Showing 45001 words to 48000 words out of 115099 words
Chapter 16 - Bamu kadai ba ne book Complete by Zainab Makawa .txt
kwance yashe yana tambayan ta may ya samay ta haka ?
Bata iya bude baki tayi magana sai nuna gurin bango takeyi inda taga wanan abin da ya bata tsoro a daren jiya.
Da kyat suka iya shiryawa suka fice a gidan a tsorace kowa da abinda yake nasawa a zuciyar shi ba mai ma dan uwa magana cikin su.
Da kyat suka samu suka isa gidan Hanna din kowa hankali a tashe a cikin su.
Suna shiga Hanna ta barke da wani irin kuka tana fadin dear ashe kasan gidan ka baida kyau kakaini don akashe ni ko?
Cikin hasala shima yace gidana baida kyau koke baki da kyau tunda nake da iyalina ban taba jin komai ba agidan sai yau da kikaje min gida da naki masifan.
Tace au haka ma zakace min dear duk da mutuwan da na tashi yi a gidan ka wani dodo ne fa nagani ban ko son na tuna kaman shi wallahi.
Yace shoutup my dear don baki san ko ni may akai min ba akanki har zaki fada min haka ko yanzun haka idona ban ko gani sosai dashi don zafin marin da akai min.
Dariya ya bata ta manta ma da abinda ke gabanta wai akan dan marin da akai mai zaice bai ganin guri da kyau.
Itako da aikawa dan karsn dukan tsiya babu maceci tace may gawani mugun halitta da ya baiyana mata.
Tace ba zan saks koda gigin zuwa gidan ka ba indai nice dama nace ma matarka ibilis ce gashi daga zancen mahaifinta ya mutu nawa uban ya mutu ba ciwon komai tare dashi.
Yace will you stop dis rubish please duk kece gurin shegen shige shigen ki kika kwaso wa mutane wanan jidalin haka.
Nan fada ya barke a tsakanin su ba karamin tashin hakali sukayi ba a ranan suka rabu baram baram a tsakanin su.
Yafita daga gidan nata ranshi a bace gashi yana son komawa gida ko wanka yayi amma tsoron gidan nashi yake ji yau da kanshi.
Office din su ya nufa hakana wijiga wijiga dashi babu shiri kowa ya gan shi sai kallon mamaki yake mashi yadda ya fito haka yau office babu shiri.
Har yama abin duniya ya damay shi haka ya daure ya nufi gidan nashi a tsorace ko wanka ya dan samu yayi yaji dadin jikin shi gashi kuma bazai iya fadawa kowa abinda ya faru dashi da karuwan shi ba a gidan shi.
Yana bude kofa ya shiga yaga komai tsab a gidan kamar babu abinda yafaru ba yadda ya barshi a hargitse ba a baya ba kafin su fita.
Wayan shi ce tai kara yasa ya dan firgita ya jada baya ya ciro wayan noba tace yagani ya sauke ajiyan zuciya.
Muka gaisa nai mashi yaya aiki ya amsa da kyat da Alhamdullahi ya tambayi jikin baba nace baba jiki Alhamdullahi ya samu sauki sosai yanzu.
Har muka gama wayan naji shi ba yadda na saba jinshi ba kamar yana cikin wani irin damuwa yanayin shi.
Na raya a raina kila baida lafiya ne ko kuma wani abinne ya samay shi kila.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
[11/4, 10:17 PM] Zuraiyah Zuzu π: π©βπ©βπ§βπ§ π©βπ©βπ§βπ§
BAMU KADAI BA NE, , ,
π¨βπ©βπ§βπ¦ π¨βπ©βπ§βπ¦
1β£6β£
ASSALAMU ALAIKUM YAN UWA DA ABOKAN ARZIKI DAKE BUGO MIN WAYA SUNA NEMAN BAYANI YADDA ZASUYI REGISTER A SABON NOVEL DIN DA ZAN FARA KWANAN NAN.
GA YADDA BAYANIN YAKE IDAN TA ACCOUNT ZAKI TURA MIN KUDIN REGISTER 300 ZAKI TURA MIN GA WANAN NOMBER DIN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK IDAN KUMA RECHARGE CARD ZAKI TURO NA 400 ZAKI TURO TA LAYINA NAGODE DA FATAN ZAKU FAHINCE NI MASOYANA MASU KAUNAN CIGABANA SAI NAJI KU NAGODE KWARAI DA HALARCIN DA KUKE GWADA MIN, , , ,
Tun tafiyan Aliyu daga gidan ta ta kwata jikin ta ba dadi sai ciwo yake mata ga wani zazzabi da ya rufe ta a lokaci daya.
