Showing 39001 words to 42000 words out of 115099 words
Chapter 14 - Bamu kadai ba ne book Complete by Zainab Makawa .txt
Maganin mahaifinki ne yace ki hanzarta kaiwa mahafinki ya sha da kunu safe da yamma insha Allahu zai samu saraka sosai ga abinda ke damun shi.
Sai kuma idan mun sake haduwa kinji kaunata ina tare dake a koda yaushe kada ki damu da nema na don muna tare dake akoda yaushe yar uwata kuma ke aminiyata ce don kina taimaka min sosai ta yadda baki tsanmani ba.
Takai kamar taki biyu ta juyo tace min sana,an ki insha Allahu zaifi nan bunkasa nan da wani dan lokaci kawai sai naga ta bace min.
A daidai lokacin ne naga kamar na falka daga barcin da nakeyi sai dai nayi zufa sosai a lokacin.
Zubur na mike zaune daga kwancen da nake duk na sharfa wani irin zufa a jikina.[11/4, 10:17 PM] Zuraiyah Zuzu ๐: ๐จโ๐ฉโ๐งโ๐ฆ ๐ฉโ๐ฉโ๐งโ๐ง
BAMU KADE BANE, , , , ,
๐ฉโ๐ฉโ๐งโ๐ง ๐จโ๐ฉโ๐งโ๐ฆ
1โฃ4โฃ
Aslamu Alaikum yan uwa da abokan arziki ina mai sanar maku da fitowan sabon littafina da zan fara typing na kudi mai suna maricin kan dutse ko Rayuwa nan da sati mai zuwa da yardan Allah insha Allahu sai dai na kudine shi ba free bane shi.
Washegari na tashi har naso saka zancen mafalkin da nayi a raina amma sai na share zancen kawai na shiga harkokina nayau da kullun kamar yadda na saba yin abina a gidan
Sai zuwa karfe sha daya na samu kaina a lokacin na kamala komai da nake bukatan yi a gidan sai hutun da nake bukatan yi kawai a raina.
Wanka nayi don nusaiba ta dade da yin barci a lokacin na riga nai mata nata shirin ko.
Bayan na fito daga wanka na zauna a gaban mirro ina shiri hankalina a kwance.
Har na kusa kammalawa ne idona yakai akan wani kulin magani dake a saman mirro na aje.
Kallon mamaki nakewa kullin don ban san wa ya aje min shi ba a gurin kuma ban san ko na may ye ba shi.
Dauka nayi na bude sai naga magani ne irin na fargajiya a ciki nikakke dashi.
Na mayar na kulle shi tare da kokarin ajewa a gurin da nagan shi aje don a zatona killa na baban Abba ne maganin.
Take mafalkina na daren jiya ya fado min a rai inda na tuna a daidai gurin da mukkadarasiya ta aje min kullin maganin da baba malam yaba da sako nakaiwa baba yai amfani dashi a gida don warakan ciwon shi.
Gabana ne yai wani mugun faduwa a lokacin tiryan tiryan abinda ya faru a cikin mafalkin yake fado min a rai na.
Sai lokacin naji kamshin baba malama ga dan kullin dana gama daurewa wanda har hanaye na suma kamshin sukeyi a lokacin.
Wani sabon faduwan gabane ta kara ziyartan zuciya na na mike da sauri zuwa falo inda Nusaiba take kwance tana barcinta hankalin kwace na dubata babu abin da ya samay ta nagani.
A cikin tsoro nagama duk wani abinda zanyi a gida na goya yarinyar ta tare da saka hijjabina na bar gidan.
Sai gidan anty hauwa na nufa cike da tsoro a zuciyata gashi ina son fada mata amma kuma na kasa kamar andaure min bakina nake ji.
Allah dai ta taimakeni ban furta mata komai ba ga halin da nake ciki har yara suka dawo muka koma gidan mu cikin tsoro ni da yaran gashi ranan ba zuwa islamiya gare su.
Suna cire uniform nabasu abinci sukaci Aisha tana gama cin abinci ta nufi back yard din inda ta saba wasan ta ita kadai.
Nafito falo na samu Abba sai Nusaiba dake wasa a gefe daya shi kuma yana kallon katun a tv .
Nace ina Aisha ya nuna min hanyan back yard da hannun shi har na fara hanya na kira ta sai tunanen abinda aka fada min ya zo min arai na.
Na ba ita kadai bace take wasa a gurin tare da sauran yaran da mu bamu ganine take wasan.
