Showing 84001 words to 87000 words out of 115099 words

Chapter 29 - Bamu kadai ba ne book Complete by Zainab Makawa .txt

16 Dec 2024

6646

ki shafa aduk illahirin jikin ki gaba daya.
Tana gama shafawa nace Alhamdullahi ubangiji ya tsare ya kare gaba dama sauran da basu sani ba ake masu zagon kasa a hakan .
Ikon Allah Aishs na batun wucewa wata mace ta bude labulen dakin da muke ciki tana fadin.
Sallamu Alaikum sai dana dago kaina kalli matar da kyau kamar ina nazarinta nace wa, alaikis sallam.
Tace nazo ne don Allah nima a taimaka min akan, , , kafin tai magana nace akan yaron ki ko ?
May kike son muyi maki da yaron ki bayan kece kikajawo wa kanki ni kuna bani mamaki bil, adam sosai sai kunyi abu zaizo yana damun ku kuma,
Kin manta lokacin da danki yafara halinshi wasa wasa ana fada maki amma kike karyata mutane yan uwan ki.
Nan gaba ma dake zaiyi kuka sosai don kece kika kara kaishi ga wanan rayuwan da yake a ciki yanzu.
Abinda ma baki sani ba yanzu shine dan ki yayi nisa yaron da aka kawo maki riko wanan dan naki ya riga ya lalata mashi rayuwan shi ta hanyan yin luwadi dashi duk da kankanta dake ga yaron .
Amma rashin saka idon ki waike kina son danki yaja anyiwa dan mutane illa a rayuwan shi saboda sakacin irin naku na uwayen yanzu.
Akan may zaki ki dinga tafiya kina barin diyan ki su kadai haka a gida a tsakanin su bayan kin san dan ki baya ji magana tun yana karamin shi.
Don Allah iyayye ku dinga kula da diyan ku saboda yaran yanzu sun riga da sunyi nisa sosai ta hanyan kallace kallace fina finan dake koyar da miyagun dabiu a gare su.
Barin yara su kadai a gida ba abin alheri bane a wanan karnin da muke a ciki koda atsakan jinsi daya suka fito saboda baka sheda mugu a fuska yanzu.
Ba wai lalai sai ka fita ba zaka hadu da mugu ko a cikin gidan ku akwai muggan diya da kuka haifa da kan ku.
Saka ido ga rayuwan yaro abune mai matukar amfani yanzu ki tashi ki koma gidan ki wanan dan yayen da aka kawo maki ki fara duba lafiyan shi tukun zaifi maki alheri kafin mu duba al, amarin daki dake bukatan addua gareshi.
Matar tamike jiki ba karfi don gwiwanta ya mutu idan har abinda aka fada mata gsskiyane yaya zatayi da dan marayan Allah datake riko.
Wanda ta kulla da zaran awal ya shigo gida duk inda fahad yake baya kara fitowa sai lokacin da yaji fitan Awal a gidan zai fito waje daga inda yakw boye.
Ashe ke nan mugun abinda yake aikatawa yaron ke nan ita hankalinta baikai ga yaron ba may yasa yake haka.
Gashi idan zaiyi kashi sai yaita ihu yana cewa zafi ciwo amma ita sam bata kai hankalinta gare shi ba.
Tana fita daga dakin wata mata tashigo da yarta ita wai bukata tazo dashi yar ta shekara hudu da aure bata taba koda batan wata ba agidan auren ta.
Nace cikin dan kada kai ai wanan matsalar taku ce bakece ki zubar mata da ciki ba kafin tayi aure.
To wanan cikin da kuka zubar shi kadai ne dama rabonta a duniya kuma kunzubar dashi.
Yanzu sai ku koma ga Allah don ba abinda ya gagari ubangiji ya taimakawa bawan shi.
Amma da kin daina wahalan yawon neman magani haka da kikeyi don kuka jawa kanku don gudun kunyan duniya.
Kun manta da kunyan lahira yafi na duniya zafi da kibarta ta haihu don Allah shine masanin gaibu.
Matar tafita da yar ta simi simi da ita take cewa lalai gurin nan kan akwai magana sosai ga wanda yazo.
