Showing 87001 words to 90000 words out of 115099 words
Chapter 30 - Bamu kadai ba ne book Complete by Zainab Makawa .txt
an tayar dani akace maryam fito falo kinyi bako sai na dauki hijjab dina na saka na nufi falon da bakon yake.
Baba malam ne yana zaune saman wani carpet na alfarma sai kamshi ke tashi gurin hannun shi rike da casbaha saye da fararen kaya kamar kullun.
Zubewa nayi kasa ina gaishe shi da zuwa kai kawai ya daga min baiyi magana ba
Ina duke gurin da na durkusa da farko har yakai karshen adduan da yakeyi ya shafa a fuskan shi.
Ya dago yana murmushi a fuskan shi yace sallamu Alaikum maryama.
Na kara amsawa tare da gaishe shi again yace yaya muke ya iyali nayi hakkuri baya kasan yatafi bauta tun cikin watan azumin tsofi bayan rabona dasu ke nan bada dadewa ba.
Yake cewa yasan abubuwa da dama sun faru gareni da yan uwa suka jefani .
Har yakai yanzu ina bakin ciki da nadama haduwa na dasu danayi na rashin ganin basuyi min adalci ba.
Shiru nayi na sada kaina kasa cikin kunya yake cewa kin san halin ku yaran zamani da rigima bakowa bace sai Aisha da Rukaiyya .
Son da nake maki ne tashafe su suma suke kaunan ki haka.
Duk inda kika saka kafan ki suna tare dake sai dai nace kiyi hakkuri don ba zasu taba cuta maki ba ba kuma zasu bari a cuta maki din ba.
Maryama ke tamuce muna tare da ku tun zamanin iyayye da kakan ni bazamu iya rabuwa dake ba yadda kike tsanmani.
Wanan abin da kikeyi wani, taimako ne na al, umma da ya fado ta gare ki don haka hakkuri zakiyi da yanayin naki hallitan.
Babu wani mahalukin da ya isa ya kankare maki wanan rayuwan sai ubangiji Allah da ya nufe ki da wanan rayuwan, haka taki rayuwan tazo maki a duniya.
Bana son jin kin kara nadama da halin da kika riski kan ki a cikin sa shi mumuni ana son duk halin daya tsinci kansa a ciki ya dinga godewa mahalicin sa Allah da yanufe da zama haka.
Daga yau bazaki kara wahala ba ko yin abinda ba daidai ba wanda zai iya sabawa ibadan ki.
Muma musulmai ne yan uwanki musan abinda addini ya shimfida muna maikyau da marakyau na rayuwan bawa.
Ni dai sauraren shi kawai nake kaina a kasa har ya gama min nasiha ina godiya kamar yadda na saba yi mashi godiya a duk lokacin da nake tare dashi.
Karshe kafin ya tafi yake miko min wani jakka daga gefen shi yake min bayanin duk abubuwan dake cikin jakar ya kare da cewa zaki dinga karban sadaka ga kowa da kika bawa tai mako gwargwadon halin ciwon maishi.
Godiya nayi bayan nasihan daya biyo baya yake ce min na dinga hakkuri da maigidana maza dama sai hakkuri don kowa da tashi kalar rayuwan.
Gargadin karshe da yai min shine kada kiji kunya ko tsoro ko nauyi akan wanan lalurar taki don taimako ba sata bane taki hanyan samun kenan da Allah ya buda maki.
Mukai sallama naga ya koma kamar hayaki yana bacewa gani na har na daina ganin shi.
Ajiyan zuciya na sauke daga gurin da nake a tsugune na dafa wanan jakkan kayan maganin da ya bani na mike tsaye.
A daidai lokacin na falka daga barcin da nakeyi tare da sauke ajiyan zuciya ga gumi na hada sharkaf a fuskana duk da yanayin sanyi irin na garin kaduna da akeyi.
Baban Abba da ke barci a gefena naji shima yana mafalki kamar yana yanayin neman taimako sai fadi yake don Allah ayi hakkuri bazan sake saka mata ido ga al, amarinta ba insha Allahu.
Ganin yana wahala sai faman motsumotsu yakeyi kamar mai neman taimako yana mika hannayen shi na kama hannunwan shi da sauri ina fadin baban Abba baban Abba lafiya kuwa ?
Firgigit ya mike a zabure yana fadin ummum ummumm maryam nagode nagode.
Nake cewa sun biyo ka ko kai ma ke nan ?
