Showing 81001 words to 84000 words out of 115099 words
Chapter 28 - Bamu kadai ba ne book Complete by Zainab Makawa .txt
tace tasha ruwa dashi mukai mata godiya na rako su har kofan gida suka wuce.
Baban Abba yana dawowa na fada mashi zuwan su hajiya tare da dauko alherin da ta kawo muna na nuna mai.
Ikon Allah yace tare da kurawa kudin ido yana tunane a cikin ranshi yake cewa.
Yanzu ita kuma maryam nata hanyan samu ke nan ta wanan hanyan iskokan da suka hau kanta.
Muryana naji ina fadin Abba dauki kudin nan ka mikawa baban ka da sauri ya dago kai yana kallo na a cikin mamaki.
Yace amika min nayi may dasu ki rufa min asiri please ?
Dariya maganan shi ya bani nace may kake tunanen zai faru dakai idan kayi muna amfani dashi matsalar dai daya ce idan ka dauki abina kai ma wata hidima dashi ko kabi wani hanyan dabai dace ba.
Yace a, a maryam kibar kudin ki a hannun ki kawai keda ke sana, a ba sai ki kara ajarinki ba.
Karban kudin nayi daga hannun yaron na raba biyu nabashi rabi ya karba yana godiya.
Bai dauki lokaci ba yafita sai ko gashi yadawo muna da kayan abinci masu yawa da zamuyi amfani dasu don Azumi.
Dama ba ai biya ba manage mukeyi kawai don bai sayo muna komai ba a gidan.
Washegari wayan hajiya ya samay ni wai na kawo zanuwan gado da kayan yara da takalma ana son saya.
Shi da kan shi ya kaini gidan nima da kyat na sheda gidan yana ganin gidan yai mamaki yadda Allah yakawo ni hurda mutane masu arzki irin haka.
Na samu an canza masu aikin gidan duk sabbin fuskane nagani a gidan sabani wa yanda na samu a farko gidan.
Taji gargadin da akai mata ke nan na zagon kasan da wa yancan suke ma rayuwan ta.
A falon kasa mu ka zauna, nan da yake muna azumi babu wani abinsha da aka kawo muna sai dai hakkurin da suka bamu kawai na ana azamu.
Tare da yaran ta da sukazo ne don zasu tafi umura suka sauka kasa cikin fara, an su muka gaisa dasu.
Nan suka shiga duban kayan daya bayan daya suna yaba kyawon kayan sun zaba don kusan ince sun kwashe bedshirt din nawa.
Suka ban kudina muna batun wucewa ne hajiya take fada muna cewa zata koma abuja gidan su dake Abuja da zama.
Tana son don Allah idan zata koma bayan sun dawo daga Umura baban Abba ya taimaka ya bata aro na muje gidan don a akwai abin da ake da bukatan naje nagani a gidan kafin su shiga gidan.
Ta cika mai ido bazai iya mussa mata ba akan komai yace kawai Allah ya kaimu lafiya.
Take cewa kada ya damu ai idan za, ai tafiyan tare dashi za, a tafi don yaga guri a can.
Haka mukai sallama bayan kuauntan da na samu dani dashi a furin hajiyan na atamfan super da dogayen riguna masu kyau guda biyu.
Shi kuma shadda ne mai tsada aka bashi har kala biyu duk bardin masu kyau dasu.
Kamar kada ta bari mu fito daga gidan har kofa ta rako mu tana muna godiya take cewa wancan ne motar taka mijin diya gaskiya wanan motar ma ai tayi karama sosai.
Bude bakin baban Abba sai cewa yayi ai ta maryam ce ma nake shiga kyautan shi hajiya Umma ta bata.
Da mamaki hajiyan ke tambaya wace hajiya Umma ke nan sai yake ce mata hajiya Umma sanda, .
Cikin mamaki take cewa hajiya Umma dai wacce na sani seneter ita hajiya yabata amsa.
Ikon Allah ashe tasan da zaman ki matar tana da mutunci sosai wallahi akwai taron da mukeyi na formwn ai tare da ita badai wani gaisawa sosai mukeyi ba.
Nace haba baban Abba hakan baida kyau yin haka kamar fallasa sirin mutum ne ga wani.
Ba wai lalai bane wani yasan abinda naiwa wani don hakan bashine alheri ba ga rayuwa.
Magana sosai yaiwa hajiya dadi tace wanan gaskiyane diyata kuma har kin sa na kara son ki a raina sosai wallahi.
