Showing 69001 words to 72000 words out of 115099 words
Chapter 24 - Bamu kadai ba ne book Complete by Zainab Makawa .txt
zan tafi na kwaso ne nagani a dakin an tara min su daga gefe daya gefen gadona.
Nace na shiga uku ni maryam cin bashi kuma harda na aljannu haka ?
Sai ganin kaina nayi kamar a kasuwa cikin wanan shago tare da bin yusuf mai shago yana ce min.
Ba bashi bane maryama ke yar uwatace bazakici min kudi ba yarda ne yasa na baki don halinki na alheri.
Nace amma kuma gaskiya, , , ,
A, a maryam ki shigar da kayan nan zasu samu shiga sosai a gurin ku idan kin tallata su sai ki kawo kudin na baki wasu.
Mussaman na dauko su don ke ki samu karuwa a rayuwan ki kada ki damu ke yar uwata ce.
Daga haka ina fadin nagode sai ganina nayi zaune saman gadona nayi tagumi kawai.
Tsoro ne ya kara kamani a lokacin duk na firgice nace nashiga uku ni maryam yanzu yaya zanyi ke nan da dukiyan mutane haka masu yawa
Mama ga sauran kayan ki wai an kawo maki muryan Abbane ke fadin haka daga falon mu.
Da sauri nafito ina mamakin wasu kaya kuma yake magana again ina fitowa sauran bedshirt din dana bari a shagon ne a cikin manyan leda.
Cikin wata murya nake tambayan Abba waya kawo su kuma yace wanan mutumin daya sauke maki kayane, zaune nakai na dora hannun na akai ina fadin na shiga uku ni maryama.
Haka na karasa wuni kamar kwai ya fashe min aciki sai na kalli kaya nakali kaina na dafe gefen fuskana.
Haka baban Abba yadawo gida ya samay ni a cikin damuwa ya lura da yanayi na gashi ina son fada mai rigimar dana kwaso amma ina jin tsoro.
Idan ma har zan fada mai may zance dashi akan kayan to may zamce dashi.
Naja bakina nai shiru sai shi da idon shi suka kai kan kayan ne yake tambayana duk wannan shirgin kayan na may nene haka ?
A sanyaye nake ce mai kayan sayarwa nane yace a razane duk wanan kayan haka masu yawa maryam naki ne sai nai shiru kawai.
Washegari nashirya sai kasuwa hankalina a tashe sai dai ina zuwa shagon nasu a rufe yake na dan jima a gurin tsaye sai ga wani mutum yazo wucewa zai bude shagon shi nake cewa don Allah malam mai shagon nan nake tambaya ?
Yace Oh Alhaji Bin Yusuf kike magana wallahi yai tafiya yace bazai dawo ba sai bayan azumi idan Allah ya kaimu zai dawo kin san azumi ya kusa zuwa.
A daga can zai tafi umurah gurin ibada insha Allahu yanayin da mutumin yaga nashiga ne yake cewa hajiya lafiya dai ko ?
Nace cikin girgiza kai a, a ba komai dama wasu kayane nazo na sara a gurin shi.
Yace ayya ai sai dai kiyi hakkuri ki duba a wani shagon ko dayake shi kayan shi duk kasuwan nan na daban ne gaskiya.
Naiwa mutumin godiya haka juya jiki a sanyaye cikin wani sabon tashin hankali ni yanzu yaya zanyi da dukiyan wanan bawan Allah haka daya jibga min a hannu na.
Yazama wajibi a gare ni dole na sa ido naga kudin shi baiyi ciwon kai ba ko kadan a gurina.
Ranan suna sai da na gama komai na fita don zuwa kama aiki saboda zama tare nima watarana , zanso aimin hakan a gidana.
Yadda na samu baki yan uwan maijego sunzo har sun kwana wasu kuma yan gari sun soma hallara ko.
Nazage na dan sake ana sha, anin buki dani sai bayan mun kamala ne na koma gida nai wanka nazo da kayana muka baje ni da su anty da yar sokoto.
Nan mutane suka fara zuwa suna tabawa aikafin ace may sai ga masaya na ta bukin suna saye don sunga arahan su ga kuma kyau.
Yar sokoto na ta faman dada kayan da quality din su bashi ne bamu yarda mubawa mutum sai dai ki saya ki zube muna kudin mu.
Sosai nai ciniki a gurin nan sai ga yar sokoto ta ballo da zancen kayan mata.
Haba nan sabon kasuwa kara buduwa min sun saya sosai wanan kan nai cinikin sa fiye da kima.
