi ta samu lafiya sosai a wannan lokaci gashi kina ganin ta takoma kamar ba umma da muka sani ba abaya.
Muna gidan baban Abba yake cewa zai tafi ya dawo sai ya dauke mu nan muka zauna dasu cikin jin dadi zakace ko mun saba da dewa dasu ne.
Hira muke sosai dasu cikin jin dadin yadda muka samu karbuwa a gidan don maman bata da girman kai ko kadan.
Umma na kula da yau taji dadin fitowan mu daga gida kodan yadda taga an tare mune a gidan oho ?
Nan hajiyan ta ke be dani don wani muhinmin maganan da take son yi dani.
Wanda ba komai bane illa akan zancen maigidan ta ne dakuma yaran su wanda yanzu shine matsalan mutane da yafi damun su.
Mun tatauna da ita sosai daga karshe ne take tambaya na wai may yasa bana son zancen sayen kwantainan da tai min ne ?
Cikin murmushi nace ba hakana bane mama kawai dai don naga kamar banda zarahin hakan ne sai nake ganin yafi karfina.
Idan banda abinki maryam dama ai sai wani ya dafa wani yake tashi ai haka duniya ya gada don haka kada kiji komai please ?
Akwai guda biyar da aka ware min don haka sai na baki daya ko biyu daga ciki kema ki more na kan ki.
Nace wai mama dayan ma na samu na hada dai mu gani tace a cikin sauki ne fa muke samun shi muma mu karu.
To amma mama sai nake ganin kamar haka ai cin amana ne ga bayin Allah.
Dariya zance na yabata take cewa ba haka abin yake ba ai maryam mutane ne da sun riga da sun ginu amma basu bin ka,idan da gwaunati ta shimfida masu gudun kada a tuhumay sune yake sa su watsar da kayan subar wa yan custom shi a gurin su.
Nace insha Allahu satin nan zan hada kudin dake gurina zaki jini da yardan ubangiji tace toke fa maryam ai a haka kike ganin mata na tashi yanzu.
Akwai na atamfofi da takalma da kayan yara wani kike so ne daga ciki su ?
Nace sai naga kamar atamfan da kayan yaran zaifi saurin karbuwa ko don su nake business din su dama .
Tace da kyau yanzu yadda za, ayi zan hada maki dana takalma sai mu raba ayi maki cumbunation din su ina ga zai fi ki gwada kawai ki gani zasu karbu don kayan suna da matukar kyau sosai .
Nace mama na gode Allah yasa mu dace tace amin ya ta haka nake son ji daga gare ki.
Na rasa may zan maki a rayuwa da zamu saka maki akan alherin da muka samu daga gurin ki idan maigidan ya dawo zan mashi bayani nasan zai taimaka maki sosai shima.
Sai bayan munyi sallah azahar yazo daukan mu mun sha kyauta sosai na alfarma a gurin ta daga ni har yara umma da yar sokoto kyautan atamfane yan super masu kyau da tsada naga inda karyan business din mata yake a gurin ta namu ashe dan mali ne.
Yar sokoto tace tabbas zama na dake maryam alheri ne babba ga rayuwana zanin da nake bin baba Iman ya sayo min fiye da shekara gashi Allah ya bani har biyu a lokaci daya.
****** ********* ******
Mijin ne yake cewa da ita ta shirya zasu tafi waje amma bata taba kawo cewa gurin dan su zasu tafi ba alokacin saida suka biya kasashe biyu yaga likitan shi suka wuce inda dan nasu yake karatun shi na likita.
Tun isan su kasan ne take kirsn layin dan nata ta sanar dashi zuwan su amma wayan nashi a kashe yake.
Haka yasa suka kama hanya zuwa gidan akai tsaye tun da suka shigo layin kida ke tashi gidan sai haske disco light ke tashi a cikin sa.
Suna karasawa maza da mata ne matasa zakace a tsirara suke sai masha,an su sukeyi sam basu damu da ganin su ba da sukayi.
Nan hankalin hajiya ya fara tashi dirct dakin sama suka hau inda dakin shi yake.
Yana kwance tare da yan mata uku suna ta aikata mashaa a dakin suna ganin su bai sa sunji ko gezau ba a jikin su har shi yaron nasu.
Ga kayan maye a ko ina dakin abin ba, a cewa komai uban ya nufe shi yadago shi duk da yana a cikin maye bai hanashi sheda mahaifin nashi ba.
