Showing 33001 words to 36000 words out of 115099 words

Chapter 12 - Bamu kadai ba ne book Complete by Zainab Makawa .txt

16 Dec 2024

6633

da nake shiga don in tambaye su mukaddarasiyat.
Mun gaisa nakawo tsaraba na basu har da zanin gadon da nake sayarwa nakawo masu yan 1,500.
Suna tajin dadi dayar matar take ce min bamu dade da hiran ki ba fa munzaci kin bar mu ke nan ai.
Nace haba ni daku yanzu ai mun zama yan uwa ko sai dai Allah ya kara dankon zumunci kawai.
Nabasu tsaraba mamaki yai matukar kamasu sosai a lokacin sai wacce nake gani kamar itace babba a gidan take cewa dani.
Amma kina da matukar kirki ke kamar ba biladam ba haliki ko shi yasa babu cutarwa a tsakanin ki da makwabciyar ki don halinki na kirki.
Wanan kalman a kullun yana daure min kai sosai wallahi dayar tace gamu da nisa amma haka kike korin zuwa ganin mu ko yaushe kuma da tarin alheri.
Ranan mijin su yana gida ashe yana fitowa naji kaina yai wani irin uban sarawa don ina ganin siffan shi gabana yai mugun faduwa.
Dayar matar ce ta kirashi wai mu gaisa dashi don sun bashi labari na.
Ya kura min ido na,wani dan lokaci kaina a kasa ban dago ba sai tsoron siffan shi dana gani amma da naji muryan shi yana fadin wanan ai costmer dina ce a kasuwa na dago kaina da sauri na kalleshi.
Sai a lokacin naga ya koma min sak mutumin da nake sarin zanin gado a gurin shi a central market.
Mun gaisai don ya koma min mutum sak wanda na sani nace a raina may yasamay ni ne kuma mutumin da ko yaushe nake sayan kaya a gurin shi har ya dauki yata ya rike min don Nusaiba ta saba dashi sosai.
Nan na sake muka kama hira dashi matan ke nuna mai kyautan da na kawo masu yace ikon Allah.
Kin saye a gurina kuma kin kawo wa iyalina shi yanzu sai yaya ke nan ?
Nai dariya nace ai wanan tsakani da su ne kyauta nan nan ba,a fasa ba insha Allahu.
Yai dariya yace masha Allahu to angode amma yaya akayi kike zuwa aanan garin namu mai nisa haka maman Nusaiba.
Matan sukace lalai malam ashe ka,santa mufa har yau ma bamu san sunan yarta ba sai yanzu muke ji .
Nace lah aiko ba nisa nan ne fa dan nesa da gari kadan yace akwai kayan da zasu shigo sati mai zuwa sai dai ba,a gama odo su bane amma suna da kyau sosai sai mun hadu a kasuwa idan kin shigo zan aje maki su insha Allahu .
Nai mai godiya nace zan tafi in gaida malam sai suke ce min Allah yasa yau ki samu malam a gida don yau jumma,a shi kin san ba,a nan yake sallah ba a makka yake sallah jumma,a idan ya tafi sai dare yake dawowa gida.
Makka kuma nace a fili sukai dariya sukace makka mana zuwa makka aiba wani babban wahala bane balle irin gurin su malam ma.
Ikon Allah nace nidai na mike don in samu malam din don yanzu al,amarin malam ya fara bani tsoro malam ko yakai malam.
Ace mutum yaje saudiya a rana daya ya dawo kuma ai abu ko ya shahara ya zama waliyi ke nan ko?
Nashiga gidan malam da tsaraban manyan zannuwan gado dana kawo masu sukai godiya nace baba fa sukace ai kin makara duk ranan jumma da yafito sallah asuba yake wucewa babban harram yaje yai sallah sai dare idan anyi sallah ishai yake dawowa gida.
Nace kai da na samay shi aidana bashi sako su kan malam Allah ya basu wallahi.
Sai amaryan tace sakon may zaki bashi a fada mashi nace kudi naso na bayar a saro min turare yan saudiya don sunfi araha a can akace sai dai ai na makara yanzu kan.
Mukai hira nace masu zan koma sai sukace na tsaya subani tsaraba kaya ne irin namu na mata da muke amfani dashi amaryan ta debo min masu yawa ita kuma uwargidan tabani wasu irin riguna na yarana masu masifan kyau da tsada wanda da wuya ma asmay shi a kasan nan.
Nai sallama dasu bayan godiya ina tafe ina mamaki gasu talkawa a ina suka samu kudin sayen wanan kayan mai matukar tsada haka wai.?