Zance wanan taron bukin ba karamin jawo min alheri yayi ba sosai don ya zama min wani silar alheri a rayuwana.
Don wani kofa ya bude min nan mata suka fara tururuwan zuwa har gida sayen kaya wasu har sari suka dauka a gurina na dan kara masu kudi a sama kadan.
****** ********* ******
Kamar yadda hajiya Umma take son tabbatarwa akan maganan mu yau sati uku ke nan da lissafin ta bayan ta idar da sallah la, asar take cewa.
Yaudaran banza yaudaran wofi dani za, azo har gida aiwa 419 don kawai aci kudina don an hada baki a cuta min.
Taja tsuki tace duk da dai maganin da takawo min yai min amfani na daina jin komai a kafana kuma yanzu yakai ma kamar banyi ciwon kafa ba a baya nake ji.
Wanan bazai zama hujja ba a gare ni ai magani sa, a ce bawai yin mutum ba ko wani.
Kawai ta samu wani wanda yasan sirin abinda ke damuna ya fada mata komai akaina gani tsohuwar banza yarinya karama zatazo har gida ta sani a kwana hakanan.
Nan take zaune saman sallayan da ta idar da sallah da carbi a hannun ta tana dan karkada kafan ta a hankali.
Kofan shigowa dakin ta aka turo da sauri ta daga idon ta tana kallon wacce tashigo dakin nata.
Kafin maishi tai magana take cewa wai Fati saunawa zan fada maki idan ina daki ki daina shigo min dakina hakane ?
Kai tsaye baki daga waya ki kirani koma may ye ki fada min may ye amfanin wayan dana saya maki har biyu don bukatana ?
Mama ba hakana bane yaya Nasir ne ne yadawo shine nashigo na fada maki .
Wa kikace Fati tace yaya Nasir ne yazo harda matar shi da yaran shi biyu baki gansu bane masu kyau dasu wallahi.
Zubur hajiya ta mike tsaye cikin mamaki tace Nasir fa kikace Fati ?
Wallahi mama shine shine ma don hoton shi dake manne a falon ki ina iya sheda shi.
Ai kafin Fati ta karasa har hajiya takai kofan daki ko ta riga fatin fitowa waje.
Yana tsaye gaban katon hoton mahaifin shi ya tsurawa hoton ido yana kallo bayan shi kawai ta hango.
Tun bata karasa saukowa ba take ambatan sunan shi Nasir kaine ko gizo idanuwa suke min ne ?
Yajiyo tare da kurawa mahaifiyar tashi ido kafin ta karaso gare shi ya zube a kasa gwiwa bibiyu yana kallon ta.
Inda yake durkushe takaraso itama zubewa tayi a gurin tana kuka matarshi dake zaune a gefe tana kallon su tajawo yaran ta zuwa jikin ta ta rugumay su.
Hajiya tana fadin Nasir ina kashige ne haka ka boye muna yadda taga ya fara dan ja da baya yasa ta tuna da gargadin da akai mata.
Tace Nasir don Allah kazo gare ni idan ba mafalki nakeyi ba nagane ka.
Jin haka yasa ya tako zuwa gurin mahaifiyar tashi suka rungumay juna baka jin komai sai kukan dake tashi a tsakanin su kawai.
Sai da sukayi mai isan sune suka lafa yake gabatar da matar shi da diyan shi ga mahaifiyar shi.
Bata jin hausa sai larabci da turanci koshi ba wani sosai take ji ba sama sama suka gaisa da hajiyan .
Hajiya ta mika hannu wa yaran da nufin suzo gurin ta amma sukaki suna makale a jikin uwar su kawai.
Nan hajiya tasa a gabatar masu da abinsha da sauran su a gaban su.
Kafin wani lokaci Fati tasa an cika masu gaba da abinci da abin tabawa sukaci suka sha aka kaisu masaukin su.
Sai da dare ne zancen wanan yarinyar da ta dauka a mayaudariya yazo mata a rai.
Lalai ya kamata ta nemo wannan yarinyar don akwai abubuwan da zata bukata a gurin ta da take son sani.
Godiyan ta ga Allah shine tayi dabaran karban nomban wayan yarinyar daba haka ba bata san inane zata zakulo taba a fadin garin nan.
Ta sake sauke ajiyan zuciya tana cewa Allah nagode ma yau Nasir ne yadawo gida cikin mu harda iyalin shi.
Idon ta ta runtse tana mai jin zafi a zuciyan ta abinda take tunane shine daga ina wanan matsalar na Nasir yafito mata.
Dayasa kai yabar gida haka na tsawon lokaci batare da kowa yasan inda ya shiga ba ?