Amma abu ga wanda yai nisa sai ya fara cewa daddy you are welcome enjoy your self please ?
Tas tas ya fara kwasanshi da mari sai da ya gigice a gurin zai kara kai mari karo na uku ne Abba shima ya dunkule hannayen shi kamar zai rama lokacin mahaifiyan ta shigo dakin tana gani tace kada ka soma Abba.
Ya dago kai yana kallon ta lokacin yan matan dake kokarin mikewa wata baka daga cikin ukun take cewa don may za, a bata masu jin dadin su haka ?
Abban ya fada gado daga baya gashi tsirara yana cewa o shirt cikin dafe kan shi sai barci.
Kuka uwar ta sake don magana ya zama gaskiya ashe abinda yarinyar nan tagani ke nan take nufi da zancen ta.
Juyawa mahaufin yayi ya fita zuwa falo inda kida ke tashi sun kai wa makwabta ko ina ya kashe kidan tare da daka masu tsawa sufice mai daga gida.
Daya bayan daya suke ficewa da bakar magana a bakin su na an katse masu jin dadin su da sukeyi.
Ranan haka suka kwana a zaune babu wanda ya uya runtsawa a cikin su don takaici.
Abban bai farfado ba don mugun mayen da yayi sai bayan an kwana a wuni likitan da aka kira ya duba shi yake ce masu drugs ya kusa yiwa lafiyan shi illa sosai.
Gashi anbinkota makarantan da yake karatu sunce ya daina zuwa ma yin karatun kusan wata hudu ke nan.
Maigidan yace kinga irin haukan ki ko ?
Mata ta fada maki abinda ake ciki amma kike ganin abin hannun ki take son ci an fada maki irin mutanen nan ana watsi da baiwan da Allah yai masu ne ?
Komai da zasu bar kasan da yaron sun kammala shi tare dashi suka dawo gida Nigeria don basu iya barin shi kasan ba.
Kowa yagan shi yasan yaga dan maye ba wanda ya tafi karatu ba don babu kimtsi ko ga irin shigan shi.
Sai bayan sati daya da dawowan su ne mahaifin ke tambayan ta inda matar nan take yana son ganawa da ita.
A lokacin ne ta tuna mun yi musayan lamban waya da ita shine tabayarbwa maigidan nata.
Ina zaune a falo tare da kowa na gidan muna hira a falo wayana yai ringin na dauka bakon nombane nagani ake kirana dashi.
Ban ki dauka ba na daga wayan muryan namiji ne naji yana min sallama gashi layin special nombane irin ta manya.
Na dauka muka gaisa yake cewa bayan mun gaisa din kina magana ne da gwauna jaha kaza.
Na kalli wayan cikin mamaki kamar mai maganan yana a gabana a lokacin.
Yake cewa idan babu damuwa don Allah ina son muyi magana dake ce ta fahinta akan matsalan yaron da kika fadawa matana.
Cikin mamaki nace ina ga bani bace gaskiya murmushi naji yayi yace don Alkah ki saki jikin ki ba wani matsala bane ai.
Dama zancen da kika fada ne ya zama gaskiya shine nake son muyi magana akai don yanzun haka yaron yana nan kasan mun dawo tare dashi.
Sai dai yana cikin wani yanayi na bukatan taimako ne shine dalilin da yasa na kiraki yanzu.
Kin san ba girma na bane a ga nazo gurin ki kai tsaye sabo da tsara gashi kuma ko banza ke din matar aure ce.
Don haka ina son jin yadda zaayi mu gana dake idan ba damu zanso satin nan ki shigo garin mu gana .
Nace ga maigidana zaku iya magana dashi duk abinda yace shike nan na mikawa baban Abba din wayan dake rike a hannu na yana tambayan wane a layin.
Amsa yabashi da fadin shi gwaunan jaha kazane matsalan dan shi ne yataso yake son ya taimaka mai yaga matar shi don kila akwai mafita a gurin ta.
Baban Abba ya aje appointment dashi bayan ya saurari bayanin shi cewa zamu shigo a karshen mako lokacin ba aiki ranan.
Haka ya kasan ce muka shirya har yaran da Umma zuwa jahan cikin tanadin da gwaunan yai muna na zuwa ganin su.
Ban taba tunanen zan ziyarci wanan jahan ba don banda kowa a can kuma ba wani dalili da zaikai ni.
Sai gashi yau a bisa wani dalili mun shigo jahan kuma ta jirgi mukai tafiyan namu.