Yace a firgice yanayi yana dan waige waige yace wallahi sun biyo ni maryam sunce yau sai sun hallakani badon Allah ya kawo ki ba a cikin wani katon rami mai namun daji sukaso jefani saida kikazo ne kika cece.
Nace ka tashi muyi sallah mu roki Allah saukin wanan Al,amarin haka ni duk kaina ya daure da wanan abin gaskiya.
Tunda muka tashi mukai sallah babu wanda ya kara runtsawa dagani harshi muna a gurin zaune har akai kiran sallah yafita zuwa sallah abinda bai saba yi ba ke nan sosai.
Nan dai muka bar zancen kowa ya kama tsabgab gaban shi na shiga kitchen don dora abincin breakfast danai masu don tafiya makaranta.
Muna shirin tafiyan su ne yafito daga daki yana shigowa falin yake cewa wanan kuma wani irin kamshine falon nan yakeyi haka ?
Sai lokaci na farga da cewa nima naji kamshi kamshine na zauren baba malam sak yake tashi a falon lokacin.
Ina jin abinda ya fadi mafalkina na daren jiya ya fado min a rai bankai ga karashe tunanen ba naji muryan Abba yana cewa mummy wanan bag din yana da kyau sosai .
Gurin da yake nuna min bag din na kalla naga wannan bag din ne da baba malam yabani a daren jiya na magani.
Gabana ne yai mugun faduwa nace a raina mafalkine ko gaskiya baba ya ziyarce ni a daren jiya.
To amma kuma idan mafalkine kawai may ya kawo wanan bag din a falon mu yanzu.
Bag din maye wanan baban Abba ne yake tambayana ganin yadda nai shock akan bag din.
Ba boye nake cewa daren jiya baba malam ya kawo min shi .
Abindana fadi ne yasa hankalin shi dagawa watau da gaskiya ina gana da mutanen boye ke nan murarar kamar yadda mahaifina yai mashi bayani ranan.
Wahalan da yasha ne daren jiya yasa shi jan bakin shi alaikum yai gum bai furta komai ba.
Saboda har wanan lokacin a firgice yake da mafalkin da yayi wanda yake gani kamar a zahiri ne yayi shi ba, a mafalki ba.
Bayan fitan su gidan na gyara ko ina na gidan tare da dora girkin abincin rana don yanzu na daina barin koda sha biyun rana yai min ban gama aikina ba tunda abokan zama na sunce na kiyayye yin hakan.
Wanan abubuwan da sukan yawa nuna muna alaman shi a gidajen mu akan mu dai wasu abubuwan da basu so.
Amma rashin sani da rashin fahinta bai sai mu kiyayye sai muyi ta afkawa munayi su kuma sai su samu sa, an wahal da rayuwan mutum yadda suke so.
Zaki ga wata idan sharane ba, a son ta dinga yi da rana ko da dare a gida da zaran tayi shi a wanan lokacin zata dinga jin ciwon kai ko ciwon jiki.
Idan wanke wanke kikeyi da rana tsaka hakan zai ita faruwa dake ko girki ko wanki da sauran su saboda suna ganin kamar mun shiga masu hakkin sune a cikin sanin mu.
Don Allah yan uwa na mata mu kula da abinda idan munyi a gidajen mu muke jin ba dadi saboda babu gidan da babu su a duniyan nan saboda tare muke dasu a gidajen mu bamu dai ganin su ne mu.
Wanka naki na yaranki gap da sallah magariba yan uwa mata mu kiyayye yin hakan musan man ma macen da ta haihu ki take da ciki a jikin ta don sunfi saukin samun su sosai wallahi.
Allah ubangiju ya tsare ya kare mu daga sherin shedan wanda muke gani da wanda bamu gani.
****** ********* ******
Ban sani ba ashe wanan abin danayi wa bawan Allah nan a kasuwa da aka sace wa dalolin shi ya jawo min wani sabon rayuwa na gaba.
Ranan da yakai kamar sati uku da faruwan haka har na manta da zancen a raina.
Sai ga baban Abba yashigo gida yake ce min maryam kina da bakin da ke son ganawa dake.
Nace baki baban Abba wasu irin baki kuma ?
Yace yanzu ina office mijin Hauwa yakirani wai nayi baki a gida danazo ne naga ashe wanan mutumin da kika taimakawa ne shi da wasu a waje suke son ganin ki.
Nace gaskiya baban Abba duk da kaima nasan ba da son ranka zaka yarda naga maza ba don haka duk abinda zai samay ni sai dai ya samay ni wallahi amma bazan yarda na kaucewa mahalicci naba.