Tsayawa nayi daga kofa ina kallon yadda tai zufa ita kadai sai surutu take zubawa jefi jefi ita kadai a gurin tana faman jera kayan wasan ta data tara wanda ni ban ma san lokacin da ta tarasu haka ba a gurin.
Kima ban taba kai hankalina ga sanin may takeyi ba ma sai yau da haka ya kasance a mafalkina.
Dole ban da yadda zanyi na juya na koma falo cike da farga na zauna sai dai hankalina yana gurin yarinyar tunda sunce basu cuta muna su.
A haka ranan na wuni a cikin damuwa da al, amarin dake damuna a raina ga waya ana bugo min kan ciwon mahaifina dake damun shi a gida.
Sai da na idar da sallah magariba ne zancen kudin da tace nawa sun karbo min yafado min a raina na mike da sauri zuwa daki don na tabbatar da zancen da tai indan gaskiyane ko rudin kaina ne kawai nakeyi.
Jakan farko dana duba babu komai a cikin sa hakan yasani sake ajiyan zuciya nasan mafalkine kawai hakan.
To zancen maganin da nagani fa dazun saman mirro na wanda har a lokacin yana aje gurin da yake ban kawar ba.
Ina jiran baban Abba ya dawo na tambaye shi ko nashi ne ya aje ban sani ba a gurin.
Har najuya nakai kofa sai zancen jakar da na dauko wa baban Abba kudin a ranan ya fado min da sauri na juya inda jakar tawa take ajiye.
Ina budewa kudine a ciki kamar yadda suke a farko suna daukan ido nafitar da sauri na kirga su cif dubu darin su yadda na bashi a ro a baya.
Ban san lokacin da nakai zaune ba a bakin gado ina fadin na shiga uku ni maryam wanan magana ya tabbata ke nan gaskiya ko?
Hankalina yai matukar tashi wanan ranan nakeji kamar na bude idona na ganni a garin gidan mu inda muka fito yafi min wanan bakon ala, amarin tashin hankali da na riski kaina a ciki a garin mutane.
A haka muka kwana a gidan ga baban Abba yanzu halinshi sai a hankali ba damuwa yayi damu ba balle ma yasaurare ni.
A cikin barci nai mafalki da uwargidan malam matar da nake kallon ta a matsayin mahaifiyata a gari tana kwantar min da hankali akan kada na saka tsoro a raina suba masu cutana bane sun fada min.
Da suna da niyar cutamin da sun dade da cutata min ko tun zuwawa na farko gare su.
Nan dai ta kwantar min da hankali tai min sallama ina falkawa na tashi da ciwon kai haka na mike na dauro alawa duk da tsoron da nake ji nakai kuka na ga Allah tare da neman tsari dani da yayana a gareshi.
Wanan sallah danayi yasa na dan ji damuwan dake damuna ya rage min a raina sosai har na samu barci mai nauyi ya dauke ni a lokacin.
Sai washegari da yamma baban su Abba ya dawo gida sai dana bari ya huta yaci abinci naga bashi da niyar fita da daren ranan.
Nasamay shi da zancen maganan ciwon mahaifina dake cikin wani hali a gida.
Fada ta hauni dashi don may ban fada mashi ba a waya na sanar dashi halin da babana yake ciki.
Yace yanzun sai aga rashin hankalin shi na rashin buga mai waya ya tambayi lafiyan shi.
Don ba za a san cewa bai gida bane a lokacin sai a ga kamar bai damu bane kawai da halin da yake ciki a can.
Ni dai hakkuri na bashi kawai mutumin da kirikiri zan kirashi yanzu yaki daukan wayan idan ma ya dauka wani lokaci fada ne zai hauni dashi kan cewa yana tsakiyan aikin shi na damay shi da bakin kirana.
Nan dai na bashi hakkuri tare da bukatan wani sati yara zasuyi hutu ina son zuwa gida na duba lafiyan mahaifina.
A takaice ya bani amsa da sai yayi tunane akai kafin naji amsa ta.
Haka na zauna tsawon kwanaki da zullumi iri iri a raina na halin damuwa da abu biyu ciwon mahaifina da anty lami ke cewa nayi kokari na shigo na gan shi da kuma zancen matsalan gidan mu na bamu kadai bane a gidan.
Tare muke da mutanen da bamu gani kuma bamu san a ina suke ba ma gidan su.
