Showing 54001 words to 57000 words out of 115099 words
Chapter 19 - Bamu kadai ba ne book Complete by Zainab Makawa .txt
kulle gidan kawai washe gari na shirya yaran nakaisu makaranta da kaina don nai masu bayanin rashin dawowan su da wuri.
Har na dawo na samu umma idon ta biyu ta kurawa tv dake aiki ido kawai nace umma na dawo ba lalaine ta amsa min ba nace ko akwai abinda kike sone Umma batace komai ba sai mumushi kawai da tayi.
Muna nan dai zaune namike na dora girki nai muna jeloup din shimkafa yaji kayan lanbun da nasayo dana fita.
Har kwana uku da dawowan mu sadauki bai dawo gidan ba nima ban nwmay shi ga waya ba balle na sheda mai aishine ya kamata yakiramu yaji lafiyan mahaifiyar shi bamu ba.
Na lura Umma ta shiga damuwa saboda yadda takan kurawa hoton shi dake manne falon ido yana tsaye a cikin kayan aikin sa.
Nakan fahinci shi take tambaya tana son ganin shi amma ba baki balle ta tambaya din.
Da yamman ranan ne mijin anty yaganshi a cikin gari shi da Hanna bayan sun gaisa yake cewa ashe baka san iyalinka sun dawo ba.
Dazun zan kai yara makaranta suke fada min wai tunda suka dawo basuga baban su ba.
Cikin mamaki yace sun dawo ne yaushe suka dawo garin banda labarin hakan.?
Yace mai yau zasu kai kwana hudu ko biyar fa da dawowa ashe tsohuwa bata da lafiyane haka tare sukazo da ita ai gobe ma naji madam din na fadin zasu asibiti da ita.
Kunya da mamakine ya rufe shi a lokaci daya shi dai mijin anty yaja motar shi ya tafi ya barsu nan.
Amma wanan matar taka she is witch wallahi kodai ba mutum bace ita wai ?
Cikin haushi yace ba mutum bace kece ko don Alla muje na saukeki na karasa gida da maganan takaicin ki can.
Sai da ya sauke ta ya nufo gida cikin darrr dashi lokacin yara sun dawo gida daga islamiya .
Ya tsayar da motar shi a kofan gida jin dirin motar shi yasa su saka ihu eh daddy oyoyo suka nufi kofan gida da gudun su.
Ina zaune naiwa Umma wanka ina shafa mata mai yashigo gidan idanuwan shi a kan mu yana kallon may nake ma mahaifiyar shi.
Umma sannu ku da zuwa yace tare da karasowa inda muke zaune da ita din.
Ya dan riko hannun mahaifiyar tashi tabishi da idanuwa kawai ba baki ba lakka.
Nan dai ya zauna tare dace min yaushe kuka dawo baki kirani ba yai wani kiban shi yai fresh dashi gwananin ban sha, awa hankalin shi da gani a kwance yake mai.
Nace ka manta ka hanani kiran wayan kane idan ba kaika kirani ba da kan ka kace na daina damun ka.
Yace amma da kika san zaku dawo ai sai ki kirani ki fada min ko don nasani .
Nace yanzun ma daka sani bai baci ba ai dai duk abinda mutum keyi don kan shi don baya mutum ke barwa kura.
Baiyi magana ba sai cewan da yayi yaya jikin nata yake yanzu akwai wani improvement ne akai ?
Nace gata nan ai a gaban ka kagani sai dai a godewa Allah kawai don a sannu ake samun sauki ga ciwo.
Shiru yayi duk guityness ya kamashi sai dan kamay kamay yakeyi kawai daganin shi baida gaskiya ga al, amarin shi.
Ya mike tare da nisawa yana fadin Allah ya sauwa yanzu akwai wani magani ne da ake bata ne ?
Nace ba wani magani bayan wanda aka karbo mata a tunga kawai shi ne har yanzu mukeyi.
Gobe ya kamata muje asibitin a duba muna lafiyan ta aga may ke damuwan ta.
Allah ya kaimu kawai nace mashi naci gaba da saka mata rigan jikin ta sai naga tana hawaye nace haba Umma idan kina tayar da hankalinki bazamu ji dadi ba mu.
Don Allah dai Umma ko may ke damuwar ki ki barwa Allah kawai don kukan nan baida wani amfani wallahi.
Ban bi bayan shi ba don banga abinda zance mai ba ko yace min idan na tafi inda yake din.
Muryan shi ne naji yana kirana namike nanufi dakin indayake na samay shi tsaye a tsakar daki ya goya hannayen shi a baya.