Gashi kuma da zai dawo yadawo mata tare da iyali da alaman natsuwa kuma a tare dashi.
Ba wani alama dake nuna yana cikin wahala a tare dashi ko wani mugun hali.
Yanzu ma wazata fara fadawa dawowan shi cikin yan uwan ta.
Wata zuciyane ta gargade ta da ta nemi yarinyar nan tukun tafara jin ta bakin ta shine mafita a gare ta don bata san daga inane matsalan shi yake ba.
Takira nomban yarinyar amma sai ace mata is swich up haka ta hakkura ta kwanta zuciyar ta tab da tunane.
Washegari na idar da sallah namike zuwa kitchen don na dorawa yan makaranta abinci don gudun makara.
Sai lokacin naga wayana dana bari yashe a falo daren jiya dauka nayi don in duba time sai ganin ta nayi a kashe.
Nasan ba kowa bane Abbane dake game da ita jiya da dare ya kashe min ita.
Kamar anajira na kunna wayan sai ga kira ya shigo a wayan nawa da mamaki nake kallon wayan sai dai bakon nomba ne ake kiran dashi.
Kamae kadana dauka sai na tuna kilafa mutanena ne da muke sana, a dasu suka kirani.
Na dauki wayan da sallamana jin bakuwar muryan da ban sheda ba nayi tana karba min sallama na.
Muka gaisa da ita acikin dadin rai take tambayan don Allah da maryam nake magana ?
Nace nice insha Allahu.
Sai naji ta sauke ajiyan zuciya tana cewa boyar Allah tun jiya nake kiran layin ki amma wayan a kashe yake.
Nace ayya kiyi hakkuri wallahi yaro ne ya kashe min ita tun jiya da dare tace Allah sarki.
Dama nakiraki ne na fada maki cewa Nasir yadawo jiya da yamma nan.
Nasir na tambaya wani Nasir sai naga kamar abu ya gilma a cikin idanuwana lokaci guda.
Nan take zance ya canza min nace dawa nake magana please ?
Tace hajiya Umma ce au hajiya kin gama zargina ke nan kina ganin kamar ni yar 419 ce ko nazo na cuta maki har gidan ki.
Ki sani niba macuciya bace taimakon ki kawai nayi don ganin halin da kike ciki.
Amma runda kin zarge ni kada ki sa rai cewa zaki kara gani na don ban son mutumin da baida godiyan Allah.
Mamakine yakama hajiya a bangaren ta tace cikin marairai cewa don Allah kuyi hakkuri duniya ne yanzu bata da tabbas kawai.
Amma don Allah dai ayi hakkuri a yafe min Allah dakika ambata yasa zamu kyale ki da mun mayar maki dashi inda yafito inda bazaki kara jin labarin sa ba ma a duniyan nan.
Nan dai ta shiga bada hakkuri hankali a tashe saida tai kamar tanayi aka hakkura mata.
Nace kin kirani ne kiji wazaki fara fadawa dawowan dan naki ko ?
Tace hakkane nace zaki iya fadawa kowa amma duk wanda ya amsa maki a cikin mamaki yakira sunan danki har sau biyu da mamaki shine munafukin ki shi yai maku wanan aiki akansa.
Ba komai ne akansa ba sai kurciyan da akai mashi don son da kike mai keda mahaifin shi ya jawo maku haka.
Tace ikon Allah insha Allahu zanyi kamar yadda kikace min din nagode nagode.
Ina kashe wayan na yanka wani irin ihu wanda yasa duk wanda ke gidan fitowa a lokacin.
Lamau nake tsakiyan falo ina wani irin gurji cikin wani irin sauti mai ban tsoro.
Baban Abba yayo kaina cikin razana ya na kiran suna na a cikin tashin hankali.
Yana kokarin tabani ne aka dauke shi aka maka shi a bango kumus ya buge.
Bai hana shi dawowa ba ya kara cakumana cikin wani murya da ba nawa ba akece mashi kada ka soma taba muna godiyan mu.
Don bamu yarda da kaiba kana cuta muna godiyar mu da mugun halin ka.
Kana sa ana zargin itace take hanaka alheri kana fifita karuwan ka akan ta duk da munyi warning din ka bai hanaka komawa gareta ba.
Zamu dauki fansa akanka nan ba dadewa ba daga kai har waccan matar banzan da kake hurda da ita.
Zamu tozartaka a duniya zamu kwato ma mahaifiyar ka da yayan ka hakkinsu da kake tauyewa.