Duk yadda yaso na fita kada mutanen suga an masu rashin mutunci naki sai dai cewan da nayi ya koma ya fada masu kada subi hanyan gabas da kayan su koma ta hanyan arewa su shigo dasu shine amsan abinda suke son ji a guri na kawai.
Yadda na fada mai haka ya fada masu mamaki da imani duk ya kama su basu fada min abinda sukazo dashi ba amma gashi na basu amsa abinda ya kawo su.
Shiru sukayi dayan na shirin yin magana wauan baban Abba yai kara nice a layin nake cewa bayan ya dauka nake cewa dashi
Ya fada masu cewa kada su biyo dasu da dare sai karfe daya daidai na rana zasu biyo da kayan da yarda Allah shine mafita garesu.
Yadda na fada mai yai masu bayani akan komai mutumin da wanan chairman din yan kasuwa ya rako yace anya Alhaji lukmanu kana ganin haka zai yi kuwa.
Da dare ma yaya muka kwashe balle da rana haka kiri kiri ace za, a biyo da kaya.
Suna hanyansu ta komawa inda suka fito ne suke wanan zancen haka.
Alhaji Lukman yace mu dai jaraba mu gani kawai don ni al, amarin yarinyar ranan ya bani tsoro sosai don ban taba kawo cewa wai dana na cikina ne zai iya yimin haka ba a rayuwana ba sai gashi yadda ta fada muna hakane ya kasance din kuwa kudin na samay su kamar yadda tafada ya kuma fara tabawa.
Baban Abba yana ciki gurina lokacin ina zaune tare da umma muna magana akan matsalan mutanen yanzu.
Zama yayi duk muka bishi da kallon yanayin shi yace wai Umma yanzu may mutane suka zamane ?
Yace mutumin da yazo ganin maryam yanzun fa ba karamin mutum bane a kasan nan wani irin hamshakin mai kudine sosai a cikin kasan nan.
Umma tace may yake so kuma Aliyu yace tambaya ta ita tasan abinda yake so dai nikan ban sani ba gaskiya.
Nace cikin mamaki wani ?
Ni kan ma ina nasan shi balle har nasan ko may ya kawo shi gidan nan ni.
Kallon mamaki yake min yace kai maryam wai ko kanki daya kuwa yanzun nan fa kika fada min abinda zan fada masu zakice kuma wai ke baki sani ba.
Nace wallahi baban Abba ni ban san komai ba akan zancen da kake min ikon Allah to Allah ya sauwa kawai yake ce min don shi a zaron shi ko gatse nake mai.
Nace wai wani mutum kake magana akai kuma wallahi Allah ban san ko wa kake magana ba.
Nan dai ya fahinci al, amarin nawa akwai daure kai a cikin shi idan basu tare dani normal nake banda wani matsalan komai atare dani.
Don haka ya zama wajibi a gareshi yasan yanayin da bani kadai nake ba don kiyayewa kawai.
Gashi abin duniya ya dami zuciyar shi ba dama yace zai wala rayuwan shi a waje ai mashi tonon silar a gida.
Nan dai muka bar zancen bakina dayazo min dashi muka shiga zance kan kayan dana tura gida kudi ya lake bai fito ba.
Anty lami tayi bi amma matar da ta kwashi kayan a gurin ta, ta hana mata kudin har suna batun zuwa kotu don kudin yana da yawa sosai ba wai kuma bata dashi bane ra, ayine kawai.
Jin haka yasa nace , a,a basai takai ta kotu ba akan kayan ta kyale ta kawai dasu bashi ke nan ba.
Sai ga kiranta ya shigo a wayana na dauka da sallama muka gaisa da ita take ce min gata a gidan matar da ta kwashi kayana .
Tazo don su kai karshen magana da ita nace bata wayan muyi magana da ita matar.
Ina dauka matan take cewa aiko ina a kaje da ita dole a bari sai ta samu kudi tabiya kudin idan kuma za, a kwata ne da karfi sai ta gani.
Allah yasa akwai mutane a gidan lokacin da muke wayan anty lami tasa handsfree a wayan kowa naji.
Nace Asabe kin san dai akai kudi a dakin ki da zaki bayar ko don kudin kayana sunan nan ki sai diyan dorawa dasu kin tara don dogon guri.
Akwai kudin Abbas da kika karba shima kin yaudare shi sunan kin sai gyada dasu kin boye.
Shin da kudin mu kike ganin zakiyi arziki ba da yardan mu ba ki ci riban da kike son samu ?
Idan kina son kanki da lafiya nabaki sati daya ki turo min da kudina idan kuma baki turo ba kinyiwa kanki.
