Showing 57001 words to 60000 words out of 115099 words

Chapter 20 - Bamu kadai ba ne book Complete by Zainab Makawa .txt

16 Dec 2024

6650

tana fita daga dakin sai naga alaman bata tafi ba tana daga bayan labule a tsaye nace dakin kawo min don yanzu zan wuce ni ina fadi ina kallon kofan inda karimay din take boye.
Sai ta wuce sadip sadip da ita kamar munafuka tace au dama bata tafi bane ashe nace ina zata tafi ta tsaya taji damay nazo maki ne .
Na juya inda hajiyan take zaune nace mama da zan baki shawara kiji da sai nace daga yau kada ki kara hawa saman kujeran nan dakike akai.
Don kujeran yasha bakin sihiri don zaune kike a cikin wani irin bakin hayaki mai muni.
Subbahanallahi tace da sauri tana kokarin mikewa sai naga ta kasa mikewa ta koma ta zauna.
Haka yasa na fahinci bata da lakkan da zata iya mikewa ne a lokacin.
Da sauri na karasa gurin ta na kamata zuwa saman wani dan timtim dake gefe nace ki zauna anan mama don shine kawai baida sihiri ajikin shi.
Tace ikon Allah ashe zaune nake a cikin mugun abu ban sani ba ni.
Kafin karimay ta shigo falon nai mata bayanin duk sakon da baba malam yabani.
Tare da fada mata zancen yan aikin ta da yace ta canza su ta sake gaba dayan su kada tabar kowa agidan.
Ashe karimay nacen tana sauri ta dawo ta dauko tiren data sa drinks aciki kamar an barar da kayan daga hannun ta suka zube dole takoma hada wani again.
Namike ina fadin ni zan tafi mama Allah ya sauwaka yasa iyakan wahalan ke nan.
Tace dakata maryam zaki tafi ban sanki ban san kuma idan kin tafi a ina zan ganki ba again.
Don haka ki bani nomban wayan ki zan kiraki insha Allahu don karin bayani.
Nabata nomban wayana ta saka a wayan ta ina batun fita sai ga karimay tashigo da kayan dauke a hannun ta.
Nan hajiyan tace sai nasha wani abu daga ciki dole na tsaya na dauki cup ina tsiyaya ruwan lemon sai dai abinda nagani yasa nabi cup din da kallon mamaki.
Na mayar gefe daya a cikin tire din na aje kallon gurin da karima take tsaye hajiya tayi tace ki bamu guri ina magana da diyata ce karimay.
Sukusuku tafita daga falon tabar mu mukadai daga hajiya sai ni.
Hajiyan tace ki sha mana diya ta na kalli cup din nai murmushi nace mama kiyi hakkuri bazan iya shan wanan abin ba gaskiya don da abu acikin sa kema kiyi hankali da da duk wani abinda zaifito daga hannun mutanen gidan nan don komai da suke baki ko bakin ki da sihiri a cikin sa.
Wanda an riga an maku shi sai a sannu komai zai daidaita maku nan bada jimawa idan har kina amfani da abinda na kawo maki.
Nace ni zan tafi sai wata rana kuma idan da rabon mu kara ganawa a tsakanin mu.
Kudi ta dauko tabani wanda ni kaina ban san iyakan su ba.
Na girgiza kaina ina cewa haba mama sako ne kawai na kawo maki banazo ne don na karbi koda kwandalla daga gare ki ba.
Har nakai kofa sai najuyo na dawo zuwa inda take a zaune nace mata kamar mai rada kada ki yarda da kowa idan ba diyan ki ba don duk an saye su suna cutar dake ne kawai a gidan nan.
Nace sai anjima nafice abina daga cikin gidan zan fitane naga wanan mutumin da karnuka sukaiwa ta, asa nace ikon Allah.
Yaya akai haka ni basu yagani ba gashi kai sun yaga ka a lokaci daya Allah ya tsare gaba nafice abina na barsu nan suna bina da kallon mamaki.
Mutumin yake fada masu yadda mukayi dashi da yadda yaga karnuka akan shi.
Mamaki ne ya kamasu nan karima ta daga waya takira wani lanban waya tana fadin hello hajiya wallahi yau da matsala a gidan nan..
Da wani irin karfi matar da takira da hajiya tace matsala matsalan may karimay.
Tace lalai hajiya tayi bakuwar wata yarinya danaji tana kiran ta da yar uwarta kuma yarinyae kamar dai ba ita kadai bace.
Don ina gani har wanan abinda muka zuba saman kujerun falin hajiya sai da tagani don naga ta tayar da ita daga gurin zuwa wani wajen.
Na bata abin sha taki tasha don nagane wani abu akan ta amma sam taki koda kurbawa ma balle tasha.
Daga ina wanan bakuwar take abinciko min ita nasan ko wacece kada tazo ta bata muna tsarin mu muna ganin mun kusa cin ma nasara ga aikin mu kuma zata jawo muna matsala ta mayar damu baya ga aukin mu.
Da sauri karimay ta bar falon takira daya daga cikin mutanen ta ta umurce shi dayabi bayana yaga inda na nufa.
Sai dai yana fita bani ba dalilina na bace mai dagani nikan ina fita na samu mota ya sauke wasu mata nashige nabar unguwar.

