Showing 51001 words to 54000 words out of 115099 words
Chapter 18 - Bamu kadai ba ne book Complete by Zainab Makawa .txt
duk abinda zakiyi kada ki yarda da hanyan kaucewa a rayuwan ki .
Addinin ki yazamo gaba a kan komai da da zakiyi kada ki bari wani abu na kaucewa ya shafi addinin ki ko kadan don gujewa sabawa Allah.
Duk da suma musulmaine kamar mu amma dole ne asamu wasu da ba su da rikon Addini sosai a cikin su suyi kokari ganin kin sabawa mahaliccin ki.
Nace da sauri insha Allahu baba bazan yarda na sabawa mahaliccina ba koda kuwa zan rasa rayuwanane ta hakan.
To Allah yai maki albarka ya tsare muna ke daga duk wani masheranci abu mutum ko aljan ko dabba ko kwaro dama abinda bamu sani ba ma.
Na amsa da Ameen baba yace amma malam din yace min yana da kyau duk ranan jumna, a ki samu wani abu kiyi sadaka daga cikin wa yan nan abubuwan daya lissafo min kamar haka.
Masa ko kosai ko kulikuli ko sugar ko sai abinci wanda akafison kibawa mubakaci don kariya.
Bake ba duk wani musulmi ana son yai daya daga cikin wanan sadakan idan da halin yin haka ga mutum.
****** ********* ******
Baban Abba yana zaune a office akakirashi da waya cewa gasu Hanna acikin wani hali an kawo su a cikin wani hali mara dadi.
Kamar kada ya tafi amma wata zuciya ta rudeshi da ya tafi ya dubasu yaga halin da suke ciki.
Yadda ya samay su ne ya tayar mashi da hankali sosai don haka ya shiga ya fita asibitin gurin ganin ya taimaka masu ga halin da suke ciki.
Don abinda taimai yana aiki sosai a zuciyar shi baibarsu va saida yaga ya shiga yafita komai kanmala yabar asibitin.
Shi da kanshi ne ya kiragidan su ya fada masu halin da yarsu keciki duk wani lalurar asibiti shi yayi da kudin shi.
Wayan da ya isheshi ne na mutane dake kiranshi akan rashin lafiyan Umma yasa ya shirya yazo gida.
Yadda ya samu umma baiji dadin ganin halin da ya samay ta aciki ba, don ba karamin jin jiki umma din takeyi ba.
Sai bayan fitan shi ne ya samu labari wai sanadiyan ciwon Umma fadane tayi sai ta fadi shine hakan ya samay ta.
Wanda ba gurin wani ya samu wanan labarin ba sai gurin yaran shi daya fita dasu yawo suke fada mai abinda ya faru.
Hankalin shi yai matukar tashi ya juyo gida ya samay ni a daki ina ba Umma abinci guri ya samu ya zauna yana cewa Maryam fada min may ya kawo sanadin wanan ciwon haka na Umma ?
Shiru nayi naci gaba da bata abincin da nake bata jin nai shiru ne yasa ya kara tambayana kamar farko.
Nace nidai ban sani ba kawai dai tagama fada ne tazo zata shiga daki ta fadi shine kawai abinda na sani.
Fada min duk yadda abin ya faru please ban boye mashi ba na kwashe duk fadan da mukayi da Umma din da abinda ta fada min kan fadan da yadda ta fadi kasan harta samu wanan sanadin haka.
Cikin wani murya yace haba haba Umma may yakaiki wanan aika aikan haka na fada maki babu kudin da naba maryam tun farko yanzu gashi alhakinta ya kamaki kin jawo wa kanki wani sabon matsala kuma.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
[11/9, 11:20 PM] Zuraiyah Zuzu ๐: ๐ฉโ๐ฉโ๐งโ๐ง ๐ฉโ๐ฉโ๐งโ๐ง
BA MU KADAI BANE A
๐จโ๐ฉโ๐งโ๐ฆ ๐จโ๐ฉโ๐งโ๐ฆ
1โฃ8โฃ
Ganin yadda jikin Umma ya tsanan ta sosai ba wani sauki kuma gashi naga yana shirin tafiya.
Yashigo dakin ya samay ni ina shafawa Umma magani da wani mutum ya bayar ai mata.
Ya dan jima a tsaye yana kallon yadda nake mata da maganin batare da yai magana ba.
Nice na kawar da shirun dakin nake cewa amma dai da Umma zamu tafi ko ?