Malam kuma ace a saudiya yake sallah masha Allah insha Allahu nan da ranan talata zan shigo na gaida malam din da yardan Allah haka nadawo gida da tsarabata.
Da yake ni ba ma,abociya amfani da kayan mata bane nan na,watsar dashi cikin jakar da aka bani shi.
Tufafin dai ne nake ta murna akan su suma dayan gidan sun bani kyautan kayan miya irin namu.

******* ********* *****
Ba,wani zaman dadi a tsakanina da baban Abba yanzu don budurwace ko karuwa oho ta matukar dauke mai hankalin shi sosai a kaina.
Ni ban damu ba sai business dina ya dauke min hankali ga komai yanzu.
Mamaki take bani don yanzu ko a gabana zai sha hiran shi na soyayya zai dinga fadin magana na,so da kauna ba tare da wani shakkana ba.
Ranan ya fito cikin shiri yake fadin shi zai fita sai kamshin turare yakeyi sosai a jikin shi.
Aisha tace Baba ina zaka masalaci yai dariya yace kai Aisha akwai ki da shirmay masallaci da daren nan zan tafi hura ne gun sabuwar maman ku .
Maman mu kuma baba baga maman mu a gida ba ka zauna kuyi hira mana da ita muma muji dadi.
Yace maman ku yanzu bata iya hira ba sabuwa tafita iyawa sosai ina jin su ban tanka mashi ba.
Sai Aisha tace ni Baba ban son sabuwa maman mu nake so yace aiko yarinya dole ki so sabuwa don baban ki yana so shi.
Tace baba please ka zauna da mu mana baba ka kunna muna katun mu kalla don yanzu don bakin hali ko tv ya hana mu kunna a gidan wau muna cin kudin wuta da yawa sosai.
Da har fridge ya hana sai da na jajirce mai don ba zan iya sayen ruwan sanyi ba a kullun.
Yace Aisha bazan zauna ba idan kuma kika damay ni yanzu na bata maki rai don naga mugun halinki daya da uwar ki shegen kishin tsiya dake yar karama dake an koya maki mugun abu.
Sai lokacin nai magana nace ni mugun hali ne dani ashe yace waya kaiki duk kinbi kin fige gurin bakin kishin ki.
Nace wa zanyi kishi karuwa ko yar dadiro zanyi wa kishi nagane may sai ko yaya kaina don may nake kiranta da yar dadiro ko karuwa.
Nace inba karuwa bane kuke taraiya har kake kwana da ita koshi hakan maynene matarka ce ita.
Kamar zai mare ni ko may yagani kuma ya sauke hannun shi idanuwan shi sun kada sunyi ja jajir dasu sosai.
Nace duk abinda kake min wallahi don kan ka Allah yana ganin ka ka kawo mu garin mutane kazo kana kuntata min ni dayaran ka.
Yace wallahi maryam idan zaki tayar min da hankali ne zan mayar daku gida in huta dama kun kai min ko ina,wallahi.
Nace ka mayar damu mana sai may dama ba acan nafi wayo ba kaine kila kake gudun kauye yanzu.
Yace haka kikace nace nace ko yanzu ka mayar da mu mana wayai hasara ba kai ba naga kaga ina kyalewa don biyayya kawai amma shine har zaka kira ni da wai mai mugun hali.
Ya kuta ya dauki keys din shi saman table yafice yana fadin zaki gane kuren ki wallahi nace naga alheri wallahi.
Na juya yaran suna zaune saman kujera sun makure a guri daya cikin damuwa a fuskan su.
Ina jin shi ya na tayar da mota a,waje motar taki tashi yayi yayi motar bata tashi ba .
Ya fito daga motan ya bude ya dan duduba komai normal ya koma ya tayar amma motan bata tashi ba shiru kake ji.
Duk yadda yaso motar bata tashi ba yashigo ciki yana tsuki ina jin karuwan tana bugo mai waya ya dago yana fadi hanna yaya ne tace naga shiru bakazo ba har yanzu.
Yaja tsaki yace wallahi motatace take ta bani matsala taki tashi wallahi ban san may ya samay ta ba
Tace bazaka shigo motar haya bane yace haba hannan motar haya tun daga nan har barnawa.
Tace ba sai ka kwana an nan ba yace aiki fa da safe sai ta kashe wayan kawai.
Shima tsuki yaja ya dan dago inda muke ya dan kalle mu cikin jin haushi yaran suna kallon shi.
Yace a hasale may kuke kallona munafukai kawai gurin ku ya cika ban fatiba din.
