Showing 75001 words to 78000 words out of 115099 words

Chapter 26 - Bamu kadai ba ne book Complete by Zainab Makawa .txt

16 Dec 2024

6658

gaba daya.
Allah ya sauwaka baba Aliyun yace tare da cewa amma wahala take sosai idan sun fita a jikin ta baba.
Yace zan bincika naji may yakamata a dinga mata idan haka ya kasance da ita.
Aliyun yace ta daice na sayo mata hantiti da yamman nan na kuma saya mata shine ta samu tai barci yanzun haka.
Baba yace Allah ya sauwaka Allah yai mata saukin wanan al, amarin daya samay ta.
Aliyu ya amsa da amin yai wa baba sallama kan zai kira shi idan sun natsu.
Zancen Aliyu ya sai mota ya zagaye uguwar mu kowa sai cina da taran naki fada masu zancen sayen sabuwar motar dayayi suyi mashi murna.
Hakkuri kawai nake basu ba tare dana fada masu asalin motar ba daga inda yafito ba.
Don ban son yawan surutu saboda ina gudun mutane su fahinci halin da nake ciki.

****** ********* ******
Tun bayan komawan hajiya gida da labarin dawowan danta ya bazu a ko ina wanda yadawo cikin yan uwan shi da abokan arziki.
Haka yasa mutane tururuwan zuwa taya hajiya Umma murna da mata farin ciki.
Nasir yazama wani sheck din malami irin na kasan indiya yanzu ya aje wani gemay mai tsawo a fuskan shi.
Sai dai matsala daya shine bai yawan magana dakowa kasafai haka ma Umma ta fahinci cewa koda iyalinshi ba wai yana yawan magana bace sosai dasu.
Bata damu da matsa mai da hayaniya ba sosai daya gaisa da mutane zaici gaba da karatun shi ne kawai kan shi a duke.
Hajiya Gajiye tazo da su cake da miyan kan saniya mai yawa wai don Nasir din tayo shi kawai da iyalin sa.
Take Umma ta fahinci maganan mukkadarasiya ta hana ta cin komai a gurin kowa idan an kawo masu.
Da batasan komai ba sai tace so da kaunane yajawo wanan alherin da takawo ma danta da iyalin shi.
Sai dai ita kanta hajiya Gajiye tasha jinin jikinta irin yadda hajiya da yan uwanta suka karbe ta a yau.
Ba kamar yadda suka saba ba abaya ita da hajiya suna matukar amintaka da junan su sosai komai a tare sukeyi.
Duk da wani lokaci tasan gajiye na mata zagon kasa ga alamarinta sosai amma takan basar a matsayin hassadane hakan kawai.
Ashe abin nagajiye ya wuce sanin ta yakai ga kashin kai don wanda ya raba ka da danka ai yana iya yin kissan kai.
Haka tafita gidan tasha jinin jikin ta sosai takai kofa zata fita ne ta yanke jiki ta fadi kasa sai da aka kamata ta tashi tafita.
Wanan faduwan ne yai sanadin kaita kwance tsawon wani lokaci sai fallasa da tonon asiri takewa kanta.
Sherin da ta aikata kawai take labartawa har yakai ga sai da aka kulle ta a daki don abin yayi yawa sosai.
Labari yazo wa hajiya Umma yadda hajiya gajiye ta koma yanzu tace ta karata a can ita ta sani don itace tajawa kanta koma may nene ya faru da ita din.






ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
[11/14, 12:35 AM] Zuraiyah Zuzu ๐ŸŒŸ: ๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ง ๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ง


BA MU KADAI BANE A, , , ,


๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ง ๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ง