Ban gane da Umma zaku tafi ba kina nufin na dauke ta haka zuwa kaduna da ita.
Nace to a gurin wa zamu barta ke nan idan mun tafi din mu ?
Ke dai zaki zauna da ita ba ida zaku tafi ku barta a haka ba lafiya ita kadai.
Murmushi nayi nace idan na zauna nan karatun yaran kuma fa yaya zai kasance ?
Yace su dawo nan da karatu su mana ai masu register a Benjamin school.
Shiru nayi don wani sabon balai dake shirin taso min kuma ke nan anan don ba zan taba yarda da wanan shawaran nashi ba.
Har yakai kofa nace da Umma zamu tafi mukaita babban asibiti a duba muna lafiyan ta a can.
Kina da kudi duban ta ke nan a can nace Allah zai hore muna insha Allahu amma zaman ta haka batare da mun san may ke damun lafiyan ta baiyi ba.
Bai kara cewa uffan ba ya sa kai yafita daga dakin akarshe ma yama bar gidan baki daya yafice abin shi.
Ina kokarin mikewa naga umma tana hawaye daga idanuwan ta haka yasani komawa na zauna kusa da ita ina cewa haba Umma ki daina saka damuwa haka a ranki insha Allahu zamu tafi tare dake can a duba lafiyan ki yafi zaman ki haka a gida dakikeyi ba, a san kan ciwo ba.
Kiri kiri ya shirya ya tafi ya bar mu sai dai ban mashi magana ba don cewa yayi idan hutu ya kare zai dawo ya dauke mu.
Haka ya koma yaci gaba wahal da kan shi akan hanna ga mahaifiyar shi da zai tafi dubu biyar ya bayar akan idon ta tagani kuma.
Hankalina ya kasu gida biyu ga gurin mahaifina ga kuma Umma da ba lafiya komai na rayuwa nice ke yi mata shi yanzu .
Yau sati biyu ke nan ga lissafina da komawa makarantar yara gasu zaune min a gida ba karatu sukeyi ba.
Kudin da yace zai turo ma asakasu a makaranta nan Auna babu su babu dalilin su ga wayan shi ma sai yaga dama yake kiran gida.
Koshi daya kira zai tambayi yaya jikin Umma dana fada mai halinda take ciki zai ce Allah ya sauwaka kawai ya kashe wayan shi.
Ranan na gama sallah ida nai sallah ina zaune kamar barci ya dauke ni sai ganin anty mukkadarasiya nayi a gabana zaune tana min murmushi.
Tace maryama kinzo kin zauna nan kin watsar da karatun yaran ki mijin ki fa bawai yadamu da halinda kuke ciki bane saboda shu, umar matar nan da yake tare da ita ko yaushe.
Duk abinda kikeyi gobe goben nan ki shirya kibar garin nan ki koma gidan ki kada yaran ki su samu matsala.
Zaman ku acan shine alheri a gare ki idan kn zauna nan zaki iya fadawa dake dasu cikin wani hali kada ki damu nasan zaki iya kawo kanki gida amna dai wanan ba matsala bane zan san yadda nayi akai kawai.
Sai kundawo kawai tace min ta mike tana murmushi tabar dakin sai na falka firgigit dani barci nayine ko may wai ?
Ina tambayan kaina don dai nasan koda barci ne ban kai minti biyar ba ma dayin shi kuma na tashi.
Kamshin da naji ya gaure dakina bawani kamshi bane sai kamshi da gidan muna kaduna yakeyi ko yaushe.
Wanda nidai nasan ban faye amfani da turare ba amma sai kaji gidan ko yaushe yana kamshin dadi idan ma mutane sun shigo sukan ce na san masu turaren da nake amfani dashi mana.
Sai dai nayi dariya kawai don dai ni nasan ban amfani da komai gaskiya.
Abinda ya fado min a raina shine maganan baba watau dai ya tabbata da jinnu nake hurda ke nan a rayuwana.
Idan ko hakane dole ne nakoma gurin mahaifina naji shawaran shi don dai abin ya fara bani tsoro wallahi ko.
Na shirya na leka dakin Umma ina cewa Umma zan dan fita yanzu zandawo insha Allahu.
Ban tsaya ba sai gidan mu na samu babana na fada mai komai yadda mukayi da bakuwana da kuma abinda naji a dakina bayan tashina.
Nan dai baba ya nisa tare dacewa maryama al, amarin naki ne sai taka tsantsan wallahi don dai abin akwai daure kai a cikin sa.