Kada ki damu idan na dawo in Allah ya kaimu lafiya zamu hadu kada kiji komai diyata.
Sai bayan mun kama hanyane muna tafe ganin raina ya baci ga abinda yai min yake cewa batare da ya kalli inda nake zaune ba.
Iam sorry please bawai na fadi haka ne da wani manufa kawai dai maganace takawo hakan ai.
Nace hakan baida kyau ne kasan kowa da sirin shi a duniya don Allah yabani ci daga karshin su bai kamata ace ina fallasa sirin wani ga wani ba sai mutane su dinga daukata mai yawan surutu.
Har muka kawo gida babu wanda ya kara magana a cikin mu don raina yai balain baci ga maganan shi.
Azikin shi daya shine watan azumi muke ciki da ranan nasan yadda raina yabaci daya dandana kuren shi gare su.
Ko yanzuma ai ban debe ma katobaran shi tsanmanin ba gaskiya sai dai Allah ya gyara ba wani abinda ya faru damu har dare.
Daga bangaren hajiya Umma na samu sako na alheri sosai alfarman watan azumi ta aiko min da kayan shan ruwa tare da kayan sallah nawa dana yarana har ma da Umma ta samu nata rabon a ciki.
Nan dai mukai azumin mu lafiya wanan shekaran sai sam barka kawai zance naiwa iyayyena sako na ban mamaki a gida don duk yan uwana sai da suka samu sakona a lokacin.
****** ********* ******
Ranan sallah kowa yana murnan sallah muyi abinci mun akai wa mutanen da nake hurda dasu.
Haka muka wuni lafiya har yamma sai nishadi muke da zagayowan wanan ranan mai albarja da Allah ya nuna muna zagayowan ta lafiya.
Na idar da sallah namike ina nade abin sallah sai gani nayi kaman wani abu ya gilma min a gabana da fararen kaya ina dubawa da kyau wani haske ne har saida ya kashe min idanuwana.
Abinda ban sani ba ashe nan na fadi kasa na fara gaisawa da yare davan daban wanda ba wanda yasan na iya yare kalan wanda nakeyi na harsuna daban daban .
Ina nuna masu godiya da farin cikin ganin wanan ranan ta sallah da yazo.
Hankalin baban Abba yai matukar tashi daga shi har umma da yarana don sai danai yare kusan kala tara kowa kuma da kalar yadda yake zuwa min idan zai zo ko zai tafi.
Umma tace ni yasu babana ashe yarinyar nan ba sabbi ne suka sake shigan taba kuma ?
Aliyu wanda kanshi a daure yake duk ya dabure ya rasa abinyi kai kawai ya iya dagawa umma.
Sai daga karshe ne bahausa tazo sukayi magana sosai dasu na fahinta take sanar mai cewa sunzo yawon sallah ne gurina saboda so da kaunan da suke min.
Shiyasa suka kawo min ziyar yau ranan sallah don yaune suka samu daman fitowa daga inda suka tafi hutu kuma sun tafi suna kewa na sun barni babu kowa a tare yace mata ai tana tare da Allah damu.
Tace na dai yarda da tana tare da Allah amma kai banda karya babu abinda kakewa godiyar mu.
Muna dai kyalekane don munga tana matukar son ka sosai a rayuwan ta idan bashi ba da tuntuni mun rabaka da ita.
Amma a gaskiya abinda kake wa godiyan mu samsam bamujin dadin shi ko kadan.
Yace to kuyi hakkuri kuyi min addua na daina mata abinda baku so.
Tace koku bani adam kunsan yaudarar mace ba kyau amma kai kullun godiyar mu tana kokari akanka baka gani.
Mun rabaka da waccan fasikar yanzun kuma ka koma akan wata bakasan wanan idan ka fada kaidinta ba tafi wacan hatsari agareka.
Don kaga ita wanan tana sallah kuma tasan Allah sai dai tana da yawan shirka wanda mu bamu kauna maishirka bamu zama tare da wanda bai tsoron Allah zamu iya maka komai akanta duk ranan daka bari ran godiyar mu ya baci akan wanan sabuwar da kake kokarin daukowa.
Shiru yayi yasan baida gaskiya duk abinda take fadi gaskiyane take cewa yanzu goron Sallah zaka bamu na rabawa yan uwana mu tafi.
Yace bansan wani irin goron kuke so ba ai dariya tayi tana cewa godiyar mu ta san mau muke so don ta tanadar muna ka bude akwai zuma akayan ta shi zaka zuba akasa kawai ya ishemu komai kadan dinsa zamu raba a tsakanin mu.