Mun maka warning kakejin maganan mu hukuntaka ranan da ka kawota gidan nan da zuman aikata zina a gidan matarka ta sunna .
Amma baisa ka daddara ba ka daina wanan harkan da kake yi yanzu duk abindaya faru dakai ka sani kaine kajawa kan ka don baku kadai bane a gidan nan kuna tare damu a ko ina sai dai a gurin da bai kamata mu shiga ba a lokacin da kake tare da godiyar mu.
Yana duke a kusa dani ya kura min ido don sam wanan muryan ko kusa ba muryan maryam din daya sani bane tashi.
Zamu tafi mubar godiyar mu ta huta hakana kada mu wahal da ita da yawa.
Sai na kara mikewa na dan lokaci can na sake wani atishawa har sauku da karfi.
Lokacin ne na bude idanuwa na da suka rine min sukai ja ina kallon duk wanda ke falon sai faman sannu suke min.
A hankali na mike zuwa saman kujera na zauna lokacin Umm dake tsaye daga kofa ta karaso gurin duk abinda akayi aka fadi akan idon ta akayi shi.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
[11/12, 11:23 PM] Zuraiyah Zuzu ๐: ๐ฉโ๐ฉโ๐งโ๐ง ๐ฉโ๐ฉโ๐งโ๐ง
BA MU KADAI BA NE A, , ,
๐ฉโ๐ฉโ๐งโ๐ง ๐ฉโ๐ฉโ๐งโ๐ง
2โฃ3โฃ
ASSALAMU ALAIKUM YAN UWA DA ABOKAN ARZIKI INA MAI KARA SANAR DAKU FITOWAN SABON NOVEL DINA DAKE AKAN HANNYA SATI MAI ZUWA DA YARDAN UBANGIJI
WANDA KE BUKATA YANA IYA KIRAN LAYINA DON YIN REGISTER A GROUP DINA NA KUDI NAGODE DA KAUNAR DA KUKE NUNA MIN A KULLUN TAKE KAUNAR KU DIYAR KU YAYAN KU ZAINAB IDRIS MAKAWA
Baban Abba yana duke a kaina sai yan tofe tofe yake min tare da faman yi min sannu yake yi hankalin shi a tashe.
Ina kada kaina dake sara min a hankali can dai na kara sake wani atishawan sai yar mikan da nayi na dinga binsu da kallo daya bayan daya duk suna tsaye akaina har yaran nawa a guri daya.
Zubur na mike yana fadin ina zaki kuma nake cewa abinci zan duba na dora girki a wuta nake gani.
Ki barshi a duba maki nace zan iya insha Allahu nasa kai na shiga sai da na gama zuba masu nai komai kafin su fita na samu guri don zazzabin da nake ji na kwanta a falo sai barci.
Ranan yaran saida suka makara haka uban ya kwashe su hankali a tashe suka tafi tare da shi.
Ban falka daga barcin danayi ba sai sha biyu da wani abu duk jikina sai ciwo yake min kamar an bani kashi nake ji a lokacin.
Tunawa da mafalkin da nayi cewa na nemi hantiti na aje na dinga shakawa idan naji banjin dadin jikina haka.
Na idar da sallah wanan nomban da aka kirani dashi da safe ne aka kara kirana dashi a lokacin.
Kamar kada na dauka sai dai na dauka daidai lokacin da wayan yake batun tsinkewa.
Muryan hajiya Umma ce take cewa kiyi hakkuri dani maryam na damay ki da kira please don Allah ko zakiyi min kwatancen gidan ki ina son turo maki da wani sako ne.
Ba bata lokaci ba nai mata kwatancen ida nake tace min sai na gan ta mukai sallama na aje wayan.
Baban Abba ne ya shigo gidan don sanin ya barni ban da lafiya yasa shi dawowa gida da wuri haka.
Nai mashi sannu da zuwa yake tambayana yaya jikin nawa nace da sauki.
Abincin ya zauna yaci wanda yazo dasu a take awaya don yasan bazan iya dafa komai ba a yadda ya barni kwance kafin ya fita daga gidan.
Yamayi mamaki da ya shigo ya samay ni zaune saman sallaya na idar da sallah lokacin.
Umma ma tafito daga daki tana min sannu da jiki suka zauna nan tare dashi suna magana.
Dirin motan da mukaji ne sun tsaya a kofan gidan mu yasa shi mikewa ya nufi kofan ya duba ko waye.
Bakin fuska ne ya gani suna fitowa daga motocin su kuma da ganin su masu fada ajine a gari don yanayin su da shigar su uwa uba motocin da suka zo dasu har guda uku.