Dariya nayi kawai daga inda nake zaune yace ai kyayi dariya tunda ban fita ba yanzu.
Nace waya hanaka fita batace kaje can ka kwana ba ai sai ka shirya kaje can din ka kwana tunda ka saba zzuwa ka kwana da ita a can.
Yace na saba sai may tinda ke keda kafata ai saiki jani ki kaini nace ban saba kaika aikata zunubi ba don haka bani zan kaika ba ma yau.
Kafin ya bani amsa sai ga kiran Hannan ya kara shigowa wayan shi again yana dagawa tace kataso ne ?
Yace ban taso ba don dare yayi tace kai dai na gane shigiyar matar ka ta hanaka fitowa yau ke nan.
Nace kece dai shegiya karuwan banza kawai kona hana shi na isa ne ai mijina nane fa.
Sai ya kashe wayan dip yace a hasale maynene haka maryam dake take waya koda ni ?
Nace dakai dai take wayan amma ta sakoni a ciki shine na bata amsa ni kuma daidai da maganan ta.
Nan mukai ta sa insa dashi a karshe ya fashe haushi ga yaran yace muna fukai ku tashi kuje ku kwanta .
Suka shige dakin su tara saura nima na gama abinda ya dace nayi na,shige na kwanta gurin su, na barshi nan falo suna ta rigima da Hanan din.
Washe gari abin mamaki yana tayar da mota sai kawai motar ta,tashi ba tare da,wani matsalan komai ba.
Yai mamaki jiya ba yadda baiyi da ita ba amma motar taki tashi mai a lokacin.
Ina gama shiri na wuce banki na ciro kudin da aka turo min na kaya na nufi kasuwa don sarin kaya.
Shagon mai bedshet na nufa muka gaisa na tambaye shi iyalin shi yace suna lafiya.
Ina cikin zabar kaya don zanuwan da ya shigo dasu suna da matukar kyau sosai wallahi.
Ina tsaka da zaben kaya wani yaro matashi ya shigo shagon yana magana kan wasu kaya da mai shagon dake rike da Nusaiba a hannun shi nace wanan kudin su nawa ne malam ?
Sai matashin ya,juyo ya kalle ni yace a,a ba matar nan nagani a garin mu ba ranan jumma,a maishagon yace itace malam maryama ke nan ai.
Nace da sauri malam.ina kasan sunan sai yai dariya ya basar yace kudin su ya haura wanda na,saba kawowa gaskiya.
Nace malam don Allah a ina kasan sunana yace ni yanzu ai har gidan ku na sani harda mahaifin ki nace kai na mayar da hankalina gare shi.
Yace ke diyar malam baba SULAIMAN bane ko ?
Nai murmushi nace malam kan a garin nan yanzu shine Baba na,wallahi.
Matashin yana tabina da kallo cikin mamaki yadda muke ta hira da mai shagon na gama zabe yai min kudin su na biya sai dai idan na biya duka kudin na bai kai ba gaskiya.
Don bazan iya karasa sauran sayayyan da nake sonyi ba nace malam sai dai na rage kayan gaskiya don ina gani kudina basu kai wanda nake son saya ba.
Yace duba dai malama insha Allahu zasu kai idan ma basu kaiba sai na baki bashi na biyo ki.
Nace a,a malam bazanci bashi ba iya kudina zan dauka na bude jakata na ciro kudi sai naga a idona kamar kudin ya karu yawa.
Nakirga kudin shi duka na bashi nabar kayan da Nusaiba nace zan shiga dayan shagon na saro kaya.
A dayan shago na sai abun da nake bukata nafito zuwa shagon turare na gaida mai shagon zan fara saye yace min malama ga sako ance nabaki tun shekaran jiya yake aje a gurina baki zo ba.
Na dubi katon ledan da take miko min wanda yake shake da turare nace sako kuma ?
Yace eh sakonki ne baba malam yace na kawo maki wai abinda kikace ya sayo maki a saudiya ne ko wa yan nan zasuyi maki?
Yace sauran bayani sai idan kun hadu zai maki nace baba malam dai na tsibiri kake nufi yace shi malama na ke nufi malama na karba ina cewa nagode yace sai dai kuma baida lafiya gaskiya yana fama da ciwon kafa sosai.
Nace subbahanallahi aiko zan tafi na gaidashi yace yana da kyau hakan gaskiya.
Maimakon na wuce sai na,shiga shagon islamic chamist nake tambayan maganin ciwon kafa na islamic.
Na muma tuna babana yana bayar da magani ciwon kafa ai a gida don haka zan mashi waya naji.