Ya mike zuwa daki da sauri yana dan dube dube yaga zuma acikin wani katon gora dana sayo ranan akasuwa.
Har zan wuce sai mai zuman ya matsa min kan nasaya zai min amfani badon naso badai tausayi mai zuman yabani yadda naga yana qahalan talla a cikin rana.
Ashe ban sani ba maishi yasan zan bukaci zuman yasa yai tabina sai na saya Allah ya taimakwni kuma na saya din.
Kafin su barni nasha wuya sosai ranan haka na samu kaina daga garesu suka tafi suka barni da ciwon jiki.
Nadai ji Umma na fadin wanan soyayyan da wahala yake ace ana son mutum haka kuma yai ta wanan irin wahala.
Umma please ki kama bakinki don Allah tunda mun samu sun tafi ni wanan abin wallahi ya fara bani tsoro Allah.
Na mike tare da bude idona lokacin har yamma yayi sosai sai mamaki nakeyi suko sai faman sannu kawai suke min.
Da kyat na iya tashi nai sallah tare da watsa ruwa duk da wankan date ba dabia na bane amma ranan dole nagasa jikina.
Ina daga daki najiyo muryan su a fallo kasa kasa umma tana fadin wallahi babana kakiyayi wanan neman matan da kakeyi kada su illata min kai.
Ni banga abinda matarka ta rasa na rayuwa ba dake wanan shegen neman matan haka.
Kudi na rudin ka har kana kokarin jefa rayuwan ka ga rudin duniya.
Kana zaman lafiya da matarka amma kai kenan zuwa sunsune sunsunen matan banza a waje.
Dama ace neman aure kakeyi ai babu mai hanaka yin abin da Allah yace amma kaike na neman matan da sukafi karfin ka kullun suna maka wayo suna karbe ma dan kudin ka.
Badon Allah ya hadaka da yarinyar kirki ba kana ganin akwai macen da zata zauna dakaine cikin wanan rayuwan haka.
Umma don Allah dai ki daina zancen nan tunda maryam bata san dashi ba a halin yanzu.
Idan ma bata sani yanzu ba idan ka matsa kace baka kama kanka ai sani zatayi nan gaba.
Kadai ji sunce sai sun maka illa a wanan karon yanzu dubara ai ya saura gare ka dai.
Fitowa na falon yasa suka daina maganan da sukeyi sai bina da kallo kawai sukeyi cikin zargin ko naji abinda suke fadi.
Ganin yadda na ga Nusaiba a kwance da kayan da suka wuni dashi a jikin su nake cewa Umma Nusaiba bata cire kayan jikin taba dashi ta kwanta hakana.
Umma tace to bari a cire mata ai ban kula da tayi barci ba ma a hakan.
Nidai na tayar da sallah na kawai nabarsu suna nan sun canza topic din zamcen su sun dauko wani sabon hira.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
[11/16, 10:30 PM] Zuraiyah Zuzu π: π©βπ©βπ§βπ§ π©βπ©βπ§βπ§
BA MU KADAI BA NE A, ,
π©βπ©βπ§βπ§ π©βπ©βπ§βπ§
2β£6β£
Tun bayan jin bayanan da Umma take wa baban Abba yasa na fahinci ya kara komawa ruwa ke nan da wata macen Amma a ina Umma ta samu wanan labarin nai ?
Ban nuna komai ba kamar naji maganan su muka dan ci gaba da hira jefi jefi dasu a falon.
WΓ shegari ne makwabtana suka shigo min yawon sallah kyautan danai masu yai matukar basu mamaki don ga al, ada cicin da drinks kawai zan basu.
Amma sai na hada masu da kudi gar dubu goma kan su yai matukar daurewa sosai ga hakan.
Sai dai da suka fahinci ni yar kasuwa ce suka basar da zancen a ransu amma sunji dadin kyaunta don dama suna da buka hakan.
Zance zamana da su Alhamdullahi sai dai ban yarda sun fahinci komai ba a tare dani.
Sallah da kwana biyu yar sokoto ta shigo gidan mu tana ce min anty hauwa yarta dake auren anan garin bata da lafiya ya.
Shiru nayi ina nazarin fita daga gida bawai ban son zuwa bane kawai dai ina gudun abin da kaje ya dawo ne idan mun fita din.
Tunda na zama fadi ba, a tambayaka ba yanzu dana gani sai na fadi ko ba, a sani ba.