Aiko jin fallasan danai mata rashin sani yasa tashiga zagina da kunduma min ashar wai tun bata fara daukan kayana ba take da arzikin ta sheri zan kulla mata ko may ?
Nace nadai fada maki in har kina son kanki da lafiya ki turo da kudin nan nan da sati daya kamar yadda na fada maki babu zancen zuwa kotu a kanki.
Anty lami ta karbi waya na bata hakkuri don da ta kafe sai tayi karanta ga gobe insha Allahu.
Ni kan tunda na samu komai ya lafa na fita zancen don nasan ya zama dole ta biya bashin nan koda tsiya koda arziki.
Ashe taje tana yada magana cewa sai tayi maganin anty lami a garin nan ita zasuyiwa sheri da kake don ana bakin ciki tana da dukiya.
Shine har ake mata hassada ita da kudin kudi ta rike taga uban da zai kwatar masu kudin su idan akwai wanda ya isa don lami tana kurin ubanta malami ne ko ?
Anty din ta kara kirana akan zancen hakkuri na kara bata nace kwandalanki ba zaiyi ciwon kaiba anty kudin ki zasu dawo gare ki insha Allahu.
Duk da haka bata yarda ba da zance na don tasan halin Asabe tantiriyar yar bariki ce kuma gashi tana hurda da manyan gari.
Kamar yadda nai masu bayani haka Alhaji Lukman ya samu ya rarashi Alhaji Sada ya yarda a bin shawaran dana basu din.
Dole ya hakkure yabi shawaran sai dai yana hango harsan da zai tafka sosai akan wanan gurguwar shawaran dana basu din.
Mamaki sukeyi yadda akayi hanya lafiya kalau har suka shigo da kayan su basu hadu da wani jamin tsaro ba a kan hayan.
Suna zaune falon Alhaji Lukman hankali a tashe sai jiran kiran wayan yarasu sukeyi suji labari mai dadi ko mara dadi akai.
Shaddodine da atamfofi irin na kasan waje dasu bag, shoes, da sauran abubuwan amfani wanda yan custom ke shan kwace masu shi, gashi wanan lokacin kusan duk rabin dukiyan shi ya narka saboda kayan nan da yake son ya shigo dasu.
Kiran wayan da akayi ne suna dubawa suka ga daya daga cikin babban yaron su ne da ke jagorantan shigowan kayan nasu.
Da sauri ya dauka yana fadin hello mustapha yaya akayine sun kama ku ko?
Dama ai nasan cewa wanan muguwar shawara ce dama yana fadin haka yakai zaune cikin dafe kai kwantena sun kai talatin da wani abu duk yayi hasaran su ke nan ake nufi.
Alhaji Lukman ne ya dauki wayan yana fadin hello mustapha yaya may ke faruwa ne may ake cikine wai please.
Wanda aka kira da mustapha din yace Alhaji Alhamdullahi komai normal don har mun shigo dasu inda kace batare da wani matsalan komai ba ko kadan a hanya.
Kai masha Allah Allah mun gode ma jin yana hamdala yasa Alhaji sada dago kai yana mai kallon mamaki yana cikin wanan halin na tashin hankali.
Hannu ne ya mika wa Alhaji sada yana cewa congratulaion Allah ya taimake mu Alhaji ya rufa muna wanan asirin.
Ai yana jin hakan yace ban fahinta ba fa may kake nufi ne wai.
Yace Alhaji sada kaya dai sun sauka lafiys har an adanasu indaya dace ko.
Wai wasa kake min a cikin wanan yanayi ko may kake shirin fada min ne Alhaji ?
Yace abinda dai kaji na fada ma din ne haka abin yake da gaske.
Masha Allahu kai Alhaji wai yarinyar nan da kake fadi mutunce ko aljanna ita ?
Yace bari kawai ni al, amarin wanan bakuwar fuskan yana matukar daure min kai.
Baka ganta bane fa yarinya ce karama da ita Allah yai mata wanan baiwan haka wallahi.
Kenan ashe ko acikin mutanen mu akwai irin yan baiwan nan sani sune kawai ba, a yi acikin al, umma ?
Kwarai kuwa akwaisu da dama sune dai boyene ba, asanin su a cikin yan adam sai wanda Allah yaiwa katari dasu kawai zai san dasu.
Allah bowayi gagara musali ita kuma wanan boyar Allah nata baiwan ke nan a haka.
Dubi dan gidan da take zaune ciki tana rayuwa acikin sa tare da tarin baiwan Ubangiji a