2โƒฃ4โƒฃ


Kwana biyu na samu dan shakat a rayuwa na banda matsalan komai a tare dani yanzu.
Don dan kwanan biyun da nayi ba abinda ya samay ni daga fanin jinnun dake damuna yanzu.
Haka yasa na ci gaba da harkan kasuwanci na danakeyi Allah kuma yana ta kara daukakani acikin sa sosai.
Yarana ina matukar basu kulawa sosai yadda ya kamata haka ma uban su yanzu naga duk dare sai ya shiga dakin kwanan su ya tofa masu addu,oi kafin ya kwanta.
Zan iya cewa yanzu a tsakani na dashi Alhamdullahi don gaba daya hankalinsa yana kan mu.
Yana dawowa dara kamar ko wani magidamci yaci abinci agida idan kuma tara yayi na dare zai dawo sai kuma gobe idan Allah ya kaimu kuma zai fita daga gidan.
Haka yasa hankalin hanna tashi sosai don yanzu dan jaye matan da yayi yasa ta shiga cikin wani hali na rashi.
Saboda ta saba ansan kudi masu yawa a hannun shi tana shagalin ta dasu.
Yanzu ko babu don bata ma ganin sa balle ya bata motar da aka bani yanzu shine yake shigan ta ya aje nashi guri daya.
Haka ya jawo kace nace a tsakanin yan uwan aikin shi sai suke zargin ko ya samu wani deal ne yayi shi kadai ba da sanin su ba.
Don har gurin controller din su sau da gulman shi ya kai amma ba a ga wani laifin daya aikata ba dole yasa suka kyale shi.
Na fito daga daki zan shiga kitchen ke nan naji wayana yana kara na nufi gurin da wayan yake a saman kujeran falo na dauka.
Wata abokiyar business dina ce tana yawan sayen kayana ta bani kudina acikin lokaci take fada min cewa akwai kawayen ta dake son kayan yara don Allah na kawo mata do yarta bata da lafiya ne yasa bazata samu zuwa ba.
Nake ce mata bazan samu zuwa a ranan ba sai washe gari don maigidana yafita aiki ko.
Bayan yadawo ne nake fada mai zan tafi gidan wanan matar don suna son sayen kaya na.
Bai so ya barni ba amma da Umma ta sa baki yace sai na dawo sai dai yake ce min nayi a hankali na dai san halin da nake ciki a yanzu nake cewa ai da yar sokoto zamu tafi bani kadai zan tafi ba gidan.
Washe gari bayan mun gama komai ne muka shirya sai gidan mun shiga da kayan da muka kwaso a cikin manyan ghana mostgo.
Nai sa, a masu son sayan kayan har sun riga mu zuwa gidan suna jiran isowar mu.
Kowace bata son yar uwarta ta zabi wanda yafi nata kyau yasa suka riga mu zuwa.
Mun gaisa na baje kayan suka fara dubawa sai gida ya rude da suratai kawai irin ta mata.
Matar gidan bata cikin falon nata tana daga ciki da yarta dake kuka cewa wai bata jin dadin jikin ta takewaya uwar tana mata tsarki .
Yarinyar tana kuka tana cewa uwar tai mata a hankali wai ta haihu ne.
Dariya yarinyan taba uwar ta tafito rike da hannun yariyar tana dariya.
Nan take fada muna abinda yarinyar take fada mata yanzu a bayi wai tana mata tsarki yarinyar ke cewa wai don Allah mama ki min a hankali na haihu ne fa.
Sai sauran matan suka saka dariya a lokaci daya suna tawa yarinyar dariya sosai wai ko a ina tasan haihuwa har take zancen sa haka.
Ido na kurawa yarinyar har na wani dan lokaci naja tsuki mai karfi nace aiba karya take maku ba haihuwa tayi.
Ido suka zaro suna kallo na take na fara wani irin hamma ina murza hannaye na .
Lokaci daya murya na ya koma wanda ba nawa ba ina fadin ku mahaukantan inane.
Yarinya ta haihu shine kuke mussa mata zancen ta da dariya haka babu tausayawa.
Wanan da kuke gani haihuwanta uku ke nan yanzu ba wasa take fada ba wanan haihuwan yazo mata da dan wahala ne yasa har ta fada maku.
Haihuwa fa maman Abba nace ba maman Abba bace mukkadarasiyatu ce ke magana da ku.
Sai duk hankalinsu ya tashi a lokaci daya nace bil, adam baku da kula akan jinjiranku ko kadan.
Yarinya tana a cikin wani hali amma kuna nufin baku fahinceta ba har kuna mata dariya haka.
Kema ai maman siyama yar ki tana da sabon ciki yanzu haka ajikin ta ki koma gida zaki samay ta tana amai yanzu haka.