Yadda aka tare mu zakace ko wasu mafada ajine akasan nan din musha taro na mutunci gaskiya.
Sai dare muka samu ganawa da wanan iyalin cikin girmamawa sosai da ba sai na fada ba.
Daga nan aka fara zance baida wani matsala na iska sai dai miyagun abokan da yake hurda dasu ne kawai suka mayar dashi haka.
Nace za, a bashi magani wanda zai daina sha har abada da yardan ubangiji bazai sake ba insha Allahu.
Mahaifin yace don Allah na taimaka masu don shine babba a cikin diyan shi ga kuma halin daya fada ciki.
Nace sai dai idan har anbashi zai galabaita amma kada su damu zai dawo daidai insha Allahu.
Duk yadda suka so yaron yasha maganin yaki a ranan dalilin da yasa ke nan suka kirani a cikin daren.
Mun samay su cirko cirko a tsaye yana tsula masu tsiya wai shi ba zaisha maganin hausa ba cikin shi yai tsatsa.
Kallo daya nai mashi cikin yanayina daya sauya nace kamar da tsawa karbi kasha shi maza.
Ya dago kai da nufin yai min tijara ban san may yagani ba a gare ni ba mussu ya karbi cup din daga gurin uwar shi ya shaye shi tas.
Takawa nayi har inda yake a tsaye nace miko min hannun ka nan ba mussu ya miko hannayen nashi gare ni.
Kamawa nayi kamar ina fitar mai da wani abu sai wani hayaki yafito daga hannayen shi nan ya kife ya fadi kasa baisan inda yake ba.
Nace akama shi akai shi dakin shi zuwa safe zai farfado kuma zasuga sauki gare shi da yardan ubangiji.
Godiya suke min sosai kamar ba a kasa garesu nake ba banyi magana ba sai hannu dana daga masu kawai alamam godiya na juya na fice daga falon gidan.
Sai bayan na shiga dakin mu ne na saki atishawa wanda ke nuna alaman abinda ya hau kaina ya fice a lokacin.
Barci sosai mukayi duk jikina da gabobina suna min ciwo da kyat na falka da safe a hakanan ba dadi.
Munso juyowa washe gari amma hakan bai samu gare mu don sun dakatar damu akan mu dan tsaya suga yadda jikin yaron zai kasance mai.
Munji dadin bakuntan da muka kai masu sosai don har tataunawa munyi da gwaunan yana bukatan a warware mai wasu yan matsalolin da suka sha mai kai.
Ba laifi yasamu nai mashi bayani sosai ya kuma gamsu mun juyo mun dawo kaduna tare da tarin alherin da ban taba tsanmanin samun shi ba daga gare su.
Mun samu hartan bukin samun girman shugaba su baban Abba naga karyan naira a gurin kamar ba gobe.
****** ********* ******
Nasha fadawa baban Abba don Allah ya daina yin dare idan ya fita amma sai yake daukan zance na a tsurku ne kawai.
Sai yaga dama yake shigowan shi easthe din mu a lokacin da da duk ya bushi iskan hakan .
Ranan yakai sha biyu da rabi yabaro gurin aikin su ya nufo gida kai tsaye ba wani damuwa a ran shi.
Tun shigowan shi easthe din yaji tsikan jikin shi ya tashi mai sosai amma bai san dalilin hakan ba yana dai tafe gida kai tsaye.
Gani yayi kamar gurin ya juye mai a lokaci daya ya hasko hsske fitilan motar shi sai yake ganin kamar yara suna wasan su babu damuwa komai.
Mamaki ne sosai ya kamashi ina yara suka fito a cikin daren nan haka kuma baima san su ba a uguwar namu gasu kamar yaran turawa daganin su.
Kamar ancd ya daga kan shi sama sai gani yayi kamar mutum zaune ya tokaro har rufin gidan mu zaune da fararen kayan shi yana shan iska abin shi.
Take yaji gaban shi ya Fadi tabbasa yau ya shedavda idon shi ba mukadai bane a gidan kamar yadda nakan sha fada mai hakan.
Ya isa da sauri yaji duk jikin shi ba dadi ga tsoron da ya mamaye mai zuciyar shi.
Da karfi yake bugun kofan gidan a gigice Allah yasa banyi barci ba dama naji dirin motar shi yadawo.
Nafito da sauri na bude gidan sai yafado ciki da sauri ya mayar da kofan ya rufe yana fadin wuce da sauri mu shiga please.
Ina fadin lafiya bai iya magana ba sai karkarawa