Nisawa nayi nace yar sokoto gaskiya bawai ban son zuwa bane amma kin san matsala ta a yanzu.
Tai tsagal tana cewa wai matsalan iskokanki kikejiwa to ai ba ko yaushe suke tashi ba sai idan da matsala a ciki.
Karfin gwiwan dana samu gurin yar sokoto ne yasa nace to zan shirya mu tafi tare din.
Anty Hauwa bata san da zuwan mu gidan ba sai da mukayi sallama muka shigo ne taji mamakin ganin mu.
Mun gaisa tare da ita muka shiga gurin mara lafiyan tana kwance sharkaf da ita da alama tana matukar jin jikin ta sosai .
Waima cikin an sallamo ta daga asibiti ke nan a hakan da muka samay ta kwamce.
Likita yace idan kwana biyu bata daina jin abinda take ji ba za, ai mata aiki ke nan.
Muna zaune saman kujera two seater dake a cikin dakin muna fuskantar ta.
Idanuwa na kura mata har tsawon wani lokaci ina kallon ta ban san yaya akayi ba na fara wani irin hamma.
Abinda ya jawo hankalin su ke nan a gare ni duk suka tsura min idanuwan su akaina.
Yar sokoto tana ganin haka tamike tsaye tana cewa tashi mu tafi maman Abba.
Amma kamar da dutse take magana haka yasa tai karanbanin kai hannun ta da nufi ta tayar dani mu tafi.
Idanuwa na da suka canza launi ne nadago kaina ina kallon ta idon ya sauya ya koma kamar ba nawa ba.
Nace cikin kakausar murya kada ki soma tabani don baki da tsarki a jikin ki.
Kallon mamaki taimin don idan ba ita da mijin ta ba amma gashi taji a bakina yanzu.
Simi simi taja baya cikin kaduwa hankali a tashe suka tsura min ido sunan maralafiyan dake kwance wanda ko anty hauwa takan manta da sunan ta Adama sai lamin da suke kiranta ne ya amshe sunan nata.
Nace Adama tashi ki zauna zamuyi magana dake ne ta fahinta tsakani da dake.
Mikewa tayi kamar ba ita bace ke ta faman wulle wulle a saman gado ba yanzu.
Nace ina son abani guri da ita ga murysna ya koma tankar na wata balarabiya dani.
Hauwa ki dawo nan dake zamu zauna don ke ce yar uwarta ta jini anan yanzu.
Na soma cewa bayan mun natsu yau rabonki da al, ada watan ki nawa shekaran ki nawa.
Tace wata takwas ke nan danayi al, adana nake gani tace na dauka ko cikine da farko amma naje asibiti sunce ba ciki bane dani.
Hannu na daga mata nace dakata baki da komai sai sakaci irin naku na matan yanzu.
Ko zaki iya tuna tafiyan da kikayi zuwa gida buki a wani kauyen ku kina a cikin al, ada a lokacin?
Ta dan yi tunane cikin yare su na yan lokoja suka juya harshen su ita da anty hauwa na basu amsan maganan su cikin ba yaren nake ji ba dai.
Nace abinda ke faruwa shine zaki tuna jinin da kika bata wani bandaki dashi kika fito don babu ruwan da zakiyi flushing din gurin dashi.
Shiru tayi tana dan kallona can ta dukar dakan kasa nace anan aka samu mai mugun halin data ga wanan abin ranta ya baci har tai maki sihiri akan sa.
Wanan ba ciwon asibiti bane kece da kanki kika jawa kanki matsala bayan kin san cewa jini na al, ada jine abin siri ga mace.
Mata da yawa suna sakaci wurin bari aga jinin al, adan su idan sunayi wanda yanzu duniya ta baci akwai sihirce sihirce da dama da za, a iyayi wa mace da wanan abin.
Zakiga wata pad ko kyalen da take al, ada bata daukan shi da dara bata san cewa yanzu ko dan uwanta na jini zai iya mata illa da wanan abin ba.
Don shi aladan nan da kuke gani wani abune na musan gashi kuma bautane na Allah amma sai kiga mata ayau suna sakaci gurin baein shi a fili.
Tundai diyan ku da suke karatu a makaratina basu san cewa rayuwan su bane a wanan fannin duk yadda kikayi da diyan arna duk da dan bujen da suke sakawa a jikin su baki taba ganin wanan abin nasu don su sun san hatsarin dake cikin yin irin hakan.
Ruwa na bukata abani a wani cup aka debo min addua kawai nai mata nace abata tasha ruwan a gaba tasha nace