Showing 9001 words to 12000 words out of 115099 words
Chapter 4 - Bamu kadai ba ne book Complete by Zainab Makawa .txt
gidan sarki barni da sunan da Allah ya rada min da kowa yasan ni da Igena.
Idan kayi niyya tafiya da su ka kwashi iyalinka ku tafi kada kuma kasa a kasa ni ga faifan gari ana zagi.
Yace umma kiyi hakkuri don Alkah idan ranki ya,baci ne amma ni banyi karan ki fa kowa ba,wallahi.
To ni dai yanzu kaji abinda na fada maka ai ka,kwashi iyakinka ka tafi da abinka idan ka tashi .
Shiru tayi can ya,nisa yace naji umma amma ba yanzu ba sai in sun shirya wani zuwa idan nadawo sai na tafi dasu.
Ya fito ina shanya kanyan fitsarin Nusai ba yake cewa sai fushi ya kare tunda Umma ta jaye kudirinta kafin nadawo sai ku shirya ko ?
Haka ya yafi yabar mu wanan shigowa sam baiji dadi ba daga gurin Umma har ni din.
****** ********* ******
Sannu sannu na,dan fara,sakewa a hankali har takai dai na,sake din amma babu wani zance akan tafiyan namu da ita.
Ranan ina nan da yamma zauns ina tankaden gari naji sallama Lawisa ce diyar makwabtan mu ta dawo daga school.
Boarding school take sunyi huta dawowanta ke nan ta shigo gurin mu gaida mu makwabta ta gaida mu
Lawisa tayi kyau ta girma kamar ba ita ba ce uwar goyon yarana kafin ta tafi makaran ta nan muka gaisa da ita har gurin Umma tashi suka gaisa tafito tana tambayan mutanen tanake cewa sun tafi islamiya dazun mun dan taba hira da ita tace zata tafi sauran gidaje su gausa.
Tana fita tashi gidan dayan makwabtan mu da zata fito ne sukayi kicibis da Laure, ta dawo daga nika,
Yarinyar ta tare da wasan jika da kaka da suka saba yi da ita a don dangin uwar lawisa ce sosai suke da zumunta da ita.
Bayan ta Laure ta dan kai mata duka tana fadin jaira yaushe kika dawo halan ?
Take yarinyar taji kamar an sara mata guduma akan tane kanta yai wani irin uban sarawa,a lokaci daya.
Da kyat Lawisa ta isa gida dafe da kanta sai ciwo yake mata nan da na zazzabi ya rufe yarinyar sai ta fara sambatu ai ranan yarinyar bata kwana ba duniya.
Da safe labarin rasuwan Lawisa ya karade ko ina kowa da abinda yake fadi a kan mutuwar yarinyar da ta dawo jiya jiya cikin uniform din ta,shiga gaida mutane.
Sati biyu da rasuwan lawisa labari ya dan fara ya duwa wai wasu samari sunganta a,tsakar dare sun dawo yawon hiran su.
Tana tsugunne da uniform din ta a jiki tana kuka, sannu sannu labari ya fara bin gari idan kayo dare a uguwan mu koda bayan goma ne zaka iya haduwa da wanan yarinyar a tsugunne tana kuka cikun uniform din ta.
Duk gari labari yakai ko ina nan aka shiga kace nace kan zancen kkowa da abinda zai fadi ga zancen.
Nikan ma dai saboda tsoro a dakin Umma na tare nake kwana don ance kishiyar maman ta tafito fitsarin dare ta ganta tsakar gida tsugune ta sa hannayen ta a fuska tana rusa kuka .
Matar da taga lawisa sai da,akai kwana biyu ana burganta duk ta zauce ta zama kamar mahaukaciya sai fadin takeyi wallahi ashe ba karya bane na ganta tana fadin Laure Laure cikin kukan ta.
Aiko zance ya bazu laure ce ashe ta cinye Lawisa ke nan nan dai da,abu yai yawa akaje tambaya,shine ake fada masu manya ce mace tai mata farat daya ta kashe ta.
Bayani dai gashi nan babu dadi ko kadan akace wallahi sai dai aiwa laure ature tabarwa mutane uguwa amma ba,a zama da ita haka tanayiwa mutane ta,asa a gari.
Tun da farar safiya akai mata koran kare daga uguwan da dan kayan ta ta bar uguwan don kada a kashe ta.
Jifa mugu mai daukan rai shine wai kuma yake gudun mutuwa din wanzan baka so a jikin ka.
Duk gidan da ka,shiga zaka samu ankafa incen aduruku a tsakar gida da kofan gida wasu har a dakunan kwanan su su yayyabe shi da ganyen don tsaro kawai.