Haka bai hana wata shigowa dakin ba tare da yar ta tana biye da ita a baya.
Suna zama nace tau duna nan kuma ka labe a jikin yar mutane kana cuta mata.
Wai may sa ku bako so a zauna lafiya daku ne may yan adam suke maku haka kuke son yawa cutata masu a rayuwan su.
Matar tace malama wallahi kamar kin san abinda ke tafe damu gashi ban fada ba harkin gani da idanuwan ki.
Nace halin yarki yasa ya shige ta don wanan gashin da take dorawa ko yaushe akanta kin san shi duna baya son zama sai irin wanan guraren.
Ida ake barin akaifa a yatsun hannu da gurin da ake barin gashin kai a sake ko da yaushe.
Sai ko gidan da ba a tsabtace ana barin kwata yana taruwa a kwatamin gidan ko ana yawan barin kwanoka ba, a wanke su ba akan lokaci kai duk dai gurin da najasa yake anan ne zaki samay shi yana mafaka.
Ku dinga horon diyan ku akoda yaushe su dinga daura dankwali ko hulla akan su su dai yawan karin gashi wanda basu san idan yafito ba a kawunan su.
Dazaki ga wanan bakin aljanin danakira maki da duna zaki ga shugan shi da kaman shi kamar yadda diyan ku na wanan zamanin suke kwalliyan su sufito kamar mahaukata da sunan kwalliya a garesu.
Wanan shiga da kuka saka ido diyan ku sunayi shike kara jan ra, ayin shi yana shiga jikin su yana jin dadin rayuwan shi.
May yasa kuke ganin basu damun diyan ku maza a kasafai sai diya mata badon komai bane don suna morewa kurciyan su ne ta wanan hanyan kawai.
Hannu nake murzawa ina mata bayani na miko mata hannun wanda magani ne ya baiyyana a cikin sa na mika mata nake cewa ta dinga yin hayaki da kuma shafawa a jikin ta har mugani zata ko kuma yi aure da zaran ya barta.
Idan bai fita ba sai musan yadda zamuyi da su matar ta bude haban zanin ta dauko dubu daya tana cewa ga wanan sadakane na bayar saboda Allah.
Kudin na kallo cikin mamaki nace kece mace ta farko da tasan wahalan da godiyar mu takeyi har ta bata wanan a matsayin taimako.
Don haka jeki da abinki amma daga kanki yazama waji duk wanda zaizo neman taimako a gurinta dole ya san abinda zai aje mata da sunan sadakan da kikace a yanzu.
Bamu bar gidan ba, sai musalin karfe biyu da rabi na rana, muka bar gidan wanda a lokacin Allah kadai yasan mutanen da sukaso gani na amma na basu hakkuri suka barni.
Kai mutane suna cikin matsaloli musan man ma mata kamar sunfi kowa matsala a wanan lokacin da muke ciki.
Mun iso gida duk jikina a gajiye yake min duk da na shaka hantitina a hanci ba iyaka.
Ganin yanayina kawai ya sa Umma ta fahinci cewa abin ya taso min acan inda muka tafi yadda nazo na kwanta mata ragwab a gida.
Tace yaya dai maryam ko abubuwan sun ziyarce kine kuma can ?
Kai kawai na gyada wa Umma na gyara kwamciyana sai barci ban falka sai biyar saura koshi saboda sallah la, asar da ban samu yi bane yasana mike.
Nan dai muke da yar sokoto da tashigo gurin ta duba jikina hira muke da ita da umma ina saka baki jefi jefi.
Haka baban Abba ya shigo gidan ya samay mu ganin shi bai sa yar sokoto tabar mu ba don yanzu an saba sosai a tsakanin mu.
Ga bakin ta ne yake jin abinda ya faru dani a unguwar da muka tafi da yadda abubuwan suka wakana.
Nan dai yake fada yana cewa wanan dalilin ne yake sa yanzu sam bana son kina fita zuwa wani gurin.
Umma tace ai wanan lalura ne kowa yasan ts kuma sai dai kowa da irin yadda tashi take zuwa mai.
Jin maganan da Umma tayi yasa yaja bakin shi yai shiru don baida abin fadi kuma.


