Showing 27001 words to 30000 words out of 115099 words
Chapter 10 - Bamu kadai ba ne book Complete by Zainab Makawa .txt
koda naji sai dai kawai na dake abina.
Maganin dai da malam tsoho ya bamu da,ban san sunan shi ba balle sunan kauyen ban fasa yi ba ina kanyi nida yara har da,baban yaran na hada mai a,man shafin shi bai sani ba yana,shafawa.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
[10/27, 10:48 PM] Zuraiyah Zuzu ๐: ๐ฉโ๐ฉโ๐งโ๐ง ๐จโ๐ฉโ๐งโ๐ฆ
BAMU KADAI BANE A,,
๐จโ๐ฉโ๐งโ๐ฆ ๐ฉโ๐ฉโ๐งโ๐ง
๐
Izuwa yanzu Nusaiba ta samu lafiya sosai a lokaci don idan ka ganta bazakace tayi irin wanan ciwon ba a baya yadda ta mulle tai kiba abinta sosai da ita.
Komai na fitar a raina ban tsoron komai yanzun saina Allah da Annabinshi kawai.
Nafitar da zancen wani abin tsoro a gidan cikin raina gaba daya yanzun haka.
Abinda ke damu na shine rashin sanin wacece matar da ta taimaka min zuwa kauyen nan ?
Ban san ta ba ban kuma da nomban wayan ta balle muyi communication da matar a waya.
Haka bai hana ni ci gaba da shirin abin da zan kaiwa mutanen arzikin nan ba da nasha ruwa a gidan su a kauyen sa ta kaini.
Don idan na masu alheri har matar ta samu labari tankar itace naiwa alheri din a hannunta.
Don haka ina ganin saura kwana biyu mu koma kamar yadda malam baba ya umurce ni na,dawo da yarinyar bayan sati biyu inda yake ya kara duba lafiyan ta.
Ganin ta samu sauki bai sa na kasa a gwiwa ba gurin komawa kauyen don in kaita akara dubata.
Haka yasa na zabo omo clean maya har guda hudu sai sunki sabulun wanka parked hudu na duba cikin kayana na na zabo turaren Oud mai kyau da kamshin gaske sosai na jefa duk kayan ga wani handbag dina babba wanda zan fita dashi da safe idan Allah ya kaimu.
Washegari tun da safe na tashi na fara aiyukan gida don na gama da,wuri na fita ko zan dace na samu matar nan da ta,taimaka min ranan.
Baban Abba yana karyawa yake ce min ba zai samu saukeni asibiti ba don haka na shirya natafi ni kadai don ta dan makara zasu fita zuwa operation cikin daji ta barauniyar hanyar da,ake smogal ciki.
Ban ji haushi ba yau sai ma dadin da naji kawai don zan samu yadda nakw so idan na fita ni kadai din.
Na gama tare da rufe gida na nufo aaibiti can a bakin get na hango inda ake sayar da goro.
Masu kyau mayan farare kursa kursa na zaba na dubu daya aka daure min a leda .
Maimako na tsaya inda tace min sai na dan tsaya wani dan guri nisa kadan shiru babu alaman motar kauyen gurin.
A hankali na gyara goyon Nusaiba na taka zuwa daidai inda muka tsaya,da ita a ranan.
Sai ko ga mota na gani irin na ranan na tsayar dasu tare da fadin suna kauyen da zani .
Mun dan taba tafiya muka kawo garin mutanen cikin motar sai kallon mamaki suke min amma ni ban damu da yanayin kallon da,suke min ba.
Ina sauka na biya kudi na gyarawa Nusaiba goyo muka fara tafiya don ban manta da hanyan da muka bi a ranan da abokiyar tafiyana.
Wanan gidan yan uwan nata da muka fara isa sukai mana taron arziki shi na shiga da sallama gaba daya suka sako idanuwan su suna mamakin sake gani na agidan su da,sukayi.
Nagaishe su daya bayan daya tare da masu yaya bayan robon mu ranan sukace Alhamdullahi.
Suma suka tambaye ni yaya jiki tare da kokarin karban Nusaiba da na sauke bayan na zauna saman kujera.
Nasan bazata yarda ba don kiuyar tsiya gareta bata yarda da kowa in ba niba.
Matar da tafisu fara,a a cikin su wace taso karban Nusaiba tace yau ina Mukaddarasiyya ?
Nace ai tun ranan bamu kara haduwa da ita ba yanzun haka ina son ganin ta amma ban san inda zan samay taba kuma.