Nashiga uku inji maman siyama din tafadi a cikin fargaba tare da dafe kirjinta cikin razana tamike tana fadin don Allah ku bari naje na leko wanan almaran da nake ji yau.
Da sauri ta mike tare da saka hijjab din ta tabar gidan acikin sauri tafice duk suka bita da kallo.
Shiru nayi kawai batare dana kara magana ba sai wata daga cikin su take cewa wanan magana akwai ban mamaki.
Wani kallo na watso mata daga inda nake a zaune ina cewa ki min shiru kina cewa haka baki san halinda mijin ki yake aciki ba kwanan zai kawo maki abokiyar zama a gidan ki.
Ta mike tana cewa kai ina yanzun kan ban yarda ba ni da mijina akwai alkawari bazai taba min kishiya ba don ni mijina dan kaki ne.
Tana nufin barin falon nace idan kin shiga gida ki daga takardan dake gefen gadon shi zaki samu sheda a guri amma aure babu fashi a gareshi.
Tsayawa tayi cak tana kallona nace jeki yanzu ki duba ki gani mana da sauri ta kwasa tabar gidan.
Yar sokoto dake a zaune kamar ruwa yaci ta mamaki da al,ajabi sun rufe ta a lokaci daya don bata taba sanin wanan labarin ba akaina.
Sauran matan da muke zaune kowace na gudun motsawa nata ya samay ta .
Maman siyama ce ta shigo gida a rude rike da hannun yarta tana kuka tana fadin wallahi amai na samu tanayi ita kadai a bayi.
Nace to ku tambaye su a ina suka samu hakan ai zasu fada maku nace Siyama fadawa uwar ki ko ke wacece yau don su sani.
Yarinyar tai shiru tana kallona cikin wani tsawa nace bazaki fada masu ba ne ?
Ta soma magana kamar muna fuka yarinya yar shekara bakwai tana cewa jecob ne yai min ciki.
Wanene jecob inji uwan tace wani ne shine mijina yau shekara biyu da mukai aure kullun dare kuma yana zuwa ya dauke ni a gidan mu dake Abuja muke kwana.
Nashiga uku inji uwar tace nice na aurawa baby deniel don yace min yana son ta.
Sai ga baby har tafi ni haihuwa don yanzu baby tana da yara uku niko ina da na biyu ke nan.
Waye jecob da Daniel yarinyar tace a school din mu daya dasu shine ya bani biscuit tun wanan lokaci muke tare dashi.
Nace yaya kuke yi ku fita dashi tace wani lokaci muna hawa bawan gyada shine motan mu wani lokaci kuma muna amfani da takalma wanda ake bari a kofan daki shine muke fita dashi ya zama jirgin mu
( Gareku masu barin takalman sawan ku a waje idan zaku shiga kwana wanan ba wai labari bane it happen always don ba kyau barin abin amfanin ku awaje wallahi )
Nace gida nawa jacob din yake dashi siyama ?
Tace mai kudine sosai yana da gidaje har a America mukan tafi wani lokaci.
Yana da motoci masu yawa a tare dashi sosai da bodyguard masu bin bayan shi don shi ogane.
Nace, matan shi nawa yanzu tace mu tara ne matan shi amma ya fada min yafi so na acikin su.
Uwar yarinyar tace na shiga uku na lalace Siyama a ina kika san irin wanan maganan haka ?
Nace ki barta tai bayani ki zaune da mugun abu a gidan ki tana halaka maki yan uwa baki sani ba.
Itace ta bayar da jinin mahaifiyar ki takuma da na kaunar ki da suka mutu a cikin wata daya a lokaci daya.
Nace ko karya nake maki siyama yarinyar ta dukar da kanta a kasa tare da girgiza kanta tace a hankali gaskiya ne.
Nace may yasa kikaba Daneil baby tace saboda inajin haushinta kada mijina watarana yace yana son ta.
Nace shi mijin baby din acikin cult din ku babbane ko karami a cikin ku ?
Tace shima mai kudi ne sosai yana da dukiya mai yawa sai dai ita baby bata son shi kullun fada sukeyi dashi.
Kuka sosai uwaye suka fara kamar ruwa yaci sauran matan dake falon lokacin.
Nace kuyi muna shiru duk sakacine iein naku na uwayen zamani yakai ku ga hakan.
Baku damu da damuwar yaran ku ba babu addua akan su idan zasu shiga barci idan kuma sun tashi haka kuke bari su fita agida.
Gurin ku kawai suyi ilimin boko su samu duniya sunan ku ya daga shine naku kawai.
Yaran ku da dama suna cikin matsalan rayuwa amma rashin kula irin naku yasa kunyi watsi da nauyin da Allah ya aza maku nasu.