****** ********** ******
Sallah da sati biyu nashirya tare da daukan kudin bin yusuf da suka damay ni na nufi kasuwa dasu.
Yar sokoto ta lake min cewa tare zamu tafi da ita don tana son zuwa shagon tagani nasan gulma ne zai kai amma tare muka tafi da ita.
Allah ya rufa min asiri na samu wai ranan suka fara bude shagon su ashe daga dogon hutun da suka tafi koshi wai akan wani dalili yasa suka bude a ranan.
Kudin shi cif na kirga na bashi tare da mashi godiya sosai.
Bayan yagama kidayawa ne yake cewa masha Allah malama maryam kinyi alkawari sosai haka ake son samun mutum da cika alkawari.
Don haka ina daga cikin wa yanda zasuyiwa bonanzan kayan shagon su na duba duk abinda raina ke so na zaba kada naji komai.
Nan ta dinga taimaka min muka dinga zakulo kaya sai dana zabi duk wani abinda nake so a shagon.
Yace bai kai yadda suke bauarwa ba na sake zaba haka muka zaba fiye da wanda na zaba da farko.
Kudin daya fada na bayar yai matukar bani mamaki yace haka yakewa customers din shi don suma su samu duk shekara.
Mun fita zuwa shagon da zan sari turare anan mukaga wani taro anyi dandazo ga wani yaro a tsakiya yana kuka yana faman rantsuwa.
Har muka shiga muka fito shagon mutanen duk suna gurin ana ta faman rikici a tsakanin su wani mutum mai girman jiki yana kwadawa wanan matashin mari.
Ni dai ban san yadda akayi ba sai ganina a tsakiyan taron nayi na dubi idon mutumin da idanuwa da suka canza launi nake cewa dashi.
Kada ka kara dukan shi may yasa ku yan adam baku da imani ne ?
Wanda ya dauki kudi ka daban wanda ka, ke duka haka daban don yana nema a karkashin ka, amma kazo ka kama wanan dan marayan Allah kana ta faman dukan shi da zargin shi.
Kan san inda kudin ka suke ka koma gida tun bai kashe suba ka karbi kudin ka hannun dan ka Abdul don yafara taba su.
Tsit mutumin yayi yana kallona cikin mamaki na kara cewa ka tafi gida saman silin din dakin shi kudin suna ciki ya boye.
Ikon Allah wanan matar kuma fa?
Wani daga cikin yan kasuwan yake tambaya nace sunana Rukaiyya daga haka na juya muka tafi Allah da ikon shi babu abinda ya samay ni ta fannin faduwan da nakeyi idan sun fita daga jikina.
Muka kwaso kayan mu mota daya muka bar kasuwan kafin a dawo har mun bace ko.
Koda mutanen suka dawo anyi nemana basu samay mu ba mun tafi, sai wani ne kece yasan ni ina yawan zuwa shagon bin yusuf sosai.
Nikan na dawo gida kamar bani bace wani abu ya faru dani a kasuwa sai mamaki irin kayan dana lodo daga kasuwa yau Umma take yi tana fadin ikon Allah maryam duk wanan uban kayan haka naki ne ?
Kice dai kece akazo wa kaduna maryam wanan irin alherin haka ?
Murmushi kawai nayi ina kaiwa zaune saman kujera nan yaran dana samu sun dawo daga school suka kewaye ni kowa na son na basu tsaraban dana saba sayo masu idan nashiga kasuwa.
Idan ka saba sayawa yaro dan abu idan kafita ko yaushe akwai yar shakuwa da yarda da aminci a tsakanin ka da dan ka.
Haka yasa nasan sun saba da idan na dawo na basu dan abinda na sayo masu don ni bani taba basu kudi nace suje su sayi abu da kan su nice dai zan saya da kaina na basu.
Don bawa yaro kudi yasaya abinda yake so kudi a hannun shi wani babban hanya ne na tallafawa lalacewan tarbiyan yaro a wanan zamani.
Duk ranan da yaro ya bukaci ya sayo abinda yasaba baka bashi kudin ba yadda ka saba mai zai iya dauka koba da sanin kaba yaje ya saya.
Wanda hakan zai kamaci gaba ga rayuwan shi har tai mai illa a gaba.
A haka mahaifin su ya shigo ya samay mu sun kewayeni ina basu tsaraban alawa da biscuit.
Idon shi kyam akan kayan da yagani na sayo yana mamakin ganin su haka da yawa.
Nan ya zube yana cewa kun dawo ke nan daga kasuwan nake ce mai yau ai da kafan dama na shiga na samu ana bonanza na kwaso kaya haka da ace ina da kudin da yafi haka ai ba karamin kaya zan kwaso ba yau.
Namike na dauko mai abincin shi ya soma ci ke nan akai sallama a kofan mu abinda yasa shi mikewa ke nan ya nufi waje gurin mai sallaman.