****** ********* ******
Malali na nufa gidan hajiya Umma gidan shima ya hadu sosai kamar na farko don zan iya cewa yama fi na farkon gurin haduwa.
Ban samu matsala sosai ba gurin shiga gidan don maigadin dana samu baida tsauri sosai kamar na aancan gidan.
Yai min iso gurin hajiya Umma akace nashigo nashiga ina ta baza idanuwana gurin kallo.
A raina nace ikon Allah baba ya hadani da irin manyan gidajen nan da sukafi karfina haka Allah dai ya ceceni daga kaidin irin manyan gidajen nan.
Ina fadin gurin hajiya Umma nazo akai min iso gurin ta tana zaune saye da lafaya data lailaye jikin ta dashi.
Dattijuwa ce sai dai da ganin ta ansha ilimi da duniya kudi kuma ba,a magana akan su.
Nan dai muka gaisa da ita ta dago idon ta dake saye cikin farin glass tace boyar Allah ban sheda ki ba fa.
Nace baki sanni ba mama baba malam ne ya aiko ni zuwa gare ke da wanan sakon ina kokarin ciro sakon daga cikin hand bag dina.
Tace banko gane baba malam din nan ba dakikace nace mata yace in fada maki mutumin da kuka hadu ranan jumma, a a saudiya matar shi tana share mai zufa kina kallon su har wanan kyalen naki yafadi a kasa.
Tace ukon Allah an koyi haka wallahi amma sai dai mutanen da nagani ba black bane su ina ganin kamar larabawane su.
Nidai murmushi nai mata ban tsaya dogon bayani ba nafitar da sakon ta na bata tare da mata bayanin komai.
Sai kallon mamaki kawai take min an kawo min abin motsa baki amma ban taba komai ba daga ciki.
Sai kallon mamaki take min tace kinga ciwon kafan nan tun ina a senet comphress watarana naji kamar na taka wani abu tun lokacin nake fama dashi nayi magani har nagaji nabarwa Allah al, amarin sa.
Yanzu idan nace zan shiga dakin nan da kike gani aiki ne babba a gare ni don ban iya taka kafan nawa da kyau sai naji shi har a cikin raina
Na mike ina fadin gajiya ni zan koma tace tsaya na baki na mota ko nace a, a sako ne akabani na kawo maki kuma nakawo bazan karbi ko kwandalanki ba hajiya.
Tace ikon Allah amma da kin karba ainice nabaki nace nagode mama Allah ki barshi kawai sakon dama ana son yazo gare kine kuma Allah ya nufa yazo.
Nace sai dai kuma yace na fada maki zancen danki dake damun ki ki daina damuwa da hakan nan da sati uku mai zuwa insha Allahu zai dawo gida.
Amma idan yadawo kada kice zaki mai fada ko magana akan rashin dawowan shi akasi aka samu ga hakan.
Har na fara takawa ina fadin sai anjima tace dakata yarinyar naja na tsaya guri daya.
Tace al, amarinki ya matukar daure min kai don dai ni na kasa fahintar komai akai.
Nace hajiya kada ki damu idan har kin yarda da Allah to ki jaraba wanan maganin ki gani.
Nace nabarki lafiya ni zan tafi tace dakata ki bani nomban ki pleaae ?
Nabata nombar a gurguje na bar gidan ban tsaya ko ina ba sai gida nadawo agajiye dani.
Kamar anbani kashi nakeji ga kaina yana wani irin sara min duk ban jin dadi a jikina haka na samu guri na kwanta sai barci mai nauyi yai gaba dani.
Har dare haka nake kwance ba lakka ajikina sai faman kasala dake damuna kawai haka na daure natashi na ba Umma maganin ta.
Tare da shafa mata nakoma na kwanta don gaba daya ban ganewa jikina ba a ranan zakace nai wani aikine.
Sai daga baya abubuwan da suka faru suke dawo min tiryan tirya nake gani kamar a mafalki akayi su.
Yadda ma akayi na shiga irin wanan gidajen haka nake tunane a raina






ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
[11/9, 11:20 PM] Zuraiyah Zuzu ๐ŸŒŸ: ๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ฆ ๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ฆ


BA MU KADAI BANE A, , , ,


๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ง ๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ง


1โƒฃ9โƒฃ




Wshegari nagama duk wani abinda zanyi da wuri don zuwa asibiti da zamuyi zuwa kai Umma a duba ta.
Shi ya kaimu asibitin ya sauke mu bai tafi ba sai da ya yankar muna kati muka bi layi don mun samu mutane da dan yawa a gaban mu.
Mun dan dauki lokaci mai tsawo kafin layin yazo a kan mu aka kiramu muka shiga gurin likitan.
Bayan yan dube dube da tambayoyi da akai muna muka gaya mai komai da yadda takeji.
Daga karshe yake cewa ba komai ke damun ta ba sai hawan jini daya saka ta a gaba.
Nan ya rubuta muna magani naje na sayo maganin nakama Umma muka nufi gida da ita.
Baban Abba bai shigo ba sai goma na dare da yan mintina yashigo gidan agajiye dashi.
Sannu da zuwa nai mashi ya nufi gurin da Umma take zaune cikin rashin jin dadi ga yanayin ta yana mata sannu da jiki.
Maganin da aka bamu yake dubawa a hankali ya dago gurin da nake yana cewa hawan jini ke nan yake damunta ashe ?
Nace eh haka sukace wai shine yai mata illa haka har ya mayar da ita hakan nan.
Allah ta sauwaka yace yamike yanufi ciki abincin shi na dauko na shirya mai a falo don ya shiga wanka a lokacin.
Yafito ya samu guri ya zauna yaci abincin shi ya koshi ba tare da ya tambayi inda na samo kudin cefane ba.
Nan kuma ya juya yana cewa yaran yau may akai masu a makaranta nan suka shiga bashi labari yana biye masu wanda nasan ba komai bane kamay kamay ne kawai yakeyi don kunya.
Ace mutum mahaifiyar shi bata da lafiya haka amma taki tsayawa ya mayar da hankalin shi akai.
Ya koma kamar wani susutace dashi kan karuwa yar duniya da ta shige mai gaba da komai.
Ni yanzu ban faye damuwa da al, amarin shi ba don al, amarin yarana da na majaifiyar shi da nake jinya yafi damuna a raina.
Don nashi al, amarin ya fita min akai ko don yanzu na riga na saba da halinshi na rashin kulawan shi a kan mu.
Mikewa nayi na shiga dakin da Umma da yara ke kwana nadan kara gyarawa tare da fesa masu sheltox don sauro da kwarin dake acikin dakin.
Gurin Umma na dawo inda take dakyat na kamata da taratara nakaita dakin na kwantar da ita na kashe wutan dakin nadawo falo gurin su na zauna.
Ina zama yake ce min kin fara bata maganin ke nan ko ?
Nace eh tafara sha tunda muka dawo dayan ne wanda bamu samu ba kawai ban bata ba gama takardan nan.
Ok kawai yace mun tare sa kawar da kan shi gareni yaci gaba da kallin wayan shi da yake charting.
Karfin hali nayi nace ga takardan ko zaka sayo muna gobe idan kafita ko ?
Bai dago ya dubi gurin da nake ba yace aje shi gurin yanzun dare yayi sai da safe a sayo.
Tun wanan lokacin bai kara bi takan takardan ba don da safe nan naga ya fita ya barshi a gurin dana aje mai.
Na fahinci cewa yanzu Umma ta kara langabewa fiye da baya ma don abin kara tabarbarewa yayi mata data fara shan na asibitin da muke mata.
Don gaba daya bata lakka ko kuzari kamar baya da muke ganin sauki yana shigan ta a hankali.
Yakai yanzun bata iya ma tasgin danake taimaka mata tana dan yi abaya.
Hakan ya tayar min da hankali ga dan ta kona fada mai ba wani abu yake akaiba sai dai yace na bata magani tasha shine yake mata aiki.
Ashe mu abinda bamu sani ba magani daban ciwo daban mukeyi don ba a hada aikin jinnu da maganin asibiti ga maganin yafi karfin jinin ta shine ke sa ta kara jin jikin da takeyi yanzu saboda ba hawan jini ne gareta ba.