Matsa mashi nayi sosai akan zancen tafiyana wanda na tayar mai da hankalin shi haka yasa ya yanke cewa na shirya idan anyi hutun sai mu tafi.
Amma ba lalai bane shi ya tafi tare da mu sai dai daga baya zai zo idan zamu dawo ta dauke mu idan hutu ya kare na yara.
****** ********* ******
Can gida kuwa Umma yakai ta tayar da hankaln ta har yakai ta fara zuwa gurin bokaye da malamai neman taimako wai na sake mata dan ta tillo daya yanzu sai abinda nace yakeyi.
Haka take zuwa guraren malaimai wai a taimaka mata dan ta tadawo gare ta.
Wasu su fada mata gaskiya cewa ba laifina bane halin shi daine ya sake nima hakkuri nake dashi a hakan.
Wasu kuma suci kudin ta ba biyan bukatan da take so a gare su don ita takai kan ta ai.
Nikan na shirya tsab daga sayen tsaraba tare da kayan da zai tafi dasu na sayarwa na a can idan na tafi don yanzu gaskiya Alhamdullahi ina da rufin asiri sosai akan harkan sana, ata da nakeyi.
Basai na jira yai min komai ba don Hanna ta yi gaba da hankalin shi akan komai nashi.
Saboda bata daukan abinda wasa akan shi kamar wani mijin ta can har shige shige takeyi don ta kara samun kan shi kawai.
Wani guri idan ta tafi da sunana zasu ce mata tayi hankali da ni don idan ta matsa a kaina zata iya rasa rayuwan ta gaba daya don ba a banza nake ba.
Haka yasa ta dan ja da zance na sai shi kawai take ta kokarin taga ta kamashi ta ko ina ta mallake shi.
A kwai gurin wani malamin da ta tafi yana dubawa ya dago kai da sauri yace mata ke kin ko san da sunan wace kika kawo muna maza ki tashi ki bamu guri kada ki shafa min laifi.
Idan kuma baki bari ba duk abinda ya samay ki anan gaba wallahi ki kuka da kanki don ma kawai an raga maki ne dayanzu sai buzun ki wallahi ko.
Nan dai ta dawo gida cike da tunanen shi ita wanan matar ta Aliyu wata irin mace ce haka shu, uma da kowa ke tsoron yin aiki akan ta ne wai.
Da yazo gurin ta take bugun cikin shi cewa wai matar ka halan waye baban tane yace mata diyar wani babban malami a kauyen mu mai koyar da almajirai karatu.
Tace shiyasa haba ni dai nasan akwai wani babban al, amari a tare da ita kan.
Yace al, amari kamar na may tace naga dai kana yawan son ta ne sosai har baka iya boyewa a ran ka.
Yace haka dai kike gani yace zata tafi gida next week ita da yara don baban ta baida lafiya zasu tafi su dubo shi.
Sai kawai tace Allah ya sa ma ya mutu mugun tsoho kawai kowa ma ya huta duk yabi a asirce mutane da mugun tsafin shi.
Cikin mamaki yace mata kina da hankali kuwa hana tace ya mutu mana ubana ne halan ?
Don kai an maka asiri baka san komai ba akai shine baka ganin laifin shi amma ina kai ina wanan matar taka yar kauye da ita kawai.
Yace look Hanna duk abinda zakiyi kada ki fara ki zagi matata da yarana ko mahaifan don bazakiji dadina ba gaskiya.
Tace don anzagi wanan tsohon mugun shine kake kokarin fada min magana may yake idan ba mugu ba munafuki kawai.
Tsam ya mike ya dauki rigan shi yasaka yabar mata dakin tana kiran shi amma bai ko juyo gare taba don dama yayi niyar kwana a gurin ta ne ranan.
Har mun rufe gida saboda yayi muna sallama cewa a gurin aiki zai kwana a ranan sai kawai gashi ya dawo yana buga gida na fito na bude mai.
Bai ko tsaya takaina ba danake tambayan shi ya kuma dawo ne bayan yace yau a gurin aiki zai kwana gashi ban aje mai abincin dare ba.
Ya shige zuwa daki ya canza kayan jikin shi zuwa jallabiya yafito falo gurin yara inda suke zaune suna kallon filin wasan yara.
Na sake futowa daga kitchen ina tambayan shi a dafa mai wani abu mai dan sauki ne yaci.
Yace no ki barshi naci abinci ko nikan na kyale shi naci gaba da harkokina da nakeyi na kawar da kaya tsakar gida komai na mayar dashi a inda yake.