Da kyat kawar ta ta samu ta mike tai wanka ta kaita asibiti don a duba lafiyan ta.
Har sai da Hanna, tai kwana biyu tana jinyar jikin ta ta samu sauki.
Ga wayan Aliyu kota kira baya daukan wayan nata don ya dauki zafi sosai da ita.
Sai dai kuma yana yawan mamaki sosai a cikin rashi na yaya akayi haka ya kasance a gidan shi gidan da yake zaune tare da iyalin shi amma su Allah ya kare mashi su daga duk wani mugun abu.
A bayane ma farko Maryam ke yawan mai korafin baban Abba BAMU KADAI BANE A GIDAN NAN FA,
Amma sai ya katse ta da sababi yana ganin wani sabon rigima ne kawai maryam take son dauko mashi ta aza mai yana zaman zaman shi.
Haka yara suka dinga ciwo baji ba gani kamar ransu zai fita amma da tai magana yace ai don gurin sabon guri ne a gare su ya jawo hakan masu.
Yanzu ma dai boyar Allah nan ya dai na jin ma tana mashi wani korafi akan gida lafiya lau take gudanar da komai nata a gidan.
Gashi dan tafiyan su da yan kwanaki ya fahinci gidan nan da akwai abinda bai sani ba a cikin sa.
Don ranan yai kokarin ganin ya kwana gidan amma abin ya gagare shi don tun da zai dawo gida ne misalin goma na dare da yake uguwar ana saurin shigewa gida gashi kuma lokacin sanyi ne take garin na kaduna yai tsit kowa ya boye don sanyi.
Yana tafe yaga kamar abu ya gitta mai ta gaban shi yafito daga gidan su yar sokoto ya nufi bayan katangar gidan su ya kashe abin da hasken mota yaga ashe kyanwace bakakirin da ita sai idon ta da ke wani walkiya a cikin haske ba dadin gani sosai.
Shiru yayi zaune a cikin motan yana nazari a ran shi na yadda zai fita ya duba ko may yagani a gurin ya gilma mashi.
Ganin babu sarki sai Allah yasa ya daure yafito daga motan tafiya yakeyi zuwa step din da zai hau dashi barandan gidan shi amma sai yake ji ida ya taka daya kaman ana takawa biyu bayan shi gashi ya saka key ya bude gidan kofan gidan yaki saurin budewa a lokaci daya can sai ga wata mujiya mai rararan murya ta rangada kukan irin nasu jin kukan yayi har cikin tsakiyan kan shi lokaci daya yana fadin lah, ilaha ilah anta subbahanaka inni kuntu minal zallumin .
Ya samu kofan ya bude mai da kyat ta fada gidan hankalin shi a tashe dashi yana hakki sama sama cikin tsoro.
Yana zuwa ya bude frisge ya fara kwankwadan ruwan goran da ya jera acikin fridge din don zuwan Hanna gidan ranan.
Basu yi amfani da komai da yasayo ba komai yana nan yadda ya barshi aje.
Ganin ya samu ya shiga gidane ya samu guri ya zauna yana mayar da numfshi a hankali.
Motsi sosai yake ji daga bayan back yard din gidan adduoi ne ya fara jerowa yanayiwa kan shi haka yasa shi dan samun sauki ga abinda yake ji.
Sannu a hankali ya daina jin motsin yana kan addua har yaji zuciyar shi ya dan samu natsuwa, a rayuwan shi.
Nan dai yai alwala yai sallah ya kwanta a tsorace ga bakin kiran layin shi da Hanna take ta yi mai amma halin da yake ciki yaki bari ya daga wayan shi.
Can kuma hana sai ganin laifin shi rakeyi tana faman fada ni Aliyu zaiwa haka yana nufin zai watsa min kasa a ido ne ko may wallahi bai isa yace zai rabu dani ba a rayuwan shi sai nayi abinda na raba shi da wanan diyar malamai din da yake aure.
Bayan ta samu sauki ta shirya da wata kawar ta da zata kaita wani kauye don ai mata aiki wanda zata samu kan Aliyu sosai sosai don sun yaba da aikin mutumin sosai a ran su.
Suna zaune a cikin motar dayar kawar tace ta fara magana tace ai ni nai arziki ranan da nake dawowa daga gurin ki da nai dare baki ga abinda nagani bane wallahi.