Nan dai hankalina yafara tashi akan al, amarin gashi danta ba ruwan shi da mayar da hankalinta gare ta.
Idan ya fita tun safe sai dare sosai yake shigowa gidan zai samu tana barci ko a kwance da safe sosai kuma zai bar gidan sai kuma dare.
Ranan da naga abin ya matsa mata yasa na tasa ta agaba ina hawaye gashi nice sillar zuwa da ita garin mutane kada wani abu yazo ya samayta a kuka dani dana kawo ta.
Nace a raina da zan ga baba malam da sai na fada mai halin da take ciki ko akwai abinda zai taimaka mata dashi na lafiyan ta.
Ina nan dai zaune inata faman sake sake a cikin raina da ga karshe dai na yanke shawara a rai na na gwada sa, at ko zan samu zuwa birnin dausayin tsibiri ko zanga malam din.
Hakana kwana da zancen zuwa dausayin tsibiri washe gari ko Allah zai sa na samu motar da zai kaini can.
Tunda safe bayan tafiyan yara makaranta nima nagama kimtsa Umma tare da bata abinci da magani na gyara ta yadda ya dace nazo gaban ta nace.
Umma zan tafi gurin wani mai magani mu gwada mu gani ko Allah zai sa mu dace amma ba dadewa zanyi ba sai nadawo.
Na dauki Nusaiba wace yanzu yarinyar tana iya zuwa ko ina da kafan ta don ta yi wayo sosai yanzu.
Na kulle gidan daga baya da ita aciki na kama hanya zuwa inda zan hau taxi zuwa kofan asibiti.
Masu motar haya suna tsayawa tambayan ina zan tafi idan nace dausayin tsibiri sai naga sun min wani kallon mahaukaciya don babu sunan garin a duk nahiyar kaduna.
Ga rana na kudar mu ni da yarinyata da muka dauki lokaci tsaye a cikin ranan kusan awa biyu da rabi ba mota garin babu dalilin ta har lokacin.
Na yanke shawaran nakoma gida kawai don nasan ba samu ma zanyi ba.
Nace Nusaibs zo mu tafi gida kinji kada raban yai muna illa hakana gashi ma rana yasoma yi sha biyu da yan mintina yanzu.
Na duka zan dauki yarinyar karaf kunnuwa na taji wani condester bus yana fadin Birnin tsibiri fa mai zuwa.
Nai saurin tare motar na fada kawai duk da rana yai muna ga tafiyan a lokacin.
Mutanen dana samu acikin motar sai kallon mamaki suke min ga tsikan jikina naji yawani tashi min a lokaci daya.
Allah bai bani ikon yin addua ba a lokacin sai dafe kaina danayi kawai da rike yar diyata dake zaune a jikina.
Muryan condester din nakara ji yana fadin masu sauka dausayin tsibiri su sauka mun kawo.
Nai farat na mike na dauki diyata naba mai motar kudi na fita abina daga motar suka kwasa da wani gudun balai sukai gaba abinsu.
Nagyara muka kama hanyan zuwa uguwar da zan nufa na yanke shawaran biya wanan gidan da nake shiga da farko idan na tafi.
Sai dai yau na samu gidan kamar suna buki don naga mata sosai acikin gidan.
Nashiga da sallamata idanuwan matan dana samu duk akaina yake gaba dayan su.
Ina gaida matan ina raba ido ko zanga daya daga cikin matan gidan dan sani tafito a lokacin.
Ke mari ga wata bil, adam fa tashigo gidan ku ko kun san da sanin zuwan ta nan ne.
Matar da akakira da Mari tafito tana fadin bil, adam kuma a gidan nan yau wacece kuma ?
Abinda nagani ne yasa naji wani faduwan gaba tare da sarawan kai ya kamani ban san lokacin dana dukar da idanuwana ba akan mari din.
A, a maman Nusaiba yau kece a gidan namu lalemarhabi da dake jin muryan wace na sani yasana bude idon tare da dago kaina dake a duke yana sara min kamar zai cire nace nice anty.
Murmushi dauke a fuskanta ta karaso inda nake tsaye tana cewa ai nazaci bazamu kara ganin ki ba ne yar uwa.
Tace sai dai gaki kinzo gidan kin samu yau

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login