Nadawo falo na zauna muna waya da anty lami dake fada min wai wasu suna son a sayo masu atamfa mai kyau zasuyi ankon shi ne.
Nace mata zan duba nagani idan da kudin da zai isheni zan sayo masu nazo masu dashi idan zamu zo din.
Yana sauraren maganan da nakeyi sai dana kare nake ce mai amma sai naga ya kamata idan zamu tafi muyiwa Umma sayayya yan abubuwan amfanin ta.
Ya juyo inda nake yana cewa gaskiya maryam banda kudi a hannu na don yanzun haka ma ina ta neman wanda zakuyi tafiya dashi ne.
Nace amma Umma sai naga kamar ta dade baa aika mata da wani abin kwarai ba gashi kuma da kan mu zamu tafi ace bamu je mata da komai na azo a gani ba.
Bai yi magana ba sai kaloon shi yakeyi Abba yana fada mashi yadda masu kamun kifi suke dubaran kama kifi a film din da suke kallo.
Can cikin zuciyar shi kuma tunane ne yakeyi akan maganan da nai mashi na umma wanda yasan gaskiya ne na fada mai.
Kwana kaman shidda ke nan da Umma din takirashi a waya tai mashi tas akaina amma yanzu gashi ni da kaina nake magana akan a taimaka mata kuma.
Tausayin mu ne ya kamashi don yasan gaskiya bai muna dede daga mu har umma din kuma ni ban taba damuwa ba gashi ita umma a tunanen ta nice nake cinye mashi kudin shi ina mashi wayo.
Shi yasa yanzu ya daina kula ta kamar yadda ya saba kulata a baya yana mata sakon kudi da yan kayan amfanin ta a gida.
****** ********** ******
Tun da safe musalin shidda saura karan wayan shine ya tayar damu daga barci.
Ya dauka naji yana tsuki Hanna ce a layin yagani kaman kada ya dauki kiran amma sai ya daga cikin muryan barci yace hello.
Sai yaji tana wani irin kuka cikin tashin hankali tana fada mashi wai yanzu aka bugo mata waya cewa mahaifinta ya rasu an samay shi ya mutu a dakin shi kuma lafiya kalau aka kwanta dashi.
Don har gurin karfe goma sha daya na dare ana hira dashi da mutanen da suke haya a gidan su.
Take zancen su na daren jiya ya fado mashi a rai inda takewa mahaifina fatan ya mutu kowa ya huta dashi.
Allah da ikon shi sai gashi mahaifin ta ne ya mutu ba nawa din da tai ma fata ba.
Da sauri ya mike yai wanka ya shirya ya tafi gidan gashi duk maganan da sukeyi a cikin kunne sukayi shi.
Da zai fita kuma nasan cewa can gurin ta ya nufa duk da raina ya baci amma sai da ta bani tausayi sosai yadda naji tana kuka a wayan.
Ya samay ta a cikin tashin hankali a gidan da take haya cikin gari don ita mutumiyar kafamchan ne ta dai shigo garine da sunan aiki kawai take bushe ayan ta da mazan banza irin ta.
Samun Aliyun da tayi ta rike ne ma yasa ta dan daina harka da wasu mazan na daban can.
Wanda ke fadin baida kudi sai gashi yana shirin tafiya kafamchan kai tsaye.
Bai dawo gida ba ranan sai bayan sallah magariba ya shigo muna gida ya samu ina parking din kayan mu na tafiya da naje kasuwa na sayo a cikin manya manyan ghana most go.
Nai mashi sannu da zuwa ya shige nikan naci gaba da shirina don banda gobe ne tafiyan mu insha Allahu.
Nan ya shige bai fito ba kwantawa yay nima ban damu da rashin fitowan nashi ba naci gaba da abinda nakeyi kawai.
Bai kara bi ta kan mu ba balle na san zancen tafiyan mu ina ya kwana a lokacin sai dai kuma ban fasa shiri ba naje saloon nayi kitso da gyaran jiki an kawo muna dinkunan da nai muna masu kyau ga kayan katin da na sayawa yara na masu kyau kala kala masu tsada da zamu tafi dasu.
Da dare na tsura shi yana waya da wani abokin aikin shi yana fadin wai an mashi rasuwa ne a kamfanchan.
Nan ma na gane cewa a garin kafancham take da zama ita don a zato na yar cikin garin kaduna ce ita.
Yana ganina ya canza zancen da yake sai da na bari ya