Ni yanzu bazan hanaki bin mijin ki ba don ban san matsalan da suka gani ba a hakan .
Don idan kinga haka akwai matsala kenan da suka hango suna son su warware maki shi ta cikin sauki.
Don haka ki shirya goben ku kama haya kutafi sai dai don Allah idan kin tafi banda fitana duk abinda zaice kiyi hakkuri da halinsa har Allah ya warware maki komai insha Allahu.
Nace insha Allahu baba bazanyi wani fitina ba da yardan ubangiji zaka samay ni mai biyayya tare dani.
Baba yace amma dai da ita uwar naku zakutafi ko don in kun tafi waye zai zauna da ita nan din ita kadai cikin wanan halin haka.
Nace baba da ita din zamu tafi gaba daya gara ma taje taganewa idon ta ko ta daina zargina hakana.
Yace a dai ta hakkuri da jama, a don gujewan shiga wahalansu don da zaran kinyi fushi akan mutum zai iya haifar da daukan fansa akan mutum batare da sanin ki ba.
Nace insha Allahu baba zan tsare da yardan ubangijin mu Allah.
Nai sallama da babana nakawo kudi nabashi nace ya rike a hannun shi bayan kwana biyu zanyo mashi sako.
Nafito na sallami mutanen gidan mu ina sheda masu cewa zan tafi gobe idan Allah ya kaimu.
Nakawo abinda zan basu na basu suna godiya suna saka min albarka da fatan Allah ya tsare hanya.
Tare da kanne na su biyu muka dawo gidan sune suka tayani shirya kayan mu Anty Lami ma tazo bayan na fada mata zancen tafiyan mu sai gata da saurinta tazo.
Naima kanne na da yaran uan uwana kyautan kayan tufafin mu da mukazo dasu da zuman idan mun koma zamu sai wasu acan insha Allahu.
Yayan mu yai maganan motan da zamu shiga wanda shatan shi za, a daukan muna har kaduna din.
Har Umma da yara sai dana shirya komai don da safe da mun tashi sai tafiya kawai da zamuyi.
Karfe shidda da rabi driver har ya iso kofan gidan mu yan uwa suka taru akan mu mun bar gidan hannun kanin Umma yace dan shi ne zai zauna a gida don ya fake muna.
Suna daga muna hannu muka kama hanya inaji wani iri a raina na rabuwa da dangina jini na da zanyi mu koma cikin waau nauin mutane da ba kowane zan iya tatance jinsin shi ba acan don rayuwan dana fada ciki yanzu.
Tafiya muke munyi nisa sosai da gida sai motar ta kiya muna driver yayi iya kokarin shi amma motar taki tashi.
Ganin zai bata muna lokaci ne yasa shi cewa ya kamata ya samu wata motar yai muna juye dashi mu tafi.
Ya tsare mota sun kai biyar ba wanda ya tsaya har mun debe rai ga tafiyan don rana ya somayi muna gashi ba wani nisa sosai mukayi da gida ba a lokacin.
Sai ga wani driver tafe shi kadai cikin wata lafiyayan mota dashi ya sanya kira, a yana tashi.
Driver mu na farko yai wa mutumin bayanin komai akan abinda yakeso damu driver motar yace shi har gaba ma zai tafi don jos zai tafi kwaso wasu kaya acewan shi.
Akai muna juye muka kama hanya nai mashi fatan Allah yasa motar tashi ta tashi yace amin hajiya nagode Allah ya tsare hanya yakaiku lafiya nace amin
Ragowan kudin da sabon driver mu yaiwa na farko abin akwai ban mamaki don bai karbi koda rabin kudin shi ba ma.
Nashiga da addua ta tare da yaran muka dauki hanya sai faman sannu kawai nakewa Umma dake a cikin wani yanayi najin jiki a lokacin.
Bamuyi wani nisa sosai ba kowa a motar cikin mu barci ya dauke shi sai driver motar ne kawai ke sharara gudun shi.
****** ********* ******
Ni dai a sani na koda barci nayi baifi na awa biyu ba ma kuma ga kaida sai karfe hudu zuwa biyar zamu shiga garin kaduna din .
Amma wai ina bude idona nagan mu a unguwar kawo da sauri na zabura na mike zaune da kyau har a lokacin kira, a ne ke tashi a cikin motar inda driver ke bin kira, an a hankali shima.
Cikin wani muryan mamakine nace inane nan don Allah dai malam ?
Yace kawo muke mana nace hasbunallahu wa,ni, imal wakeel.