Shiru shiru bai dawo ba har tsawon wani lokaci ya shigo sai dai fuskan shi a daure ina zaune a kasa gaban table ya zube min kudi masu yawa zasu kai kusan dari biyar.
Bin kudin nayi da kallon mamaki kudin ki ne da kikai aiki a kasuwa aka biyo ki dashi nan.
Kudina na taambaaya cikin mamaki yace eh kudin ki mana bakin shiga kasuwa ba yau kiika kashe wuta.
Na kada kaii ina cewa gaskiiya bani bace don ban masan wanan maganan ba ni.
Baiyi magana ba nima dai shiru nayi ina tunanen may nayi har za, a kawo min kudi masu yawa haka ?
Ummace ganin yanayi take sake tambayan shi wai kai bakai mata bayani ne akan kudin ka zube mata kudi a gaban ta tace ma ba ita bace.
Yace Umma ni may zance yanzu ace nayi laifi wasu Alhazai ne yan kasuwa sukazo wai taga suna rigima akan an sacewa chairman din kasuwa makuddan dollolin shi shine tafada masu inda kudin yake suna zuwa suka samu yadda ta fada din hakane shine suka kawo mata wanan a maysayin tukwaici gareta.
Nace ni gaskiya ba abinda ya samay ni a kasuwa balle suce hakan bani bace ka mayar masu da kudin su don Allah.
Kedawa kuka tafi kasuwa sunce min ku biyu ne ai ?
Nace a hankali ni da yar sokoto ne muka tafi tare yace Abba kira min yar sokoto a gidan ta idan tana nan.
Yaron yafita da sauri ya nufi gidan yarsokoto din shiko yaci gaba da fadin ni wallahi wanan abin ya fara isata wallahi dole na dauki mataki akai sai dai aga laifina.
Tayaya mace zata dinga lamayawa a cikin kasa a gaban maza kuma a kasuwa akan wani dalili can na daban.
Ai bake kadai bace a gari ga mata da yawa may zaisa basu bisu ba sai kece za, a saka a gaba haka kamar ke kadaice mai aljannu.
Ka iya bakin kafa babana wallahi idan ba ita kadai bace kowa ba da kalan nashi ba da kuma irin yadda abin ke kasance mai.
Yar sokoto tashigo gidan tare da Abba yanayin ta a cikin damuwa don bata san dalilin kiran da akai mata ba din.
Tambaya ya jefo mata yana cewa don Allah yar sokoto da kuka je kasuwa may yafaru a can ki fada min gaskiya tsakanin ki da Allah.
Bata rage ba bata kara ba duk abinda ya faru ta labarta mai nima sai lokacin ne na san may akayi.
Yace bata zube ba a furin bayan su fita daga jikin ta tace a, a wallahi muna hanya dai naji tayi atishawa kawai abinda nagani ke nan amma har muka kawo gida ba abinda ya samay ta.
Ajiyan zuciya ne ya sauke yana cewa yanzu naji magana amma gaskiya ni bazan yarda hurda da maza ba gaskiya.
Kai al, amarin iskokan maryam fa masu taimako ne su aduk inda sukaga matsala don haka kaba kanka lafiya.
Da yake musulmaine take tare dasu aikaga sun san kaida da darajan aure basu bari komai ya samayta ba a gaban maza.
Nan zaka gane farfarun mabiyane tare da ita masu sonta da alheri ne ba tsiya ba.
Yace ni gaskiya ya kamata na fara tambaya kan wanan al, amarin don abin ya fara bani tsoro wallahi.
Kadai bi sannu na fada maka kada kajawo wa kan ka matsalan da zaka kasa fitar da kanka ciki.








ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU[11/27, 9:32 PM] Zuraiyah Zuzu ๐ŸŒŸ: ๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ง ๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ง


BA MU KADAI BANE A, , , ,


๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ง ๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ง
2โƒฃ7โƒฃ




Hankalina yai matukar dagawa akan wanan abin daya faru dani a kasu ba don komai ba sai don mutuncina na diya mace a matsayina na matan aure.
Ranan zaman falo ma gagara na yayi nakoma daki abin duniya ya damay ni sosai a rai na sai tunanen yadda zan samu maraba da wanan abin nakeyi.
Nayi dana sani yafi dubu a raina ranan nayi dana sanin haduwa da su danayi wanda nake ganin na hadu da mutanen kirki ne da farko .
Ashe ban sani ba da jinnu nake taraiya yanzu ga abinda suke kokarin jawo wa rayuwan aure na matsala kuma.
Shima fushin yake haikan haka muka kwanta kowa da abinda yake ji a zuciyar shi.
Can cikin barcina na fara mafalki kamar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login