Sai Hanna take cewa kikai arziki ko ni nai arziki ni da gidan Aliyu aka tashi kashe baki ga irin abinda nagani bane wallahi sai driver Napep din dake tukin mota ta gaba yace mai kikagani haka har ya tsorata ki yar uwa tace bari kaidai ban san ma yadda zan maka bayani ba kai dai bari kawai sai sukaji yace may kika gani ne wai hajiya.
Tace kai dai kawai bari na sha wuya wallahi ai dai nayi arziki dana samu kaina sai mai tukin motar ya juyo inda suke tare da fito da siffan shi a fili tare dacewa, Like disπΉ ?
Gaba daya suka daga suna kallon shi ya bude baki hakkoranshi kamar kacan mashin fuskan shi kamar na wani halitta can take suka rude suka shiga tsala ihu.
Sun dai bude ido sunga taron mutane a kansu ana tambayan ina suka fito don ba, a san su ba.
A rude suke magana suna cewa a tare masu mota su hau zuwa gida sai a hankali suke kallon yanayin mutanen gurin ba irin yanayin mutanen kaduna bane da sauri kawar take tambayan inane suke nan wai aka ce masu suna kwatarkwashi ne yanzu haka.
Gaban su yai mumunan faduwa suka rude gankalin su yai matukar tashi sosai dajin inda suke.
Ga wani karon dute suna gani maigirma da ba iyaka a gefen su sai suka kara rudewa.
Gurin maigarin aka kaisu sukai mai bayanin su daga kaduna suke sun shiga taxi ne zuwa wani unguwa shine suka gansu anan din.
****** ********* ******
Sosai na cinikin kayan da nazo gida dasu na sayarwa wanda haka ya tayar da hankalin Umma dake ganin yadda mata suke shige da fice a gurina
Don sayen kayan kowa yana yaba kyawon su ga atamfan danakawo guda hamain ansaye kudi hannu an bani kudina don ban cika masu kudi ba har ana nema a kara guda talatin da dan kai.
A cikin kayana naga wasu kunshin leda guda biyu wanda ban san dasu ba na bude don na duba sai na duba naga ashe atamfane guda biyu aciki masu masifan kyau dasu sai dayan ledan mai turare dan saudiya da dadumar sallah mai tsada acikin sa.
Take na tuna zancen tsaraban da akace zan gani a kayana naba anty na Lami da babana nasu ne nagane kan sakon don haka na aje idan zan tafi nakai masu abinsu.
Nan Umma ta shiga saka magana tana cewa yanzun kan ta sheda ita no kudin dan ta yake shiga watau nice nakarbe mai komai nashi nake juyawa don na fishi.
Har yakai ta kira dan nata cikin fushi take fada mai bakaken magana duk yadda yaso ya fahintar da ita bata yarda da zancen shi ba.
Yace wallahi wallahi umma babu ko kwandalana a cikin kudin da maryam take sana, anta dashi asalima ni ban san ida ta samu kudin ta ba ta dai ce min makwabciyar muce ta bata aron kudi take juyawa.
Maganan shi bai sa Umma ta yarda dashi ba saima ta kashe wayan ta a karshe kawai.
Na shirya ni da yara zuwa gidan mu wuni don tunda mu kazo ban samu zuwa mu wuni ba saboda gyaran gidan da nakeyi .
Na samu mahaifina zaune a dakin shi bayan na gaisa da matan babana muka dan taba hira dasu na dauki ledan sakon shi zuwa dakin shi.
Nan muka gaisa dashi yana dan wasa da yarana yake cewa mutanen kaduna kuna can abinku kun boye ko?
Ya juyo gare ni yana cewa yaya shi maigidan naki kuma nace yana lafiya baba.
Ledan sakon kayan shi na mika mai cikin ladabi nace baba gashi akace idan nazo na baka.
Da mamaki yake kallon ledan yake cewa ikon Allah dagawa ke nan wanan sakon haka.
Na gyara zama nace wallahi baba wata boyar Allah ce Allah ya hada ni da ita ban santa ba batasan ni ba.
Sai dai haduwa da ita ya zama min babban alheri ga rayuwana yanzu.
Baba yace dama haka duniya take idan Allah ya tashi ikon shi ga bawa babu mai hanawa .
Yanzu kinga wanan ciwon danayi gashi mutumin da ban sani ba ya baki magani kin kawo min wanda shine makarun ciwon nawa.
Nace yyawa baba raban wani mutum da ya daukeni da mashin nan kofan gida yai min wani magana akan ka.