Nashiga da sallamana nace gani yace maryam wai may kike nema danine a rayuwan ki.
Nace ban fahince ka ba fa yace bazaki fahince ni ba ai don may nace ku zauna gida zaku kwaso jiki ki kwaso su ku dawo.
Watau kina nufin ni ban isa dake bakw nan ko komay kike nufi da hakan ?
Kun dawo kuma baki nemay ni ba kunyi zaman ku kawai ba wani labarin komai balle nasan may kuke ciki a gidan.
Wai ma yanzu da kika kwaso Umma kikazo da ita nan may kike son nayi mata anan wanda can gida an kasa yi mata.
Ban san lokacin da nace wai baban Abba may ke damun kane yanzu haka mahaifiyar ka kai kadai a gareta kai kadai Allah ya bata amma har ka tsaya kana wanan maganan haka akan ta.
Wallahi kaji tsoron alhakin hakin mahaifiya kada ya kama ka Allah.
Idan banzo da ita nan ba can kake son mu barta ita kadai ko kuwa yaya kake so nayi da ita.
Kace zaka turo da kudin makarantan yara asaka school acan amma kazo karuwan ka ta dauke maka hankali ka manta da zancen kowa a ran ka.
Kasan dai ina da halin da zan iya sa su makaranta acan amma don naga kaima baka damu da su ba yasa na barsu hakanan.
Yanzu shine kake bakin ciki don mun dawo dawowan namu akwai abinda zai hakanane daga halin da kakeyi kana sa yan uqanka suna zargina a banza don kawai na boye masu halin da kake ciki damu anan komay.
Har yanzun zaka bode baki kace wai may mukadawo yi nan yanzu to kasani mundawo ke nan wallahi babu inda zamu tafi na fada maka.
Yace ai idan baku tafi don Allah ba indai akan wanan gidan ne dole ku tafi kodon rigiman dake cikin shi don dai ni banda wani kudin da zan kama hayan wani gidan kuma yanzu a garin nan.
Nace ba matsalan komai a gidan nan sai wanda yajawo da zafi ne yake ganin matsala dama a rayuwan shi gida ma ka huta akan shi bazamu canza gida ba nan dai inda muka saba zamu zauna din.
Allah zai kare mu dayardan shi insha Allahu bamu ganin komai sai alheri.
Umma kuma mahaifiyar kace idan ka kulata ruwan ka idan ka barta ma rukan ka ni dai duk abinda nake mata don Allah nakeyi mata ba don komai ba.
Yace ai haka zakice waya ja mata aanan matsalan ba duk keba ai kin san komai kada ki mayar dani karamin yaro mana.
Keda kikaja mata aikece mai wahala yanzu dawa kike wahalan bake kadai ba.
Nace koba Umma ba bani fatan injawa wani wahala balle Umma da take a matsayin uwa a gurin na mahaifiyar uban diyana kuma.
Yanzun dai sai ki shirya gobe aje asibitin ba ganin iyaka bane dama yasa kika kwaso kuka zo don ki kulla min sheri.
Nace idan ni banga iyakarka ba ai karuwan ka zataga naka itada yanzu saboda ita baka hanin kowa da gashi a duniyan nan sai ita da uan uwan ta kawai.
Kada kace ko ban san kudin da kake kashewa ne akan taba amma ga mahaifiyarka nan ba lafiya ko a jikin ka.
Yace nakike nan dama bakin kishi kudinki nake bata ko nawa nace nawakan ai yafi karfin bata wallahi idan kuma mutum ya musa ne ya gwada kai mata inbai yabawa aya zaki ba.
Nasani ai kada kice ban san yanzu kin sake daga maryam din danasani zuwa wata maryam din ba can.
Kallon mamaki nai mashi jin abinda yace min don nasan akwai wani abinda ya sani gamay dani wanda ni ban sani ba ke nan.
Yanzu aini maryam komai za, a iya kirana tunda karuwa ta hana mu dawo mun dawo zamu bata maku tsarin ku na cin duniya.
Kamar zaiyi magana yadda ya tsura min ido sai kuma ya kasa furta komai sai kutawan da yayi kawai ya juya yafita daga dakin.
Haka ya fito dakin ranshi a bace munyi kaca kaca dashi wanda nasan duk maganan mu yana a kunnen Umma din tanajin komai da kowan mu yake fadi.