Ban kara tsinkewa ba sai da naga driver ya sha titin da zai kaimu uguwar mu ba tare da nace mai uffan ba.
Nace a raina bari naga iya fudun wanan mutumin dai a karya.
Sai shiga kawai yake hanyoyin da zasu sada mu da gidan mu kawai ina bayan mota tare da Umma ina kallon ikon Allah.
Bakin get din shiga easthe din mu driver ya ja motan shi ya tsaya kallon mamaki nake mashi kawai ga tsoron daya kamani har a fili.
Bai min magana ba nima haka din sai cewa danayi duk da naga mutumin ustazu ne shi bai son magana da mata don bai muna magana ba tun shigowan mu motar tashi.
Nace malam kai wanene please ?
A ina ka san mune wai da har kasan inda zamu tafi ne wai nifa ban ganewa wanan tafiyan na mu ba fa ?
Kamar bai son magana cikin murya kalar ta larabawa yace ni kanin kawar ki ce itace tace na rage maku hanya ai tai min kwatancen gidan ku kuma.
Kawata wata kawata ke nan yace idan kun hadu zatai maku bayani da kan ta insha Allahu.
Nace muna da kaya sai ka karasa damu don Allah kaga kuma mamana bazats iya tafiya ba da kanta.
Yace insha Allahu kawai yaja mota sai kofan gidan mu nan ya sauke muna kayan mu yaja motar shi yabar mu nan a tsaye cikin mamakin shi.
Ina faman nanatawa a raina kawata to wata kawar nawa ke nahiyar mu kuma har tasan gidan mu haka anan.
Na dauko key din gidan dake hannuna acikin jakata don dama nasan da wuya mu samu baban Abba a gida idan mun isa.
Na bude gida nice nafara shiga ciki da sallama na wanda yarana ma sun saba shiga guri da sallama don jin ko yaushe ina yi idan zan shiga guri.
Gidan fes yake ba wani kazan ta ko ina a gyara sai walkiya yake yasha gyara sai kamshi ke tashi kawai ko ina na gidan.
A raina nace ikon Allah ashe baban Abba zai iya gyara gida haka kamar mace.
Na zaunar da Umma a saman dogon kujeran dake falon na juya na shiga shigowa da kayan mu dake kofan gidan dake bude.
Sai dana gama shigo da kayan na bude fridge na dauko ruwa na kawowa yaran da Umma suka sha.
Muna nan nace bari na zuba masu abincin dana dafa muna wanda da niyata muci a hanya Allah bai nufa muci din ba.
Muna gama cin abinci na umurci kowa yaje yai sallah don lokaci yayi na sallah azahar lokaci sai mamakin yanayin tafiyan mu kawai nakeyi a raina.
Inda nai sallah naiwa umma alwala itama tayi sallah nazauna nan barci ya dan kwashe mu lokacin.
Can cikin barci naga mukkadarasiya tana muna sannu da zuwa tare da labarta min ai kanin tane ta tura ya dauko kuma itace tasa motar ya lalace don a dauko mu batare da mun wahala ba sosai.
Tace wai ke maryama sai taushene zaki daina tsoron mu ne dakikeyi haka?
Firgigit na falka naga kowa barcin shi yakeyi banda Aisha da bata a cikin falon lokacin.
Take mafalkina ya dawo min a raina ina kallon kofan shigowa gidan yana a rufe kamar yadda yake da farko kafin na kwanta.
Nakai dubana akan kofan back yard din mu nagan shi abude da sauri na karasa kofan.
Aiko na hangota a cikin rana tayi zufa zufa da ita sai wasan ta takeyi ita kadai a cikin rana tana suraitai tana awon ruwa a wani goran room fresh tsoho.
Nace ke Aisha taso ki cire kayan jikin ki ki saka masu sauki kin hada wani uban zufa haka a cikin rana ku bakujin zafin rana ne wai ?
Jin muryana yasa yarinyar kaduwa sosai tamike dasauri a tsorace nace jiki sake kayan jikin ki hakana kada su baci.
Tace mama idan na sake nadawo nayi wasana nace ki dawo Aisha amma kuma rana yai yawa yanzu ki bari anjima ko ?
Sai bayan munyi sallah la, asarne naba Abba tsaraba yakaiwa anty Hauwa da yar sokoto sai lokacin ne suka san dawowan mu garin.
Da yamma nai muna girki har dare mukaci muka jona kallo baban Abba bai dawo gidan ba.
Ganin dare yayi yasa na