Yace na fada maka wai ka daina fitan dare misalin biyu zuwa uku na dare ka dan sahirta don lokaci ne na wasu daban ba namu ba.
Ido baba ya tsura min yace maryama waya fada maki haka din ?
Nace wani mutum ne mai mashin daya daukeni yai min wanan magana ni kuma gaskiya ban san shi ba a garin nan.
Na kuma bashi kudin mashin yace wai na barshi saboda Allah ya sauke ni ya wuce abin shi.
Maryama anya ba abubuwan uwarki bane kuwa suke bibiyan rayuwan ki ina tsoron kada ki gado Amina fa tun tuni don al,amarinki da siffan ki duk irin daya ne dana mahaifiyar ki.
Nace baba idan zasu cuta min yadda suka cuta mata da bazan yafe masu ba gaskiya don irin yadda mama ta wahala kafin ta rasu ban taba mantawa da hakan a rayuwana.
Yace Allah dai ya kyauta don kinga wanan magana da kika fada min yanzu ba wani mahalukin daya san shi sai ni da abin ya faru akaina.
Ban kuma taba fadawa kowa shi ba balle nace ko maishi yaji ne a wani guri.
Shigowan su anty Lami da yayan mu habbi bai hana baba fadan abinda yai niyar fadi ba.
Yace na tashi wani dare don nai tsarki nayi alwala sai naga wata yarinya tsugune a tsakar gidan nan tana kuka.
Nai mamakin yadda ga gida a rufe har tashigo gidan nan na haska mata toci ina fadin wanene a guein nan ?
Bata daina kuka ba har na karaso inda take tsugune nace ke daga ina kike ne sai take ce min daga gidan malam mudi take ni dai a iya sani na garin nan ban san waye malam mudi ba.
Nace may yakawo ki gidan nan kuma cikin kuka yarinyar ke fada min cewa tayi dare ne shine ta samu an rufe mata gida.
Nace ke ko boyar Allah ina kika tsaya har dare yai maki baki koma gida ba nan dai nai mata fada kan ta kula da rayuwan ta daga karshe na saka ta gaba don nakaita gidan su.
Ga mamakina a unguwar nan dai babu gidan sama amma sai naga ta runkari wani bene dani tace nan ne gidan nasu wanda sai an hau za, a samu kofan shi.
Haka na daure muka hau sama da ita na buga kofan kusan sau uku aka bude kofan gidan.
Mutumin da nagani ban san shi ba a garin nan nai mashi sallama tare da bashi hakkuri ta karbi yar shi ya daina fushi da yara wani kallo mutumin yake min kamar na tsana ban damu ba nidai hakkuri na bashi na juya don in sauko daga benen.
Sai baba yai shiru tare da girgiza kan shi tace ashe ban sani ba gamo nayi don maimakon naga gidan sama sai kawai nagani a saman katon iccen kukan nan dake kofan gidan Tanko.
Yaushe rabona da hawa icce koda karami ne balle irin wanan katon iccen haka.
Da dabara da addua na sauko daga iccen lokacin har an fara kiran sallah asuba.
Tun dana dawo gida zazzabi mai zafi ya rufe ni tun shine wanan ciwon haka ya sarke ni wanda ba, a san makarin shi ba sai da kika kawo min wanan maganin da mutumin nan ya bayar ki kawo min.
Kinga ke nan akwai ayan tambaya ga bayanin da mutumin nan yai maki ranan ke nan ba mutum bane ta dauke ki kema a mashin din.
Tsoro ya ziyar ce ni sosai da yake akwai yan uwa na a dakin sai ban fadawa babana halin da nake ciki ba a kaduna.
Yanzu baba dama ciwon ka shafan jinnu ne gaka ashe shiyasa anata magani kamar ba, ayi ciwo sai gaba takeyi kawai.
Baba Yace badon wanan maganan da maryama tazo min dashi ba yanzu da ban fadi wanan labarin ba har wani yaji don idan na fada gurin zai koma yana ba mutane tsorone.
Mun dan dauki lokaci muna magana kan zancen ida baba ke kara fada muna abubuwan da zamu kiyayye kan jinnu kamar fita misalin sha biyun rana zuwa daya na rana haka kuma zubar da shara a wanan lokaci ko yin girki da rana tsaka da mata keyi da kuma lokacin da almuru yayi koda dakin ka zaka shiga ka dinga sallama a wa yan nan lokacin.
Yace ai kinga kamar mahaifiyar ki da rana tsakane an aike ta tun tana karama suka shige ta.
Shine dayake muggaine nata