Muma Umma tashigo gidan da ganyen ta tayayaba shi ko ina a tsakar gidan.
Zuwan da akayi gurin mai magani ne na mayu aka samu ta har aka daina ganin Fatalwan Lawisa karamar yarinya yana fitowa.
Cikin wanan lokacin ne na tashin hankalin da muke ciki Aliyu ya iso garin.
****** ********* ******
Ya,samay mu a firgice da zancen abinda ya faru da yarinyar da yasani mai min rainon yarana idan na haihu ko yaushe muna like da juna idan aike ne ko girki duk itace mai min shi.
Umma kan da taga fitina a,fili sai cewa tayi kai ni wanan abin ya isheni haka garama ka dauki iyalinka kutafi nisa yafi min wanan fitinan.
Yau ace wanan gobe a ce wancan babu kwanciyan hakali a gari ko kadan .
Kaga kwanaki ma wani abune yake yawo gida gida ba dama mace ta zubar da kanzon tuwo a bayan gida ko makwarara sai abin mai kama da maciji da kan jaki ya tasa gidan gaba duk dare sai yazo neman abinci.
Umma tace dama mu an fada muna zuba abinci a makwarara yana kawo aljanne a gida ko macizai da wasu miyagun abu masu binda dare.
Amma kaga su yaran yanzu sun yarda wanan al,adan suna daukan shi wai canfine kuma wallahi ba canfi bane.
Gaskiyane duk gidan da ake irin wanan sakacin gidan nan bai rabuwa da ciwo da sauran saddabaru cikin shi.
Allah ya kyauta yace tare da yiwa yarinyar addua umma tace gashi ance mutuwan mayu wuyan sha,ani gare shi.
Ko kwanaki anan kauyen garin ake labarin yarinya ta mutu budurwa bayan wata biyar sai ga labari wai wani mahalbi ya tsunce ta a dajin zamfara ashe ba mutuwan Allah da Annabi tayi ba.
Yace umma ai ban manta ba mutumin da ya mutu wani lokacibai irin hakane ya faru dashi mana.
Nan gida ana cewa ya mutu sai ga,wani bayerabe zai dawo saman mashin din shi ya ganshi yana sauri ya tsaya su gaisa yake ce mashi sauri yakeyi baban shi ya aike shi ne.
Amma idan yaje gida ya fadawa matar shi ta duba kasan gadon su akwai kudi idan ta haihu asai ragon suna dashi.
Mutumin yana iso gari yaga antaru kofan gidan su wanda ya mutu din yake tambaya akace mai ai wanine ya mutu shinema yanzun aka dawo, kai gawan shi yanzu.
Sai cewa yayi a,a wallahi badai wani ba kan wani da muka hadu dashi yanzu a hanya har yabani sako yace yana sauri ne baban shi ya aike shi,
Yace nace matar shi ta duba kasan gadon su akwai kudi nan a dauka asai ragon suna idan ta haihu.
Koda akaje aka duba akasamu kudin kamar yadda mutumin ya fadi nan aka gane cewa mahaufin nashine yakashe shi ta sihiri.
Ai har nan akazo dashi gidan sarki yasa aka kore shi gari .
Umma tace kwarai kuwa haka akayi wallahi aikai dai mutane yanzu sai addua wallahi don son duniya ya rufewa mutane ido sosai.
Shiri muke tayi na tafiyan mu don ba lokaci sosai duk da dama ni kan na,shirya abina a asirce da safe ana gobe zamu wuce ne na tafi gidan mu in yi masu sallama.
A zaure na samu mahaufina nake fada mashi gobe ne zamu tafi yai murmushi yace maryam uwar rigima sai da dai kika sa Ige ta yarda da zancen tafiyan nan ko?
Dan murmushi nayi na dukar da kaina kasa can naji yana neman sani abu a cikin kayan shi yana fadin.
Kin san yanzu duniya tayi nisa sosai bari na dan baku wani dan abu dake da yaran sai kuyi amfani dashi kafin ku bar garin nan ku tabbatar da kunyi shi yau din nan.
Rubutu ne yabamu da kuma wani ganyen magani yace mu yi wanka da hayaki dashi nan yabini da addua da fatan alheri.
Nashiga ciki na samu su Inna su ma nan suka dan bani nasu tsaraban tare da min nasiha.
Tun a gidan mu mukayi abinda baba yaba mu muyi da kuma muka dawo gida muka kara yi ni da yaran harda maigidan a cikin hikima shima na bashi yayi.
Duk wani dan abinda zamu bukata mun yaba da sai dai su kayan aiki ne yace kada nahe da komai duk a can zamu sayi wasu.