Yaran ku idan sun fita baku san dasu wa suke hurda ba baku san tambayan su damuwar su ba baku saka ido ga dabiun su ko kadan.
Nace siyama yarinyar ta karba kamar muna fuka nace yau zan raba ki da Jecob din ki kina so?
Kai ta girgiza min nace saboda may bakya so na rabaki dashi ?
Tace I love him mummy.
Kuka uwar ta ta kara nace amma kin san ba adinin ku daya ba ko dashi ?
Tace na sani amma yace kadda mummy ta dake ni nayi addini na ba zai hanani ba.
Idanuwana da sukayi jajajir na kafe yarinyar dashi nace zo nan take ta karaso inda nake zaune na kama hannunta a hankali ina murzawa kamar wasa nake mata.
Sai ga yarinyar tana kuka cikin wani irin murya sautin wani yaro mukaji yana fadin don't live me Siyama please i love you .
Iam dying becouse of you .
Nace a cikin wani murya mai kaushi live her alone go back to your people don't ever come back to her life.
Kuka sosai akeyi ana fadin mummy don live us please ?
Ruwa nace abani da sauri wata matar ta miko min ruwa a cup na gunda ruwan abakina tare da matse yarinyar na dura mata a bakinta na shafe mata fuskanta da sauran ruwan.
Nan ta kwanta tana wani irin birgima akasa cikin sauti kala kala na ban tsoro.
Uwar zata tabata na hanata yadda naiwa yarinyar farko haka naiwa baby din ita ma take yaran sukai ta birgima a kasa sai zuwa wani lokaci suka lafa nake cewa karbi nan tare da mika masu hannaye na.
Garin magani ne suka gani shi na basu nace asaka aman shafin yaran a dinga shafa masu daga yau ba abinda zai kara samun su da yardan Allah.
Matar da ta fita zuwa binciken gidan ta tashigo da kuka tana nuna muna resist din da tagani na kayan lefen da mijin ta ya hada kusan miliyan daya da wani abu.
Tana cewa ku cece ni wallahi ashe da gaske ne aure zai kara bai fada min ba.
Nace ki rufa muna baki bakece kika jawa kanki ba kullun ba mutunci gare ki sai bani bani ya gajine da halinki yasa zai kara aure.
Idan kuma kince zaki dauki wani mataki a haka zaki samu matsala sosai a rayuwan ki.
Wai ma kuwa kin san wanda mijin ki zai aura kuwa to bari na fada maki sunan ta hajara diyar wani babban mutum ne a Abuja.
Don haka kiba kanki lafiya shi ne zaman lafiyan ki don an wuce ki ga komai.
Nace nabarku lafiya sai na fara wani irin atishawa a lokaci daya take na duka gurin da nake a zaune na lamay masu a kasa.
Cikin karfin hali yar sokoto take kiran sunana maryam maryam maman Abba na amsa mata da kyat tare da nuna mata hand bag dina.
Tamiko minjikin ta yana rawa da kyat na lalabo hantirina na shiga shakawa kamar zan tura shi a hancina duka.
Sai lokacin na dan samu sa, ida a raina na mike ina fadin tashi muje gida please.
Duk matan sun shiga tashin hankali sosai nan muka barsu cikin tashin hankali muka fice gidan.
Koda muka iso gida a gajiye nake kaman an bani kashi jikina ba lakka tare dani.
Nan na zube a falo ina mayar da numfashi haka baban Abba ya shigo ya samay mu.
Cikin kidimay yake fadin may ya faru kuma please abin ya tashi ne kuma ko yaya ?
Dama maman Abba tana da jinnu ne haka masu karfi a tare da ita ashe ?
Nan dai ra kwashe labarin abinda ya faru take fada masu fada ya farayi bayan ya gama sauraren ta.
Yana fadin ni wallahi maryam ina gudun kada wanan matsalan naki ya jawo min magana a garin nan.
Wanan ai ba so bane basu taimaka maki sai dai su sakaki yiwa mutane tonon silla kawai.
Gaskiya gara ku bar garin nan zaifi min kada a fahince halin da kike ciki kija muna matsala.
Ni dai ina kwance ina sauraren shi ban iya cewa kallallahu ba don ko ni abinda akace inayi yanzu ya fara damun rayuwana sosai.
Yar sokoto tai muna sallama ta tafi tana fadin zata dawo da yamma ta duba ni insha Allahu.
Tana fita gulma bai bari ta shiga gidan ta ba tun a kofa take kwadawa anty hauwa kira.
Anty hauwa dake kitchen tafito da sauri take cewa yau anty naga abin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login