Ina fitowa naga fuskanta ya baci alaman bacin rai karara a fuskan ta ban tsaya ts kanta ba naci gaba da aiki koma maynene dai yau ai taji ma kunne ta hakin da tilon dan ta yake ciki.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
[11/9, 11:20 PM] Zuraiyah Zuzu ๐: ๐ฉโ๐ฉโ๐งโ๐ง ๐ฉโ๐ฉโ๐งโ๐ง
BA MU KADAI BA NE A, , ,
๐จโ๐ฉโ๐งโ๐ฆ ๐จโ๐ฉโ๐งโ๐ฆ
2โฃ0โฃ
Alhamdullahi don kwana biyun nan dana fara yiwa Umma maganin gurin baba malam, kuma na daina bata maganin asibiti wanda ke wahal da ita din.
Aiko gaskiya Alhamdullahi don yanzu yakai Umma har tana dan iya mikewa daga zaune a inda take a kwance.
Zata iya daukan wani lokaci mai tsawo a zaune idan kuma zata kwanta da kanta zata koma ta kwanta.
Sai dai har zuwa yanzu babu baki a tare da Umma din sai dai kwatance kawai mutum zai fahinci abinda take so a rayuwan ta.
Nan dai na dan samu saukin al, amarin do iyanzu ta rage sake najasa a gurin da take zaune don takan nuna min alaman bukatan ta.
Zancen sakon baba malam gun matan da ya turani ne ya ke ta fado min a zuciyata.
Haka dai yasa na yanke shawara washe gari zan rufe idona na tafi don kyaun alkawari cikawa.
Na cewa baban Abba da zai fita da safe ina son zuwa na karbo kudina da sako a gurin wata mata a GRA don matar bata san mun dawo garin ba.
Kallon mamaki ne yai min yace kin ko san inane GRA maryam ?
Abin naki har yakai kin fara hurda da manyan matan gari haka ashe ban sani ba ?
To ki dai yi a hankali don GRA ba unguwar zuwan tallakawa bane don ki sani.
Nace insha Allahu nai godiya akan bari na fita da ya barni nayi batare da ya hana ba.
Yana fita na shiga shiri na don ranan ba school yaran suna gida zasu zauna tare da Umma a gida.
Tsab na shirya tare da daukan sakon maganin da baba malam ya bani na kaiwa matan nan biyu da yace nakai masu sako da kaina.
Shatan mota na dauka sai unguwar Allah ya hadani da mai motan kwarai kwatancen gidan hajiya Aisha nai mashi kawai yace ya gane.
Yace gidan matar tsohon shugaban kasa ko wancce take mininster mata na yanzu ko ?
Nace gaskiya ban sani ba amma muje dai bai tsaya ba sai kofan gidan muka tsaya.
Kallo daya naiwa girman gidan naji gabana ya fadi sosai amma yaya zanyi dole na daure na idar da alkawarin dana daukan wa baba malam din.
Na rasa ko inane kofan shiga gidan Allah ya taimakeni naga wata mota tana fitowa daga cikin gidan haka yasa nagane kofan shi gidan.
Na sallami mai motan daya kawo ba canji dubu daya nace ya tafi dashi nabar mashi yana ta godiya yaja motar shi ya tafi inda naga motar nafitowa na dan rabe daga gefe tafice nikuma na shiga gidan.
Gidane irin ta manya wanda tsayawa fasalta shi bata lokacine don an kashe miliyoyin narai a ginin wanan gidan .
Wasu mutane ne na hango saye da uniform duk iri daya a jikin su haka yasa na karasa inda naga kamar magana suke na siri a tsakanin su kuma suna rabon kudi.
Suna ganina dayan ya taso kaina haikan yana fadin ke waya shigo dake gidan nan ki kuwa san inda kika shigo kuwa.
Ba tsoro a raina nace dashi nazo ne naga hajiya yace wace hajiyan a ciki ?
Nan fa daya sai naji bakina kawai yace hajiya babba din nazo gurin ta sai naga yana min wani kallo sama da kasa yana mamaki kamar ni zance nazo gurin hajiya a haka dani.
Yace tasan da zuwan ki ne ko kuwa naki ya kawo ki gurin ta abinda kuka saba matan yanzu yin maula ?
Nace idan ma nayi maka kama da mai maula ne sai ka canza tunanen ka don bashi nazo yi bani.
Jinan malama ba,azuwa ganin hajiya babu appointment idan mutum ba dan uwan ta bane don ki sani.
Nace kai tsaye a gadarance ka fada mata ga maryam tazo ganin ta kawai.