Yaiwa umma sayayya sosai duk wani abin bukata sai da ya aje mata kafin mu wuce da safe duk yan uwa na sunzo gidan akan idon su motar mu ya tashi sai a lokacin naji kuma rashi jin dadin tafiyan da zamuyi mubar gida da kowa namu.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
[10/27, 10:48 PM] Zuraiyah Zuzu ๐: ๐ฉโ๐ฉโ๐งโ๐ง ๐จโ๐ฉโ๐งโ๐ฆ
BA MU KADAI BANE,,,,
๐ฉโ๐ฉโ๐งโ๐ง ๐จโ๐ฉโ๐งโ๐ฆ
5โฃ
INA GODIYA GA IRIN KAUNA DA SOYAYYAN DA KUKE NUNA MIN A KULLUN MASOYA NA DA BAZAR KU NAKE RAWA ADDU,AN KU GARENI YANA MIN DADI ALLAH YASA MU CIKA DA KYAU DA IMANIN UBANGIJIN MU A ZUCIYAN MU,,,,
Tafiya mukayi sosai ban taba sanin ma ya iya mota haka ba sai da naga yadda yake sharara gudu damu a hanya saman titi.
A gaskiya ba abinda yafi dadi ga rayuwan ma,aurata kamar su kasance a tare a ko wani lokaci.
Zan iya cewa yauce rana ta farko a cikin tarihin rayuwan aure na da Aliyu da muka samu kebewa dagani sai shi a cikin ni shadi haka.
Don duk abinda yagani a hanya zai dan waiga inda nake ko gurin yaran yace na saya maku abukaza ne.
Wanda a gida ba dama ya sayo muna dan wani abin marmari umma ta kama mai fada ke nan wai yana son bata mu da kwadai.
Iyakar mu dashi kayan girki kawai idan ma baya gari mun shiga cin tuwo ke nan da miyan yauki ko na taushe shine, na dadi idan anyi.
Ga wani kulawa na musan man da yake nuna muna wanda bamu saba da hakan ba gare shi saboda ganin idon Umma .
Yanzun ne na fahinci Umma ashe ba karamin takurawa rayuwan mu ni da yaran mu tayi ba .
Duk da ban da wani matsala da ita a fili amma ashe a badili akwai kuntatawa a zaman mu kusa da ita.
Gashi ko wani gari muka kai ko kauye sai ya fada mana sunan garin da dan tarihin shi har muka isa kaduna misalin karfe biyar da rabi na yamma.
Sai bin garin muke da kallo garin ne wanda ganin shi ma yafi jin labarin shi sosai.
Haka mukai ta tafiya har muka zo wani unguwa mai jama,a cikin shi sosai a hankali yake shiga wani titi mai tsawo har muka sha kwanan wasu gidajen dake jere da yawa duk kusan zubin su daya.
A Gida kusan na karshe ya tsayar da mota yana fadin Alhamdullahi da,sauri na dan kalle shi tare da duban zubin gidan.
Gida ne mai kyau ginan zamani komai a tsare yake a hankali na dan runtse idanuwa na tare da fadin Alhamdullahi a raina wanda yafito cikin irin gidajen mu na kauye yau mune a cikin irin wanan gidan .
A gaskiya ba karamin arziki mukayi ba da umma ta amince da zuwan garin nan don komai abin birgewa ne gurin .
A hankali ya bude motan shi ne ya fara fitowa daga cikin motan yana cewa oya bisimillah ko ?
Nace Auzu bikalamatti llahi tamat min kulli shedanin rajim.
Na sauko a hankali daga cikin motan tare da fadin La ilaha illa antta subbahanaka inni kuntu minal zalumin.
Tau fa duk addua a ne haka maryam nace ba dole na nemi tsari ba ga Allah yaya da sabon gurin da zamu shiga.
Shi ya hau matakalan da akayi three step kafin a hau baran dan gidan ya nufi kofan yana budewa a hankali.
Muna bayan shi ina dauke da Nusaiba a hannuna muka shiga nace salamu Alaikum wa kikewa sallama kuma a gidan ko ance maki akwai mutane ne.
Nace baba yace ko dakin kane zaka shiga kai sallama tukun kafin ka shiga ciki.
Sai bin gidan nake da kallo gwanin ban sha,awa gida ne irin na ma,aikata akai tsarin shi daki biyu da falo ne sai kicin da bathroom sai ta baya a kwai kofa daga kicin inda zaka dan fita wani dan fili karami duka a cikin gidan.
Ya sa kujeru a falon a cikin dakin kuma dayan dakin da gado dayan babu gado a cikin shi sai katifa katuwa a kasa.