Cikin fara,a da yar dariya matar tace aiko bazaki sake ganin ta ba sai Allah inda Mukkaddarasiyya ce.
Nafito da dan tsaraban da na kawo masu ina fadin kuyi hakkuri da,wanan don Allah baida yawa aiwa yara wanki biscuits da sweet arabawa yaran shi.
Sunji matukar dadi da abinda na kawo masu suna min godiya idona yana akan kayan da suke aiki dashi wanda ya banbanta matuka da irin wanda muke amfani dashi dana sani.
Bayan na dan huta namike tare da goya Nusaiba ina cewa zan tafi naga malam babba ya duba yarinyar .
Har kofa suka rakoni suna min godiya tare da min fatan alheri ina cewa ai insha Allahu idan na sake dawowa zan kara shigowa mu gaisa da su.
Ina tafe yan garin suna bina da kallo cikin mamaki har nakai makarantar malam baba inda na samu yara ba iyaka masu daukan karatu a gurin shi.
Cikin gida na shiga ban tsaya waje ba nai sallama matan shi a zaune na samay su suna hira.
Suna ganina suka shedani ,a,a maraba da bakuwar mukkaddarasiya yau kece a gidan namu haka ?
Suka bani abin zama muka gaisa dasu suna tambayana yaya jikin Nusaiba nace jiki Alhamdullahi.
Nafito masu da abinda nazo masu dashi na basu sunyi mamaki matuka da wanan alherin da nazo masu dashi.
Wani dan lokaci muna fira jefi jefi dasu akan al,amarin mijin su da irin baiwan da Allah ya bashi na sanin magani kala kala.
Wani yaro kyakyawa fari ya shigo yace malam yace bakuwa tashigo a tare muka shiga da yan matar malam din dauke da tsaraban da na kawo masu zata nuna mai.
Mun gaisa matar da mashi yaya bayan rabo ya amsa da Alhamdullahi yana tambaya yaya jikin Nusaiba din nace gata malam tun rana da na fara magani har yau bata kara kwanci ba.
Matar ta nuna mai abinda nazo masu dashi yace ikon Allah yar gidan Amina tanan kuma kika fito min lalai halin ki na alheri ne dole mukkaddarasiya taji tsoro akanki.
Yace wa matar da fatan kun yi godiya ko tace malam mungode ai don bamu san akwai masu halin mutunci haka ba a zaton mu?
Tana fita na ciro goro da turaren da nazo mai dashi nace baba ga wanan ba yawa ayi hakkuri dashi.
Ya kura wa abinda nakawo mai ido yace may yasa kika wahal da kanki haka akaina ?
Na dukar da kai cikin murmushi da ladabi nace baba albarkan ka nake nema yasa nai hakan.
Yace tona gode ubangiji Allah ya albarkaci rayuwan ki duniya da lahira yace miko min hannun ki nan na mika mai ba tare da ya rike hannun ba ya runtse idanuwan shi kamar yana min addua na dan tsawon lokaci can yace masha Allah,
Allah ya kara tsare muna ku bakiya daya yafadi tare da mikwa Nusaiba hannu sai kawai naga yarinyar ta nufe shi.
Da fara,a a fuskan ta ya dauke ta yana mata wasa tare da bin jikinta tana shafa mata magani.
Yace min ba dai aljan ko mutum ba Fatima akan diyan ki tsakanin ki da su sai alheri ba dai sheri ba kan .
In har dai kinyi masu abin da na baki a baya ki masu insha Allah ba abinda zai faru daku da yardan Allah.
Yabani wasu yan abubuwa yace naje dasu gida tare da fada min yadda zanyi dasu nai mashi godiya har zan daga yake ce min banji kin min tambaya irin na bani adam ba ?
Na koma na zauna ina murmushi nace baba sai idan ka fahintar dani don sani a gare ku yake Baba.
Yace Fatima ke bakya sana,a ne irin ta neman kudi?
Nace cikin kunya baba bana komai yace baki ra,ayine ko may nace ina da ra,ayi sai dai ban san yaya zanyi ba ya miko min wani dan kullin gari yace karbi wanan.
Hannu bibiyu na mika na karba yace tun anan gabana ki diba ki shaka shi sai ki dan tauna kadan sauran ki murza a hannuwan ki har zuwa habar hannun ki.
Yadda yace haka nayi yace to shafe fuskan ki da hannayen ki nayi yadda yace min yace ubangiji ya albarkace ki.