Na kwaso kayana a gajiye na dawo gida na samu baban su Abba ya dawo a lokacin ya bini da kallo tare da kallon kayan da,aka,shigo min dasu niki niki cikin gida.
Yace wai ke Maryann ina kike samun kudin sayen wanan kaya haka masu yawa.
Nace Allah ne ya bani daga,aro ya zama min alheri yanzun ma har na biya wacce ta bani jarin kudin ta nawa nake juyawa kawai.
Yace dama ke nake jira kudi nake so aro har zuwa wani sati na mayar maki nace kudi kamar nawa yace dubu hamsin kawai nake son aro zanyi amfani dasu ne yau din nan.
Nace anya ina dasu bari dai na duba nagani ina dubawa na samu akwai su na kirga na miko mashi ya karba tana sauke ajiyan zuciya.
Jin waya yasa na bar gurin na shiga ciki na aje jakata na kewaya ina fitowa naji yana cewa nace ganinan zuwa na kawo maki mana.
Fitowa falon yayi daidai da mikewan shi zai fita nace ina kuma zaka yace zama kike son nayi maki a gida dama.
Ko na zauna wani abu zakiyu min ke dake guduna yanzu ma har yakai kofa nace Baban Abba ya juyo.
Nace wallahi udan kaima karuwan ka amfani da kudina ban yafe ba.
Yace don kin ara min kudi shine kuma zaki saka min doka a kansu ina ruwan ki da abinda zanyi da kudin kuma ?
Nace nidai na fada maka wallahi ko yafice yana cewa wanan kuma matsalarki ce ai.
Bai tsaya ba sai gurin hannan ya nufa yaba ta dubu talatin daga cikin kudin ta amsa a wulakance tana cewa talatin kawai zaka bani nidake son sittin a gurin ka.
Yace tayi hakkuri tai maneji dasu ko su da kyat ya samo su don yanzu damane babu harka sosai yanzu.

****** ********* ******
Yana fita makwabta da suka gane ina sayar da kaya yanzu suka cika gida suna dubawa sai lokacin ne na bude ledan da Baba malam ya aiko min dasu.
Turaren da na gani a ciki sun bani tsoro don masy matukar tsadane da kamshi sai manya zasu iya sayen su.
Don ko a shago ban iya sayen ko daya a cikin su idan na tafi sarin kaya ga,wa yan nan sun cuna mana shagon kyau da kamshi sosai.
Nan yar sokoto take cewa zata kaini gurin wasu yan garin su akwai buki sai na nuna jayan acan don manyan mata ne zasu hadu a gurin.
Naji dadin hakan sosai nai mata godiya washe gari ko nace zan tafi in raka yar sokoto gurin buki na kai kayana bai hanani ba yabarni na tafi.
Kayan kan sun karbu sosai wallahi kusan duk a gurin na rage wasu wasu sukace zasu zo har gida su duba su gani.
Ban tsaya ba na bar mutumiyar a can na dawo gida abina ina murna nan na bugawa mai shago waya akan ya aje min sauran washe gari zan zo na dauka.
Washe gari na shirya na tafi kasuwa sai dai ina son sai na tafi gurin Baba na ganshi idan na dawo sai na tsaya kasuwa.
Mota na shiga kamar kullun sai gurin baba malam sai dai yau ba masu karatu kamar kullun na shiga cikin gida kai tsaye.
Na gaisa dasu na basu tsaraban kankana da lemon da nazo dashi nasu daban wanda na rikowa babana daban.
Nashiga gurin shi muka gaisa sai dai gaskiya yana jin jiki nace baba ashe kuma ba lafiya haka ?
Yace wallahi kin san yaran bani adam basu da hankali kadan ne daga cikin ku masu hankali sune wallahi duk kaucewan da nayi sai da yahau kaina da mahakaciyar ku watau (mota) yabi takaina ya wuce.
Yace shiyasa wallahi idan an hadu da mash rashin imani a cikin mi suke daukan mumunan hukunci a kanku din su rama ketan da akayi masu.
Abin tausayi yarana sun bi yaron don su dauki fansa duk dana hana su amma sai suka samu ashe wai sauri yakeyi zai tafi asibiti uwar shi bata da lafiya nace su barshi Allah ya bata lafiya.
Nace amin baba sannu baba na sa hannu a jakata na dauko maganunuwan da nazo mashi dasu na bashi yace ikon Allah mahaifinki ne ya aiko min dashi ko ?
Nai mamaki yadda yasan hakan nace eh Baba matarshi ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login