Falon akwai tv dan maudaidaici da fridge a cikin shi da labulaiya a ko wani windows din gidan.
Na lumshe idona cikin jin dadin ganin sabon gidan namu na nufi dayan kujaran na zauna tare da shimfide Nusaiba sama.
Dakin ya wuce direct bayan ya kunna muna fankan sama da wutan falo don yamma yayi a lokacin.
Can ya fito ya sauya kayan jikin shi muna zaune da yaran yace ,a,a zama kukayi a nan Abba kaga sabon gidan ku ko ?
Yau ka gudu kabar Umma ko ai bazaka ci masan safe ba nan dai babu masa kuma babu umma da ta saba baka masa duk safe kana ci.
Nai dariya daga inda nake zaune nace ai Abba ya iya butulci ko yai kuka zai rabu da Umma yau am a yai wani kemaymay dashi.
Baban shi yace nima fa naji mamaki yaron nan na dauka zai kuka da zamu wuce fa don ita wanan ya shafa kan Aisha yace ba tada damuwa taga baban ta.
Muna nan zaune naga ya fara shigo muna da kayan mu ciki mikewa nayi na tsaya daga kofa ina karba kayan ina shiga dashi ciki.
Har muka gama yashigo yana cewa wancan dakin dake da katifa dama cewa nayi sai ku zauna da yara a ciki kafin a gama gadon shi wanan kuma sai muyi sharing ni dake ko ?
Nace mun gode dariya na bashi don shi mutum ne mai son dariya idan yaso yace barin fita in samowa yaran nan abinda zasu ci kafin suyi barci.
Yana fita naji ta da motar ya barmu a gida sai ni da yara a hankali na bi gidan da kallo na mike daga inda nake zaune ina shiga ko ina ina dubawa a hankali.
Gidan yayi gaskiya ba laifi idan mutum ya samay shi ko a gida ne ai ya gode shine mai hali.
Nan na fara gyara kayan mu ina kai ko wani inda ya dace Abba yana tayani dauka da Aisha.
Bathroom din nashiga naga akwai ruwa a fanfo yana zuwa ga shower daga sama kuma shima akwai ruwa a cikin shi.
Na ce bari nai masu wanka kafin yamma ya karasa sosai kafin yadawo nayi masu wanka ko ina shafa masu mai ya shigo yana cewa kunyi sallah dai ko ?
Nace anyi kiran sallah ne yace bakiga duhu yayi bane ba massalaci a uguwan amma munyi magana za,a gyara wanda aka gina na uguwan harda islamiya mun roka aimuna don yara saboda akwai nisa da inda ake zuwa karatu da nan.
Namike na bar yaran na shiga nai alwala nazo falon nata da sallah bayan ya nuna min gabas.
Na idar nai adduan sosai yadda na saba zama bayan magariba nai addua don yaran ne ma na mike na basu abincin da ya sayo muna kafin suyi barci.
Tare na zuba masu sukaci basu wani dade ba barci ya dauke su nan muka zauna muna hira dashi sai misalin tara da wani abu na kwashi yaran zuwa daki da yace shine nasu yace amma da yake basu saba kwana su kaida gashi bakunta kukeyi ki kaisu daki sai mu kwana tare dasu nan nai masu shimfida a kasa na kwantar dasu su duka ukun na dawo na kwashe kayan da muka ci abinci nakai kitchen.
Bai dade ba shima ya shigo dakin ina duke ina wa yaran addua akan su shirin kwanciya yakeyi shima.
Nagama abinda nakeyi na kashe wutan na kwanta nima duk da gajiyan hanyan dake a kan mu bai sa ya huta ba ranan sai da ya sauke nauyi a kaina.
Waahegari tun biyar muka tashi munyi wanka na shiga kitchen don yace bakwai yake zuwa aiki watarana ma shidda da rabi yake wucewa.
Ina kamalawa na tayar dashi don har barci yaso ya fara daukan shi a lokacin ko.
Wanka yayi ya shirya yafito ya zauna ya karya sannan yake ce min shi zai tafi zai aiko akawo min abinda zamuyi girki dashi da rana.
Nan ya fita ya barmu nida yara ya wuce gurin aikin shi ban kwantaba don ban saba kwanci ba nan na shiga gyara fasalin falon yadda naga ya dace min dashi.
Yaran suka tashi nai masu wanka na basu abin karyawa muka dawo falo na kunna masu tv suna kallo ganin muna da dan abin da muka zo dashi nai masu jeloup da kifin da mukazo da shi.
Sai bayan har sun gama cin abinci ne mai kawo