Nace amin baba tace ke kadaice a gurin mijin ki zan baki wanan amma bazan fada maki amfanin shi amma zaki gane daga baya.
Namike ina cewa baba na gode zan tafi sai na kara dawowa yace yana da,wuya ki dawo ki samay ni kuma amma duk sanda kike da wani bukata akaina zaki iya kiyastawa a ranki kamar kingani a gaban ki da yardan ubangiji zanji bukatan ki fatima.
Ke abin tausayawace a gare mu don kina da kima da mutunci ga duk wani malami indai yakai malami a jinsin mu.
Mahaifiyar ki ta wahala sosai agurin bakaken jinsin mu amma bata yarda ta kauce ba kamar yadda suka bukaci da tayi masu biyya akan ta kauce su taimaka mata.
Karfin addinin ta yasa ta ki kauce wa bukatan su ta kommace ta mutu da ta kauce masu haka sukai ta,wahal da ita har Allah ya karbi ran ta ta tafi kowa ya huta.
Sauran bayani watarana zan maki yadda zaki fahinci may ya faru da ita.
Jikina yai matukar sanyi jin yadda mamana ta wahala a hannun wasu muggan mutane don bukatan su a kan ta.
Nai sallama da malam na shiga gidan shi nai sallama da matan shi sukaita min godiya na barsu na tafi.
Nai mamaki danagan ni a bakin asibiti sai ban damu ba na tare taxi aka dauke ni drop sai quarters din mu na dawo a gajiye dani .
Tunda na dawo ban fadawa kowa ga abinda mukayi da Baba malam ba na bar zance kawai a raina.
****** ********* ******
Ina zaune yara sun fita zuwa islamiya don sunyi hutun boko a yanzu Anty Hauwa ce tashigo gidan mu muna zaune muna hira,da,wayan ta a hannu tana dan kallon abubuwa a cikin wayan.
Can take ce min kai maman Abba zoki ga wasu bedshet haddadu masu kyau ina dubawa sukai matukar shan jinin jikina naga may zai hana nima na fara sana,an irin su tunda kayan mata ne kuma abin amfani.
Nace gaskiya da zan samu kudi zan gwada sanan su insha Allahu kila na dace a kansu sanan ya karbu.
To amma kuma kudi fa kudi sune matsalana yanzu ina zan samu kudin yin wanan sana,an nawa.
Har mukai sallama da ita sai tunane nake a ina zan samu kudin da zanyi wanan sana,an da nake son yi yanzu ga zancen ya matukar tsaya min a raina.
Sai zancen mu da malam Baba ya fado min a rai na son nayi sana,a nima na tsaya a kafana.
Nasan halin baban Abba a gurin kudi idan bashi yai ra ayin bani kudi don kan shi kudi bai banbaruwa a hannun shi ko kadan.
Kyautan shi dani dubu daya ne dubu biyu baima taba bani dubu biyar ba a rayuwan mu cur.
Haka dai na yanke shawaran cewa zan daure na tambaye shi na fada mai manufana nason fara sana,a a gidan.
Bayan ya dawo daga gurin aiki muna zaune yana hira da yara ina yan aiyukana a gidan.
Sai da na gama komai na samay su a falon ina cikin atamfan wax da akai min dan dogon riga mai sharf dashi.
Na zauna tare da fadin wai ya dan kallo ni yana cewa may kikayi da kike wash haka nace tunfa safe nake tsaye a gidan nan yanzun ko nagama ai dole na dan huta ko ?
Murmushi yayi yace kinji dadin ki ke wallahi kina zaune gida baki baki baki fari amma har kina fadin wai ke kingaji a haka.
NNace yauwa Baban Abba dama ina son fada ma wallahi sana,a nake son na fara na zannuwan gado sai na sara anan na,turawa anty Lami dashi can gida.
Yace kina da kudi ke nan ashe nace ina naga kudi kai dai nake so don Allah ka ara min please.
Take ya daure fuskan shi yace banda kudin da za,a salwanta Maryam kada ma ki soma wanan zancen don bazan bayar ba.
Nasan tunda ya fadi haka har cikin zuciyar shi yake maganan nan kuma ya hau fada yana ta masifa inda yake shiga ba nan yake fita ba.
Shiru nayi ina sauraren shi har tsawon wani lokaci naja bakina nai shiru kawai.
Sakawa nake ina warwarewa ina zan samu kudi koda nace a sayar da kayan dakina nasan ba,wasu kudi sosai zasuyi ba kayan.