Dariya naba mutumin bai gama dariyan ba yaji muryana ina umurtan shi da cewa zaka fada mata kona kirata na fada mata ka tsare ni da surutu a get.
Yace au ashe ke zancen ki da gaskiyane bari nakira naji idan tasan da zuwan ki idan kuma tace min bata sani ba kinga karnunkan can na keji yanzu na kwance maki su suyi kaca kaca dake a gurin nan.
Nace Allah ya baka sa, a dama haka kuke yan hana ruwa gudu asakaku ga rigar arziki kuce zakuyi wa mutane tsiya.
Kallon mamaki yake min inda ya daga waya yakira wani layi yana bayani wai watace tazo sunan ta maryam tana son ganin hajiya babba.
Ban san may akace mai ba nadai ji yace gaskiya ba wata bace can amma dai ta kafe lalai sai taga hajiya din.
Nace don Allah malam kana bata min lokaci ni ina da abinyi kaji banan kawai zan tsaya ba please.
Wacce yake wayan da ita taji muryana sai cewa tayi abani wayan na karba take cewa wacece ke hajiya tasan da zuwan ki ne ?
Nace kifada mata ga maryam tazo kawai zata gane idan kin fadi hakan tace ok kijira ni ina zuwa.
Sama ta hau ta samu hajiya a falonta na sama zaune tana ganin shigowan ta tabita da kallo.
Tace hajiya sannu da hutawa tace yauwa sannu karimay.
Hajiya wai wata ce maryam a bakin get take son ganin ki wai kin san da zuwan ta tace.
Hajiya ta nanata sunan tace maryam ku maryam fa wata maryam ke nan ?
Ta kada kai tace gaskiya ban san da zuwan ta bani sai dai idan ba gurina tazo ba.
Wacce ta kira da karimay tajuya zata fita daga dakin har takai kofa mafalkin da tayi jiya tana fadin maryam nagode nagode kinji ne yafado mata arai.
A take tace karimay karimay taja ta tsaya guri daya tace na tu kice tashigo please.
Ta sauko kasa tace wa maigadi ance ya nashigo daga ciki .
Yace kinyi arziki wallahi da na hadaki da karnun kan nan yau sun yaga min ke don naga baki da mutunci.
Kalman nashi yabani mamaki na ja natsaya nace nice ban da mutunci kace yace kidai shiga tunda kinyi sa,a ance ki shiga din.
Kallon mamaki kawai nake mai kaman zanyi magana sai kawai nasa kai na shige gidan kaman dama nasan kan gidan da farko.
Ashe shigana da kaman second mutumin nan baiyi aune ba sai gani yayi kamar an sako karnukan nan dake a daure sun yo kanshi ba bata lokaci suka haushi da cizo da yakusa sai da sukai mai yagayaga da suturan shi.
Da kyat yan uwanshi suka kwace shi ga karnun kan nan yana ta hakki yana mayar da numfashi guda guda yasha cizo.
Da sallama na shiga falon wanda zance acikin film dai nake ganin makamancin sa a kasashen turawa ko indiya.
Sallama nakeyi kamar ba kowa a gidan sai da ga can har na yanke shawaran na koma baya naji an karba min gaisuwa na.
Wata matace fara doguwa maikarfi da ita tafi daga wani kofa tana cewa kece maryam dake neman hajiya ?
Nace da ita nice atakaice.
Wani irin kallo tai min kaman zatayi magana sai kuma take cewa bisimillah muje nakai ki gurin ta ko.
Nace nagode.
Sama muka hau sai bin gidan da kallon ikon Allah nakeyi bazakace a Nigeria kake ba idan kana wanan gidan.
Falon da muka shiga na kasa tantance dashi dana kasa ko wani ne yafi haduwa dakyau.
Can na hago matar dana zo gurin ta zaune saman wani kujera mai kama da royal cushion tana zaune a takure ta dafe kanta da hannun ta daya.
Nai sallama ta dago kai da sauri tare da tsura min ido tace maryam sannu da zuwa.
Yadda ta tare ni zakace ko tasan ni ne a baya tace karimay kawowa bakuwa abin motsa baki.
Nace ai hajiya dakin barshi ba zama zanyi ba yanzu zan tafi nazo ne kawai nakawo maki sako.
Wani hayaki nagani yana tashi daga kujeran da take zaune akai wanda nasan ba lalai bane kowa yana ganin hakan.
Hajiyan take cewa ai dai ko bazaki dadw ba bakizo ki tafi babu abin tabawa ba ko ?
Nace tona gode matar