Bayan kamar kwana biyu ina gyaran daki naga kudi a dakin yan dubu dubu masu yawa nai mamaki yadda yabar kudi hakanan bai fada min ba na boye.
Sai da ta dawo da yamma nake cewa yaya akayi kabar kudi a fili haka baka fada min a boye ma ba duk da dai babu maishigowa gidan amma kuma komai yana son siri aiko ?
Yace cikin mamaki kudi wasu kudi kuma maryam gaskiya ni ban bar kudi ba anan gidan.
Na mike na shiga daki na kwaso kudin nace gasu fa wanan nake magana saman mirror na samay su fa.
Ba kudina bane na bashi amsa da fadar haka.
Yace maryam na fada maki ba kudina bane wallahi ki ajesu kila zaki tuna wanda ya baki ki boye mai.
Nace ni wa zai ban kudi boyo kuma gidan nan bayan kai ka kuma ce wai banaka bane to na waye ?
Kamar yadda yace din boye kudin nayi guri mai kyau ko zai zo ya tuna daga baya in bashi abin shi.
Har yara sai da na tsure su na tambaye su suka rantse min ba nasu bane su basu ma san komai ba akai.
Tsoro ya kama ni nace kodai sun fara irin harkan su John ne ban sani ba haka nakan raba dare ina,adduoin tsari akan yaran gaba dayan su ko zanga wani alama amma babu sign din komai a kansu.
Bayan kamar wata daya na kara fito mai da zancen kudin yace shifa ba kudin shi bane bai san may su ba.
Amma na barsu zai karba idan ba,a san ko na waye ba nace mai naji kawai.
Ina zaune inda nai sallah magariba sai faman tunane nakeyi ba wanda ya fado min a rai naje na tambaya kan zancen kudin sai Baba malam kawai don haka na yanke shawara zan tafi gurin shi na tambaya akan kudin.
Cikin dare muna barci ne sai ga Baba malam nagani a mafalki na ya shigo falon mu a cikin fararen kayan shi cikin kamala.
Na rasa inda zan shi na kawo mai ruwa yace min ya gode a koshe yake yana rike da,sanda a hannun shi irin na manyan mutane.
Yarana yake bi da kallo daya bayan daya yana murmushi yace maryama kin tara zuria masu albarka anan Allah ya tsare maki su.
Nai mashi godiya yake cewa maryama kince kina son yin sana,a zanin gado shine na baki jari kiyi kuma gashi naga har yanzu baki fara ba wanan kudin da kike tambayan ko na,waye bana kowa bane nakine.
Nine na baki su saboda Allah don ki fara sana,a dasu na bude baki zanyi magana sai naji an bude kofa ba kowa nagani ba sai wanan matar da ta kaini gurin shi da farko namike da fara,a cikin jin dadin ganin ta zan tare ta sai ta wuce ni zuwa gurin shi da fara,a tana cewa la Baba yau kaine a gidan namu da kanka.
Yanunani da yar yatsa yace ga wace ta kawoni gidan nan nazo ne ba dadewa zanyi dama bayani ne nazo nai mata don na turo a kawo mata sako amma bata fahinci ko daga ina sakon yake ba.
Ta juyo gare ni tace wanan abokiyar zamanane baba tana yawan takura min sai dai halinta yana da kyau don tasan hakkin makwabtaka.
Tsohon ya mike yana cewa dake da ita duk jikokina ne don haka ku sulhunta kanku kafin ta baci maku yakai kofa ban samu cewa komai ta juyo yana min murmushi ya fice daga gidan.
Najuya inda take a tsugune don in mata magana naga wayau bata gurin kuma ba alamanta ma agidan lokacin.
Nan suka barni ina mamaki yau malam babane har a gida na da kanshi to ya gwada msi gidana ?
Matar nan mai mutunci ne tafadi min a raina nace tace makwabciyata ce ita amma a ina .
Zubur na falka daga barcin da nayi ama sai kamshi nakeji irin na turaren malam da nakanji idan naje gurin shi.
Zufane ta fara karyo min ta ko ina sai yau ne karo na farko danaji tsoron abinda ke faruwa dani ya kamani.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU[10/27, 10:55 PM] Zuraiyah Zuzu ๐: ๐ฉโ๐ฉโ๐งโ๐ง ๐จโ๐ฉโ๐งโ๐ฆ
BA MU KADAI BANE A,,,,,
๐จโ๐ฉโ๐งโ๐ฆ